Skip to content
Part 28 of 37 in the Series Shirin Allah by Maryam Ibrahim Litee

Tana tafe tana share hawaye har ta isa gidan Gwoggonta.

Ita kaɗai ta samu tana kallo, ta zauna sai ta rushe da kuka. Gwoggon da ke duban ta tun shigowar ta hankalinta ya yi matuƙar tashi ta fara tambayar ta abin da ya faru, cikin kuka ta zayyana mata
auren da za a yi wa Abdurrashid don ba ta haihu ba, har rana an sa.

Hankalin Gwoggo ya ƙara ɗagawa sai haƙuri take ba Hamida ta ce “Na soma amso miki taimako na haihuwa sai ki kama min dariya ki ce ke ƙalau kike.”

Haka Abdurrashid ya shigo ya same su haƙuri ya yi ta bayarwa ƙarshe ya nemi Hamida ta tashi su tafi fafur ta ƙi Gwoggo kuma ba ta matsa mata ba don yadda ranta ya yi mummunan ɓaci, itam ma kamar za ta fashe da kuka.

Da ya gaji ya ce ma Gwoggo ta ƙara ba ta haƙuri zai tafi zuwa dare zai zo su tafi, da safe zai koma Abuja tare da Hamida don ya gaji da waɗannan fitintinun.

Gwoggon ta ce “Idan ka tafi da ita karatun da na ji tana faɗin za ta cigaba fa?

Ya ce “Sai ta cigaba a can.” Ya tashi ya tafi.

Bayan tafiyarsa Gwoggon ta rarrashe ta ta yi shiru har abinci ta matsa mata ta ci.

Yamma liƙis sai ga kiran Hajja Yanah, suna gama gaisawa ta ce “Sai na ji shiru ban gan ki ba ƙanwata.
Ta ce “Wallahi kuwa da ma zan kira ki ban samu fitowa ba, mijina kuma ya zo daga Abuja ya ce gobe zai koma tare da ni can,ni fargaba ta idan na tafi can ya zan yi in samu kayayyakinki? Ga dilka da aka fara min.”

Ta yi murmushi mai sauti da har Hamida ta ji “Kar ki damu ƙanwata a Abuja ma muna da branch, zan turo miki address na wurin, kina shiga Abuja ki nemi wurin za ki samu komai har ma da waɗanda suka fi waɗanda na ba ki.

Daɗi ya kama Hamida ta ce “Na gode Aunty.” Ta ce “Ba komai ƙanwata ni ma na gode.” Suka ajiye waya ta tura wa Hamida lambar da ta ce.

Har takwas Abdurrashid bai dawo ba. Hamida ta shiga ɗakinsu suna yammata har yau komai na nan, kullum kuma sai Gwoggo ta gyara shi tana sauke baƙi idan ta yi.

Ta haye katifar bayan Sheltos ɗin da ta fesa ya baje, barci ya fara ɗaukar ta sama-sama ta jiyo muryar Gwoggo tana kiranta, ta buɗe ido Gwoggon na tsaye “Ki tashi mijinki ya zo ku koma gida.

Ba tare da ta tashi ba ta ce “Don Allah Gwoggo ki ƙyale ni in kwana anan ba na son gidan can.”

Gwoggon ta yi shiru cikin tausayin ta sai ta juya falo inda Abdurrashid ke zaune “Ta roƙe ni in bar ta kar ta koma gidan yau, ko za ka yi haƙuri da safe sai in rako ta ta ɗauki kayan da za ta tafi da su?

Ya yi shiru cikin tunani kafin ya ɗago “Ki yi min izni in shiga in fito da ita Gwoggo.”

Hanya ta ba shi ya tashi ya shige gefen katifar ya zauna yana jan ƙafarta, tunanin ta Gwoggo ce ta dawo cikin marairaicewa ta furta “Don Allah Gwoggo ki tausaya min ki bar ni ko na koma can ba zan iya barci ba.”

Sai kuma ta ji ƙamshin turaren Abdurrashid ɓigit ta buɗe ido amma ba ta juyo ba “Ki yi haƙuri ki zo mu koma, ki yi sallama da Daddy da su Aunty Karima, don sammako za mu yi ki kuma yi parking ɗin kayanki.”

Ko motsi ba ta yi ba ya matso kusa da ita sai ta ji ya kwanta bayanta “Mu kwana nan kenan?

Gabanta ta ji ya buga meye haka Abdurrashid zai yi ? Ko da ta san ba ya jin nauyin Gwoggo ba ta zaci zai iya shige ta ya shigo ciki ba.

