Skip to content
Part 20 of 37 in the Series Shirin Allah by Maryam Ibrahim Litee

Washegari da safe ko da ta yi sallah shirin makaranta ta soma. Wadda Aunty Karima ta ɗorawa alhakin gama abin karin Hamida kafin fitar ta Sch ta zo ta gaya mata ta kammala.

Ta fita zuwa dinning ɗin ta haɗa tea ta zuba agada da ƙwai a flate sai ta koma ɗakin, akan mirror ta ajiye plate ta tsaya tana karyawa tana duban agogo don lokacin tafiyar su ya yi ko me ya hana Abdurrashid fitowa? Turo ƙofar da aka yi da shigowa gabaɗaya ya sa ta kai idonta wurin, a shirye yake ya yi kyau kamar kullum sauke idonta ta yi ƙasa ta yi sai ta soma gaishe shi, ya tako inda take kasa cigaba ta yi da karin sai ta juya bakin gado inda ta ajiye hijab ɗinta da Sch bag ɗinta sai ta dawo ta ɗauki kayan karin nata ya gane nufin ta ta kammala sai ya fice ta bi shi a baya.

A kitchen ta ajiye sai ta bar sallahun idan Auntyn ta fito a ce mata ta wuce.

Yau a makaranta Walida ba ta zo ba Hamida ta rasa yadda za ta yi ta san ko lafiya har sai da aka tashi Abdurrashid ya ɗauke ta ya hau titi ta ce “Yau ƙawata ba ta zo ba.”

Ta gefen ido ya dube ta kamar ba zai yi magana ba har sai da ta fitar da ran zai ce wani abu kafin ya ce “Me ya hana ta zuwa? Cikin damuwa a fuskarta ta ce “Ban sani ba, ko za ka kai ni gidan su in gano? Shiru ya yi bai amsa ba har ya sa cikinta ɗurar ruwa, don sai take ganin ta ɓata mishi ne.
Sun zauna shiru har suka isa barraks ɗinsu.

Suka fito ganin Sojoji ko ta ina ya kayar da gaban Hamida sai dai ganin Abdurrashid tare da ita ya ɗan kwantar da hankalinta, suka wuce Sojoji na ƙasa da shi na sara mishi.

Wani kyakykyawan Office suka shiga wuri ya nuna mata ta zauna shi kuma ya hau kujerarsa Computer yake taɓawa tsawon lokaci kamar ma ya manta tana wurin har zaman ya soma gundurarta.
Knocking aka yi kafin ya bada umarnin shigowa wani soja ne ya shigo sai da ya sara mishi kafin ya ajiye wata jaka da ya ɗauko me ɗauke da kayan abinci.

Sai da ya juya Abdurrashid ya miƙe wurin da ya ajiye ya nufa ya zuba abincin da ke ta turiri, da hannu ya kira ta ta taso kujera ya ja mata ta zauna, shi yana tsaye “Ki ci abincin sosai ina zuwa zan duba wani patient ɗi na.”

Ya faɗi yana tsiyaya mata drinks sai da ya fita ya ja ƙofar ta fidda ajiyar zuciya, cokalin ta kama ta shiga cin abincin a hankali, ta ci ya yi rabin wanda ya zuba mata sai ta sha drinks ɗin ta rufe komai, nan ta cigaba da zama tana kallon TV da ke aiki a Office ɗin.

Ya dawo wata ƙofa da ke a cikin Office ɗin ya buɗe sai ya shiga ya kira sunanta, a hankali ta taka ta same shi gado ne ƙwaya ɗaya rak a ɗakin yana kwance a kai, ganin ya tuɓe kayan jikinsa ya sa ta sunkuyar da kai hannuwansa ya buɗe “Zo nan.”

Ta ji muryarsa kan nata na sunkuye ta ƙarasa gaban gadon “Ki zo nan.” Ta ji ya kuma maimaitawa ta tayar da kai ta dube shi sai ta ga inda yake nuna mata ta zo ɗin ƙirjinsa yake nunawa da hannu ba ta da zaɓi dole ta taka ta kwanta kan ƙirjinsa ya kai hannu ya cire hijab ɗin jikinta da ƙyar ya samu ya cire rigar don yadda ta kamata ta ƙanƙame jikinta a jikinsa kasantuwar ba komai jikinta sai rigar, ya shiga sha’aninsa ya yi nisa komai ya kwance masa wayarsa ta shiga kukan neman agaji bai kula ta ba har sai ta katse ta kuma ɗaukar kuka a kasalance ya kai hannu don kashe ta gabaɗaya, idonsa ya yi arba da sunan Aunty gyaran murya ya yi don saita kansa ya ɗaga wayar “Lafiya Abdurrashid har yanzu ba ku dawo ba? Ya jiyo muryarta cikin damuwa. “Lafiya lau Aunty na biya barrak ne, muna nan dawowa.”
Kamar za ta ƙara magana sai kuma ta yi shiru “Sai mun dawo Aunty.”

