Skip to content
Part 17 of 37 in the Series Shirin Allah by Maryam Ibrahim Litee

A farkon Gate ɗin Hamida na duban wurin saida abincin Gwoggonta sai ta ji kewarta mai yawa ta kamata. Suka wuce zuwa gida, yana parking sai da ta bari ya fita kafin ta buɗe ta fito.
“Mu je wurin Aunty Karima su gan ki waɗannan ‘yan rawar kan.”
Kai ta gyaɗa sai ta bi shi a baya.

Yanzu ma kamar da safe zaune suka same su sai dai ba a falon da suka gan su da safe ba, gaishe su suka yi Aunty Karima ta kira mai aikinta ta ce a kawo musu abinci, kai ya girgiza ya ce A’a yanzu za su wuce a kai musu can.

Daada ta ce “Sai dai kai a kai maka can, yarinyar nan a kawo mata anan a can daga kai sai ita ina za ta iya cin abinci a gabanka kana wannan tsare gidan?

Tashi ka tafi abin ka miskili ka fi mahaukaci ban haushi.” Kan ya kuma girgizawa yana ƙara shan mur “Zan jira ta ta gama.” Ba Daada da ta kama tafa hannaye tana dariya ba iyayen ma dariyar suka so yi sai suka fuske. Ana kawo abincin Daada ta ce “Kai mata can ɗakin da yaran nan suke, tashi maza ki je ki ci ki samu ki isa sasanku ki yi wanka ki huta.”

Ta miƙe ta bi bayan yarinyar tana jin Daada na ce wa Abdurrashid “Da yau za mu koma duka to Auntynka ta matsa sai a zauna a yi mata sati, ni dai ba za a yi wannan rashin hankalin da ni ba, na dai haƙura yau amma gobe idan Allah ya sa mun kai ba za ka dawo aiki ka same ni ba.”

“Me zai hana ke ma ki yi haƙurin satin Daada?

Kai ta girgiza “A’a iyayenka dai da suka biye mata ganin tana kuka su zauna, zan tafi yaran ma za su tafi saboda makaranta.”

Bai yi magana ba sai sumar kansa da ya shafa yana sane da tausayin Aunty Karima da mahaifiyarta da yan’uwanta ke ji saboda rashin haihuwa ga shi kuma ita ɗin ita ce yar auta.

Hamida na shiga ta samu kowa na harkarsa Hanan da Mimi mutanenta suka yo kanta sai da ta gaisa da kowa ta zauna ta zuba abincin, Hanan shiri suke za su fita duk da ba yunwa take ji ba saboda abin da suka ci a makaranta ta ji daɗin yadda Daada ta yi mata don ba ta san yadda za ta yi ta ci abinci gaban shi ba.

Tana ci suna ɗan taɓa hira har su Hanan suka kammala shirin su suka fice sai ita da Mimi tana ta satar kallon Aunty Mami yar wajen Momi Binta ta farko tana haɗa kayanta tana kakkaɓin wai budurwa ce a haka amma aka sa Aunty Aina a gaba da ta yi girma don Hanan ta ce mata shekara biyu kacal Abdurrashid ya ba ta, ko da yake yar wajen Aunty Safiya ta farko ita ma babbar ce har ma ta fi Aunty Mamin girman jiki.

Ta gama ta sha ruwa sanin Abdurrashid na jiranta ya sa ta ƙi tayin da suka yi mata na ta shiga ta yi wanka ta ce zai yi faɗa idan ta daɗe har falon Mimi ta rako ta yana zaune har lokacin ganin fitowarta sai ya miƙe ta yi musu sallama ta bi bayansa.

Da suka isa wuri ya ba ta ta ciro key a jaka ta buɗe sai ta kauce ya shiga sannan ta shiga, kayan jikinsa ya soma cirewa aka yi knocking shi ya buɗe ya karɓo abinci, yana zaune yana ci Hamida ta rasa yadda za ta yi ta cire kayanta yana zaune, ganin ba ta da zaɓi ya sa ta dole ta miƙe zuwa gaban wardrobe akwatunan ta riƙa buɗewa har ta samu wanda Abayas suke ciki ba tare da ta tsaya zaɓe ba ta zaro wadda ke kusa hijab ɗin ta ɗaura a maimakon zane ta cire rigar har za ta zura Abayar sai ta tuna littattafan da take karantawa yadda rayuwar aure take, a gidan Gwoggo wanka ɗaya take yi da safe idan za ta tafi makaranta, idan ka ga ta ƙara wani to unguwa za su fita, a litattafan da take karantawa tana jin abubuwan da ake yi don kama zuciyar miji har da wanka da kwalliya.

