Skip to content
Part 23 of 37 in the Series Shirin Allah by Maryam Ibrahim Litee

Har wadanda ke ciki suka fito suka shiga cikin gida ba su lura ba.

Isowar Daddy dan wurin Aunty Safiya ya zo da gudu ya ce musu wallahi Hamma ya dawo. Hanan ta dan harare shi “Wuce nan mai karya kawai.”

Yaron ya dan yi narai narai kafin ya hau rantse sai ga yara sun yi hudu da gudu suna fadin Hamma ya dawo cikin suka bi su cike da mamakin ta inda Hamman ya shigo su ba su gan shi ba dan sun manta da motar da ta shigo.

A babban falon gidan kowa na zaune ana ta farin ciki da murna na dawowar Abdurrashid shi din yana zaune tare da abokinsa Usman yadda su Hanan suka gaishe su sai dai ba su zauna ba suka shige ciki Hamida gado ta fada ragwab tana jin ta a wani yanayi wai yau Abdurrashid ta gani da ma zai dawo kamar yadda kullum take kwana ta tashi da tunanin hakan.

Hanan da Mimi sai shegantaka suke mata Hanan na cewa Hamida za ta riga Mimi amarcewa. Sun dade a dakin kafin Aunty Zainab ta shigo “Ku da ma kuna nan ? Ke Hamida mijinki har zai tafi ba ki mishi wata gaisuwar kirki ba.”

Hanan da Mimi suka hada ido “Tafiya kuma Aunty? In ji Hanan”I za su je gidan Daada shi da abokinsa.
Mimi ta ce “Wai yaushe ya dawo?

Aunty Zainab na juyawa ta ba ta amsa “Jiya ya dawo,fito Hamida ki je ki same shi har sun fita.”
Hanan ta kamo hannunta tana jan hanci wai guda take mata ganin ta ki tashi Mimi ma ta kamo dayan hannun dole ta tashi ta fara takawa suna mata sowa.

Abdurrashid da ke tsaye jikin motarsa shi da Usman bayan samun wayar Aunty Zainab da ta ce kar ya tafi ya tsaya Hamida ta zo su su gaisa Usman ke ta magana yana sauraren shi “Wai yanzu duk zuka zukan yammatan nan yan’uwanka ne?

Kai Abdurrashid ya daga mishi “To ina amaryar tamu don ban gan ta ba cikin su (Don ba wani sanin Hamida ya yi ba ganin sa da ita bai fi biyu ba tun kan su tafi ko a hoto bai kara ganin ta ba)
“Tana nan kuma cikin su.” Abdurrashid ya ba shi amsa “Na ga wata a cikin su kallo daya na yi mata ta tafi da ni kuma gaskiya zan gaya maka ina son ta.”

Ta wutsiyar ido Abdurrashid ya dube shi kafin ya kai ga magana Hamida ta tunkaro su ganin dan gyalen da ke jikinta bai boye komai na halitttarta ba ya bata ran Abdurrashid ganin ga Usman a wurin.
Motar kawai ya bude ya fada ya ce ma Usman “Bismillah mu wuce.”

Ta karaso daidai Glass din da yake haramar rufewa ta tsaya ya yi bala’in daure fuska ya dube ta “A haka kike fita kina ganin daidai kike da su Mimi?

Ido ta kada ba ta yi magana ba wanda ya sa ba Abdurrashid ba hatta Usman da ya kafe ta da ido sai da ya ji ya fada wani yanayi.

Ganin ba ta da niyyar magana ya ce “Kauce to za mu wuce.”

Ta juya don komawa ciki Abdurrashid ya hadiyi wani abu don takaicin Usman ya ga bayanta.
Har ya tayar da motar ya bar gidan Usman bai dawo daga kidimar da ya yi ba fahimtar Hamida da ya gani zuciyarsa ta amsa daga kallon farko da ya yi mata ita ce matar amininsa wani zafi kirjinsa ya dauka har suka shiga gidan Daada ba wanda ya yi magana kowa da abin da ke damun zuciyarsa Usman sai mamakin Abdurrashid yake kana da wannan tsaleliyar macen ka yi tafiyar shekaru ka dawo kuma ka bar ta ka kwana kai kadai. Da ya rufe idonsa hotonta ke masa gizo,wani irin yanayi yake ji da bai misalto,a wahalce ya ga wayewar gari.

