Skip to content
Part 11 of 37 in the Series Shirin Allah by Maryam Ibrahim Litee

A inda ya bar su Aunty Karima nan ya dawo ya tarar da su ita da Daada.

Daada ta ce “Tubarkalla Abdul ka iya zaɓe yarinya mai nutsuwa da hankali, da ganin ta iyayenta mutanen arziki ne ga ta kyakkyawa.” Aunty Karima ta dauka “Yarinyar fa kyakkyawa sai dai wannan yarinya sharaf Abdul ba ta yi maka ƙuruciya ba?

Daada ta karɓe “Ba wani ƙuruciya za ta tashi a irin tarbiyar da yake so, duk abin da ya ɗora ta a kai za ta tashi.

Aunty Karima ta kaɗa kai “Har na ji ta bani tausayi yarinya ƙarama yadda za ta iya da miskilancin Abdul. Dubi yanzu yadda ya yi mata kafin su shigo da gani ma tsoron shi take.” Daada ta murmusa irin murmushin su na manya “Mace ce fa, maganin miskilancin na shi za ta yi komai ƙanƙantarta, don kar ma ki zo kina ƙorafi ɗanki kaza kaza.”

Aunty Karima ta yi yar dariya “Ka ji Daada wannan yar yarinya har wata dabara za ta iya? Kai Daada ta gyaɗa “Ai shi kenan Allah ya ba mu yawan rai.” Abdurrashid dai na jin su bai tanka ba sai Aunty Karima da ya duba “Daddy kuwa ya shigo? Ta ɗaga mishi kai “Kana fita yana ta tambayarka ma. Miƙewa ya yi sai ya fice sasan mahaifin nasa ya isa Mami ya samu don ita ke da girki ta ce mishi ya shiga wanka zama ya yi har ya fito cikin jallabiya mai guntun hannu ta yi masa tayin hawa tebur bayan sun gaisa da dansa ya ce “Bari tukun in gaido Daada. Ya fice ta bi shi da kallo Abdurrashid ma zama ya yi yana latsa wayarsa don jiran daddyn nasa.

Gaisawa suka yi da surukar tasa ya ce “Ai ina hanya Karima ke sanar mini zuwan naku.”
Ta ce “E mai gidan ne ya ɗago ni, ashe kishiya yake son yi mini.”

Alhajin edai bai gane ba ta ƙara mishi bayani inda ta ba shi labari tun daga wayar da Karima ta yi mata har zuwan Hamida yanzu.

Fuskarsa ta washe da fara’a “Na ji dadi sosai don bani da buri irin in ga auren Abdul, ni da Allah bai bani yayan ba na riƙe na shi, za mu yi magana da shi inda iyayen yarinyar suke, sai a yi maganar auren kafin ya tafi, ya dawo sai a yi biki.

Sun gama tattauna maganar ya koma sasansa.
Mami da ta tare shi ta ga fara’ar da ya shigo da ita ta ce “Ya dai? Ya amsa mata da “Abin farin ciki ne ya same mu.” ita ma ta ɓalle da fara’ar “Danki ne ya samo mata. Ta ce “Ai kuwa ɗazu ya zo da ita ta gaishe mu.”

Suka isa dinning ya yafito Abdurrashid ya tashi ya isa ya ja kujera sai ya zauna, uban na cin abinci yana kallonsa ya san nufin sa Abdurrashid din ya zuba ya ci ya ce “Daada ta sanya ni na ci abinci sosai. Ya ce “To shi kenan a ina ka samo mata? Mami da ke tahowa ta karɓe “Ai Abdul da dai zai canza, duk yammatan da ke garin nan yayan manya da ma Nigeriar gabadaya ya rasa wadda zai ɗauko mana sai yar masu saida abinci? Uban ya dube ta babu wani alamar firgici ko bacin rai a fuskarsa a hankali ya ce “Yar wane gidan ce? Ta ce “Cikin Estate din nan take, wani ƙaramin ma’aikaci ne Babanta. Uwarta ce mai sayar da abinci a Estate din nan. Saboda Allah ai ba girman mu ba ne.”

