Skip to content
Part 5 of 9 in the Series Sharri Kare Ne by Rukayya Ibrahim Lawal

YARBI

Ɗan Hakin Da Ka Raina

“Na amince.” Na furta can ƙasan maƙoshi, duk da na san wannan alƙawarin ba zan iya cika shi ba don kuwa idan aka ɗauke babbar wayata a cikin kayana na amfanin yau da kullum ba ni da wata kadarar da za ta haura dubu goma, kuma bana zaton zan iya sadaukar da wayar don ceton alƙawarina.
“Mene ne cikakken sunanki?” Iya abin da ya tambaya kenan yayin da ya yunƙuro da zimmar fita daga ofishin.

“Noorhan Aminu Zinyau.” Na faɗa a taƙaice ina bin shi da kallo.

Bai sake ce da ni kanzil ba ya fice ya bar ni zaune cikin fargaba ina tsoron ya yi mini ta baya ta rago, amma dai a yadda na fahimci yanayinsa ya riga ya tsorata da barazanar ƙanjamau da na yi masa ya janye ƙudirinsa, hakan ne ma ya ɗan sama mini ‘yar nutsuwa.

Can bayan wasu daƙiƙu masu tsayi ya turo ƙofar ofishin ya shigo hannunsa riƙe da wata farar takarda mai ɗauke da rubutu a jiki ya miƙa mini tare da komawa mazauninsa, ya janyo lokar jikin teburinsa ya ɗauko wata gajeruwar takarda tare da biro ya turo ta gabana.

“Saka hannu a nan.” Shi kaɗai ne abin da ya faɗa sannan ya zauna a kan kujerarsa yana ci gaba da yi mini Kallon ƙurilla.

Ni ma ban ce ƙala ba na ɗauki takardar tare da dubawa, ina karantata a cikin raina domin na fuskanci ko takardar meye. Takardar ba ta komai ba ce face takardar yarjejeniyar biyan bashi da take ɗauke da sunansa tare da saka hannu, sai kuma wurin da aka tanada a jikin takardar musamman don saka suna da sa hannun mai karɓar bashi.

Na ɗaga kai ina kallon yadda ya sake shan kunu. A raina na ce ‘Lallai yau na ɗebo ruwan dafa kaina. Allah ka fitar da iya a rogo.’ Ba wani jinkiri na cike komai na miƙa masa ba don ina saka ran cika alƙawarin yarjejeniyar ba, kawai dai na tari aradu ne don faɗin kai.

“Ok, za ki iya tafiya na cika nawa aiki, saura naki alƙawarin.” Na miƙe da hanzari bayan na saka takardata a jaka ko godiya ban yi masa ba na juya na fice daga ofishin cike da jinɗaɗi duk da ina cikin yanayin da bai kamata jin daɗin ya samu muhalli a zuciyata ba.

Ina ƙarasawa zauren gidanmu na jiyo tashin sautin Ummana tana faɗar “Manta da su ƙawata hassada suke yi mana ganin mun fi su nasibi a harkar…”

Jin hakan ya saka ni maƙalewa a zauren domin cika burina na jin sana’ar da suke yi.

“Ni fa ba wai ina yi ba ne don faɗakarwa kawai ina yi ne don kasuwanci, kin san a da na fara da nufin yin faɗakarwar amma ɗan abin da nake samu bai taka ƙara ya karya ba kuma bana samun masaya sosai. To yanzu na dawo daga rakiyar zancen, abin da masu bibiya suka fi so da saya shi zan yi…”

Ta ɗan dakata can ta bushe da dariya tana faɗar “Ƙawata ba ki da dama, kawai ki manta da su ai hassada ga mai rabo taki ce da sannu za ki ga yadda zamu ci gaba da tsira muna girma har mu kai matsayin da tumɓuke mu daga tushiyarmu zai yi wuya.”

Nan ma tana zuwa ta tsahirta kuma ba na iya jiyo sautin kowa sai ita kaɗai hakan ya saka na yi hasashen cewa a kan waya take zancen sanin ba wata mace a gidan face mu biyo sai dai kuma idan baƙuwa ta yi.