Ba ta karaya ba ƙin ko motsi ta yi don ta ga idan ya ji ta ƙi tashi zai tashi ya tafi sai dai har suka kai minti ya yi ashirin ba shi da niyyar tashin sai ma wasannin da ya fara yi da ita “Tashi to mu je.” Ta furta a hankali, zaune ya tashi bai yi magana ba, sai da ta ɗauki mayafinta ta bar dakin ya miƙe ya bi bayanta shi ya yi wa gwoggo sai da safe ita wucewa kawai ta yi.

Suna zuwa gidan sun shiga sun yi wa Daddy da Aunty Karima sallama ba ta tsaya shiga part ɗin Mami ba tana ganin ya karkata zai shiga can ta wuce ta yi tafiyarta, ɗakinta ta shige ta datse shi ma da ya zo ya taɓa ƙofar ya ji ta datse sanin ko ya yi faman bugu ba za ta buɗe ba na shi wurin ya koma ya kwanta.

Ita sai da ta gama shirya kayanta sannan ta kwanta.

Kamar yadda ya ce da sassafe suka bar garin don haka sha biyu na rana sun shiga Abuja.
Sai kallon barrack ɗin Hamida ke yi tana auna banbancin su da waccan ta Kano.

Wasu rukunin gidaje masu kyau ya tsaya kafin tsayawar tasu sai da ya nuna mata wani gidan ya ce shi ne na Usman, kauda kai ta yi ba ta yi magana ba.

Ta yaba da kyan gidan na su an kuma ƙayata shi da komai na more rayuwa.

Kan Sopa ta miƙe tana jin wata gajiya na ƙara bin gaɓoɓinta, sai jin daɗi take sanin Aunty Ainarta anan barrack ɗin take, duk da ba wata jituwa a tsakanin su ta roƙe shi a washegarin zuwan su ya bar ta zuwa gidan Aunty Aina, a murtuke ya ce “Ba yau ba.”

Ya dai yi mata bayanin mai mishi kula da gida Namiji ne, amma ya sallame shi saboda zuwan ta. Sai dai zai nemi a samo musu mace ko dan makaranta da za ta koma.

Ya fita sai ga Jamilar Usman ta zo mata wuni tana ta murna da dawowar Hamida, yamma sosai ya zo suka tafi. Da daddare Abdurrashid ya ce ta shirya gobe zai turo akai ta gidan Momi, idan ya tashi aiki sai ya je su dawo. Tana gidan Momin ta samu wayar Aina ta ce ta zo ba ta nan, kunya ta kama Hamida ta ce “Ki yi haƙuri Aunty Aina, jiya na tambayi zuwa gidanki ya ce sai weekend. Ta ce “Allah ya kaimu.”

Kafin wucewar ta sun yi maganar ci gaban karatunta da Momi Binta.

Ta yi ta samun baƙi har satin ya ƙare

Sai ranar Lahadi ta samu Abdurrashid ya ce ta shirya su je gidan Aina duk da ba ta samu wunin da ta so ta yi ba don sai La’asar suka fita dole ka gan su su ba ka sha’awa, Hamida cikin atamfa take ɗinkin riga da skirt da suka zauna dam a jikinta sai mayafi da ta sa iya kafaɗa wanda ba mai duhu ba ne ya bayyana kwalliyarta,jelar gashinta ta ɓullo kan kafaɗarta. Ga ƙamshinta da ke sukurkuta Abdurrashid yana tashi.

Shi kuma ƙananan kaya ya sanya da suka yi matuƙar amsar sa. Sun jero suna hira kamar sababbin amare, akwai ‘yar tafiya tsakanin gidajen su da na su Hamida.

Aunty Aina ta tare su da murnarta. An cika musu gaba da kayan maraba da baƙo, sun ɗan zauna ta ce su zo su gaishe da Brigadier yana falonsa. Ita ta yi musu jagora yayin da Hamida ta zauna bayan yin sallamarsu Abdurrashid sara mishi ya yi, Aina ta nuna Hamida “Yau dai ga ƙanwata Hamida da ba ku taɓa haɗuwa ba.” Ya yi murmushi “Gaskiya kam.” Hamida ta gaishe shi asalin ƙato ne baƙi mai ƙaton tumbi kamar mai tsohon ciki. Hamida sai ta ga har ya fi kyau a hoto kan yadda ta gan shi a fili, duk tsawon shekarun nan Allah bai taɓa haɗa su ba don ba mutum ba ne mazauni har kuma wurin Abban Abdurrashid yana zuwa ba ta taɓa katarin ganin shi ba. Bai da muni a fuska sai dai baƙi.

