YARBI
Ɗan Hakin Da Ka Raina
"Na amince." Na furta can ƙasan maƙoshi, duk da na san wannan alƙawarin ba zan iya cika shi ba don kuwa idan aka ɗauke babbar wayata a cikin kayana na amfanin yau da kullum ba ni da wata kadarar da za ta haura dubu goma, kuma bana zaton zan iya sadaukar da wayar don ceton alƙawarina."Mene ne cikakken sunanki?" Iya abin da ya tambaya kenan yayin da ya yunƙuro da zimmar fita daga ofishin.
"Noorhan Aminu Zinyau." Na faɗa a. . .