Ƙarfe sha ɗaya na safe aka wuce da Aina zuwa gidan mijinta da ke Abuja.
Bayan wucewar su kuma su Malam suka zauna shawara kan yadda za a yi da Hamida, Gwoggo Indo ta ce a ba ta ita na sati biyu ta tafi da ita Kano ta gyara ta, sai ta dawo da ita Daura inda yan’uwan Abdurrashid za su zo bikon ta.
Malam ya ce sati biyu ya yi yawa, kwata kwata saura wata guda tafiyar mijinta.
Ta ce to kwana goma
ya ce ba laifi. Don haka ana tashi taron Gwoggo ta soma harhaɗa nasu ya nasu zuwa Azahar suka bar garin don shatar mota ta dauka.
Suna isa ko gama hutawa ba su yi ba Gwoggo Indo ta fara haɗa abubuwan da Hamida ta ga tana ba Aina kuma ta san tana sai da su “Ai yanzu dole in miki shirin da duk san da ya san ki zai kiyaye, daga nan mu za mu fara juya shi, wannan biyayyar da kika ga ina mishi shi zai dawo yana min.
Kunya ce ta lulluɓe Hamida jin zancen ta ko da take da shekaru sha biyar sarai ta fahimci inda zancen Gwoggo ya dosa don ba abin da ba ta sani ba a karance karancen da take ko da ta miƙo mata cup ƙin karba ta yi sai da Gwoggon ta yi da gaske ta sha kaɗan dole aka sa a fridge sai fada Gwoggo take ta ce ke da alama wannan shegen rashin son maganin naki ba za a yi abin arziƙi da ke ba. Tana cikin faɗan Nurse Saratu ta shigo ta tambayi abin da ya faru Gwoggo ta gaya mata abin da Hamida take na ƙin shan maganin gyara, ta ce sam ba ta kyauta ba ta dubi Hamida “Tashi mu je gidana ni in ba ki, Haj Indo ɗauko maganin.” Gwoggo ta ɗauko ta ba ta Hamida har da ƙwalla.
Kafin zuwan Hamida ba wata hulɗa tsakanin Gwoggo da Nurse Saratu illa ta idan an haɗu a yi ina kwana ina gajiya, amma tun zuwan Hamida take son ta bunu-bunu ta sayi abu ta aiko ta ce a ba Hamida hakan ya janyo shiri sosai tsakanin ta da Gwoggon.
Tana gaba Hamida na bayanta har suka shiga gidan, an yi sa’a yaranta ba su nan suna gidan kakannin su tun sallah sai hutu ya ƙare za su dawo.
Ajiye cup din ta yi ta shiga kitchen ɗinta sai ga ta ɗauke da wani cup din ta miƙa wa Hamida “Sha wannan.” Hamida ta mika hannu ta karɓa don girman matar da take gani ta kai bakinta, nan da nan ta shanye saboda maganin ba ɗaci ba komai sai lemon tsami da aka saka wanda ta ji ya yi mata daɗi.
“Maganin sanyi ne Hamida.” Ta faɗi tana ƙoƙarin zama “Shi ya kamata mu maida hankalin ba yaranmu ya yin da muka zo aurar da su. Ba mu yi ta ɗura musu magungunan ƙara ni’ima ba, ba yanzu suke da buƙatar maganin ƙara ni’ima ba sai sun haihu tukuna, idan za mu aurar da ƴaƴanmu ba mu bar su sun je ma mazajen su da ainahin ni’imar da Allah ya yi musu ba mun ƙara musu da wani daɗi na musamman wanda idan ya sake su zai yi wahala su gamsar da mazajen su da ainahin ni’imar su.
Ki yi ta zuwa Hamida ina ba ki magungunan sanyi kin ji? Hamida ta ɗaga mata kai.
Tashi ta yi ta koma kitchen din ta fito da wani haɗin maganin ta ba hamida shi kam babu daɗi amma da yake ta iya dabara da madara ta haɗa tana sha ta ba ta madara ta ce sai kuma gobe. Da haka Hamida ta tashi ta tafi gida, Gwoggo ta yi ma Saratu waya ta ce ta sha ta ce tas ma kuwa, ta ce to ita za ta dinga aiko mawa tana ba ta.
