Skip to content
Part 19 of 37 in the Series Shirin Allah by Maryam Ibrahim Litee

Tana nan kwance har sai da ta ji an tayar da sallah a masallacin da ke cikin estate din ta yi yunƙurin tashi, a daddafe ta kai kanta bathroom ruwa mai zafi ta tara da dabara da dauriyar da ta sanya ta shiga ruwan tana runtse ido, ga hawaye na gudu kan kuncinta sai da ta ji ya soma sanyi ta zubar ta sake wani, wankan tsarki ta yi sai ta yi wanka da ruwa mai zafi, sosai ta ji dama lokacin da ta fito doguwar riga har ƙasa ta samo ta sanya ta yi sallah ta lallaɓa za ta hau gado ta kwanta ta hango inda jini ya ɓata zanen gadon dole ta yaye shi ta kai shi bathroom ta sanya a laudry ta dawo kamar ta duba wani ta shimfiɗa sarawar da kanta ke yi wanda bai rasa nasaba da kukan da ta sha ga zazzaɓi da take ji zai rufe ta ya sa kawai ta kwanta, barci ya yi awon gaba da ita.

Knocking ɗin da ake ya farkar da ita ta miƙe a hankali ta isa ƙofar sai ta buɗe mai kawo musu abinci ce ta karɓi tiren tana gaishe ta tare da bayanin Haj ta ce ta ji shiru ba ku fito ba, ba ku yi magana a kawo muku abinci ba.

Ta ce “Shi ya fita ni kuma ina barci.”

Mai aikin ta juya don isar da saƙon, ita kuma ta shiga da abincin sama-sama ta ci ta rufe ta koma ta kwanta da za ta samu maganin zazzaɓi da ta sha ƙila ta ɗan ji dama, hakanan dai ta ci gaba da kwanciya har ta ƙara jin wani knocking ɗin wannan karon tana buɗewa sai su Aunty Karima ta gani yau ma kamar jiya su dukkan su, ta ba su wuri tana musu sannu da zuwa suka tambaye ta ƙafa ta ce ta yi sauƙi ita har ga Allah ta ma manta da ƙafar, don sawun giwa da ya take na raƙumi.

Suna ta karantarta wayar Aunty Karima ta yi ƙara cikin masu aikinta ne take shaida mata an yi baƙuwa ta ce Hamida take nema abokiyar aikin Abdurrashid ce.

Ta ce ta kawo ta. Da isowar matar ta gabatar da kanta ga su Momi Binta Abdurrashid ne ya turo ta ta duba matarsa suka ce ba matsala.

Ta matsa jikin gadon tana tambayar Hamida yadda take ji ta ciro kayan aikinta tana haɗa allurai, jikin Hamida ya soma rawa ta ce tana jin fitsari ta ce ok ta sauka gadon yadda take takawa tana buɗe ƙafa ita kuma tana daɗa nazarinta.

Ba ta daɗe ba ta fito ta koma bisa gadon ta ce mata ta gyara Hamida ta shiga yarfa hannu ga kunyar su Aunty Karima tana ji kuma Allah ya sani ba za ta iya tsayawa a yi mata allurar ba.

Kalaman rarrashi matar ta shiga yi mata gane ba ta son allura amma Hamida ta ƙi tsayawa sai ma maƙurewa da ta ƙara yi jikin gado su Aunty Zainab da ke kallon su kowacce na ƙara ƙarfafa zarginta kan abin da ke damun Hamida.

Wayarta ta ciro ta kira Abdurrashid ta ce mishi Hamida fa ta ƙi tsayawa ya ce ok ta ba ta wayar, ga mamakin Hamida maimakon magana cikin faɗa-faɗa da ta yi tunanin zai rufe ta da shi saɓanin haka cikin taushin murya yake rarrashin ta ta tsaya a yi mata ta ce ita tsoro take ji, ya ce ta ba Dr wayar ta karɓa ta ce jikinta akwai zafi ya ce ta ƙyale ta kawai idan ya dawo zai mata. Sallamar su Aunty Karima ta yi ta fita, su ma addu’ar Allah ya ƙara sauƙi suka yi mata da yi mata bankwana.

Sun fito Dr na ƙoƙarin shiga motarta Aunty Zainab ta ƙarasa inda take ta ce “Kuma Dr za ki tafi ba ki duba ta ba.”

Ta ce “Da ma allura zan yi mata kuma da ta ƙi Dr ya ce in ƙyale ta.”

Kina ganin idan ta shiga ruwan zafi ba zai wadatar ba daga ba ta son allurar?

Aunty Zainab ta jefa mata tambayar. Ta ɗan furzar da iska “Ya danganta daga wasu matan zuwa wasu, wata ko gezau babu abin da yake samun ta daga farkon fara mu’amalarta da ɗa namiji, wata kuma za ki ga abin ya zo da tsanani sosai kamar wannan.”

