A inda ya bar su Aunty Karima nan ya dawo ya tarar da su ita da Daada.
Daada ta ce "Tubarkalla Abdul ka iya zaɓe yarinya mai nutsuwa da hankali, da ganin ta iyayenta mutanen arziki ne ga ta kyakkyawa." Aunty Karima ta dauka "Yarinyar fa kyakkyawa sai dai wannan yarinya sharaf Abdul ba ta yi maka ƙuruciya ba?
Daada ta karɓe "Ba wani ƙuruciya za ta tashi a irin tarbiyar da yake so, duk abin da ya ɗora ta a kai za ta tashi.
Aunty Karima ta kaɗa kai "Har na ji ta bani tausayi yarinya. . .