Kwanan su uku da dawowa suka yi wani baƙo da daddare Malam Buhari ba ya nan ya je Daura.
Har falo Gwoggo ta ce ya shigo sun gama maganarsu ya tashi ya tafi washegari kuma Aina ta yi shiri cikin matuƙar kwalliya ta ce Hamida ta zo ta raka ta kasantuwar ba Islamiya ta shirya ita ta riƙe mata madaidaiciyar jakar da ta sanya kayanta, suka yi wa Gwoggo sallama suka fito gidan.
Shatar a daidaita sahu ta ɗauka wani wurin daukar hoto a Goron dutse suka je, hotuna kala-kala a ka yi wa Aina sai na karshe ta ce Hamida ta shigo.
Yana ƙare Edition mai hoton ya tura mata a wayarta da ta mika wa Hamida wayar sai kallon hotunan take don hakika sun yi matukar kyau.
Suka fito bayan ta biya suka dawo gida.
Kwana biyu tsakani mutumin da ya zo wurin Gwoggo ya dawo suna gaisawa ta ce “Ya ya Haji Ilyasu an dace? Ya yi dariya ya yin da yake kora lemon da Aina ta ajiye mishi “Ƙwarai kuwa Hajjaju, ai ‘yar taki ce ba daga baya ba.
Mutum biyu suka taya, Alh Abbas banki sai Brigadier Bala Kafur, Gwoggo Indo ta zaro ido “Da gaske ko da wasa Haj Ilyasu? Ya ce “Wallahi Hajjaju, Alh Abbas banki yana so amma a huta yake so don akwai naira, ko ni tukwici na mai gwaɓi ne idan na kawo ta, ba ma ita ba ita kam ta haye don yana ba mata kudi kamar bai san zafin su ba.”
Gwoggo ta ce “Ina ji cigaba.”
Ya ce “Sai Brigadier shi da aure yake so don matarsa ta rasu ta bar mishi yara hudu duka maza, yaran ma duka suna waje suna karatu, sai dai shi ma ko bunsuru haka ya gan shi Hajjaju.
Ya miƙa mata wayarsa don ta gan su a hoto. Ya ce “To ya ya Hajjaju? Ta ce “Ai kai ma ka san wanda zai yi aure zan zaɓa neman mata kuma yanzu Allah na tuba ai sai wanda Allah ya tsare.
Ta kwala wa Aina kira ta fito sai ta miƙa mata wayar da yi mata bayani.
Ya miƙa wa Aina katin Brigadier “Na ba shi lambarki zai kira ki anjima.” Aina ta gyada kai Gwoggo ta ce “Amma ka gaya mishi ba maso auren ya ja lokaci ko? Ya kama baki “Kin ga yadda ya rikice a kanta? Ai ina ganin ko cikin satin nan a ka ce zai amince.” Gwoggo Indo ta gyara zama “Alhamdulillahi na ji daɗi sosai Haji Ilyasu zan maka transfer cikon kudinka.” ya yi dariya “Girmanki ne Hajjaju, gobe zai iso daga Abuja don asalinsa mutumin Kano ne dan ganawa da Haj Aina a gidan gonarsa, sai dai ga shawara Hajjaju ki gargaɗe ta kar ta kuskura ta bari ya yaudare ta ta bada kanta, auren nan zai yi wuya a yi shi.
Gwoggo Indo ta ce “Kar ka ji komai ba abin da zai faru Aina ta iya takunta.”
Sun ƙara tattaunawa ya tashi ya tafi.
Ranar sun yi kwanan farin ciki Gwoggo da Aina
Washegari ya zo suka gana da Aina kuɗaɗe masu nauyi ya jiƙa ta da su waɗanda ya nemi ta ba shi acc no ya yi mata transfer Gwoggo dai har rawa ta taka Aina ta samu miji kuma na kere ma sa’a.