Ya ce cikin muryarsa da ba ta gama dawowa daidai ba yana shafa sumar Hamida da ke hawaye don azabar da take ji wadda ta kasa banbance ta da ta ranar farko.

Aunty ta yi zaune saƙare da waya a hannu cikin tunani kiran Aunty Zainab ya shigo wayar ta ɗaga suna gaisawa da tambayar lafiyar iyali Aunty Karima ta kada baki “Ita Momi me cewa a ɗauko matar Abdurrashid kar ya kashe musu ‘ya, to kiran da ki kai min zaune nake ina jimami, tun safe da ya fita da yarinyar nan zuwa makaranta har yanzu bai dawo da ita ba.”

Dariya Aunty Zainab ta yi “Kin ji ki za ki damu kanki da gangan, kina biyewa Momi sai ma ya biyo ta har ɗakinki idan ba ki mayar masa da mata ba za ki gane Allah da girma yake.”

Dariya suka yi Aunty Karima ta ce “Ni dai umarnin Momi nake bi.” Ta ce “Ai sai ki yi ta bi ki takurawa ɗa na, bawan Allah ya kusa tafiya ku bar shi da matarsa sai ku wani ɗauke masa ita.”

Aunty Karima ta yi dariya tana jinjina kai. Suka canza hirar zuwa ta wajen birhtday ɗin da yarinyar Aunty Safiya za ta yi wani satin.

Bayan dogon lokaci Abdurrashid ya sarara wa Hamida bathroom ya shige yayin da ita kuma ta dunƙule wuri ɗaya wani barci na fizgarta.

Ya fito yana goge kansa da tawul bai tashe ta ba, kintsa kansa ya yi sai ya fice.

Ta ɗan jima kwance kafin ta yi ƙarfin halin tashi zaune sai ta miƙe a hankali ta shiga bathroom ɗin, wankan tsarki ta yi sai ta kuma yin wanka ta fito unifoam ɗinta ta mayar kasa fita Office ɗin nasa ta yi ta zauna bakin gadon don kunyar abin da ya faru tsakanin su.

Ta daɗe zaune sai ga shi ya shigo “Zo mu tafi.” Abin da ya ce mata kenan ya juya ta tashi ta bi shi a baya bayan ta ɗauki Sch bag ɗinta har inda ya adana motarsa.

Sai da ya hau titi ya ce “Ina ne gidan su ƙawar ta ki? Ta faɗa mishi Goron Dutse ƙofar waika sai da ya shiga ƙofar waikan yake tambayar ta inda zai riƙa bi ta yi ta nuna hanya har suka kai gidan.

A hankali ta buɗe ƙofar ta fita zuwa cikin gidan mahaifiyar Walidar ta samu a tsakar gida tana shara ta tari Hamida da murna tana amarya ce a gidan namu? Hamida dai sai murmushi take ta tambayi Walida da hannu ta nuna mata ƙofar ɗaki ta ƙarasa da sallama Walida na kwance saman kujera da wayarta a hannu ta ɗago tana duban Hamida “Ke kuma daga ina a haka a yammacin nan kuma da unifoam?

Na zo ne in duba ko lafiya ba ki je makaranta ba, wai me ya faru?

Hamida ita ma ta jera mata tambayoyin don ta samu kauda tambayar da ya yi mata “Ciwon kai na tashi da shi amma na ji sauƙi Amarya, na ga har kin fara ƙyallin goshi.”

Hamida ta kama baki “Ban son sharri Walida.”

“Allah ba sharri ba ne kin ƙara kyau a ‘yan kwanakin nan.

Fuska ta taɓe “To na ji.”

Sun ɗan zanta Hamida ta miƙe sanin Abdurrashid na jiran ta ta yi wa mahaifiyar Walida sallama suka fita tare ta gaishe da Abdurrashid ya amsa sau ɗaya sai ya kauda kansa, Hamida ta buɗe ƙofar ta shiga ya ja motar tana jiran jin ko zai mata faɗan shanya shi da ta yi sai ta ji shiru har suka isa.