Ranar da suka yi kwana biyu da dawowa hankalin Gwoggo ya soma tashi tana ta magana Abdurrashid ba kira ba zuwa tunda aka ɗaura aure, wane irin abu ne haka? Hamida dai da ta fito wanka tana kwalliya tana jin ta ƙaramar riga ta sanya don uban zafin da ake zambaɗawa baƙa da dogon skirt komai ba ta sanya a kanta ba ta fito falo ta kwanta bisa dogon cushion da wani littafi da ta samo a gidan Saratu mai suna RANAR NAKA na marubuciya Maryam Ibrahim litee hakika ya yi mata daɗi.
A daidai wannan lokaci da Gwoggo ke sababinta Abdurrashid bai daɗe da isowa daga birnin Ikko ba ya samu ƙannen mahaifiyarsa su uku sun iso kowacce daga inda take aure bisa jagorancin mahaifiyarsu Daada don taran ɗan nasu su yi masa murnar aure.
Haj Binta da suke kira Momi Binta ita ke bi wa mahaifiyarsa a Abuja take aure wani ƙusan gwamnati take aure ita ma kuma babba ce a Jami’ar Abuja da ke gwagwalada, yaranta hudu duka mata.
Sai mai bi mata Aunty Safiya ita kuma sarkin Katsina na lokacin take aure yaranta biyar mata uku maza biyu.
Sai Aunty Zainab a Yola take kusa da mahaifiyarsu ita ma dai mijinta hamshaƙin ɗan kasuwa ne yaranta uku biyu mata sune manya sai karamin namiji.
Aunty Karima ce autar su da Allah bai ba haihuwa ba.
Wanka kawai ya yi ya fito wurin su yana ƙoƙarin gaishe su Daada ta ce “Ya na ga kana wani ɗaure ɗaure miskili ka fi mahaukaci ban haushi. Har ranar auren naka ma ba za ka yi fara’a ba? Ƙara shan mur ya yi ya zauna yana gaida iyayen nasa Daada ta ce “Ka ji yadda mahaifin naka ya yanke ko? Za a kawo maka amaryar taka bayan sati biyu da ɗaura aure, za a ajiye ta a sasanka ya ce yanzu zai fara maka ginin gidanka wannan filin na jikin gidan nan. Jin ya ƙi magana har ta yi shiru sai ta ce “Wai meye damuwar ne? Kai fa ka kawo yarinyar nan, an kuma ɗaura maka aure da ita ka kasa farin ciki.” ya ce “Ko da na kawo ta ni na ce a ɗaura min aure yanzu? Just 15 years ne fa da yarinyar Aunty.” Ya ƙare maganar yana duban Aunty Safiya wadda duk a cikin su ta fi tsananin kamanni da mahaifiyarsa don haka sai ya yi ta ganin ta kamar mahaifiyar tasa, ko gidajen su kafin ya je na kowa ya je na ta.
“Haƙuri za ka yi ɗa na daga ka ga yadda abin ya zo.” Ta ce mishi cikin sigar rarrashi.
Amma Daada ɗaga kai ta yi “To sai me, ko shekarunta sha biyu ba ta isa aure ba? “To idan kun ɗauko ta ku kawo ta part ɗin Aunty Karima.” ya ce ma Daada.
“Nakan dai za mu kawo ta sai in ga tsiya.” Miƙewa ya yi ya ce musu zai je ya dawo, Momi Binta da ta kafe shi da ido cikin medicated glass dinta, ta dubi Aunty Zainab “Part din nasa za mu kai ta Zainab mu ga idan zai koro ta.”
Dariya sauran suka yi “Daada ta ce “Za ta yi maganinsa ne, ba dai mace take ba yake raina ta?
Fitar Abdurrashid gidan Gwoggo Indo ya nufa, yau bai tsaya kiran waya ba kai tsaye ya shiga gidan da sallama.
Gwoggon ce ta amsa sallamar don daga ita sai Hamida ne a gidan suna zaune a falo Hamida na kwance tana karatunta, Gwoggo na gyara ƙumbarta.
Gwoggo ta yi mishi iznin shigowa ya shiga Hamida dai ko motsi ba ta yi ba har ya zauna ya gaida Gwoggo, sannan ta ce “Ina wuni? Ya share ta kamar bai ji ba, Gwoggo ta miƙe ta yi waje Hamida ta tashi, zaune amma ta gaza ɗaga idonta don kunyar shi da take ji wai
shi ɗin yanzu mijinta ne.
A hankali ta miƙe zuwa kitchen ta ɗauko ruwa ya bi ta da kallo wai wannan yar yarinyar ce matarsa, ta kawo ruwan ta koma ta zauna ya shiga tambayar ta game da karatunta za a koma meye da meye take buƙata? Ta faɗa mishi, kiran da Gwoggo ta ƙwala mata ya sa ta ficewa daga falon ta isa tana fadin “Ga ni Gwogg.”