Abdurrashid ke kai da kawo a Office dinsa cikin matuƙar damuwa da tunani, yana cikin Sojojin da aka tura America yin wani course na shekaru huɗu. Ba don komai tafiyar ke ɗaga mishi hankali ba tunda ya samu labarinta sai don Hamida ya za a yi ya tafi ya bar ta da Gwoggo Indo? Wane hali zai dawo ya same ta? Ya daki tebur ba zai yuwu ya tafi ya bar Hamida wurin Gwoggonta ba, to ya zai yi? Duk iya tunaninsa kansa ya ƙulle ya rasa samun mafita. Jin da ya yi kansa na daukar zafi ya sa ya tattara ya na shi ya na shi ya bar Office din.
Gida ya wuce kai tsaye bai tsaya neman Auntynsa ba ya shige wurinsa ya kwanta. Sai da ta ji shirun ya yi yawa don ta ga motar da ya fita cikinta ta leƙa shi ganin yana barci ta koma ba ta san rufe ido kawai ya yi zuwanta uku ana hudun ta same shi zaune tambayar lafiya yake ta yi ya ce E ta ce to ya fito su ci abinci ya ce ba ya jin yunwa, sai ta yi turus! ƙoƙarin jin damuwarsa ta yi amma ya dage ba komai.
Kwana biyu suka dauka tana fama da shi ga mahaifinsa ba ya gari sai ta kira mahaifiyarta a waya ta gaya mata a ranar ta zo daga Yola.
Abdurrashid ba shi da labarin zuwanta sai da ya dawo daga Office.
Zaune take a falon Auntynsa bayan carpet din da ke malale an shimfida mata darduma, ga cima kala kala nan an jera gabanta.
Da sauri ya ƙaraso yana fara’ar da ba wanda zai ce ya iya ta, ya zauna gabanta ya shiga latsa ƙafarta “Daada kin sha tafiya, ga ƙafa kina fama da ita.” Ita ma fara’ar ce kwance kan fuskarta na ganin jikan nata mafi soyuwa a gare ta, wanda ya fito daga babbar ɗiyarta ta mutu kuma ta bar mata shi.
“Tafiya ma a jirgi Abdul, ai ba wata wuya.” ta tura mishi flate “Zuba abinci ka ci Abdul.” ganin bai ɗauka ba ta shiga zuba mishi ya ce “Da kin bar shi Daada zan zuba da kaina. Ba ta yarda ba cigaba ta yi ta gama ta tura mishi ta tsiyaya mishi lemo “Ka dawo wurin aiki Abdul, maza ka ci.”
Murmushi ya yi yadda take mayar da shi kamar Wani ƙaramin yaro “Ban yi wanka ba Daada, na canza kayan jikina.”
“Ka yi wankan daga baya, yanzu dai ka ci abincin.” ya fara cin bai fasa murmushi ba sosai yake cikin farin ciki da ƙaunar da yan’uwan mahaifiyarsa da kakarsa ke gwada mishi.
Sai da ta ga ya kusa cinyewa ta ce “Mamanka ta tado ni, wai kwana biyu kana cikin damuwa ta rasa yadda za ta yi da kai don ka ƙi gaya mata.
Kai ya jinjina sai ya ture flate din “Daada kenan, ita fa Auntyn na gaya mata ba komai.” hannu ta dora bisa goshinta sai ta kama kuka sambatun maganar da take yi ya daga hankalinsa “Allah ga ɗan maraya nan, kai ka san damuwarsa ka shiga lamarinsa ka yaye masa ba… “Yi hakuri Daada, ki yi shiru zan gaya miki. Sai ya miƙa mata hankacif dinsa ta goge fuska sai da ta natsa ya ce “Wata yarinya Allah ya sa min son ta Daada, ƙarama ce ƙwarai don ko shekaru sha biyar ba ta haɗa ba, kuma Course din da na ba ki labari an tura ni abin da ke ɗaga mini hankali idan na tafi na mariƙiyar yarinyar wadda take hannunta tana da son abin duniya, ina tsoron abin da zai faru.
Ya ƙarashe yana kallon idonta.