Ita kaɗai ta shiga part ɗin Aunty Karima shi na shi wurin ya wuce, ba ta ga Auntyn ba har ta shige ɗaki unifoam ta fara tuɓewa ta sauya da wata doguwar riga ta atamfa ba ta ɗaura ɗankwalin kayan ba wani siririn gyale ta rufe kanta.

Knocking ta ji ana yi ta ba da umarnin a shigo cikin masu aikin Aunty Karima ce ta ce ta zo ne ta kwashe kayan datti ta ce suna laundry ta wuce kwasowa Hamida ta fito bayan ta tambaye ta inda Aunty Karima take ta ce tana ɗakinta.

Sai da ta yi knocking ta zo ta buɗe sai ta ga Hamida hanya ta ba ta ta ce ta shigo kujerar da ke ɗakin ta nuna mata ta zauna tare da gaishe da ita, bayan gaisuwar shiru ya biyo baya sai Auntyn ta miƙe mu je falo suka fito suka zauna suna kallo har sai da aka yi kiran sallah suka miƙe don zuwa bada farali, sai da aka yi sallar Isha’i Abdurrashid ya shigo bai daɗe ba magana kawai suka yi da Aunty Karima ya bar sashen.

Da wuri Hamida ta kwanta don wani barci da ta ji tana ji. Da asuba ko da ta yi sallah anan inda ta idar da ta kuma ɓingirewa sai ji ta yi ana ja mata ‘yan yatsu, kafin a hankali ta buɗe idonta, Abdurrashid ta gani tsugune gabanta cikin shiri yake na wani lallausan yadi da hular da ta zauna a kansa sai ƙamshi yake.

Ta yunƙura ta tashi zaune tana gaishe shi ba tare da ta yarda sun haɗa ido ba “Daura zan tafi in yi godiya in kuma yi musu sallama.” Saurin wartsakewa ta yi cikin mamakin jin wai Daura ya nufa da safiyar nan.

Addu’ar Allah ya kai shi lafiya ta yi mishi ya ce “Ki tashi ki yi shirin makaranta kar ki makara, Malam Adamu zai zo ya kai ki.”

Tsaye ta miƙe kamar yadda shi ma ya miƙe ya kama hanyar barin ɗakin.

Wanka ta yi ta futo ta shirya sai ta lalubo wayarta Innawuro ta kira sai dai har ta ƙari ɓurarinta ba a ɗaga ba sai ta rubuta Text massege ta tura wa Yaya Aliyu kan ya gaya wa su Innawuro Abdurrashid na bisa hanya ya taho Daura.

Ta kashe wayar sai ta fito Sch bag ɗinta da hijab a hannu, ta samu an haɗa mata abin break ta karya sai ta fita inda Malam Adamu ke jiran ta.

Walida ta zo makaranta suna tare har a ka tashi suka tafi tare suka rage mata hanya ganin ba Abdurrashid ba ne.

Dare sosai ya dawo don haka ba su gan shi ba sai da safe Aunty Karima da wuri ta fito don tana so ta ga Abdurrashid da ba ta gani ba a daren jiya, sai da suka gaisa ya ba ta wata ƙatuwar leda da su Innawuro suka haɗo shi da ita ta karɓa ta buɗe tana godiya man shanu ne mai yawa sai ƙwan zabi ta kira cikin masu mata aiki ta ce ta kai kitchen.

Ya dubi Hamida da ke tsaye ya ce su wuce.

Ranar da suka dawo ɗaki Hamida ta shige ta hau gado tana tsefe calabar kanta a haka ya shigo ya same ta yana daga tsaye ya harɗe hannayensa yake ƙare mata kallo, sai duk ta takura yana tsayen har ta gama ya ce “Ki same ni ina mota.” Kai ta gyaɗa sai ya fita fuskarta kawai ta gyara sai ta zura hijab a falo ta samu Aunty ta yi mata bayanin abin da kenan.

Wani hamshaƙin wuri ya kai ta da sai macen da ta isa ke zuwa wurin aka gyara mata kan har ƙafa a ka wanke mata a mota ya jira ta fuskarta ta yi fayau ta ƙara kyau saboda gyaran kan na gwanaye ne.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Shirin Allah 19Shirin Allah 21 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.