“To ƙawata sai an jima, idan Nooryn ta dawo zan faɗa mata saƙon gaisuwarki.” Tana kai nan a zancen da ta sake yi na ji ta yi shiru da alamar ta kammala wayar, cike da jin takaicin kuɓucewar damar jin abin da nake so a karo na biyu na yi sallama tare da shiga gidan.

Fuskarta ɗauke da murmurshi ta amsa mini tana faɗar “Sannu Noory ya jikin?”
“Da sauƙi Umma.” Na amsa mata a gajarce ina ƙarasawa daga ciki.
“Ina ita Nuriyyar ba ta rako ki gida ba?” Ta tambaya fuskarta na bayyanar da mamakin ganina ni kaɗai.
“I Umma, ai kin san gidansu a kan hanyar asibitin yake shi ya sa na ce kawai ta koma gida zan ƙaraso da kaina.”

Na ba ta amsa ina yunƙurin cire hijabin da ke jikina duk na yi gumi sharkaf a dalilin ranar da na ɗebo a waje. Ga kuma yanayin ana tsakiyar bazara ne.

“Ai shi kenan, na godewa Allah da ya dawo mini da ke lafiya. Ba ni takardar gwajin na ga.”
Da ma na hasaso hakan za ta faru. Allah ya yi mini gyaɗar dogo na samo takardar ai da ban san me zai faru ba a lokacin kuma.

A yadda na san Ummata da basira ta wannan hanyar kaɗai za ta iya tabbatar da zarginta a kaina, ga ta da bin ƙwaƙƙwafi sosai.

Da ma tun da na fara ciwon nan a cikin zarginta nake shi ya sa nake kula yayin aiwatar da duk wani motsi a cikin gidan namu, kamar dai yadda ɗan wasa yake kula da takonsa a filin wasa gudun samun matsala.
Hannu na saka a jakata zan ciro takardar gwajin sai wannan ambulan ta faɗo ban lura ba. Ina ƙoƙarin miƙa mata takardar gwajin ita kuma tana ƙoƙarin sunkuyawa don ɗaukar ambulan ɗin.

Sai a lokacin idanuna ya kai can kuma na lura da abin da yake shirin faruwa don haka cikin zafin nama na sunkuya na riga ta ɗauke ambulan ɗin a firgice.

Ta miƙe tana bi na da kallon mamaki ba ta tamka mini ba, ni ma ban ce kanzil ba na miƙa mata takardar na wuce ɗaki cikin hanzari.
Ina shiga ɗakin na kwanta ina tunanin hanyar da zan bi na ɗauki fansa a kan Amir.

Duk da na amince zan ajiye dukan wani mummunan ƙudiri da ke taskace a raina amma fa wutar ɗaukar fansar da ke cin zuciyata ba ta mutu ba sai ma zaɓalɓala da take ƙara yi a kullum kwanan duniya.

“Shin haka za ki zuba ido ga wanda ya saka ki a tashin hankali da ƙuncin rayuwa yana yawon shi a gari cike da walwala? Ba za ki ƙuntata duniyarsa kamar yadda ya yi sanadin ƙuntata taki ba?’ Wani ɓangare na zuciyata ya jero mini tambayoyin.

A hankali na furta “Duk da ni ce silar faruwar komai amma fa sai na ɗauki fansar juya mini baya da ya yi a lokacin da na fi tsananin buƙatarsa a kan koyaushe.”

Na yi wani maƙetacin murmushi “Kowa ya ci tuwo da ni miya ya sha, za ka tabbatar da cewa ka yi kashi gonar fara.”

Gama wannan zancen kedawuya na ɗaga wayata na lalibo wata lamba na danna mata kira, ƙara biyu ana uku aka ɗaga kiran.

“Assalamu alaikum Kamal barka da rana.” Ya amsa mini da Wa’alaikumus salam barka dai manya ashe talaka yana da rabon sake jin ɗuriyarku?”