Ajiyar zuciya tsohuwar ta fidda “Wannan ai mai sauki ne Abdul, a ɗaura muku aure kawai Abdul kafin ka tafi a kawo ta nan wurin uwar taka har ka dawo.” kai ya girgiza “Aure kuma Daada? Ina faɗa miki ko sha biyar ba ta haɗa ba.” sai me don ba ta yi sha biyar ba? Mu nan da ka gan mu sha biyu aka yi mini aure kuma ba abin da ya same mu.” ya kuma girgiza kai “Wannan zamanin ku ne Daada yanzu lokaci ya canza. Ni dai ina ganin zan nemi su maida ta wurin iyayen ta har in dawo.” ta ce “Su iyayen ka san waɗanne iri ne? Sai ma an yi bincike kan iyayen a ina suke? Ya ce “Suna Daura amma asalin su mutanen Adamawa ne. Sai kuma ta washe baki “Ka ce tushen mu daya, ita yarinyar a ina take? Ya ce “Cikin Estate din nan suke zaune da mariƙanta, in kika gan ta Daada tana da nutsuwa da tarbiya da alama iyayenta ma mutanen kirki ne.” “Za ka kai ni in ga kishiyar Abdul kafin in tafi.
Daidai nan Aunty Karima ta fito kusa da mahaifiyarta ta zauna Abdurrashid ya ce “Barka da gida Aunty.” ta amsa tana mishi sannu da dawowa ya juya gun tsohuwar “Zan ma kawo miki ita Daada.”
Aunty Karima ta tambayi abin da suke tattaunawa Daada ta yi mata bayani shi kam mikewa ya yi ya shiga ciki wanka ya yi ya shirya cikin ƙananan kaya da suka yi matukar amsarsa ya fito cikin ƙamshi.
Daada da Aunty Karima suna nan zaune inda ya bar su ya ce musu zai fita Daada ta ce “Wurin Kishiyar tawa za ka? To ina gaishe ta.” murmushi ya yi bai yi magana ba sai Aunty Karima da ya ce wa “Zan fita Aunty. Ta ce “Sai ka dawo Abdul.”
Ya fita ya fada motarsa bai burki ko’ina ba sai gidan Gwoggo da ya kira ta a waya ya ce yana waje cewa ta yi ya shigo, da ma za ta kira shi tana son magana da shi.
Ya fita cikin motar ya shiga cikin gidan tana zaune falonta ta amsa sallamarsa ya shiga sai da ya zauna ya gaishe ta ta kwala ma Aina kira wadanda suka shiga ciki ita da Hamida jin zuwansa ta ce ta kawo mishi lemo da ruwa ta wuce kitchen don kawowa Gwoggo Indo ta dubi Abdurrashid “Da ma ina neman ka.”
(Don yanzu ta ji rokon Hamida ta bar ce mishi Yallabai) “Babban yayanmu a gida wanda shi ne yake kamar mahaifinmu ni da iyayen su Hamida ya kira ni ya yi mini magana kan aurenta. Ya yi saurin dago ido ya dube ta sai kuma ya mai da kai ya sunkuyar “Akwai yar’uwarta a gida za a yi aurenta da kuma Aina, watan sallah suka sa, da ma tun kafin dawowar Hamida nan akwai wanda yake ruƙonta to yanzu ya shigo gida yayanmu ya ce zai bayar da ita gare shi. Wata zufa Abdurrashid ya ji tana tsattsafo masa, ta cigaba “Shi ne na roƙi yayan namu kan akwai mai son Hamida a Kano ita ma tana son sa ya yi haƙuri ya bar maganar wancan da ba ma son sa take ba.”
Jin ta yi shiru ya ce “Zan je gida zan sanar da iyayena, yadda muka yi zan dawo in faɗa miki.” ta ce “To.” ya ce “Ta shirya mu je ta gaishe da kakata.” nan ma to ɗin Gwoggo ta kuma cewa.
Yana fita ta ƙwala kiran sunan Hamida suka fito tare da Aina ta ce “Ki yi wanka da shiri mai kyau ya ce za ku je ki gaishe da kakarsa.”
Da wadda Hamida za ta iya yi wa musu ce da ta ce ba za ta ba, amma kan ba yadda za ta yi ta juya zuwa ciki don yin shirin.
Aina ta haɗa mata ruwan wanka ta sanya mata turaruka a ciki da ta fito kuma ta taya ta shiri simple make-up ta yi ta sanya riga da zane babban mayafi ta rufe jikinta duk da ba mai kauri ba ne ta zura takalmi sai ta fito, Gwoggo Indo ta yi murmushi “Ma sha Allah kin yi kyau yammatana, Allah ya cika min burina in ga auren ki da Abdurrashid ki shiga gidan Shehu Bello.” ita dai fita ta yi tana fadin “Sai na dawo Gwoggo.”
