Skip to content
Part 1 of 37 in the Series Shirin Allah by Maryam Ibrahim Litee

Shimfida

Abdurrashid ne tsaye a Office ɗinsa waya kare a kunnensa sai sakin tsaki yake, Usman abokinsa ko a ce amininsa ya shigo Office ɗin, sun dubi juna ya ƙaraso ciki.

“Me ya faru na ga kamar ranka a ɓace?  Usman ɗin ya ce mishi daidai yana zama, tsakin ya kuma ja “Hamida nake ta kira wayarta ta ƙi shiga, fita za mu yi da major Daniel zuwa Suleja. An cire network a inda za mu, kar ta ji ni shiru.”

Usman ya ce “Ni ma na tashi, gida zan wuce yanzu, zan leƙa in sanar mata kafin in shiga gida.”

Abdurrashid ya ce “Yawwa.” Tare suka fita sai da Usman ya ga tafiyar su kafin ya faɗa motarsa ya bar wurin zuwa gidan Abdurrashid.

*****

Hamida da ke tsaye gaban mudubi tana ƙare ma kanta kallo kwalliyar da ta ɗanɗasa tana jiran isowar ogan.

Less ne mai asalin tsada kalarsa ruwan zuma dinkin doguwar riga ta kamata ta fidda komai na halittarta, ta gyara gashinta ta yi ɗauri mai kyau, ga ƙamshi mai daɗi tana yi.

Jin knocking ya sa ta fitowa tana tunanin mai taya ta aiki ce saboda makaranta da take zuwa da ta fita ba daɗewa tunaninta ko mantuwa ta yi.

Ta buɗe ƙofar sai ganin Usman ta yi haɗe rai ta yi tana jin da ta san shi ne da ba ta buɗe ba, za ta mayar da ƙofar ta rufe ya danno dole ta yi baya “Saƙo ne daga mijinki, za ki hana ni in shigo.”

Ta ƙara ɓata rai ganin shu’umin kallon da yake jifanta da shi, ta ja tsaki “Ka faɗi saƙon ka wuce.”

Ƙamshin da take yi da wanda falon ke yi ya shaƙa sai ya lumshe ido kafin ya buɗe su tar bisa ƙirjinta idanuwansa har sun canja kala don wata fitina da yake ji.

“Ƙamshi kike, falonki ƙamshi yake, ki taimake ni in raɓi wannan ƙamshin naki, ko ba zan same ki ta aure ba don giftawar Abdurrashid ki bar ni in mayar da kwaɗayina na wutar sha’awarki da ke ruruwa a raina ki bani dama in nuna miki irin son da nake miki. Mijinki ya tafi Suleja ya nemi wayarki bai samu ba ki bani dama. Ja da baya Hamida ta soma ganin yana nuho ta ga wani uban tsoro da ya rufe ta ganin daga ita sai shi ta shige daki ta datse ta faɗa gado tana kukan wannan wace irin masifa ce, sai da ta ji tashin motarsa ta miƙe ta leƙa ta window.

Kasa fitowa ta yi  tana zaune a ɗakin har  sai da Abdurrashid ya dawo,  yamma sosai ya dawo. Ganin  ƙofar a buɗe kuma ba ta fito tarar shi  ba ya ba shi mamaki sai da ya shigo ciki ta fito ganin ta duk a wani firgice ya ƙara ba shi mamaki “Me ya same ki?  Ya tambaye ta yana  harɗe hannayensa a ƙirji ganin yadda ya tsare gida ta ƙaraso ta sanya kanta gefen kafaɗarsa don iya tsawon nata kenan “Mene ne na ce?  Ya kuma maimaita tambayarta “Ji na yi kamar ana motsi a gidan.”

Tsaki ya ja jin me ta ce hannunta ya kama zuwa ɗakinsa bakin gado ta zauna tana bin shi da kallo  sai da ya gama duk abin da zai yi suka fito zuwa dinning ya yi nisa da cin abinci ya dube ta ganin ba ta da niyyar ci ya cigaba da tsare ta da ido duk da ta gane  me yake nufi ba ta cin ba har ya ƙare ya ce “Kin ci ne?  Ta ɗaga mishi kai alhali ba abin da ta ci ita ba ta san yadda za ta yi da wannan masifa ba.