Sun koma falon Aina Abdurrashid bai zauna ba ya ce zai dawo anjima. Sun yi ta hirar su yaran Aina na maƙale da ita, da brigadier zai fita sai ga shi har falon Aina daga shi sai shirt da baƙin dogon wando,ya zauna yana jan Hamida da wasa ita dai nauyin shi take ji ya miƙe kuɗi masu nauyi ya ba Aina ya ce ta bai wa Hamida, ta yi godiya amma ƙasan ranta tana jin kuɗin sun yi yawa.

Jamilar Usman tana ta mita da ciwon baki ta waya ta ƙi zuwa gidanta, dole ta daure ta je kamar tana kan ƙaya haka ta ƙosa ta bar gidan don kar Usman ya dawo ya same ta.

Tuni Hamida ta saba da zaman Abuja. Ta je shagon Hajja Yanah na Abuja, ƙwarai take jin daɗin abubuwan da take saye a wajen, domin dai yanzu ta san ta ƙara matsayi a wurin Abdurrashid, fushi da ita yanzu bai iyawa tuni ya daina dogon fushin duk laifin da za ta yi masa, hakan ya sa ba ta jin ƙyashin kashe ko nawa ne ta saya.

Tana zumunci sosai da Momi da iyalanta musamman Hanan da suke aminai.

Ga shi ta samu ta ɗora karatunta, ranar da bata zuwa makaranta za ta je gidan Aina don Brigadier ya tambayi Aina me ya sa ƙanwarta ba ta yawan zuwa? Ta ce tana zuwa makaranta kuma mijinta ba ya yawan barin ta fita..Ya ce “Zancen kawai, duk garin nan tana da wanda ya fi ki ne? Zan yi mishi magana.” Har office ya kira Abdurrashid ya yi mishi faɗan hana zumunci tsakanin yan’uwan biyu,hakan ya sa duk san da Hamida ta so zuwa ba ya hana tIdan ta je kuma idan Brigadier na gida falon Aina zai zo ya zauna Ainar kan ce mata “Janinki ya haɗu da na Brigadier, ga sunƙin kuɗi ba fashi ta zo sai ya ba ta.

Hamida ba ta ƙara jin ɗuriyar auren Abdurrashid har sai da wata rana ta saci jin yana waya sai faɗa yake kan shi fa ba dole, don babanta ya kuma ɗaga waccan ranar da ya sanya shi meye na shi? Su suke abin su, in ma shekara goma zai ƙara kan waccan ɗayar da ya sanya da farko matsalar su ce. Da ta gama ji ta ji ba daɗi amma sai ta manta kawai.

Lokaci na ta shuɗewa wata uku ya rage ta kammala karatunta da wani hantsi ranar ba za ta shiga Sch ba.

Zaune take gaban mirror ta fito wanka shafe-shafenta take yi kafin ta yi wa fuskarta kwalliya,da ta ji ta ɗauki ƙamshi mai daɗi sai ta miƙe ta ɗauki kayan da za ta sanya daga inda ta turare su, doguwar riga ce ta atamfa ta kafa ɗaurinta jin shigowar saƙo daga wayarta ya sa ta kai hannu ta ɗauki wayar saƙon daga Aunty Aina ne take shaida mata ba ta jin daɗi in ba ta komai ta zo. Hankalinta ta ji ya ɗaga Aunty Aina ba lafiya? Mayafinta ta ɗauko ta yafa, saƙon kar ta kwana ta tura wa Abdurrashid ta nemi izni za ta gidan Aunty Aina ba ta da lafiya.

Har ta zo waje tana rufe gidan kiran shi ya shigo jikin Ainar ya tambaye ta ta ce sai ta je ta gano.
Mota ta ɗauka don ta isa da wuri. Tana parking fitowa ta yi ta shiga ciki, ba ta gamu da kowa ba cikin masu aikin Ainar, har ta isa falon Aina ganin ba kowa ta wuce bed bedroom nan ɗin ma shiru sai ta yi tunanin ta kewaya ne zama ta yi don ta jira ta sai ta ciro wayarta tunanin kiran wayar Ainar ya zo mata ta kira lambarta, jin ringing ɗin wayar na tunkaro ta ta katse kiran tana jiran ta shigo, sai dai a maimakon Aina mijinta ne ya shigo, gaban Hamida ya yi mummunan faduwa ganin daga shi sai guntun wando murmushi yake mata yana shigowa kuma ya mayar da ƙofar ya rufe tumbinsa yake shafawa yana ci-gaba da murmushi.

Tsaye ta miƙe “Ina Aunty Aina? Ta tambaya kamar za ta fashe da kuka.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Shirin Allah 27Shirin Allah 29 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.