Bai ce mata komai ba sai duban Abdurrashid da ya yi “Haka ne? Abdurrashid ya gyaɗa mishi kai “Sai dai Daddy ruƙonta ake anan din iyayenta na Daura, asalinsu kuma mutanen Adamawa ne.
Kai ya gyaɗa “Daada ta faɗa mini komai, zan je da kaina in ga iyayen nata. Abdurrashid ya yi yar fara’a “Na gode Daddy.” ya miƙe ta falon Daddyn nasa akwai hanya da za ka bi ta kai ka har bedroom dinsa ta can ya bi.

Mami ta shiga tunani mijin nata babu abin da yake musa mata idan ta faɗi, buƙatar Abdurrashid ita ce kawai sama da ta ta a wurinsa.

Shi din ma Daddyn duk da ganin gaskiyarta kan abin da ta fadi hakanan yake jin wani abu na jan shi kan wadda Abdurrashid din ya kawo.

Hamida na shiga falon Gwoggo ta tare ta da murna ta karɓi ledar ta zazzage less ne mai asalin tsada sai atamfa super wax sai turaruka Designers. Ta riƙa juya kudin “Kin ga halin girma, shi kenan kin samu na sallah.

Mai neman Aina ya je Daura bayan dawowarsa ya tura magabatansa an tsayar da magana za a yi biki rana daya da Amina don haka Gwoggo da Aina shiri suke ta yi.

Gwoggo ta je Daura ta yi ma Malam bayanin wanda ke son Hamida iyayensa za su zo bayan sallah ya ce Allah ya kaimu.

Gwoggo dai ta yi sa’a wannan karon Abdurrashid ya yi mata abin da ya kamata don boot ya ciko da kayan abinci ana gobe azumi har da su irish da kwai da kayan Tea.

Mami dai ba ta hakura ba yayar Engineer da ita kadai ta rage masa da suka fito ciki daya ta je ta gaya ma wadda Abdurrashid ya kawo kuma Engineer ya goya mishi baya, takanas ta taso ta samu Engineer ta nuna mishi rashin dacewar wannan aure da zai biye wa Abdurrashid a yi, hakuri kawai ya ba ta ya ce ba zai tilasta Abdurrashid ba abar shi ya auri wadda zuciyarsa ke so.

Da ta tashi wurin Aunty Karima ta wuce ta ce “Da hankalinki Karima Abdurrashid zai rasa matar da zai aura sai yar tuwo -tuwo yar masu saida abinci, har Mariya ta fi ki son Abdul.”

Ita ma hakuri ta ba ta ta ce suna son farin cikin Abdul.

Cikin fushi ta tashi ta tafi.

Ana saura sati daya sallah Abdurrashid ya zo da daddare wurin Hamida sai da ta zauna motar ta gaishe shi ya amsa yana tambayar ta Exam da suke yi da ma ta san zai tambaya don haka ta fito da papers din sai ta mika masa sai da ya gama gani tare da gamsuwa da abin da ya gani sai ya fita ya ciro wata kyakkyawar jaka ya bata ya ce dinkin sallah ne in ji Aunty Karima ta yi godiya bai jima ba ya wuce.

Ranar sallah dukkan musulmi yana tashi cikin farin ciki haka ta kasance a gidan Gwoggo Indo sun yi abincinsu kala biyu na sallah sun yi cincin sun soya nama. Masu aikin Gwoggo duk sun tafi gida sallah, Hamida ta je sallar idi tare da yaran maƙociyarsu Nurse Saratu.

Washegarin sallah Aina za ta karɓi baƙuncin mai girma Brigadier Bala Kafur sai shiri suke ita da Gwoggo Abdurrashid dai ba wanda ya ga yar ƙafarsa ya dai kira waya ya yi wa Gwoggo barka da shan ruwa. Aina ta ce tare da Hamida za ta sun gama shiri sai ga Walida dole Aina ta tafi a motar da ya turo a ɗauke ta Hamida ta zauna wurin baƙuwarta, Laila ma ranar ta zo, wuni zungur Walida ta yi ma Hamida sai magrib ta koma gida Aina ma sannan ta dawo suka baje ana duba katinan auren da ya bata, sai nairori da ya cika mata account da su na hidimarta da kawayenta, da yake ita ba ma mai yawan kawaye ba ce, kasafinsu kawai suka kama ita da Gwoggo.
Sun shirya ana saura sati guda bikin za su wuce lokacin Gwoggo ta kammala da kayan dakin Aina an kai.