Asalin Labarin

Lokaci ne na hunturu hazo duk ya rufe sama buji haɗi da iska ke kaɗa jama’a.

A cikin garin Daura, a unguwar Tawalala gidan Mal Muntari, Dattijuwa Innawuro ce tsugune a filin tsakar gidan, gabanta turmi ne sai ƙwarya da take ƙara lailaye furar da ta cura. Riga da zane ne a jikinta na atamfa, sai ɗayan zanen da ta naɗe shi a kanta.

Akwai giccin ɗaiɗaikun matan gidan a wurin, wasu na girki wasu kuma suna aikin ta su furar, walau ta sayarwa ko ta sha a gida, don gida ne da ya yi suna kasantuwarsa gidan yawa jama’a suna masa lakabi da gidan Fulani don asalin su mutanen Adamawa ne.  Har gida ake shigowa sayen furarsu.

Sunan Hamida dattijuwar ta shiga kira, yar yarinya da shekarunta ba za su haura sha uku ba ta fito daga wani ɗaki da ke can yamma da gidan ɗauke da madaidaicin farin bokitin roba, ta karaso tana fadin “Ga ni Innawuro.”  Mita dattijuwar ta shiga yi “Kika shige ɗaki sai mutum ya rasa me kike?”

Murmushi yarinyar ta saki, cikin shagwaɓa take cewa “Shiryawa fa nake Innawuro.” Ba tare da ta kuma magana ba Innawuro ta miƙe ta nufi rumfarta inda yarinyar ta fito, tukwanen ƙasa ne shanye a wurin, zama ta yi ta fara shafe su da farar ƙasa, tana hangen yarinyar tana harhaɗa kayan da ta yi amfani da su, sai da ta maida komai a mazaunin sa sai ta ɗauki ɗan bokitin da ta fito da shi wanda ta zuba kawunan furar da Innawuro ta cura.

“Assalamu alaikum.” Wata murya ta kwararo daga ƙofar shigowa gidan, Hamida ta ta da kanta tana duban inda ake sallamar, doguwar mace ce ingarma, wadda ke tsaye ba alamar ranƙwafawa, kyakkyawar bafulatana irin su maza ke wa kirari da mace mai fasali ko ta yi aure ba mu dangana ba. Sanye take cikin wani tsadadden less lullubin gyale ta yi tana rataye da jaka ƙamshin turarenta ya cika wurin kana ganin ta ka san kanta a waye yake. Hamida ta ƙarasa wurin ta da sauri tana mata sannu da zuwa, yara biyu ke biye da ita suna rike da kaya ta rungumo kafadar Hamida suka shiga dakin Innawuro. Abin ka da gidan yawa kafin ka ce me kowa ya ji Gwoggo ta Kano ta zo, sai shigowa ake ana gaishe ta tana ta rabon tsarabar da ta yo musu. Hamida da ta gama gaishe ta sai ta mike don tafiya aiken da za ta zuwan Gwoggon tasu ya dakatar da ita.

Kafadarta ta dafa “Za ki bi ni diyata mu yi tafiyar mu birni ko?  Wani iri Hamida ta ji ba ta yi magana ba sai ta yi murmushi ta fice har ta dauki bokitin ta bar gidan maganar na yawo a ranta sanin yayar mahaifin nata da ba ta taba haihuwa ba yaran yan’uwanta take dauka ta tafi da su Kano suna taya ta sana’arta ta sayar da abinci. Ni karatu zan samu Malam ya bar ni, ba za ni Kano sayar da abinci ba. Ta fadi a ranta daidai ta kawo gidan da za ta kai aiken, wanda tsakanin su gida hudu ne.

Gini ne na zamani, ta shiga da sallama a kofar daki ta ga maigidan yana tsaye, ya yin da matar gidan ke zaune saman wata farar kujera, matar ta fara gaishe wa wadda tana ganin Hamida ta kunbura kamar an sa mata yeast, mijin shi fara’a ya  fara “Amaryata ke ce tafe?  Hamida ta wuce dakin mahaifiyarsa da sauri ta gaishe ta ta mika mata hurar, ta juyo ta baro gidan tana jinsa a bayan ta duk kuma kiran da yake mata bata waiwayo ba har ta shige gida.