Aunty Zainab da ta yi tagumi ta ce “Kuma kina gani Dr yarinyar nan ta isa ɗaukar ɗawainiyar ɗa namiji?

Yar dariya ta yi “Ƙwarai kuwa wadda ba ta kai ta ba ma za ta iya, sai dai yanzu tana buƙatar a bar ta ta ɗan huta don da alamu ta ji jiki, na so duba ta sosai amma kin ga ta ƙi idan ya zo zai kula da kayansa.
Aunty Zainab ta yi mata godiya likitar ta faɗa motarta ita kuma ta juya zuwa part din Aunty Karima labarta ma yan’uwanta yadda suka yi da Dr ta yi kowacce ta ce da ma ta zargi haka “Momi Binta ta ce “Ɗan rainin wayo to da yana a’a kar akai ta.”

Sauran suka fashe da dariya ita ba ta yi dariyar ba sai ƙarawa ta yi da cewa “Ni da ma ban so aka kai masa yarinyar nan ba ya je ya kashe musu ‘ya, to Daada ta ce sai dai a yi haka, don haka Karima ki je ki dauko yarinyar nan ki kawo ta wurin ki maza ba haƙuri ne da su ba dubi yadda ta koma yau kawai ba kuma ɗaga mata ƙafa zai yi ba.

Aunty Zainab ta ce Dr ta ce ba wata matsala na farko ne kawai, da an bar masa matarsa ga shi tafiya zai yi.”

Hannu ta ɗaga mata “Ban yarda ba, ki ɗauko ta Karima ki faɗa mishi in ji ni.

Yanzu ki je ki ba ta abinci ki tabbatar ta ci kafin ya dawo ya duba ta.”

Aunty Karima ta ɗaga kai sai ta miƙe “Bari in duba sun kammala girkin in kai mata kuma ku ci kafin ku wuce.

Ta wuce kitchen din ta ɗauki wasu yan mintoci ta fito mai aikinta na biye da ita da tray ba ta samu kowa ba cikin yan’uwan nata a inda ta bar su sai suka shige part ɗin Abdurrashid ita da ke gaba ta yi knocking Hamida ta buɗe tana faɗin “Sannu Aunty.”

Za ta karɓi tray a hannun mai aikin Aunty Karima ta hana ita ta karɓa, shigar ta ganin Abdurrashid wanda ba su san sadda ya shigo gidan ba yana gyara gado ya sa ta ji kamar ta koma sai dai ya riga ya gan ta, ta wuce ta ajiye musu tray ya gaishe ta yana ba ta labarin kiran da ya samu na gaugawa wanda shi ya hana shi shigowa, amma yanzu zai shigo ya yi sallama da su Momi ta ce “To amma don Allah ka tsaya sai ta ci abinci na zo dama in tsaya ta ci a gabana na ga kuma ka dawo.”

Ya ce “Za ta ci Aunty na gode.” Ta juya ta fita.

Sai da ya gama gyara shimfiɗar ya wuce bathroom zanen gadon da ta ɓata ya wanke sai ya fito tana ta satar kallonsa daga inda ta idar da sallah “Taso to.” Ya ce yana nufar wurin cin abincin, wanda ya zuba mata ya kuma matsa mata sai da ta kusa cinye shi ya ƙyale ta da ƙyar don cewar da take ta ƙoshi.

Hannunta ya kama zuwa bakin gado maimakon ya bar ta ta zauna kan cinyarsa ya ɗora ta wasa ya riƙa yi da ita yana hura mata iska a kunne wanda duk ya ta da mata tsigar jiki.

Ba ta ankara ba sai dai ta ji ya soka mata allura yau ma ba ta ji zafi ba sai da ya gama liliya mata ya ja ta suka kwanta, ba ta ɗau wani lokaci ba ta yi barci ya zare jikinsa ya rufe mata rabin jikinta sai ya bar ɗakin.

Ya samu suna ta shiri. Shi da Aunty Karima suka yi musu rakiya Air port.

Momi kuma da kanta ta faɗa masa Hamida ta dawo part ɗin Aunty Karima.

Shiru ya yi cikin tunani don ba halin tambaya sai dai ya zargi sun gane abin da ya faru da Hamida a yau.

Sai da suka ga tashin su suka juyo Aunty Karima kaɗai ta koma gida shi komawa ya yi wurin patients ɗinsa.

Tana ajiye mayafinta wurin Hamida ta tafi ta samu ta tashi har ta yi sallar La’asar ta tambaye ta jiki ta ce ta ji sauƙi ta shaida mata za ta koma part ɗinta don haka ta ɗauki kayan amfanin ta.

Akwati guda ta cika Aunty Karima ta kira mai aikinta ta ɗauka wani ɗaki da ke jikin wanda su Hanan suka sauka Aunty Karima ta kai ta aka sanya mata akwatin a wardrobe sai ta kwanta kan lafiyayyen gadon.

