Skip to content
Part 12 of 37 in the Series Shirin Allah by Maryam Ibrahim Litee

An je Abuja an shirya wa Aina wuri, daga Daura mutum biyu suka zo sai nan mutanen arzikin Gwoggo su ma su biyu sai Laila cikon ta biyar.
Ba su samu tafiya Daura ana saura sati daya ba sai ana saura kwana huɗu, har sai da Gwoggo Indo ta yi taron bikinta anan duk da da yawa za su bi ta har Daura, Walida ma ta ce za ta je tare da itan suka tafi da Laila da wasu aminan Gwoggo.

Sun shiga Daura yamma liƙis, shigar su gidan gida ya ruɗe sai maraba ake musu, wasu na rafka guɗa na isowar Amarya, dakin da Gwoggo Indo ke sauka idan ta zo nan suka sauka.

Hamida dai dakin Innawuro ta ruga don ta rasa wa tafi kewa tsakanin iyayenta da kannenta da Innawuro, kan ƙafafuwan Innawuro ta zube ita kuma ta shiga shafa bayanta murna suke sosai na ganin juna, har sai da Innawuro ta ce ta je Innarta ta gan ta.

A gindin murhu ta samu uwar, duk da daɗin da ta ji na ganin Hamida ga girman da ta ga ta yi ta ƙara kyau da gogewa irin ta mutanen birni kallo daya ta yi mata sai ta ci gaba da hura wutar Hamida ta yi dan sansarai kafin ta furta cikin sanyin jiki “Umma.” ta ɗago sai ta miƙe ta shiga daki, a cikin ta amsa gaisuwar Hamida har tana tambayar ta suna lafiya? Ba su jima ba ƙannenta suka dawo makaranta anan Hamida ta samu kyakkyawar tarba.

Har mahaifinta ya dawo sai murnar ganin babbar ɗiyar ta su yake.

Sai da ta ci tuwon dare ta koma wurin Innawuro, Innawuron ta ce Gadanga na ta neman ki, ko ya leƙa ki can? Ta girgiza kai “Bari in je in gan shi.”
Abinci ta samu yana ci, ya ce “Ai bari na yi in kammala sai in isko ki wurin Umman.” ta yi murmushi tana daukar yaron Aliyun da bai wuce wata uku da haihuwa ba, kuma sai sannan Asabe ta yi haihuwar fari.

ya nuna mata wuri ya ce ta zauna ta zauna da yaron a hannunta “Yaya ka manta da ni.”
Shi ma ya murmusa “Wane ni in manta da yar ƙanwata.”

Daidai nan Asabe ta fito daga ɗaki, ganin Hamida ya sa gabanta faɗuwa tare da ɗan tsawaya turus! sai da mijin ya ce “Ke kuma fa da kika ja kika tsaya? Saurin wayancewa ta yi ta ƙaraso, Hamida ta juyo cikin fara’a ta ce “Ina wuni Aunty? Ta amsa da lafiya a daƙile.

Hamida ba ta da mu ba don ta riga da ta saba, wurin Yayanta ta juya wanda idan ta koma fannin Innarta kawunta ne don ƙane yake wurin Innarta, amma shi fannin Malam yake tsayawa bai komawa fannin Innawuro kanwa yake da ita.

Hirar su suka cigaba da yi ba tare da sun lura da halin da Asaben take ciki ba, don hankalinta ya yi ƙololuwar tashi da ganin yadda Hamida ta zama budurwa, ga kyau ta ƙara na maƙerin yammata da ya fara ƙera ta.

Gabadaya ta zama yar gayu, ita kam hankalinta ba zai taɓa kwanciya ba idan ba gani ta yi an aurar da Hamida ba.

Sallamar da ake daga ƙofa ya sa Hamida miƙewa don ta shaida muryar Gwoggo Indo, Aliyu ma ya mike ya ce “Gwoggo da kanki? Ta miƙo wa Hamida waya “Kiran Hamida ake.” suka ƙara gaisawa da Aliyu sai ta juya.

Kamar jira wayar ta shiga kuka, kan dole Hamida ta amsa kiran gaban Yayanta, Abdurrashid ne wanda rabon ta da shi tun zuwan da ya yi ya ta tafi da fushi.

Gaishe shi ta yi ya ce “Me ya sa ta tafi ba ta kira shi ta gaya mishi ba? Shiru ta yi sanin hali ya sa ya katse kiran kawai.

Ta sauke wayar ta yi ta dubi Aliyu da ke duban ta sai ta wayance da miƙewa “Yaya bari in mayar wa Gwoggo wayarta, daga nan in kwanta.” ya ce “To ki huta gajiya ƙanwata.” Ta dubi inda Asabe ke zaune tana danna wayarta ta cika ta yi dam! Ta ce “Sai da safe Aunty.” ciki ciki ta amsa da “Allah ya ba mu alheri.” ta fice sai dakin da Gwoggo Indo take da mutanenta ta mika mata wayar sai ta juya, Gwoggon ta biyo bayanta sai da suka kai harabar gidan suka tsaya “Kin ga Allah ya rufa mana asiri Abdurrashid ya kira, duk hidimar nan da nake tunanina na gare shi.”