Ba ta yarda ta shiga wurin Innawuro ba sasan su ta mike da mahaifiyarta ta fara cin karo tana zaune a tsakar dakinta tana bai wa karamin danta magani. Kallo daya ta yi wa Hamida ta mayar da kanta ga abin da take, kusa da mahaifinta ta zauna wanda ke zaune yana cin abinci, kannenta su biyu maza su na zaune su ma su na cin abincin  ta yi wa babanta sannu da zuwa ya ce ta je ta zubo kai ta girgiza ta ce ta ci abinci.  Kannenta suna gamawa rige rige suke su taho wurin ta, sai dai ita tashi ta yi ta soma gyara wurin da suka bata, ta hada kwanonin za ta wanke babanta ya ce ta bar su akwai sanyi.

Ta dan jima tare da su,  ta mike ta koma sasan Innawuro ba ta samu Gwoggon su ba wanda ta yi murna da hakan don gudun da take kar ta kuma yi mata zancen bin ta Kano, sai dai ta tambayi Innawuro ina Gwoggo Indo?  Ta ce tana dakin Malam.

Malam Abdurrashidu wanda kowa ke  kira da Malam Audu  ya dubi kanwarsa bayan ta gama ba shi labarin makasudin zuwan ta,  ta zo ne a ba ta Hamida ta tafi da ita birnin Kano. Duk da ba ya son daukar yayan yan’uwansa da Tilon kanwar tasa wadda Allah bai ba haihuwa ba take yi, don shi da daya Allah ya bar masa mai suna Aliyu, Ga ta ita kadai ce mace a cikin, su maza shida da iyayen su su ka haifa,  ba zai iya duban ta ya ce mata A’a ba, sai dai yana tuna yadda za a raba Innawuro da Hamida, Hamida ta daban ce a wurin ta, amma ba shi da karfin halin furta hakan.  Ya ce Mata “Yaushe ne tafiyar?  Ta ce sai jibi,  don akwai bikin diyar kawarta da za ta halarta. Ya ce” Allah ya kaimu. Ta mike tana godiya ta bar shi cikin mutuwar jiki yadda zai soma labarta ma Innawuro.

Gwoggo Indo na komawa ta samu Hamida ta fito wanka tana murza mai, daga ita sai zane ta yi daurin kirji. Gwoggon ta shiga kare mata kallo tana sake sake a ranta. “Shekarun ki nawa yanzu Hamida?  Hamida ta dago ido ta dube ta “Sha uku ne Gwoggo.” Ta gyada kai  Wannan nan da shekaru hudu zuwa biyar da za a yi maganar auren ta ba karamar mace za a gani ba. Gwoggo Indo ke fadi a ranta.  Doguwa ce mai murjajjen jiki, ga ta fara kamar sauran yaran gidan nasu, sai dai ba ta da dogon gashi irin nasu sai dai na tan ma yana da cika har gaban goshinta ya kwanta lambam wanda ya kara kayata yar kib kib din fuskarta ga idanuwanta dara dara sun kara fidda kyanta. Yadda jikinta yake lukwi lukwi za ka za ci yar gidan wani hsmshakin ce, don ta fi kama da yayan hutu.

Ajiyar zuciya ta fidda tuna abin duniyar da za ta samu wurin mazan da za su mutu kan son yarinya.  Ta mike  ta dubi Innawuro da ke damun hura, “Bari in je gidan bikin nan Innawuro.” Ta ce “Haba dai, ba ki bari ki sha hura ga ta ina da ma miki.” Ta dubi tarin kwanonin da aka tara mata daga sasan yan’uwanta ta ce “Cikina ba wuri Innawuro, kun cika shi taf, bari in je.” Suka yi mata fatan dawowa lafiya ta fice.

Sai da aka yi sallar Isha’i Hamida ta koma sasan iyayenta ta yi hira da babanta da kannenta, mahaifiyarta saboda kunyar yar fari ba ta shiga sabgarta. Sai da ta ga mahaifiyarta ta fara yi ma kannenta shimfida sai ta yi musu sai da safe ta baro sashen.  Har kuma lokacin Malam Audu bai iya sanar ma kowa  bukatar da kanwarsa ta zo masa ba, yana dakinsa yana juyayi, ya yin da Innawuro ke nata dakin tare da Alh mustafa dan kawarta wanda Hamida ta kai hura gidansa dazu.