Kallo daya ya yi mata duk da kyan da ta yi masa sai ya kawar da fuskarsa ta zagaya ta shiga, sai da ta rufe ƙofar ta ce “Ina wuni? A ƙasan maƙoshi ya amsa ya tashi motarsuka bar wurin.
A kusa da sasan Auntynsa ya farker motar ya buɗe sai ya fita ba ta yi gigin ko taɓa ƙofar ba sai da ya ce “Ke ba za ki fito ba? Ta bude sai ta fita lokacin ya fara tafiya sai ta bi shi a baya, sannu cikin nutsuwa take takawa har ya yi nisa ya waiwayo ya gan ta can baya ya jira ta ta ƙaraso “Ke ba ki iya sauri ne? Ya ce mata cikin ɗaure fuska ba ta yi magana ba ta sunkuyar da kai.
Wata ƙofa ta glass ya murɗa wadda na ciki ke ganin na waje amma na waje ba ya iya ganin na ciki, don haka su Aunty Karima da Daada da ke zaune a falon suna kallonsu ya fara shiga ta bi bayansa bakinta dauke da sallama daga Daada har Karima fara’a ce ta suɓuce a saman fuskarsu ganin zaɓin Abdurrashid. Aunty Karima ta miƙe ta taro Hamida ta kamo ta har inda take zaune Hamida ta sauka saman kujerar ta zauna ƙasa inda Daada ke zaune ta gaishe ta ta kama hannun Hamida ta sanya cikin nata “Na yaba Allah ya miki albarka yarinya.” ita dai kanta na sunkuye ta ɗago kadan ta gaishe da Aunty Karima, kafin ka ce me an cika gaban Hamida da kayan taran baƙo amma ta kasa taɓa komai Aunty Karima ta ce ta ci mana nan ɗin gidan su ne. Amma Daada ta ce ta bar ta fillancin kenan.
Ta zauna tsawon awa guda Abdurrashid ya shigo dan dama ko da ya kawo ta bai zauna ba fita ya yi “Oya tashi mu je.” ya fadi ba tare da ya dube ta ba.
Ta mike ta yi musu bankwana Aunty Karima ta shiga ciki ta fito da ƙatuwar leda ta ba Abdurrashid ta ce ya riƙe ma Hamida ya karɓa suka fita.
Wannan karon ita ke gaba yana biye da ita yana biye wa tafiyarta, sun zo wurin motar wata mota ta iso har ta gifta su ta yi ribas ta dawo aka sauke glass wadda ke zaune a owners coner ta bayyana kallo ɗaya Hamida ta yi mata ta gane Hajiyar da suka zo da Gwoggo ta sayi maganin mata ce.
Abdurrashid ya matsa inda take “Ba dai surukar tawa ka kawo ba ka kai min ita ba.” ta fadi tana murmushi, ganin bai yi magana ba yana shafa ƙeya ya sa ta ce “To shi kenan, ku ƙarasa mu gaisa.”
Ya ce “To Mami.
Da ɗan tazara tsakanin sasan haka suka bi bayan motar tata san da suka shiga har ta zauna cikin nutsuwa Hamida ta gaishe ta ta amsa sai ƙare mata kallo take tana son tuna inda ta taɓa ganin yarinyar ido ta rage “Kamar yarinyar Haj Indo ko da kuka taba zuwa tare ko? Hamida ta ɗaga mata kai.
ya miƙe “Bari in kai ta gida Mami.” ta ce “Ba laifi.” ita ma ciki ta shiga rafa na dubu guda ta ba Abdurrashid ta ce ya riƙe wa Hamida ta ƙara da cewa “Ka san daddynka na hanya ko? Ya ce “”E mun yi waya ba jimawa zan yi ba.
Yana ajiye ta kayan da Aunty Karima ta bata ya sanya kudin wurin Haj Mariya a cikin ledar ya mika mata ta ce ta gode ta shige ciki ya juya da motar.