Har suka shirya suka yi wa Daada sallama suka koma gidan Aunty Zainab don yi musu sallama su koma Kano a yau.

Sun zauna falon Daada inda iyayen ke zaune aka kawo musu abin karyawa duk da sun ce sun karya a gidan Daada suna yar hira sama sama. Hamida da ba ta san zuwan su ba ta fito don shiga kitchen ta samo ruwan zafi ta hada Tea daga ita sai rigar barci kalarta sky blue mai botura a gaba hannunta guntu ne, kanta ba komai sai kwantaccen gashinta da ta kama da ribbon sai da ta ratsa su ta ga Abdurrashid da Usman ta kara da sauri ta shige kitchen din.

Yayin da wani shauki ya dauki Usman wani tukukin bakin ciki ne ya turnuke Abdurrashid ganin Hamida a haka ga Usman zaune.

Kasa fitowa ta yi daga kitchen din har mai aiki ta shigo ita ta aika wurin su Mimi ta ce su ba ta after dress ko hijab, after dress din aka kawo mata ta zura ta rufe gyalen sai ta fito ba ta yarda ta dubi inda suke ba ta shige daki su Hanan na zaune a dakin Mimi, Mimi na danna wayarta Hanan na yan wake wake,ta zauna tana kurbar Tea a hankali.

Abdurrashid da ke zaune ya rasa yadda zai yi ya tashi zuwa dakin da Hamida take sai kallon kofar da ta shiga yake hakika ya zo ne don ya tafi da matarsa amma ya rasa yadda zai dubi idanuwan su Momy ya fada musu hakan.

Da dai ya ga ba shi da zabi rufe ido ya yi ya mike ya ce ma Usman yana zuwa.

Murda handle din kofar ya sa kowacce ta dago ido ganin shi ne kowacce ta shiga nutsuwarta sun fara gaishe shi kafin kowacce ta sulale suka bar dakin suka bar Hamida da ta sunkuyar da kai ganin fitar su ta soma gaishe shi,bai amsa ba sai hannayensa da ya harde a kirji ya sa mata ido “Ke haka kika ga ana tarar miji idan ya yi doguwar tafiya?

Kai ta dago sai suka hada ido ta yi saurin mayar da kan ta sunkuyar “Ka yi hakuri.

Kalmarki kenan a yi hakuri, me ya sa kike fita yadda kike fita ko kin manta igiyar auren da ke kanki?
“Na bari ka yi hakuri.

Ta kuma furtawa a hankali “To ni zan tafi sai kin dawo kenan.”

Saurin duban shi ta yi ganin sun hada ido ta kauda kai, ya juya don barin dakin komai ka sa cewa ta yi har ya fice ya ja kofar.

Tana nan zaune ta ji wayarta ta dauki kara cikin sanyin jiki ta mika hannu ta dauko ta Abdurrashid ne ta daga ya ce “Ki same ni ina waje.”

Kai ta daga kamar yana kallon ta sai ta mike ta tube rigar barcin ta fada bathroom wanka ta yi cikin sauri ta shafa mai ta murza hoda ta dan sa turare,jallabiya baka da gyalenta ta sanya sai ta fita cikin sauri sanin ta bata lokaci.

Wani dan lungu da idan ka fita zai kai ka parking space nan ta bi, Abdurrashid ta hango karshen lungun ya sa gudun numfashinta ya karu ta dai daure har ta isa inda yake ji ta yi ya fizgota ta ya sa ta a bango sai ya matse ta.

*Wai me kike yi min haka? Kin ki fitowa ne don in gaji in tafi? Daga abin da kike min kenan, to na fasa barin ki anan da ke zan tafi.”

