Skip to content
Part 16 of 37 in the Series Shirin Allah by Maryam Ibrahim Litee

Wani dogon corridor suka tarar tafiya suka yi mai ɗan nisa kafin suka isa wasu ƙofofi guda biyu suna duban juna, dayar kitchen ne dayar dakin Abdurrashid.

Tafkeken daki ne wanda aka ƙayata da kayan more rayuwa komai na dakin purple ne da ratsin fari.

Ba su wani zauna ba bayan Aunty Zainab da ta kamo ta ta zaunar da ita bakin gado suka yi mata sallama, sai da ta tabbatar da tafiyar su ta ɗan yaye rufar tana duban dakin, haƙiƙa ɗakin ya tsaru kamar ma ta ce ba ta taɓa ganin ɗakin da ya yi mata kyau a ido buɗe ba sai dai a fina-finan kasashen ƙetare da suke kallo, duk da dai gabadaya gidan ma ko’ina ya haɗun.

Karaf! Idonta ya shiga wani hoto na Abdurrashid da ya yi kyau ƙwarai da kayan soja yadda hoton ya fito raɗam kamar zai yi magana ya sa Hamida saurin kawar da idonta don sai ta ga kamar a zahiri yake kallonta.

A wata kusurwar ta ga wani tafkeken hoton, su Aunty Karima ne ganin su su shida cif ya ba ta damar gane Daada ce da yayanta su duka, tana ƙoƙarin fidda mahaifiyar Abdurrashid a cikin su ta gano wani frame kan dressing mirror hoton wata kyakkyawar bafulatana ne wadda Hamida ta ga kamar Aunty Safiya sai tunaninta ya ba ta zai yi wahala ba mahaifiyarsa ba ce.

Murɗa handle din kofar da aka yi ya sa ta saurin mayar da rufarta ta yi ruf, Abdurrashid ya shigo shi dariya ma ta ba shi ganin uban lulluɓin da ta sha har fuska ita nan dole amarya “Ina wuni.” Ya tsinkayi muryarta. “Lafiya.” Kawai ya ce ya wuce wurin wardrobe dinsa don tuɓe kayansa, yana kuma gama tuɓewar wata ƙofa ya nufa ya murɗa ya shige motsin ruwa da Hamida ta ji, ya ba ta tabbacin bathroom ne wanka yake, fitowarsa ɗaure da tawul ya sa Hamida da ta ƙyallaro idonta ta ƙasan mayafi tana yi masa kallo ɗaya sai ta kuma dunƙulewa.

Sai da ya gama duk abin da zai yi ya miƙe bisa sopa “Ki tashi ki cire wannan uban lulluɓin ki yi shirin kwanciya, sun shirya miki kayanki a wardrobe.” Ɗan mutsu-mutsu ta soma jin zancensa kafin ta miƙe kanta ƙasa ta isa gaban wardrobe din a hankwali ta buɗe, ganin kayan maza ta rufe ta ƙara buɗe wata ƙofar Allah ya taimake ta ta ga akwatunan aurenta, gefen su kuma an jera sleeping dress masu tarin yawa, ba tare da ta tsaya zaɓe ba ta zari ɗaya sai ta rufe, bathroom ɗin ta shiga duk abin nan da take Abdurrashid yana kallon ta ta ƙasan ido ya miƙe ya rage hasken fitilun dakin wayarsa ta ɗauki ƙara a kan kujerar da ya taso ya isa ya ɗauka sai ya yi picking abokinsa ne Usman. Ya ce “Wallahi kai kam ba ka da mutunci, yanzu saboda Allah kazar da na yi maka kara na saya maka sai ka bar ni da ita? Ni sai yanzu na gan ta. Bayan ka sulale ka ƙi kowa ya raka ka, yar kazar ma ka kai wa yarinya sai ka isa ziƙau ko haka ka ga ana yi.

Ɗan murmushi ya yi “A ina zan ɗauko ku mu taho ɗakin na wa? Ku bari idan lokaci ya yi sai ku rako ni, amma yanzu raino zan yi.”

Usman ya ke ce da dariya “Ka ji ɗan iska wa za ka rena? In za ka kwashi r.. “

Abdurrashid ya katse kiran sanin sharɓo ta zai yi.

Hamida na shiga bathroom ɗin sai da ta kama ruwa sai ta canza kayan, wata jar riga ta dauko mai sulɓi hannunta na shimi ne tsawonta iya gwiwa, ba ta san yadda za ta yi ta fita gaban Abdurrashid a haka ba don haka mayafin kayan da ta cire ta mayar jikinta sai ta fito gadon ta haye, ta yi lamo ta gaza barci don wata fargaba da take ji, wai ita ce a daki daga ita sai namiji, sai dai da yake barci ɓarawo ba ta san sa’adda ya ci ƙarfinta ya yi awon gaba da ita.