Takalmin da ta gani kofar dakin yasa ta gane ko waye, ta shiga da sallama shi ya amsa da fara’ar da bai iya hana kansa ita matukar zai ga yarinyar, sanin idan ba ta gaishe shi ba za ta sha fada wurin Innawuro ya sa ta gaishe shi, sai ta tsallake can karshen gado mai rumfa ta yi kwanciyarta bayan ta lalubo littafin hausa da ta samo aro. Tana karatunta suna hirar su har ya tashi tafiya sai da Innawuro ta gama kirga kudaden cinikin tukwanen kasarta da  aka kawo mata,da kudin hurar da Mustafa ya kawo mata sai ta hau gadon da Hamida take “Me yasa idan Alh Mustafa ya gan ki ya yi miki magana ba ki yi masa?  Kara lafewa ta yi kamar tana barci  “Ina sane sarai ba barci kike ba.” Turo baki ta yi kamar tana kallon ta  “Ni to me zan ce mishi?  Duk inda ya gan ni sai ya yi ta takura mini.”  Ba takura ba ce kauna ce, mai son ka ai ya fi wanda bai son ka.” “Kauna kuma Innawuro?  “, E kauna Hamida, don yau dai ya zo mini da zancen yana rukon ki, har sanda za a yi maganar auren ki, ya ce in gaya wa Malam. Kin ga ke ba za a dade ba aure zai dauke mini ke. Hawaye Hamida ta shiga yi “Ni Innawuro na fada miki ban son aure karatu nake so, ki roki Malam ya bar ni in ci gaba da karatu ga su Habiba (kawarta) har za su je js2. Innawuro  ta lalubo wayarta ta kunna torch din wayar haske ya wadaci wurin har tana ganin yadda hawaye ke sauka bisa kuncin Hamida. Janyo ta ta yi ta shiga rarrashin ta kamar yadda ta saba, don ba ranar da za ta fito ta fadi ba ta yi mata kukan son ta ci gaba da karatu ba, don yarinya ce mai kulafucin karatu sai dai rashin sa’ar da ta yi kakanta Mal Muntari tun yana raye bai yarda da karatun yaya mata ba, iyakar su primary school bayan mutuwarsa kuma Mal Audu babban dansa ya dora kan wannan akida ta mahaifin na su, don da yarinya ta kare karatun primary za ta ci gaba da zuwa Islamiya har Allah ya kawo mata miji ta yi aure, to ita ma dai bara ta kammala karatun primary school ta bi sahun yan’uwanta da suka rayu a gidan ba ta zuwa ko’ina daga Islamiya sai taya Innawuro da Innarta aiki, sai karance karancen littattafan hausa saboda son karatunta duk inda ta gani sai ta aro ta zo ta karanta.

Lallashi sosai ta yi mata amma yin shirun Hamida ya gagara don gani take kamar auren za a yi mata, don Mustafa tun tana karama kwarai lokacin ko aure bai ba yake mata wasa duk inda ya gan ta sai ya rika kiran ta  matarsa.

Da kyar ta hakura ta yi barci.

Da safe da wuri ta fita ta tashi ta je sasan su ta taya Innarta aiki. Maimakon ta dawo wurin Innawuro wani sasan daban a cikin gidan ta mike, an gyara shi ya fita na zamani sabanin sauran sasan gidan ginin kasa ne. A kofar farko da ta shiga wanda shirin da aka yi masa zai fahimtar da kai kitchen ne, wata mace ta samu zaune ta ta sa gas a gaba da tukunya a kai, kallo daya ta yi wa Hamida ta maida idonta kan tukunyar. Hamida ta gaishe ta ta amsa a dakile “Ya Aliyu ya tashi?  Hamida ta tambaye ta, ba ta yi magana ba sai kai da ta daga, ta wuce ta ta murda handle din kofar da ke kallon ta ta yaye labulai ta shiga da sallama, tsararren falo ne ta hango shi kan dinning yana break past ya amsa sallamarta ya yafuto ta da hannu ganin tana niyyar zama kan kujerun da suka yi wa falon kawanya. Kamar wadda kwai ya fashe mawa ta karasa inda yake, ya turo mata kujera ta zauna a sanyaye turo mata kwanonin da ke gabansa ya yi amma ta gaza taba komai, shi ma tsayawa ya yi ya dogare hannayensa a habarsa ya zura mata ido “Mene ne damuwar? Wa ya taba mini yar kanwata Innawuro ce ko Malam ko yaya Fatima?  (Innarta)  girgiza kai ta yi sai ga hawaye nan take ya ci serious yana tambayar abin da aka yi mata cikin kuka ta soma gaya masa damuwar ta yadda take son karatu da kuma wannan Mustafan da ya da me ta. Rarrashin ta ya yi ya ce zai je ya samu Malam ya kara rokon shi ya bar ta ta je makaranta, maganar Mustafa kuma wasa ake mata.