Ya fadi cikin rada da sai ita da suke hade kadai za ta iya ji.

Usman da ke cikin mota yana hango Abdurrashid a lungun,ganin ya matse Hamida ya ji wani abu ya danne mishi kirji ya runtse ido cikin matukar takaici.

Hannunta Abdurrashid ya kamo suka fara tafiya inda motar take a baya ya cusa ta ya koma gaba ya zauna kusa da Usman da ke driver seat ya tashi motar ya zurfafa cikin tunani ya ji Abdurrashid na taba mishi kafada kallon shi ya yi sai ya ji muryar Hamida a baya tana fadin ina kwana sanin da shi take ya amsa yana dan tonon ta.

Sun isa Airport sai da suka sayi ticket din Hamida suka zauna har jirgin ya karaso.

Da suka sauka airport na Kano sun samu Baba Adamu yana jiran su.

Sai da suka sauke Usman a gidansa sai suka wuce sabon gidansu suka sauka,alwala Abdurrashid ya yi da shigar su ya wuce masallaci.

Hamida tana ta ta alwala tana jin yana kara burge ta saboda tsaida sallarsa,kafin ta kabbara sallah sai da ta kunna wayarta don tana ganin sun baro gidan Daada ta kashe ta gudun kar a kira ta ta ce me? Baba Abu mai aikin Aunty Karima ta kira ta shaida mata sun dawo ta kawo abinci a gidansu idan sun gama. Tq cilla wayar bisa gado bayan ta kuma kashe ta ta tayar da sallar.

Ta idar tana addu’a Abdurrashid ya shigo kallo daya ta yi masa ganin daga shi sai guntun wando sai ta sunkuyar da kai ya tako inda take hijab dinta ya zare sai ya dago ta ya sa ta a jikunsa ganin yana kokarin cire mata riga ta narke mishi “Yunwa nake ji.”

Yi ya yi kamar bai ji ta ba ya cigaba da shafa ta knocking din da aka fara ya sa ya sake ta ya zauna bakin gado ya dafe goshi da sauri ta nufi kofa don da gaske yunwa sosai take ji.

Ta tari Baba Abu ta karbi babban tray da ke hannunta sun gaisa babar ta yi mata barka da dawowa sai ta juya ita kuma ta isa dinning ta ajiye za ta juya ta kira Abdurrashid ta ji shi bayanta ta bayan ya rungume ta sun jima a haka kafin ya sake ta ya ce ta ci abincin shi ta fara zuba mawa sai ta zuba ma kanta tana ci tana jin idanuwansa na yawo a kanta duk da ta ki daga ido har ta ji ta koshi ta mike ta ture kujerar ya ce “Ina za ki?

Kai ta langabe “Wanka zan yi.”

Ya ce “Haba wane ke yarinya na dai yi hakuri kin ci abinci.

Daga haka hannunta ya kamo zuwa dakinsa bai saki hannun ba sai bisa gadonsa, a ranta ta ce da ne yake dauka ta ,yanzu ko ko da yake soja sai ya yi da gaske ya iya daga ni.”

Nauyinsa ya daura mata yana gaya mata maganganun da suka sa ta runtse ido ya fara nisa wayarsa ta shiga neman agaji,banza ya yi da ita ta har sai da tsinke ta kuma daukar wata karar ya dauko ta da niyyar kashe ta sunan Aunty Safiya ya gani yana yawo saman screen din kasa kashewar ya yi ya daga “Hello Aunty.”

Daga can bangaren ta ce “Ka tafi da doughter ne?

Ya ce I Aunty.”

Yana jin sautin ajiyar zuciyar da ta fidda ta ce “Sai da anjima.”

Ta katse kiran ya cillar da wayar ya dawo kan Hamida wadda ta kashe kunne tana sauraren su.
Komai ya gama kwance mishi wayar ta kuma daukar kara ,wannan karon bai bi ta kanta ba ta yi ta yi tana tsinkewa har Allah ya gajiyar da mai kiran ya hakura.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Shirin Allah 22Shirin Allah 24 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.