Daf da za a tayar da sallah ya farka hasken fitulun dakin ya ƙara, dakin ya gauraye da haske sai ya wuce bathroom ya ɗauro alwala ya fito ya hau pray mat ya kabbara sallah yana idarwa ya tashi zuwa gaban gadon yana murza hannuwansa Hamida da ke kwance abin ta da gani ta yi nisa cikin barcinta har yar rigar da ke jikinta ta yaye santala santalan cinyoyinta, daga ita sai dan pant, bai jima yana kallon ta ba ya fara kiran sunan ta, a hankali take amsawa ba tare da ta buɗe ido ba ko ta tashi “Ki tashi ki yi sallah.”

Ya faɗi yana fara tafiya don gudun makara.
Hamida dai ba ta ma san yana yi ba don cikin cikin gajiya take, rabon ta da ta yi barci mai daɗi kuma isasshe tun kafin tafiyar su Daura ga laushin katifar da shimfidun da suka kara nutsar da ita.

Har ya dawo sallar tana nan inda ya bar ta sosai ya tashe ta kafin ta miƙe idonta a rufe don ji take kamar sannan ta kwanta, a daddafe ta isa bathroom ya bi ta da kallo ko da ta fito a gado ta gan shi ya kwanta ya rufe jikinsa, ta ga hijab ya ajiye mata saman pray mat ta dauka sai yi sallar.

Tana gama yan addu’ointa ta kwanta saman pray mat wani barci mai dadi ya kuma daukarta “Ki tashi ki yi shirin makaranta.”

Ta tsinkayi muryarsa cikin barcinta, ba shiri ta buɗe ido “Wai wane irin barci kike, kin san dai yau za ku koma sch ko?:

Saurin duban shi ta yi, idon da suka haɗa ya sa ta sunkuyar da kai sai kuma ta miƙe, har ya yi wanka tawul ɗin da ke ɗaure jikinsa ya ba ta tabbacin hakan. Bathroom ta shiga sai kuma da ta shiga ta cire hijab din jikinta, tana wankan tana tunanin komawarta makaranta a yau, tare da mamakin hakan.

Wasu tawul da ta gani guda biyu babba da ƙarami. Ta ɗaura babban daga ƙirji zuwa cinyoyi sai ta mai da hijab din ta fito. Fitowarta ta yi daidai da knocking ɗin kofar ya tashi kan wata kujera da ya zauna riƙe da jarida yana sanye da boxer da farar singlet, tana jin shi da mai bugawar sai da ya gaishe shi sannan ya karɓo tiren hannunsa ya wuce ya ajiye a tebur ɗin cin abinci da ke dakin.

Gaban mirror ta zauna ta yi farin ciki da ganin an shirya mata kayan kwalliya. Mai ta murza sai ta shafa hoda karshe ta fesa turare, ta mike don neman sa wa idonta ya sauka kan sababbin unifoam ajiye a kan gado riga da wando ne sai hijab, ba ta san inda suka sanya mata undies ba don haka dole ta zura rigar da wandon ba tare da ta sanya komai a ƙasa ba, rigar ta kama ta fiye da nata na gida don haka ta yi saurin zura hilab din tana satar kallon inda Abdurrashid ke zaune yana gaɗa Tea.

“Idan kin kammala ki zo ki yi break past ko ba ki ga za ki makara ba?”

Ta nufi inda yake kanta a ƙasa, ta ja kujera ta zauna “Amma kin san za ki ɓata hijab dinki ko? Ya faɗi yana turo mata plate din da ya zuba mata soyayyar agada da ƙwai. Kamar za ta yi kuka ta miƙe don cire hijab ɗin akan gado ta ajiye shi sai ta kasa komawa har sai da ya kira ta, muryarsa da ta ji cikin tsawa ya sa hantar cikinta kaɗawa, ta nufe shi cikin ɗaga ƙafa, ta fakaice yake duban ta ya yin da yake jin yanayinsa na canzawa har ta iso ta zauna. Tea da ya haɗa mata ya miƙo mata ta karɓa tare da furta kalmar godiya tana ta sha kawai ba tare da ta haɗa da komai ba don kunyar zaman shi a wurin, agogon hannunsa ya duba sai ya miƙe kayansa ya sa tana ganin ya gama fesa turare ta mike ta isa inda ta ajiye hijab dinta ta sanya mamaki ne ya dabaibaye ta da ta ga ya ciro jakar makarantarta ya mika mata, ta amsa suka bar dakin sai da ya rufe ya mika mata key ta sanya a jaka yana gaba tana bin shi a baya har falon mahaifinsa, Haj Mariya suka samu ita ta shiga ta shaida mishi zuwan su ya fito cikin malum malum kawai ba yar ciki.