Auntyn ta ce “Ko za ki zo mu je falo ki ɗan huta da zaman ɗakin? Kai ta girgiza “Zan kwanta Aunty.”
Ok kawai ta ce ta fita sai ta ja mata ƙofa.

Abdurrashid sai da aka yi sallah ya dawo, saboda aikin da ya tare shi amma duk abin da yake Hamida na maƙale a ransa ya ƙosa ya dawo don ya ga halin da take ciki.

Da ya shiga ɗakin bai gan ta ba sai ya nufi part ɗin Aunty Karima ita ya tambaya inda Hamidar take ta nuna masa hanyar ɗakin da hannunta.

Ya shiga da maƙallaliyar sallama ta ɗago daga kwancen da take tana amsawa zama ya yi bakin gadon yana jin sannu da zuwan da take masa kanta ya ruƙo ya ɗora saman cinyarsa yana shafa calabar da ke kanta, “Ya kike jin jikin yanzu? Ta ce “Na ji sauƙi.”

“Kin ci abinci? Ta ɗaga masa kai “Me ya sa ba za ki fita wurin Aunty ba kin kwanta nan ke kaɗai?
Ta ce “Na fi son in kwanta.” Wayarsa ya ciro ya kira Aunty Karima ya ce ta sanya a kawo masa abincinsa nan. Anan ɗin ya ci har ya sa Hamida ta ƙara, sai goma ya tafi da ya ga Hamida ta soma barci.

Ya gama duk shirin kwanciya amma ya gaza barcin kewar Hamida yake ji yana jin tsaurin hukuncin Momi Binta da ta raba shi da matarsa a daidai da ya san muhimmancinta. Sumarsa ya shafa yana mai lumshe idonsa tunanin cikin nishaɗin da ya kasance a daren jiya yana gilma mishi, hannu ya sa ya shafo inda ta fi kwanciya ɗankwalinta da ke wurin ya ɗauko ya kai fuskarsa ƙamshin da take yi da ke fita cikin ɗankwalin ya natsar da shi har ya shiga barci cikin kwanciyar hankali.

Da asuba yana dawowa sallar asuba ta ƙofar da ke sa da mutum da part ɗin Aunty Karima ya bi ya isa ɗakin Hamida ya samu ta idar da sallar Asuba ya ja ta zuwa gado suka kwanta, tambayar yadda ta kwana da jiki yake yi, ta ce ta samu sauƙi.

Ya ce ta huta yau ba sai ta je Sch ba zai faɗa musu ba ta da lafiya. Ta ce za ta iya zuwa, ya ce a’a ta dai kwanta.

Sai da gari ya yi haske ya zare ta cikin jikinsa ya fita.

Ko da ya shirya bai dawo ta nan ba sanin Aunty Karima a daidai wannan lokacin barci take.

Barci sosai Hamida ta yi bayan tafiyar Abdurrashid. Da ta tashi sai ta yi wanka ta shirya cikin doguwar rigar materiyal ta fita tana ƙamshi mai sanyi.

Kan ɗaya daga cikin kujerun falon ta zauna TV ta zura wa ido har ta ji shigowar Aunty Karima ƙara shiga nutsuwarta ta yi kafin ta soma gaishe ta, ta amsa cikin fara’a ta gayyace ta zuwa wurin cin abinci tare suka karya sai suka dawo falon suka zauna suna kallo.

Kiran Gwoggo Indo da ya shigo wayar Hamida ya sa ta miƙewa ta koma ɗaki ko da suka ƙare wayar yan Daura ta kira daga nan ba ta koma falon ba a ɗakin ta zauna ta ɗauko littattafanta na makaranta tana dubawa da ta yi sallar Azahar samun kanta ta yi da son yin kwalliya don ta burge Abdurrashid ganin duk sa’adda ta yi kwalliya yadda yake yawan kallonta wanka ta sake ta yi kwalliya sosai don zama da Aina ta ƙware a naƙaltar yadda ake yin ta.

Yau har da su jambaki ta gyara girarta ta feffesa turaruka less ta sanya ɗinkin riga da skirt da suka yi cif a jikinta ta yi kyau ba kaɗan ba, sai ta samu kanta da kasa fita wurin Auntyn don tana jin kunyar Auntyn ta ga ta sake kwalliya ta gane don Abdurrashid ta yi.

Gado ta koma suna chat da Hanan ƙarar buɗe ƙofar ya sa ta ɗago ido ganin shi ne ta ji mamakin hakan ta duba agogo sai lokacin biyu ta yi.

Sannu da zuwa ta yi masa ya miƙo hannu sai ya kamo ta ya sanya ta a jikinsa sun daɗe a hakan kafin ya ce mu je falo ki ci abinci in ji Aunty. Ta kaɗa kai ya sake ta sai suka fito falon tare da Auntyn suka ci abincin shi yana gamawa ya ce zai je ya yi barci bai fito ba sai La’asar gidan ya bari sai dare ya dawo shi da abokinsa Usman.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Shirin Allah 18Shirin Allah 20 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.