“Ki yi mishi maganar kuɗaɗen gyaran amarya da na ƙawaye, kina dai ganin kudin da a ka ba Aina.
Ta ɗaga mata kai ta ce shi kenan ta je Hamida ta koma jiki a mace sai dai ba ta san wane baki za ta buɗe ta yi masa maganar kuɗi ba.
Ganin ya share ta sharewar ma har ta fi ta kullum ya sa ta janyo littafinta ta ci gaba da karatu. Jin motsin keys ɗinsa ya sa ta ɗaga kai sai ta ga ya miƙe ya fara tafiya ita ma ta miƙe ta bi bayansa har inda ya saba ajiye mota buɗewa ya yi ya ɗauko wani kwali sai ya miƙa mata ta amsa da godiya sai ta koma ciki jikin Gwoggo har rawa yake wurin karɓar kwalin ta buɗe, waya ce dalleliya samfurin Samsung. Gwoggo ta ce “Ita kenan ya ba ki ina kuɗin? Ta girgiza kai “Bai bani ba.” Sababi sosai Gwoggo ta hau yi har Allah ya gajishe ta ta yi shiru.
Abdurrashid zaune falon wani abokinsa ko ma a ce amininsa mai suna Usman a washegarin ranar da ya dawo Lagos fita za su yi amma Usman ɗin ya ishe shi da mitar tun aurensa wata uku kenan Abdurrashid bai zo ya ga amaryarsa ba.
Shi ne yau ya zo wayarsa yake taɓawa amma yana hankalce da sakarcin da amaryar ta Usman ke ta zubawa angon nata, shi kuma yana aikin tarairayarta.
Abin ya ishi Abdurrashid ya dubi agogonsa sai ya miƙe tsaye “Haba Malam ka zo mu tafi.”
Usman ɗin ya miƙe amaryar ta sha gabansa wai ba zai fita ya bar ta ba. Ya riƙe ta a jikinsa yana faman rarrashi Abdurrashid dai ficewa ya yi ya rabu da shi ya dan jima a motar sai horn yake danna masa ya fito ya same shi yana shiga motar Abdurrashid ya tashe ta, sai da suka yi nisa ya dube shi ta wutsiyar ido “Mace ta yi ta maka sangarta kana faman biye mata.” Cikakken murmushi ya yi “To ai shi ne son.” Abdurrashid ya jinjina kai “Sai ku yi ta fama ai.” Usman zai yi magana ya ga Abdurrashid ya tsaida motar ya ciro wayarsa Gwoggo Indo ya kira ya ce ta turo mishi Hamida ƙofar gida. Sai duban ƙofar gidan Usman din ke yi har Hamida ta fito Material ne jikinta ɗinkin doguwar riga sai ɗan gyale da ta yane kanta.
Abdurrashid bai buɗe mota ba ta tsaya saitin inda yake ta gaishe shi kafin ta gaishe da Usman, wata leda da ke kusa da inda yake zaune ya dauko ya mika mata “In ji Aunty ta ce in kawo miki.” Ta furta “Na gode.” Ganin ya tashi motar ta gane tafiya zai yi sai ta ja baya kafin ta juya ta shiga gida.
Ƙin kallon Usman ya yi da ke mishi wani duba na mamaki har dai ya gaji ya ce “Amma dai Allah ba ita ba ce amaryar? (Don a gaban shi Auntyn ta bayar da saƙon ta ce ya kai wa surukarta.) “Ita ce, ka ga na huta da shan ɗawainiyar da kuke sha, yarinya ce ƙarama sai yadda na juya a ba ta.” Usman ya yi dariya “Lallai kam! Kana raina mace mutumina, komai ƙanƙantar ta kana gane wace ce ita juya ka za ta yi kamar waina a tanda. Ka more wallahi kyakkyawar yarinya.”
Abdurrashid da ya balla mishi harara zai yi magana wayar Usman ta shiga ɓurari amaryarsa ce Jamila. Kare wayar su ya ce “Mutumina maida ni gida.” Ya ce “Me ya faru? “Ba komai zan koma wurin amarya, kiran da ta yi min duk ta sukurkuta ni da kalamanta.” Abdurrashid ya taɓe baki “Ba inda zan kaika Malam, zan sauka gida ka wuce da motar.” Hakan a ka yi a Gate dinsu Abdurrashid ya sauka Usman ya juya da motar.