Na yi ‘yar dariya ina cewa “Kamal kenan ba a raba ka da zolaya.” Nan mu ka ɗan ƙara gaisawa sa’annan na yi gyaran murya na ce da shi, “Wai ni kuwa Kamal ina mutuminka ne? Kusan wata kenan ban saka shi a ido ba.”

“Wane mutumin fa?” Ya dawo mini da tambaya cike da mamaki.

“Amir nawa mana, akwai wanda na ba ka ajiya bayan shi ne?” Na faɗa ina kalato murmushin ƙarfin hali.

“Kina nufin ba ki san ya yi tafiya ba? Kusan wata ɗaya kenan fa, meke faruwa ne?”

Murmushi mai sauti na yi kafin na ce da shi, “Haka ne na tuna ya faɗa mini. Don Allah Kamal wani taimako nake nema a wurinka.” Na ƙarashe zancen da ragaggiyar murya ina satar kallon ƙofar shigowa ɗakin nawa.

Ya amsa da to Allah Ya Sa zai iya.
Ban tsaya amsa masa da Amin ba kamar yadda ya kamata na yi bayan ya yi addu’ar, kawai sai na ce da shi, “A matsayinka na aminin Amir bayan ni ba ka san wata yarinya da take da matuƙar muhimmanci a rayuwarsa ba? Ina nufin wacce zai iya sallama farincikinsa a kan nata. Wacce zai shiga ƙunci idan ta faɗa ƙuncin rayuwa.” Na gyara zamana tare da tattare hankalina don kwashe samfuran jawaban da za su zamo amsar tambayata.

“I to, akwai wata Zakiyya ‘yar baffansa ce ba ta fi sa’ar ki ba, yana tsananin ƙaunarta. da yana da iko ko ƙuda ba zai bari ya hau kanta ba. A taƙaice dai Amir zai iya bada rayuwarsa don ceton tata a hasashena kenan.” Ya maido mini amsar da ta faranta mini rai sosai.

“Da kyau! Abin nema ya samu matar falke ta haifi jaki.” Na faɗa a hankali.

“Me kika ce?” Ya tambaya.

Cikin saurin baki na ce da shi, “Ba komai. Na ce don Allah idan ba damuwa ina son hotonta da cikakkun bayanai a kanta.”

“Shi kenan amma ban fahimci ma’anar duk wannan ba. Me za ki yi da bayananta haka?” Na mayar masa amsa da cewa “Wata bazata nake shiryawa Amir, don Allah wannan ya zama sirri a tsakaninmu ko shi bana son ya sani.”

Ya amsa mini da in sha Allah tare da alƙawarin tura mini iya waɗanda yake da su bada jimawa ba.

Sa’annan na katse wayar bayan mun yi sallama na ɗauko babbar ina na buɗe ina jiran saƙonsa, ba wani ɓata lokaci wasu daga cikin jawaban suka shigowa.

Na yi murmurshin cin nasara irin na mai gasar da ya samu nasara sannan na kira Nuriyyah. Ba ɓata lokaci ta ɗaga alamar ta huce salam daga ɗumin fushin da take.

Bayan mun gaisa na ƙara ba ta haƙuri sannan na na ɗora da faɗar “Mu haɗu a duniyar sama zan tura miki wani aiki. Ki taimaka mini ki aiwatar da gaggawa.”

Ina gama faɗa na kashe wayar don kada wani ma ya ji makircin da muke kitsawa. Na kwafe su tsaf daga wurin shi na tura mata bayanan yarinyar tare da bayanin abin da nake so a yi da su.

Gaskiya Noorhan kin iya bariki ta yadda gogaggiyar ‘yar bariki ba za ta nuna miki tuggu ba. Wai duk yaushe kika koyi wannan?_ Abin da ta rubuto mini kenan bayan ta gama karanta bayanai na. Jin motsi alamar ana nufo ɗakin ya saka na yi saurin tura wayar bayan katifa na kifa kaina a filo ina ƙoƙarin rufe idanu.

