Skip to content
Part 21 of 37 in the Series Shirin Allah by Maryam Ibrahim Litee

Ana gobe tafiyar Abdurrashid da daddare ya kwanta amma sam ya gaza barci.

Wayarsa ya jawo ya kira layin Hamida wadda ke zaune tana karatun makaranta, ta ɗauka bakinta ɗauke da sallama “Ki zo yanzu ki same ni.” Ya faɗi cikin dakewa ga mamakinsa ji ya yi kamar za ta fashe da kuka ta ce “Kar Aunty ta gane Hamma.”

“Sai me don ta gane? Ina jiran ki.” Ƙit ya katse kiran tagumi ta rafka da hannu biyu ta shiga tunani.
Ta jima a haka kafin aka turo ƙofar ɗakin saurin kai dubanta ta yi Abdurrashid ne, ji ta yi gabanta ya soma bugawa da sauri “Tashi mu tafi.” Ya faɗi ba alamar wasa a fuskarsa ta miƙe ba ta ɗau komai ba har wayarta daga ita sai wata yar yala-yalan rigar barci mai guntun hannu tsawon ta iya gwiwa sai wata yar mitsitsiyar hula a kanta.

Gaba ya sanya ta yana biye da ita, ta ƙofar da za ta sada ka da kitchen ɗinsu suka bi, suna shiga bathroom ta faɗa kafin ta fito ta hau gado, shi zama ya yi riƙe da laptop dinsa har ta soma barci ta ji an rungume ta abin da yake mata ya sa dole ta wartsake.

Daren dai bai bar su sun samu isasshen barci ba ta yi koke kokenta har ta gaji ta yi shiru da ƙyar ta tashi sallar Asuba da ya tashe ta, tana idarwa gadon ta koma duk da barcin da ke idonta ƙin yi ta yi tana jiran ya shigo ta shaida mishi za ta tafi.

Da ya shigo ta faɗi mishi shiru ya yi sai da ya hau gadon ya janyo ta jikinsa bayani ya yi mata za a riƙa sanya mata rabin albashinsa duk wata ta riƙa yin duk buƙatunta, sai gargaɗin kar ta kula ƙawayen banza ta kuma dage da mayar da hankali a karatunta.

Da ya gama gaya mata barcinsa ya shiga yi yayin da ita zullumi ya hana ta yi har dai ba ta san sa’adda ya yi awon gaba da ita ba.

Zare jikinsa da ya yi cikin na ta ya sa ta buɗe ido Meye tuna abin da kenan ya sa ta fara zare ido tana ganin ya shiga bathroom ta miƙe da sauri har tana tintiɓe ta fice shigar ta ƙofar da ta haɗa sasan Aunty Karima da na shi sauri ta ƙara ta samu ta shige ɗaki sai dai haɗa idon da suka yi da Auntyn wadda ke zaune bisa dinning tana break past ya sa ta tsayawa cak cikin wata irin kunya da nauyi da ta ji sun lulluɓe ta “Ki zo ki karya.”

Ta ji muryar Auntyn cikin kunnanta “Zan yi wanka tukun Aunty.”

Ta faɗi cikin dauriya sai ta cigaba da tafiya.

Wanka ta fara yi ta yi kwalliya cikin wasu riga da skirt na English wear ta rufe kanta da ƙaramin gyale.
Kasa fita ta yi saboda kunyar Aunty Karima har sai da ta aiko mai aikinta kan Hamida ta zo ta yi break fast ta fita tana takawa a hankali kamar mara gaskiya kanta a ƙasa ba ta samu Auntyn a falo ba har sai da ta kusa kammalawa. Goma saura su Momi Binta suka shigo gidan har da Daada sun zo bankwana da Abdurrashid haka ya fito ya samu kakar tasa da yan’uwan mahaifiyarsa dukkan su, mahaifinsa ne dai har yau bai dawo ba.

Kewaye shi suka yi suna ta mishi addu’a har lokacin da zai bar gidan ya yi barikinsu zai fara zuwa inda za su haɗu da sauran abokan tafiyar ta shi cikin su har da amininsa Usman, don haka ba damar yi masa rakiya daga shi sai direba suka bar gidan.

Daada tana ta addu’ar Allah ya tsare mata shi a duk inda ya samu kansa Kowa na gidan sai da ya fito har Mami Mariya da mutanen part ɗinta suna tafiya sai aka dawo kan Daada da ke ta kuka ana ba ta haƙuri har ta sa yayan nata ƙwalla.