Aina ta dubi inda Hamida ke zaune tana duba katinan “A cikin kudin nan zan yi wa Hamida sayayyar kayan da za ta sanya da biki.” Gwoggon ma Hamidar ta duba “Wace sayayya kuma za ki yi wa Hamida duk kayan da surukarta ta aiko mata? Ai sun ishe ta cin biki.”

Ganin kamar Ainar ba ta gamsu ba ya sa ta ce “Ba fa ƙaramin gida za ki shiga ba Aina, dole kayan daki na masu abin za a yi miki.” Aina ta daga kai.

Gwoggon ta ƙara kallon Hamida “Abdurrashid bai zo ba, ba zuwa ba aike.” ita dai shiru ta yi Gwoggo ta yi yar mitarta ta hakura.

Sai washegari da yamma Hamida na yi musu tuwo a kitchen dinsu na falo, dukkan su marmarin tuwon suke Gwoggo da Hamida don sun rabu da cin shi ya kira Gwoggo a waya lokacin tana bayan dakunan su tana tsefe kanta ta ce ya shigo ta mike ta daure kanta ta shiga ciki don shaida wa Hamida zuwan nasa shi kuma ya shigo ya yi kyau ƙwarai cikin wata farar shadda da aka yi masa karamar riga mai guntun hannu yau har da hula da ta zauna a kansa ta ƙara mishi kyau.

Tana mishi maraba ta shiga falon yana bayanta sai da ya zauna ta shiga kitchen din ta shaida wa Hamida Allah ya sa ba ta daɗe da yin wanka ba don ba ta yi wanka da wuri ba shadda ce jikinta dinkin doguwar riga ta karbe ta ba kadan ba.

Ta samu tana kwashe tuwon a leda ta karba ta ce ta je wurinsa sai da ta debi naman da suka soya da cincin sai ta dauki lemo ta fita a gabansa ta ajiye sai ta samu kujera can nesa da shi ta zauna tana gaishe shi, Gwoggo ta fito bayan ta kammala kwashe tuwon, nan Abdurrashid ke shaida mata babansa ya ce zai je Daura nema mishi aure ranar daurin auren Aina don ya gano abokinsa Aina za ta aura wanda ya kasance shi ne uban gidan Abdurrashid a aikin Soja. Gwoggo ta cika da farin ciki ta shiga daki ta debo katin bikin sun yi goma ta kawo mishi, suna magana sama sama Hamida ta yi amfani da damar ta koma kitchen kuɓewar da za ta kaɗa ta dauko ta dawo ta zauna tana yankawa, idon Abdurrashid na kan TV har ta gama miyar ta zubo ta kawo mishi ta dai zubo mishi amma ba ta sa ran zai ci ba ita tunaninta bai ma ba ta yana cin tuwo ba ta ji ya ce mata ina Spoon ta mike ta je ta kawo mishi ya ci sosai har ta ji mamakinsa daga inda take zaune ta ji muryar Gwoggo tana kiran sunanta ta mike tana amsawa waya ta ba ta Aliyu ne ke neman Hamida ta karba cikin jin dadi ta dawo falon tana amsa kiran cikin shagwaba tun da ta zo bai taɓa zuwa ya gan ta ba, shi kuma ya shiga rarrashin ta, sun daɗe kafin suka yi sallama Abdurrashid da ke kallon ta ta wutsiyar ido ya juyo gaba daya bai taɓa gani tana farin ciki irin na yau ba, wani kishi ya mintsini zuciyarsa sanin da namiji take wayar fuskarsa ya ɗaure dan dauriya mai yawa ya sa wurin danne zuciyarsa har ta ƙare wayar “Da wa kike waya? Ya tambaye ta cikin daka tsawa! Raurau ta yi sai ta sunkuyar da kai don ta matukar tsorata na ce “Da wa kika yi waya? Ya kuma maimaitawa gane ba za ta yi magana ba ya ja mummunan tsaki sai ya mike ya bar falon, ta ci gaba da zama shiru tana tumanin inda ta kuskuro shi.

Ko da Gwoggo ta shigo ba ta gaya mata komai ba har sai da aka kwana uku Gwoggo ta ji shiru bai kira waya ba sai take tambayar Hamidar ta faɗa mata duk yadda suka yi, ba ta yi ƙasa a gwiwa ba ta kira shi a waya tana tambayar abin da Hamida ta yi mishi ya ce tsakanin mu ne Gwoggo. Ta ce “To to a dai yi hakuri.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Shirin Allah 10Shirin Allah 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.