Daga ita sai hijab ɗin da ta ɗaura ya tsaya mata iya gwiwa ta wuce zuwa bathroom ɗin wanka ta yi sai ta yi alwalar sallar La’asar don ta yi Azahar a makaranta tawul ɗin ta ɗaura ta rufa da hijab ɗin sai ta fito har yanzu yana wurin cin abincin idonsa na kan wayarsa ganin haka ya sa ta ɗan saki jikinta ta zauna tana kwalliya a tunaninta hankalinsa bai kanta, ba ta san yana hankalce da duk motsinta ba turare ta fesa ƙarshe sai ta bar wurin zuwa bakin gado inda ta ajiye rigar da ta ciro ta ɗauka ta sanya ta a jikinta sai ta haye gado ta zaro wayarta a ƙarƙashin pillow tun daren jiya ta tura ta missed call biyar ta samu ta shiga dubawa Gwoggo Indo ce sai Aunty Aina sai ƙanwar Aunty Laila Sajida.
Aunty Aina ta fara ƙoƙarin kira sai na ta kiran ya shigo ta yi picking da farin ciki “Aunty Aina kin manta da ni.”

Ita ma daga ji murmushin take ta ce “Ya za a yi in manta da yar ƙanwata? Na so zuwa Dinner ɗinku Brigadier ba ya nan ranar, shi ma bai samu zuwa ba.”

Hamida ta shagwaɓe fuska na yi kewarki sosai Aunty Aina.” Ita ma ta amshe “Ni ma haka yar ƙanwata “Ina fata kina aiki da abin da kike karantawa a littattafan da kike ƙwaƙwahe mawa, ki kula da mijinki ba wai ki zauna ki yi dunkum ba.”

Ta saci kallon inda yake sai ta yi murmushi “Ba na yi Aunty Aina.”

“Yawwa to yanzu ne za ki yi amfani da abin da kike karantawa amma masu kyau, sai ki bar marasa kyan a inda kika karanta.”

Ta ce “To Aunty Aina.”

Ta ce “Bari in bar ki ki huta sai anjima.

Murmushi ta kuma yi “To Aunty na gode.

Ta kashe wayar daga can ɓangarenta tana jin mai jin tausayin Hamida ita dai tausayi yarinyar ke ba ta sai ta ga ba za ta iya da Abdurrashid ba yadda yake wayayye gogagge ba za ta iya dabarar da za ta kama abin ta ba.

Hamida ta ajiye wayar tana jin wani farin ciki da hirar da suka yi da yar’uwar ta ta.

Wani littafinta na makaranta ta dauko tana dubawa har lokacin La’asar ya yi tana kallon miƙewar Abdurrashid ya yo alwala da ya fito ƙananan kaya ya canza wanda Hamida ta ga kamar bai taɓa mata kyau irin na yau ba. Ya fesa turare duban inda take tsaye za ta kabbara sallah ya yi “Zan je masallaci idan na fito zan je wurin wani abokina, ko zan shigo sai na yi sallar Isha’i.”

Kai ta gyaɗa mishi tare da faɗin “A dawo lafiya.”

Ya fice ta kabbara sallah ta idar tana addu’a ta j yo kukan wayarta ta miƙe ta isa inda ta ajiye ta, sunan Mimi da ta gani ya sa ta fara murmushi tana kuma dauka ta ji muryarta tana cewa “Sai ki samu ki fito ai daga ya fita.”

Ido Hamida ta buɗe tana fiddo harshe “, Bai ce in fito ba ki zo mu yi hira don Allah.”

“Ki rufa min asiri ya yi mana kashedi.”

Allah ki zo ba yanzu zai dawo ba, ya ce sai ya yi Isha’i.”

A’a dai Aunty Hamida.”

“Don Allah ni dai ki zo.”

“To shi kenan na ji zan zo, amma ki buɗe min ƙofar kitchen iyakata nan idan na ji shigowar shi in sulale.”

Hamida ta yi murmushin jin zancenta,

“Na ji ki dai zo.”

“Tam gani nan.”