Hamida dai tashi ta yi daga inda ta makure ta koma ɗaki sai duk take jin ba daɗi da tafiyar tasa don ta fara sabawa da shi. Tana nan kwance ta yi rub da ciki Aunty Karima ta aiko ta zo su yi sallama da su Daada yau za su koma da ta fito gaban Daada ta tsuguna Daada ta dafa kafaɗarta ” Ki yi haƙuri kin ji wannan yarinya, kamar yau za ki ga ya dawo, ki yi haƙuri kin ji?”

Sai kuma ta fara hawaye Hamidar ma hawayen ta kama sai kuma ta bar na ta kukan tana lallashin Hamida dukkan su kowacce da abin da ta kawo ma Hamida suka ba ta ta yi musu godiya sai da suka raka su suka ga tafiyar su sai suka dawo.

Suna tafiya Hamida daki ta kuma komawa ta kwanta tana jin wani irin ba daɗi game da tafiyar ta shi a haka Aunty Karima ta zo ta same ta sai da ta tashi zaune Auntyn ta ce ta je ta kwaso kayanta a can wurin nasu ta tambaye ta akwai key a hannunta Hamida ta ɗaga kai.

Cikin sanyin jiki ta nufi part ɗin tana buɗe kofar sai ta ji wani iri tana kallon ɗan zaman da suka yi tare da shi a dakin, bakin gado ta zauna ta yi zugum har sai da wayarta ta ɗauki ƙara Hamma ta gani rubuce yadda ta yi saving ɗin no sa kamar yadda yayan yan’uwan mahaifiyarsa ke kiransa.

Cikin rauni ta yi sallama ya amsa mata sai ya yi mata bayanin yanzu haka suna Lagos nan da awanni biyu kuma jirginsu zai tashi. Cikin makyarkyatar murya ta yi mishi addu’a nasiha ya kuma yi mata ta kula da kanta da kuma karatunta har Allah ya dawo da shi.

Kai take ta ɗagawa kamar yana ganinta sun jima kafin ya ce mata ana kiran shi ya katse kiran ta rafsa tagumi da hannu biyu ta daɗe a haka kafin ta shiga ɗibar kayanta sai dai ba duka ba akwati guda ta ɗiba sai ta rufe wurin.

Washegari lahadi Engineer Shehu Bello ya dira ƙasar.

Aunty Karima ta tasa Hamida suka je ta gaida surukin nata.

A part ɗin suka samu Mami shi Hamida ta fara gaida wa kanta na ƙasa sannan Mamin ba su jima ba Aunty Karima ta mike ta biyo ta suka fito, za ta wuce ɗaki Auntyn ta ce ta zauna falo su yi hira idan ta shiga ɗaki tunani ne zai dame ta.

Hakan aka yi nan ta zauna har suka ci abincin rana sai ta shiga daki ta yi sallah ba ta kuma fitowa ba har ta yi sallar La’asar tana zaune inda ta idar da sallar ta yi shiru cikin tunani aka shiga knocking ta daga kai ta dubi ƙofar kafin ta bada izinin a shigo. Cikin masu aikin Aunty Karima ne ta ce tana da baƙuwa a falo ta ce tana zuwa sai ta miƙe ta cire hijab ɗin, ta fita falon don ganin baƙuwar, Gwoggonta ta gani ta karasa da fara’a tana mata sannu da zuwa kujerar da Gwoggon take ta zauna kusa da ita tana gaishe ta.

Sai kuma ta miƙe ta ce bari ta gayowa Aunty Karima zuwan Gwoggon. Tare suka fito suna gaisawa Aunty Karima ta koma ciki. Gwoggo ta dubi Hamida “Mun yi waya da Malam ya ce min mijinki ya je Daura yi musu sallama. Yaushe ne tafiyar ta shi?

Hamida sai ta ji ba ta ji daɗi ba da Abdurrashid bai je ya yi ma Gwoggonta sallama ta ɗago cikin jin nauyi “Ya tafi yau Gwoggo.” Ta yi yar fara’a “Ashe na zo a daidai, kuɗaɗen magungunan da na kawo miki za ki kawo sai kuma cikin kuɗaɗen da ya bar miki ki bani in ƙara jarin.”

Waige waigen da ta ga Hamida na yi ya sa ita ma ta waiwaya ganin ba kowa ta ce “Meye kike yi kamar wata mara gaskiya?

Ajiyar zuciya Hamida ta yi “Gudu nake kar wani ya ji Gwoggo.”

