Zura mata ido ta yi cikin tunani. Da ta gaji da kukan sasan iyayenta ta yi, ta wuce Innarta tana yan ayyukanta, ba ta tayar da kai ta dube ta ba gadon Innarta ta haye tana share hawayen da suka ki daina gudu kan fuskarta.
Lokaci lokaci Innarta tana shigowa ta dauki abin da ya kawo ta ta fice ba ta ce mata ki ci kanki ba. Har ta ri ga ta saba da rashin kulawar da take fuskanta daga Innar ta ta idan tana yi wa Innawuro kukan Innarta bata son ta, sai ta kwabe ta da cewa “Kul! Ba son ki ne ba ta yi ba, kara ce da kawaici irin namu na Fulani. Sai Hamida ta ce to ke ba kina wa ya Aliyu magana ba? Murmushi Innawuro ke yi ta ce “Ai Gadanga ba na fari bane, sai da na yi hudu suna mutuwa, sannan shi shi kadai Allah ya bari.
Innawuro kanwa take wurin kakar Hamida wadda ta haifi mahaifiyar ta, ita kuma ta riki mahaifiyar Hamida sakamakon rasuwar yayar ta ta, da ta tashi hannun Innawuro Iro kanen Malam Audu(mahaifin Hamida) ya ce yana so suka yi musu aure ta zauna gida daya da Innawuro.
Haka kannenta suka dawo Islamiya suka kewaye ta suna tambayar ta me ya same ta? Baban ta da ya shigo shi rarrashin ta ya yi ta yi da alama Malam ya fada mishi, ita dai Innar tana sauraren su.
Da daddare suna zaune a daki su biyu Innawuro da Hamida. Lallashin ta take ta tashi ta sanya ma cikin ta wani abu, don rabon ta da kai wani abu bakinta tun kafin labarin tafiya da ita kano ya riski kunnuwanta. A haka Aliyu ya shigo ya same su, ya tambayi Innawuro abin da ya faru da Hamida, ta maida mishi yadda aka yi, shiru ya yi kafin ya ce “Ya ma za a yi hakan ya yuwu? Bari in je wurin Malam din. Ko da ya samu mahaifinsa da korafin ya za a yi duk tarin yaran da ke gidan nan Gwoggon tasu ta ki zaben kowa ta raba Innawuro da Hamida, kuma kowa ya san ita kenan gaban ta, aka dauke mata ita ya za ta yi?
Karshe ya kare da rokon mahaifin nasa da ya roki Gwoggo Indo ta canza Hamida da wata yarinya daban, a bar Innawuro da jikarta.
Shiru ya yi yana sauraron dan nasa cikin yarda da zantukan da yake fadi, sai dai ba zai iya mishi abin da yake son ba. Gyaran murya ya yi kafin ya shiga yi wa dan nasa bayanin da ya sa dole ya koma wurin Innawuro jikinsa a mace yana taya ta rarrashin Hamidar yana yi kuma yana ba Innawuro hakuri, don su biyun duka tausayi suke ba shi.
Matarsa Uwani ta gaji da jin shiru don dawowar sa kenan, kaya kawai ya tube ya taho gaida iyayen sa, ta biyo shi, Zama ta yi ta gaishe da Innawuro. Ganin yadda su su biyun suka tasa Hamida sai wani rarrashin ta suke ya kona ranta, ta dai daure ta hadiye malolon bakin cikin da ya taso mata, ta tambayi abin da ya same ta. Innawuro ce ta yi mata bayani, wani farin ciki ya ziyarci zuciyarta, Allah ya kai kaya masauki ta fadi a cikin ranta, amma sai ta fuske ta ci daci ta shiga nuna alhinin ta, gajiya ta yi da zaman ganin ba shi da niyyar tashi ta fita ta koma part dinta.
Innar Hamida ta shigo dauke da kwanoni, gaban Innawuro ta duka ta ajiye, yi ta yi kamar ba ta ga me suke ba, za ta juya Innawuro ta kira ta, gargadi ta yi mata idan Hamida ta shigo wurin ta ta lallashe ta. Da kai ta amsa umarnin Innawuro sai ta bar musu dakin.