Ta kashe wayar sai ta zare hijab ɗin jikinta ta nufi ƙofa da wayar a hannunta, kitchen ɗin da suka shiga ya sada su da part ɗin Aunty Karima ta buɗe ta shiga sai ta buɗe waccan ƙofar ba jimawa Mimi ta iso tana shigowa ta mayar da ƙofar ta rufe ta murza key, wata drower da ke jikin window ta haye “Muna hira ina kallon parking space da na ga motar Hamma in fece.”

Hamida ta yi dariya tana zama kan wata kujera,

“Don Allah meye na wani jin tsoron Hamma?

Mimi ta yi tambayar tana ɓata fuska . Hamida ba ta yi magana ba sai murmushi da ta yi,

“Gaskiya ki canza taku, kwalliya za ki riƙa mishi wadda za ta ɗauke masa hankali ki daina nuna kina jin tsoron shi shagwaɓa za ki riƙa mishi in ya fara miki faɗan nan nasa sai ki shagwaggwaɓe masa.”

Hamida ta riƙe baki “Ikon Allah ke duk ina kika san wannan oh!

Ta tafa hannaye tana kaɗa ido “Kin ji ki ba mace nake ba? Saboda Allah sai ya yi ta miki mazurai maganinsa za ki yi.”

Suka kwashe da dariya. Girman jikin su ɗaya Hamida da Hanan sai dai sai dai Hanan ta bai wa Hamida shekara biyu don ita yanzu sha bakwai take.

Hirar su suka cigaba da yi kamar sun shekara da sanin juna Hamida ta hilace ta har sai da suka shiga ɗakin da Abdurrashid ke ta kashedin kar a shigar masa ta taya ta ciro akwatunan aurenta suka duba kayan ciki ta ciccire waɗanda za ta yi amfani da su, wata uban sun atamfa da aka yi wa haɗaɗɗen ɗinki Mimi ta ciro mata “Ki sanya wannan da kin yi wanka kafin ya shigo.”

Suka gama duba kayan suka mayar bayan ta yi wa Mimin tayin ta ɗauki abin da ya burge ta ta ce Sam.

Ƙofar ɗakin suka dawo Mimi ta yarfa ma Hamida ƙananun calabar da suka sauka kan dokin wuyanta calabar ta kai su har magrib don haka a guje Mimi ta fice.

Hamida ta koma ɗaki ta yi sallah sai ta wuce gaban mirror tana duba kitsonta wanda ya ƙara ma fuskarta kyau, ta gyara fuskar ta fesa turare don zuciyarta da ke gaya mata kar ki wani ƙara wanka in kika biye wa masu kuɗin nan motsi kaɗan wanka sai mura ta kama ki a banza.

Take ta yanke ma kanta kullum za ta riƙa wanka sau biyu idan ta yi da safe sai kuma dare kamar yadda take karantawa idan an yi wanka da daddare sai a yi wa Maigida kwalliya.

Kayan da Mimi ta cire mata su ta sanya ai kam ba ƙaramin amsar ta suka yi ba har ta kasa barin gaban mirror tana ta duban kanta, ɗinkin ya zauna a jikinta ya kamata cas! Riga da skirt ne, tana riƙe da ɗankwalin a hannu Abdurrashid ya shigo ta nufi wurinsa tana masa sannu da zuwa da karɓar jakar da ya shigo da ita da mamaki yake kallon kwalliyar da ta sheƙa sosai ta yi mishi kyau har ya so ya shagala da kallon ta.

Ko da ya cire kayan jikinsa daga shi sai singlet da boxers ya zauna kan ɗaya daga cikin kujerun da ke gefe ɗaya yana kallon labaru a tashar CNN.

Hamida dai bakin gado ta zauna har aka kawo masu abinci, suna zaune suna ci wanda shi kaɗai ke cin abin shi don idanuwansa da take ji suna kanta.

Da suka kammala inda ya taso ya zauna ya umarci ta kawo mishi littattafanta na makaranta ta tashi ta dauko kusa da shi ya nuna mata ta zauna ta zauna a ɗarare tambayoyi yake mata tana mishi bayani yadda ta fahimta ta miƙa masa littafin ƙarshe ya haɗa har hannun nata ya riƙe hannun wanda ya sha ƙunshin amare ga shi fari tas ba ƙaramin kyau ya yi masa ba kome kuma ya tuna sai ya yi saurin sakin hannun daga haka mikewa ya yi ya koma kujerar da ya kwana jiya ya kwanta.