Kafin Gwoggo Indo ta kai ga magana Aunty Karima ta fito cikin shiri ta ce wa Gwoggo ta gaida gida ita za ta fita suka yi mata fatan dawowa lafiya.

Sai da Hamida ta tabbatar da fitar ta ta saki wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya.
Ta miƙe ta cewa Gwoggo Indo tana zuwa ɗakinta ta koma ta fito da Sch bag ɗinta a hannu inda ta tashi ta koma ta zauna ta shiga caje jakar kuɗaɗen ciki ta fitar tuni Gwoggo Indo ta taɓe baki ba dai ta yi magana ba har sai da ta miƙo mata kudin ta karɓa kamar ta karɓi kashi. “Na meye su kuma waɗannan? Hamida ta ɗan karyar da kai na break ɗina ne da yake ba ni.”

Na ji na break ɗinki ne, ina kuma abin da ya bar miki da zai tafi? Koko hakanan ya bar ki salin alin?
Hamida ji ta yi zuciyarta ba ta yarda ta faɗa mata ya ce a riƙa ba ta rabin albashinsa ba. Don haka ba ta yi magana ba sai ƙara marairaicewa da ta yi.

Gwoggo ta yi ƙwafa “Gaskiya da sake hakan ba za ta taɓa saɓuwa ba Allah ya dawo da shi lafiya, dole in saita mishi zama. Amma tafiyar shekaru huɗu ka sa kai ka tafi ba ka bar wa mace komai ba wannan wane irin maƙo ne da hannun jarirai kake da shi?

Hamida dai tuni hankalinta ya fi na ɓarawo tashi don tsananin tsoron da ya rufe ta kar cikin masu aikin Aunty Karima wata ta ji Gwoggo don yadda take buɗe murya.

Ta dai gama sababinta ta miƙe Hamida ta bi ta don ta yi mata rakiya sun zo daidai part ɗin Mami Gwoggo Indo ta dubi wurin “Kin ga baiwar Allan nan ba karamin alheri nake samu da ita ba, amma saboda aurenki da Abdurrashid ta datse cinikayya tsakanin mu. Da aka kawo sababbin kaya na kira ta cewa ta yi in bar shi, kuma ni na san ba inda za ta sayi kaya masu kyau irin nawa.” Hamida dai ba ta tanka ba har ta kai ta bakin get sai ta juyo.

Washegari Hamida tana daki tana shirin makaranta Aunty Karima ta shigo ta yi mamakin hakan sanin ba ta fitowa da wuri bare yau ita ke da mai gidan.

Cikin girmamawa Hamida ta gaishe ta ta yi murmushi “Da ma na ce ba Abdurrashid bari in duba ki kar ki yi latti.”

Ta ɗan sunkuyar da kanta “Na tashi Aunty.”

Ta ce “To ya yi.”

Ta ajiye mata kuɗi saman dressing mirror “Ga shi nan in ji Daddy kuɗin break.” Ta ce “Na gode Aunty, ya fito ne in gaishe shi?

Ta ce “Ki bari idan kika dawo lokacin shi ma ya dawo Office sai mu je ki gaishe shi.”

Hamida ta gyaɗa kai sai ta fita Hamida ta karasa shirin ta ta fita sai da ta karya kumallo ta fita inda Malam Adamu ke jiran ta.

Ba su samu wayar Abdurrashid ba sai da ya yi sati da tafiya lokacin Hamida ta fara sakin jiki da Aunty Karima don yadda take saka ta a jiki duk fitar da za ta yi indai ba Hamida na makaranta ba da ita take zuwa.

Walida kuma tunda Abdurrashid ya tafi sai ta sarfaci zuwa gidan Hamida duk weekend.

Wani dare ta samu wayar Gwoggo Indo Laila ta haihu. Sai da gari ya waye sai ta faɗi ma Aunty Karima Auntyn ta ce sai zuwa yamma sai su shiga barkar ta tambaye ta inda gidan mai jegon yake.
Ita ke driving Hamida da ta sha dogon hijab tana gefenta.

Baban Amir suka fara gani zaune a kofar gida shi da Amir, cikin matukar girmamawa ya gaishe da Aunty Karima

sanin ita ɗin kowace ce.. Tana wucewa ya soma tsokalar Hamida da Amarya ashe ana ganin ku? Murmushi ta yi ta kama hannun Amir suka shiga ciki.

Har Gwoggo indo sun samu a ɗakin mai jegon wadda ta yi ta ina a saka da Aunty Karima.
Sun ɗan zauna kafin suka tashi don komawa gida.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Shirin Allah 20Shirin Allah 22 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.