Da safe ma lallashi Innawuro take ta yi Hamida ta tashi ta harhada kayanta don yau za su tafi.
Sallamar da ake a kofar daki ta sanya su daga kai, Gwoggo Indo ce, ta karaso ciki tana amsa sannu da zuwan da Innawuro take mata, sun gaisa ta yi mata ya taro ya tashi? Kallon Hamida ta yi wadda ke gaishe ta, yadda ta ga kwayar idonta ta koma yasa gabanta bugawa, ” Kar dai ace yarinyar nan ba ta son bi na? Ta raya a ranta, kauda tunanin ta yi ta hanyar yafuto ta. “Zo nan Hamidata.” Ba musu ta ajiye rigar da take ninkewa ta isa gabanta za ta tsuguna ta janyo ta jikinta “Me ya samu idon ki? Shiru Hamida ta yi “Kar dai ba ki son bi na? Nan ma shirun ta kuma yi ta ci gaba “Ki gaya mini abin da yasa ba ki son bi na, idan na ji kina da dalilin da ya fi nawa zan bar ki, kin ji yar diyata? Amma ki yi tunani da kyau duk sauran yan’uwan ki da na dauka ko wacce irin daular da take ciki, irin mazan da suke samu a can su aura.” Da dabara da hila ta samu Hamida ta fada mata ba ta son tafiya ne saboda tana sa ran Malam zai hakura ya bar ta ta ci gaba da karatu. Murmushin nasara ta yi “Yaro man kaza, idan kika bi ni zan sanya ki makaranta ki yi karatun ki ba tare da Malam ma ya sani ba, ko ba ki ga su sauran duk sun yi karatun a hannuna ba? Murmushi ya subuce a fuskar Hamida “Ko ke fa yar diyata, yi maza ki shirya kar rana ta yi mana.”
Da hanzari ta mike duk da dadin da take ji burinta zai cika za ta yi karatu, kasan ranta cike take da alhinin rabuwa da Innawuro da iyayenta da yan’uwanta.
Ta juye ruwan wankanta ta je ta yi, ta fito tana rawar sanyi kasantuwar saman bandakin budadde ne. Ta shiga daki tana shiryawa Innawuro ta shigo ta dan ji sanyi ganin ta hakura tana shiryawa, Gwoggo Indo ta yi murmushi “Kin gan ni da mutumniyar tawa ta hakura ko? Ita ma murmushin ta yi “Ai hakan ya fi.” Suka maida idon su kan Hamida da ke sanya kaya riga da zane ne na atamfarta ta sallah yar rigar ta zauna mata cas! A jiki, hijab ta sanya mai ruwan kasa ta janyo takalminta shi ma na sallar ne ta goge sai ta fita don yi ma iyayenta sallama.
Ta dade tsugune gaban Innarta kamar ba za ta yi magana ba sai kuma ta fara mata nasiha da ta kama kanta banda shashanci, duk wani namiji kar ta saki jiki da shi kai kawai Hamida ke dagawa karshe ta ce ta shiga duk dakunan mutanen gidan ta yi musu sallama a ranta tana ta ma yar ta ta addu’a Allah ya tsare mata ita ya kare mata ita daga duk wani abin ki.
Shigowar babanta yasa Innar ta kauda kai kamar ba ita ke mata magana ba, zama ya yi shi ma nasihar ya yi mata kannenta sun tafi islamiyar safe kasantuwar yau lahadi, kudi ya ciro ya mika mata. Ta fita ta zaga dakunan matan gidan tana musu sallama, ba ta ga Aliyu ba ya yi sammakon fita, da wurin Malam ta yi karshe shi ma nasiha ya yi mata daidai yadda Shekarun ta zai dauka karshe ya sanya mata albarka.