Da haka ya samu ta yi shiru. Matarsa Uwani ta shigo dauke da wani bowl ta dire shi gaban mijinta, dan tsakalar abin da ke ciki ya yi sai ya mike umarni ya ba Hamida ta kwashe kwanonin ta je ta karya. Yana  tsaye ta hada komai tare suka fita yana cewa Uwani sai ya dawo. ta raka su da harara kamar idonta zai fado don wani malolon bakin ciki da ta ji ya tokare ta, tana bala’in kishin shakuwar da ke tsakanin yarinyar da mijinta, duk da bakin da jama’arta ke ba ta na kar ta wani damu Aliyu shi kadai ya tashi dakin mahaifiyarsa shi da mahaifiyar Hamida,  daga bisani bayan ta yi aure aka kawo musu yayen Hamida, da shi a ka yi renon ta har ta isa yaye aka kawo musu yayen ta, kallon kanwa yake mata duk da in ya koma ta wurin mahaifiyar ta diya ce a wurin sa. Amma zuciyarta me kishin ta ki yarda da hakan gani take kamar wata rana zancen zai sauya.

Aliyu na gaba Hamida na bin shi a baya da tire niki niki. Dakin mahaifinsa ya shiga ita kuma ta shige na Innawuro, tana sauke tiren Innawuro ta bi ta da kallo don ta gano daga inda kwanonin suka fito “Ga shi Innawuro ya Aliyu ya ce in taho da su.” Kai ta gyada mata “To kwashe ki je ku ci da kannen ki.” Ai sun tafi makaranta Innawuro, Ke ba za ki ci ba?  Ta girgiza kai tana ci gaba da muttsuka kwanan nan hurarta, ta gama ta kafa kai sai da ta shanye ta mike don soma ayyukanta, yau dai ba za ta yi hura ba, don tana da costomomi masu saye kowa kuma da ranar da take yi masa. Tashi Hamida ta yi ta dauko flacks da kayan shayi ta san Innawuro ta cika mata shi da ruwan zafi me dauke da Lipton da kayan kamshi, ya Aliyu ke sawo musu kayan shayi daga Malam har Innawuro babu mai sha. Karinta ta yi mai kyau wanda ya rage kuma ta adana ma kannenta, za ta fita ta wanke kwanonin Aliyu ya shigo, suna gaisawa da mahaifiyar sa ta wuce ta yi wanke wanken. Ta dawo daga kai ma Uwani kwanoninta Aliyu ya fito Innawuro na biye da shi tana yi masa addu’a ita ma Allah ya bada sa’a ta ce ta san ko za ta ji yadda suka yi da Malam sai ya dawo.

Gado ta haye don ba aikin da za ta yi wa Innawuro Innawuro kuma ta wuce dakin Malam, ganin sa zaune cikin damuwa wadda ta lura tun jiya ya rage walwala yasa ta tambayar sa lafiya?  Barin kashi a ciki ba ya maganin yunwa, don haka ta maza ya yi ya gaya mata.

Dauriya mai yawa wannan baiwar Allah ta sanya don hana bayyanar wannan tashin hankalin da ta shiga jin wannan zance me kama da saukar kirsimati,  a fuska, amma hatta jikinta rawa yake, addu’a ta yi sai dai duk yadda ta so basarwa su ci gaba da hirar su kamar yadda suka saba hakan gagara ya yi ta mike don barin dakin ya ce ta turo mishi Hamida

Yana soma gaya mata ta matse kanta a cinyoyinta tana hawaye, da ya sallame ta dakin Innawuro ta koma tana mata kuka da magiya ita ba za ta Kano ba ta koma saida abinci,  ita karatu take so.  

Shirin Allah 2 >>

2 thoughts on “Shirin Allah 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×