Hamida cigaba ta yi da nazarin litattafan na ta har sai da ta soma hamma ita ta kashe kayan kallon ta kashe fitilar ɗakin, ganin kamar ya yi barci yau wasu riga da wando ta sanya da suka yi daidai da jikinta masu taushi ta kwanta, ba ta wani jima ba barci ya sace ta.

Ya daɗe yana juye juye don barci da ya gaza ɗaukarsa bai taɓa tunanin yar yarinya kamar wannan za ta dagula tunaninsa ba, amma duk laifin su Daada ne ya roƙe su da kar su kawo mishi ita amma ba su ji ba, shi kuma ya yi ma kansa alƙawari shi da ita sai ya dawo lokacin ta zama mace sosai.

Kamar an tsikare shi ya miƙe fitilar ɗakin ya kunna ɗakin ya gauraye da haske ya taka gaban gadon ya zura mata ido sai ga shi zaune wani abu ke mishi yawo a jiki, ƙirjinta da ya ɗago saman rigar ya tsura wa ido bai taɓa tunanin ta kai cikar haka ba, hannu ya kai zai taɓa ta sai kuma ya janye da sauri ya ɗora hannun kan fuskarsa don zuciyarsa da ke kwaɓarsa. Ya daɗe cikin wani kafin ya tashi ya koma wurin kwanciyarsa.

Asubar farko Hamida ta farka zumbur! Ta duro gadon tuna ba ta wanke unioform ɗinta ba jiya.
Motsinta ya farkar da shi don yau ya makara saboda rashin samun barci da wuri tambayar ta abin da ya tashe ta ya yi ta kwaɓe fuska kamar za ta yi kuka, ta ce “Ba ta wanke uniform ba.

Ya ce idan an kawo abinci ta bayar da unifoam ɗin a wanke mata, ta duba wardrobe ɗin akwai wasu.
Da sauri ta miƙe ta je ta kama buɗe-buɗe sai ta ci sa’ar ganin su waɗanda ta ƙirga dozen ɗaya ne cif har na jiya, bakin gadon ta koma ta zauna don ya shiga toilet ɗin sai da ya fito ta shiga da ta fito ta samu yana sallah ita ma ta yi haramar sallar, yau ko barcin ba ta koma ba shirin makaranta ta hau yi bayan ta gyara gadon shi ma kuma ta hana shi sukuni da gilmawar da take ta gabansa, ya rasa me ya sa yau ta watsar da lulluɓin da take take mishi yawo a haka.

Sun karya tare kafin suka fita yau bai biya da ita wurin Aunty Karima ba wani corridor ya bi da ya sada su da wani ƙatataccen falo da ya tsaya mata bayanin idan ta yi baƙi ta kawo su nan.

Suka fita suka fita suka shiga mota suka bar gidan.

Ran Hamida bai so ba da bai kai ta yi
sallama da su Hanan ba wanda ba ta san dalilinsa na yin hakan ba.

Sai da ta dawo ta samu ba su tafi ba suna dai ta shiri gaisawa kawai suka yi ya ce ta wuce su je.
Suna cin abinci ta roƙe shi za ta je ta yi Daada sallama sabulan akwatinta ta ɗebo ta sanya a leda da za ta wuce ya ce me ta sanya a leda ta ce sabulu, ya ce me za ta yi da shi ta ce Daada za ta ba ganin bai kuma magana ba sai ta wuce.

Da ta kai wa tsohuwar ba ƙaramin sanya mata albarka ta yi ba tana ta yaba hankalinta.

Zamanta ta yi wurin su Hanan har sai da za su tafi, suna ta shiga motocin da za su kai su Airport shi ma ya fito sai da suka wuce ya ce su koma part ɗin Aunty Kariman hirar su suke tana sauraren su gara shi yana ɗan sanya baki idan sun tsoma shi har sai da aka yi kiran sallar La’asar ya ce zai fita daga can, ita kuma nan ta cigaba da zama har aka yi magrib sai Aunty Karima ta ce ta koma part dinsu ta yi wanka ta yi ma mijinta kwalliya.

Hakan kuwa aka yi wankan ta yi ta sheƙa ado da wasu ubansun riga da wando daidai jikinta ba ta sa komai a kanta ba sai calabar ta da ta kwanto wuyanta.

Ta koma ta zauna tana taɓa wayarta duk da TV da ke aiki.

Yau ma da ya shigo ganin ta a haka ba ƙaramin taɓa shi ya yi ba, ya dai maze kawai.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Shirin Allah 16Shirin Allah 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.