Hamida dai ta ce Hmm. “Ina kuma ƙawar ta ki? Ta tambayi Hamida “Wai Walida? Ta bi yammatan amarya.” Gwoggo ta tafa hannu “Wannan ‘ya da saurin sabo take, yanzu har ta saba da ƙawayen Aminar? Hamida ta girgiza kai “Ba su ta bi ba, su Aunty Aina ta bi.” ta ce “To shi kenan.” ta ce “Bari in je in kwanta Gwoggo.” ta ce “Allah ya tashe mu lafiya.”

Zaune ta samu Malam da shi da Innawuro ta ƙara gaishe shi sai ta wuce ciki don ta yi shirin bacci, Innawuro ta biyo bayanta wata yar madaidaiciyar cooler ta nuna mata “Nama ne aka kawo mana daga wurin ɗan’uwanki ɗauki ki ci.” ta buɗe farfesu ne na naman ciki yanka biyu ta ci ta ta dubi Innawuro da ke tsaye har lokacin “Zan karya da shi da safe.” Innawuro ta ce “Allah ya kaimu.” ta cire kayan jikinta ta sauya da doguwar riga mara nauyi sai ta kwanta.

Ta fara barci sama sama ta ji shigowar Innawuro ta gama kaye kayenta ta hau gadon ta kwanta Hamida na bayanta.

Da safe ko da ta tashi ta yi sallah komawa ta yi ta kwanta sai takwas ta tashi, gyaran wuri ta taya Innawuro sai ta fita don gaida mutanen gidan.

Ta sha mamakin sasan su Laila, an buge ginin ƙasa an mayar da shi bulo da bulo, ta samu Amir ya tashi bacci, Laila ta miƙo mata shi anan sasan ta samu ruwan zafi ta yi masa wanka, sai da ta gama shirya shi ta tafi da shi sasan su, ba ta yi mamakin daga wayewar gari har Innarta ta gyara wurin kamar ba mai yara ba.

Ta tambayi ƙannenta ta ce sun wuce Islamiya, Babanta yana zaune yana shan koko da ƙosai, kwanon ya turo mata bayan ta gaishe shi “Maza ki sha.” Shan ta yi tana ba Amir suna hirar su, har sai da babanta ya fita kasuwa sai ta bar sashen.
Wanka ta koma wurin Innawuro ta yi ta so zuwa inda su Amina ke zaman sitting daga ita ce kusan sa’ar ta, to amma saboda Walida dole ta nufi inda su Aina suke.

Daga can suka wuce wurin su Amina, a can suka wuni.

An fara shagalin biki sosai ana gobe durin aure da safe misalin ƙarfe goma Hamida ta shiga wurin Aliyu don tun ran da ta zo ba ta ƙara shiga ba suna tare da Walida da ta saba da kowa ana ta hidima da ita.

Sun shiga zai fita ya ce “To mu je.” ya wuce suka bi shi a baya har waje inda Walida ke raɗa mata “Wannan hand some din fa waye? Murmushi ta yi tana duban sa tuna uban kishin Asabe a kansa, amma ba ta ga laifinta ba don ya Aliyun ne ya haɗe kyakkyawan bafulatani ne ga jiki ya ajiye na shaidar hutu da yake ciki.

Za ta yi magana ya juyo sai ta yi shiru, sun isa inda ya ajiye motarsa bai shiga ba jingina ya yi jikinta yana tambayar Hamida har da ita za a Abujar? Ta ce “Ka ji ya Aliyu, in ban je gidan Aunty Aina ba wa zai je? Ya ce “Haka ne.”

“Aunty Asabe fa za ta? Ya girgiza kai “Ba inda za ta.” Wata haɗaɗɗiyar mota da ta tsaya Hamida da Walida suka bi da kallo, ta daɗe tsaye ba wanda ya fito har suka cigaba da hirar su, Hamida ta shagala tana dariya har gyalenta da ta rufe kanta saboda ba ta sa dankwali ba yana zamewa ta kamo shi sai ta ga an buɗe motar, ganin wanda ya fito ya sa ta gintse dariyarta. Cikin mamaki suka dubi juna ita da Walida Abdurrashid ne, tana jin kunyar Aliyu ba za ta iya ce mishi wurin ta Abdurrashid ya zo ba, sai Walida da da ma ke neman shiga wurin Aliyu ta ce “Ya Aliyu ga fa saurayin Hamida ya zo.” Ɗan murmushi ya yi “Kauce Hamida.” ta matsa daga jikin kofar1)j motar ya bude ya faɗa ciki yana faɗin “Ki gaida surukin nawa.”