Umma ce ta leƙo ɗakin tana faɗar “Wai ni kam Noory ina Amir ne? Na jima ban saka shi a ido ba. A ce duk da ciwon da kika sha amma ba alamar zai zo dubiya? Ko dai kun yi faɗa ne?” Na sake kalato murmushin ƙarfin hali a karo na biyu ina kallon ta na ce

“Uhmm! Umma yana lafiya kuma ƙalau muke. Na manta ne ban sanar da ke ba ya yi tafiya makwanni uku da suka gabata.” Ta gyaɗa mini kai alamar gamsuwa sa’annan ta juya tana faɗar “Allah Ya dawo da shi lafiya. Yaro mai hankali ni kam na yi mamakin rashin zuwan shi, ashe da dalili.”

Bayan ficewar ta na sauke doguwar ajiyar zuciya na miƙe na ɗoro alwala duk da lokacin sallar azahar bai yi ba. Na koma ɗaki, kai tsaye na zarce ma’ajiyar littafaina na ɗauko Alqur’anina wanda rabona da karanta shi a gida har na manta. Na fara rera ƙira’a a hankali.

A take na ji wani irin sassanyan sanyi mai sanyayawa da samar da nutsuwa yana ratsa zazzafar zuciyata da ta gama gobarewa da wutar ɗaukar fansa haɗe da nadama.

Ina kammala karatun na rufe littafin na fara jan carbi ina faɗar “Rabbig-fir li wa tub alayya innaka antat-tauwabur-rahim.” Ban manta ba ya sayyadinmu ya taɓa faɗa mana cewar wannan istigfari ne da manzo (s.a.w) yake yawan yin shi a lokacin da yake zaune a majalisi. Kuma ya faɗa mana cewa istigfari yana maganin kowacce irin damuwa da take damun zuci da gangar jiki, yana yaye talauci ma sa’annan yana kusanta ka da ubangiji domin Allah subhanahu Wa ta’alah yana son masu tuba.

Kiran sallar azahar da ya ratsa masarrafar jina ne ya saka ni miƙewa na yi shimfiɗa na gabatar da ita. Da na kammala sai igiyar tunani ta yi mini dabaibayi zuwa shuɗaɗɗun watanni biyar baya.

Da misalin ƙarfe 9:30 na daren ranar wata Laraba ina kwance a kan katifa ta na saka ɓoyayyiyar wayata da Amir ya siya mini ɓoye a ƙarƙashin filona ina karatun da na saba na je ƙarshen wani littafi mai suna Duniyar Daɗi shauƙi ya gama kama ni. Wata zazzafar sha’awa ta taso mini da na rasa abin yi sai na kunna datata da nufin kafa tarko ga duk wanda ya fara shigowa gonata. Amir ne ya fara faɗawa komata don kuwa koda na hawo na riski saƙonsa da yake cewa,

“Na yi missing ɗinki da yawa Sweet, ban sani ba ko kin yi bacci ba na son na takura miki.” Damar da na samu kenan na fara aika masa da emojis na murmushi da kissing sannan na rubuta. “Na fi ka shiga kewa sosai Darling.” A take ya maido mini da emojin murmushi sannan ya rubuto “Ke dai kawai kowa na shi ya sani, amma dai na ƙagu a ɗaura mana aure na huta da azabtar da zuciyata da kike.”

Dariya na tura masa kafin na rubuta “Ni da nake jin ma kamar na haɗiye ka.” Na saka alamar jin kunya da shauƙi. Shi ma dariyar ya maido mini tare da, “Ah! Ki haɗiye nin mana ai ni naki ne. Zan ji daɗin samun haɗiya daga maƙogwaron da yafi kowanne muhimmanci a rayuwata.”

“Ina tsananin buƙatarka a kusa da ni Darling.” Na sake tura masa sa’annan na kashe datata a hanzarce. Duk da cewa a rubuce ne muke zancen amma na san ya fahimci cewa ba wasa a cikin furucina, don kuwa magana makamanciyar wannan ba ta taɓa ratsa tsakaninmu ba.

Ko mintuna biyu ba a rufa ba sai ga kiran shi ya shigo wayata. A nan muka ɗora daga inda muka tsaya, na ci gaba da hilatarsa cikin shagwaɓaɓɓiyar murya yayin da ya kasa tsallake tarkona a wannan ranar ya biye mini muka yi hirar da ta sauka a kan layi.