An rako su ilahirin mutanen gidan. Hamida tana kankame da hannun Innawuro har gaban motar da aka zo daukar Gwoggo Indo. Da kyar ta saki hannun ta shiga motar tana mayar da hawayen da suka balle mata kamar sakarai ya kunna famfo, Innawuro ma juyawa ta yi tana share kwalla.
Sun dauki hanya, hawayen Hamida sun tsaya sanadin lallashin da Gwoggon take mata. Sai kallon hanya take duk kuma inda suka tsaya sai ta samu abin da ta saya wa Hamida na ci, kafin barci ya sace ta ta bingire tana kwasar barcinta. Gwoggo Indo ta dubi inda take wani lallausan murmushi ya subuce a fatar bakinta.
Sun shiga Kano ta dabo karfe uku na rana. Wanda ya yi daidai da farkawar Hamida sai kallon birnin take Sharada phase 3 suka shiga, suka rika wuce rukunin gine ginen kamfanoni, wani tafkeken Get direban ya danna horn get din ya bude ya cusa hancin motar zuwa ciki sai mamaki Hamida ke yi wannan wane irin gida ne? Don dai ba za a kira shi unguwa guda ba sai dai gari guda. Sun wuce dogayen gine gine masu kyau da tsari da tun tana kirga su har lissafin ya kwace mata ta yi tagumi kawai.
Wasu rukunin gidaje masu iri daya direban ya tsaida motar a gaban daya daga ciki, suka fito cike da nuna gajiya a fuskokin su, Gwoggo Indo ta kai idonta inda wata dalleliyar mota ke tsaye kusa da inda suka tsaida tasu duhun gilasan motar ba zai ba ka damar gane wadanda ke ciki ba ta bude baki za ta yi magana murfin motar bangaren mai zaman banza ya bude, yarinya budurwa wadda shekarunta ba za su haura ashirin ba ta fito cikin shigar wani yadi mai santsi take dinkin riga da skirt da suka yi dam a jikinta ga ta da ma ma sha Allah komai ya ji sai wani siririn mayafi da ta ajiye a kafadarta, wurin su tayo fuskarta kunshe da fara’a har ta karaso inda suke Hamida da ke tsaye kamar ta kada suruka don mamakin shigar yar’uwar ta ta, ita dai wannan kwalliya ta yammatan zamani da ake yi da sunan wayewa basu taba burgeta ba, ko dan ba ta kai budurwar bane? Dafa kafadarta ta yi “Sis Hamida da ke Gwoggo ta taho? Na ji dadi sosai don na yi zaton Innawuro ba za ta bamu ke ba. Dan murmushi ta yi “Sannu da gida Aunty Aina, mun same ku lafiya? Ta kama hannun Hamida zuwa cikin gidan bayan ta gabatar da Hamida ga mutumin da ya fito a mazaunin direba yana gaishe da gwoggo Indo. Ta ce “Wannan sister ta ce sunanta Hamida.” Aina diyar wan baban Hamida ce, ita tun tana karama kwarai gwoggo Indo ta dauko ta. Sun shiga ciki gidan flat house ne mai kyau sai filin tsakar gida mai dan girma sai wani daki falle daya kusa da filin an daura manyan tukwane a karshen gidan mata hudu ke tsaye a wurin, nan gwoggo Indo ta tsaya don da ma tun suna hanya Hamida ta ji gwoggon tana waya ta ce a hada komai a jira ta sai ta iso.
Hamida ta gaishe su suka wuce ciki wani falo suka shiga ba wani mahaukacin girma ne da shi ba amma an kayata shi da ababen more rayuwa. Kofofi uku ne falon ta ja ta zuwa daya, dakin barci ne babu gado sai katuwar katifa da aka lailaye da shimfida mai kyau, kasa carpet ne mai matukar laushi. Da hannu ta nuna mata kofa ki shiga nan ki yi wanka zan kawo miki abinci.” kai ta daga mata ta shiga don yin wankan ita kuma ta fice. Da ta gama wankan sai ta dauro alwala ta fito ta kabbara sallah tana cikin sallar Aina ta dawo dauke da madaidaicin faranti ta ajiye har sai da Hamidar ta idar “Zo ki ci abinci yar kanwata.” “To Aunty Aina. Da ma can sanin da ta yi ma Ainar idan sun je Daura, ita din mai kirki ce da haba haba da mutane, bata fuska ta yi “Ya kike mayar da kayan da kika cire?