Sun gaishe shi suka mike har take jin tafiya Daddyn zai yi a wannan rana. Kitchien din da ke duban kofar dakinsa suka shiga akwai wata kofa ita suka shiga ta sada su da part ɗin Aunty Karima, sun samu iyayen sun tashi haka ma wasu daga cikin yaran “Me zan gani haka ni Shatu, ina za ka kai musu yarinya da farar safiya? Daada ta faɗi tana kama baki. “Makaranta.” ya ba ta amsa yana zama kusa da ita iyayensa ya fara gaidawa yana sauraren sababin Daada

“Bokon banza! Yarinya da ɗanyen amarci daga shigowa ɗakin miji jiya ka fito da ita ka kwashe ta wai za ka kai ta makaranta?”

Hanan ta ce “Ke dai Daada me ya ruwanki, mutum da matarsa?”

Daƙuwa Daada ta yi mata “Da ruwana ja’ira.” Shi dai miƙewa ya yi yana musu sallama “Ai shi kenan, mai abu da abun shi kai naka ido.” Ta ƙarashe faɗi tana taɓe baki iyayen su ka bi shi da addu’a Hamida ta bi bayansa, Mimi da ke maƙe bayan kujera don ganin Abdurrashid ta ɗago “Sai kin dawo amarya za mu shigo.”

Gaba daya ya waiwayo sai ya yafito ta da hannu ɗaya ya juya ya ci gaba da tafiyarsa, ta fito ta bi bayan su tana wara ido har sai da ya kai gaban motar da zai fita cikinta ya tsaya yana duban Mimi “Duk yar rawar kan da ta shigar min ɗaki sai ta sani, ku bari idan aka gina mata wurinta sai ku yi ta shiga.”

Ke kuma fa da kika tsaya? Ya ce da Hamida, cikin dan tsoro ta kama handle din ta buɗe ta shiga.
Dunƙulewa ta yi da suka fara tafiya don ban da sanyin safiya hakan bai mishi ba sai da ya kunna A.C ƙamshi mai daɗi ke fita cikin motar, har kuma suka isa ba wanda ya ce uffan, kowa da abin da yake saƙawa a ransa.

Yana tsaida motar a harabar makarantar ta soma murmushi don Walida da ta hango tsaye tana sauri ta fita, ta kama ƙofar sai dai ya rufe “Saurin me kike wa kika gani kike fara’a? Sai da ta sunkuyar da kai ta ce “Ƙawata ce.”

Bai tanka ba illa kuɗi da ya ciro a aljihun wandonsa ya ba ta ta yi mishi godiya ta sanya a sch bag ɗinta sai ta fita tana mishi addu’ar Allah ya tsare.

Wurin da ta ga Walida ta nufa, suka tari juna da murmushi duk da ƙaiƙayin da Walida ta ji a zuciyarta na ƙyashin dami a kala da Hamida ta tsinta.

Suka kama hannun juna zuwa wurin Assembly “Sai ga ki amarya, ina nan tsaye har na fara missing ɗinki kamar daga sama na ga isowarki.”

Murmushi Hamida ta yi ba ta yi magana ba.
An kammala Assembly sun shiga Class ana ta gaggaisawa na kwana biyu ba a ga juna ba ba su lafa ba sai da malamin farko ya shigo.

An fita break Hamida ba ta fita ba duk da ba ƙoshi ta yi ba da safe, aka aiko kiranta ta miƙe ta fita, wani soja ne ɗauke da ledoji biyu daga wurin Abdurrashid saƙon ya fito.

Ta juya tana neman Walida don abin da za ta ci Walidar ta fita nema ta shaida wa Hamida ba ta karya ba, sun ci sun yi ƙat har suka yi wa na kusa da su tayi don duk yayan wani da wata ne kowa na ji da kansa.

Ana tashi tare suka fito sai dai duk yadda Hamida ta yi da Walida ta zo su rage mata hanya kamar yadda suka saba ƙi ta yi, don ita ma tsoron Abdurrashid take.

Sai da suka kusa isa inda motar take Walida ta ƙwace hannunta daga ruƙon gam gam da Hamida ta yi mata “Sai na zo ganin ɗaki amarya.”

Ta wuce suna ma juna murmushi
Ta kama murfin motar ta buɗe ta shiga “Ya aiki? Ta ce mishi lokacin da ta daidaita zamanta a motar.

Bai amsa ba sai da suka hau titi ya ce mata “Me yarinyar nan take ce miki da za ku rabu?”

Ɗan shiru ta yi gabanta na faɗuwa kafin ta furta “Ta ce za ta zo ne.”

“Ina za ta zo? “Wurina.” Ta ba shi amsa
“Kar wanda ya zo kika kai shi part ɗina, duk wanda ya zo ki kai shi part ɗin Aunty Karima.”

Kai ta ɗaga daga haka kuma har suka kai gida ba wanda ya kuma magana sai kiɗan da ya kunna yana fita a hankali.

<< Shirin Allah 15Shirin Allah 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×