Wannan hirar kuma ita ce mafarin tarwatsewar rayuwata, ita ce ta buɗe ƙofar tashin hankalin da ke bibiyar rayuwata, ita ce silar fatattakar farinciki daga zuciyata ta yi wa damuwa shimfaɗa a zuciyar tawa ta samu fakewa.
Ina zuwa nan igiyar tinanina ta tsinke na rushe da kuka cikin siririn sauti “Astaqfurullah! Astaqfurullah!!” Na fdinga maimaitawa a hankali. Ganin damuwa ba za ta bar ni na ji daɗin kaɗaicin ba, na miƙe na fita waje ina taya Umma wasu aika-aikacen gida.

Bayan kwana biyu Nuriyyah ta kammala aikin da na rataya mata nauyinsa, don haka na yi sabuwar dabara na karɓi sabuwar number Amir ta waccan ƙasar da yake chat da ita na aika masa saƙo kamar haka;

“Barka da wannan lokaci kyakkyawana, fatan ba ka manta cewa akwai baikonka a kaina ba mijin mafarkina, ina ga lokaci ya yi da ya kamata ka kawo sadakina.”
Ya jima bai hawo ba, can bayan wasu awanni masu tsayi sai ga saƙon shi kamar haka.
“Lallai yarinyar nan wuyanki ya isa yanka da alama kin manta da kaifafan makaman yaƙin da na tana da. Ki sani wannan ne kashedi na ƙarshe da zan yi miki.”

Ina karantawa ina gabatar da wani shu’umin murmushi da ni kaɗai na san fassarar kayana. ‘Lallai ma wannan gayen, ya kamata na tuna masa da cewa kan mage ya waye.’

Don haka ba ɓata lokaci na rubuta masa sa kamar haka;
“Kada ka damu, ina sane da shirinka sai dai a yanzu makaman da nake riƙe da sun fi naka tasiri matuƙa.” Na saka alamar murmushi sannan na tura masa.

“Ko yaya Alhajinka zai ji idan idanuwansa suka gane masa mummunan aikin da kuke aikatawa kai da Zakiyyarka?” Na sake tura masa.

Take ya turo mini wasu emojis da suka alamta mini ya shiga ruɗani kuma yana neman ƙarin bayani. Murmushi kawai nake zabgawa ganin haƙata na gab ta cimma ruwa.

Wannan karon ban yi rubutu ba wani hoto na tura masa wanda aka sauya fuskokin wasu fajiran mutane zuwa fuskarsa da ta Zakiyya. A ƙasan hoton na rubuta “Gaskiya na ji daɗin amfani da wannan fasahar. Ina yi maka godiya da ka tuna mini da wanzuwar ta.”

Ko minti ɗaya ba a rufa ba sai ga kira da number ƙasar ƙetare. Ina sane na yi biris da shi sai da ya kira kamar sau uku ana huɗu sa’annan na ɗauka.

Koda jin yanayin muryarsa ba sai an faɗa mini cewa hankalinsa a tashe yake ba. a”Me kike so?” Ya tambaye ni da karyayyiyar murya. Ba kunya na yi ɗan guntun murmushi na ce da shi “Ka tura gidanmu a kawo sadakina nan da wata ɗaya za a ɗaura mana aure. Idan ba haka ba ba iya wancan hoton ba ina da sinƙin bidiyoyi da hotunan da za su tabbatar da laifinku. Yanzu dabara ta ragewa mai shiga rijiya idan ya ga dama ya faɗa ta kai.”

Ina gama faɗa na kashe wayar ina ƙyalƙyala dariya cike da annashuwar da ta yi hijira daga gare ni tun bayan bayyanar mummunan al’amarin da ke tare da ni. “Da ma ɗan hakin da ka raina shi ke tsokale maka ido.” Na furta a hankali, kafin na ci gaba da sabgogin gaba na zuciyata fes kamar ba wani dattin damuwa a cikinta.

Share it pls

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sharri Kare Ne 4Sharri Kare Ne 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×