Hannun juna suka kama zuwa inda Abdurrashid yake da sallama suka karasa gabansa bai amsa ba illa saman lebensa da yake cijewa. Suka haɗa baki wurin gaishe shi Hamida ta ce “Ka zo mu shiga ciki.” Ya girgiza kai “Waye wanda kuke tare? “Yayana ne.” “Yayanki? Ya tambaya cikin ɗaure fuska “Yaya Aliyu ne, Baban shi Yayan babana ne, maman shi kuma ƙanwar kakata ce.” Hamida ta yi mishi wannan bayanin don kare kanta daga fushin da ta ga Abdurrashid ya shiga.

Ba ta san ambaton sunan Aliyu ƙara tunzura shi ya yi ba don ba zai manta wanda ta ambata a wayar da ta yi ba tana farin ciki, yau kuma ya gan su tare “Ok yi min iso wurin Malam.” Ta juya Walida ta bi bgidan a ta ssmu Malam din na haramar fita, Innawuro ta gaya mawa ita kuma ta gaya wa Malam ɗin ya ce Walida ta koma ta yo mishi jagora.

Walidar ta juya cikin mugun saƙe saƙe tunda ta zo ta ga gidan su Hamida ta ji ta ƙara raina masu kuma ɗan Shehu Bello ne ke son yar cikin gidan, wani ƙyashi ta ji tana wa Hamida tare da addu’ar watsewar abin.

Ta samu Abdurrashid ta faɗa mishi saƙon ya bi ta a baya suka shiga gidan
har ɗakin Malam.

Sosai Malam ya yi masa kwarjini don cikar kamalar da yake da ita ya gaida Malam cikin girmamawa da nuna surukuta ya kuma gabatar da kanshi a mai son Hamida.

Malam ya ji dadi sosai, ya ce Idan Allah ya kaimu gobe mahaifinsa zai zo nema masa auren ta. Sun daɗe suna hira a cikin hirar Malam yake ba shi labarin mahaifin Hamida ƙane ne a wurinsa, mahaifiyarta kuma mahaifiyarta yaya ce wurin mai ɗakinsa mai ɗakinsa ta dauko mahaifiyar Hamida tun tana ƙarama ta riƙe ta, da ta girma suka aurar da ita ga ƙanensa suka haifi Hamida da ƙannenta.

Natsuwar da Abdurrashid ya samu da Malam ya sa shi ma ya ba shi labarin Course din da zai tafi, da kuma rashin son da yake ya bar Hamida a Kano, ya roƙi Malam da ya dawo da Hamida gida sai a nema mata wata makarantar anan, kafin ya dawo.”

Malam dai jinjinawa ya yi ya ce shekaru huɗu nan gaba Hamida ta ƙara su ba a kauda ita ba? Ya ce shi dai a taimaka mishi duk da hankalin shi ba kwance yake ba da barin ta a Daura idan ya tuna zai bar Hamida da dan’uwan nan nata.

Malam saboda yadda ya ji yaron ya kwanta mishi ya ce zai duba. Abdurrashid ya yi ta godiya. Innawuro ta shigo suka gaisa, ta ajiye mishi fura da ta dama mishi, bayan ta fita kuma ta sa aka kira mata Asabe ta ce ta yi abinci mai kyau suna da baƙo sai dai zuwa sha biyu ya yi musu sallama bayan Gwoggo Indo da ta ji labarin zuwan shi wurin Walida ta zo sun gaisa, sai dai bai yarda ya tafi ba ya ce a kai shi ya gaishe da mahaifiyar Hamida, Walida Innawuro ta aika ta gaya mata mai son Hamida zai shigo ya gaishe ta.

Walidar ta raka shi ya dubi sasan nasu na ƙasa ne da aka kewaye da kwano, ƙasan wurin a share yake tas, sai gefe guda randunan ruwa, da sallama suka shiga dakin kujera ƙwaya ɗaya ce rak sai tabarma da aka shimfida ɗakin sai ƙamshin turaren tsinke da aka kunna, akan tabarmar ya zauna daga uwar ɗakanta ta ɗan leƙo ta sha lulluɓi ban da aiken daga Innawuro yake da ba abin da zai sa ta yarda a turo mata mai son Hamida ya gaishe ta ta amsa ya ajiye kuɗi masu kauri a saman tabarmar suka fito haka Malam da Innawuro ma ajiye musu, a mazan gidan Baban Laila ne kadai bai fita ba, don akwai aikin da ba a ƙarasa ba a sashin nasu wanda Laila ce ta sa a ka gyara part din iyayen nata.
Ya gaishe shi shi ma ya yi mishi alheri.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Shirin Allah 11Shirin Allah 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.