Dan daburcewa Hamida ta yi “Ban ga mai ba ne.” yar harara ta bata “Ba ga kayan kwalliyata can ba.” Hamida ta dubi inda take nuna mata wani dan tebur ne kayan kwalliya ne lodi guda shirye bisa kansa. Tv da ke makale jikin bango ta tashi ta kunna ta bar shi a tashar Arewa 24. Ta tube rigar sai ta isa gaban kayan kwalliyar mai ta murza ta juyo wurin Aina “Aunty Aina ba ki da farar hoda? “Ita kike shafawa? Sai ta daga kai “Ba na shafa ta, amma gobe idan na shiga kasuwa zan sawo miki.” godiya ta yi mata za ta mayar da rigar ta tsayar da ita “Ki sake wasu kayan kawai kin san Gwoggo ba ta son kazanta.” don haka wucewa ta yi inda yar jakar kayanta take ta ciro doguwar rigar atamfa ta sanya ta nufi inda abincin yake jallof din shinkafa ce wadda ta ji kifi da ganye sai juice na kwali, Aina na gefen ta tana danna wayarta, da kammalawarta hamdala ta yi ta koma kusa da Aina ta zauna ta maida hankali kan kallon maimaicin shirin gari ya waye.
Da ta idar da sallar Isha’i tana zaune a inda ta yi sallar ta lalace wurin kallon Aina da ke kwalliya za ta yi bako.
Wata doguwar riga ta sanya da ta kama ta tsam ta fidda duk wata sura ta ta, ta tubke dogon gashinta wanda ke ta sheki tana ma kanta wankan turare suka hada ido da Hamida murmushi ta sakar mata “Yaya dai Hamida? Ita ma ta maida mata murmushin “Kin yi kyau Aunty Aina.” ta ce “Ko? Ta ce Allah kina da kyau sosai Aunty Aina. Yar dariya ta yi mai kamar shessheka “Har na kai ki kyau Hamida? bude baki ta yi “Ni kuma ai kin fi ni kyau. Ni da su Ummi (yaran gidan su) ke tsokala ta kullum, wai ni ce ba ni da dogon gashi da dogon hanci, duk sun fi ni. Ta karashe maganar tana bata fuska, don nuna yadda abin ba ya mata dadi. Wani lallausan murmushi ta kuma saki “Kyale su kin ji karya suke, ko da suka fi ki dogon gashi da hanci ba su fi ki kyau ba suna da nasu kyan ke ma kina da naki, ke naki kyan ma mai ban sha’awa kike da shi.”/murmushi Hamida ta yi kafin ta kai ga magana aka turo kofar da sallama wata yar yarinya ce da ba za ta wuce sa’ar Hamida ba sai dai Hamida ta fi ta tsayi ita kuma ta fi Hamida jiki. Hamida ta duba “Ki zo in ji Aunty. Sai ta juya ta tube hijab din da ta yi sallah sai ta bi bayanta.
Gwoggo Indo suka samu zaune kan daya daga cikin kujerun falon ita da maigidanta Malam Buhari, kasa Hamida ta zauna tana gaishe shi ya amsa cikin fara’a yana tambayar ta mutanen gida, Aina ta fito “Zo mu je ki raka ni Hamida.
Mikewa ta yi ta isa inda Ainar ke tsaye sai ta dan rage murya “Ki yi hakuri Aunty Aina na gaji barci nake ji.”
Murmushi ta yi “Ba damuwa yar kanwata. ” Hamida ta yi musu sai da safe za ta koma ciki Gwoggo Indo ta ce ta kwashe kwanonin da suka yi amfani da su ta mika kitchen, sai da ta kai ta wuce daki. Ta kwanta har ta soma lumshe ido Aina ta shigo da ledoji niki niki