Skip to content
Part 31 of 37 in the Series Shirin Allah by Maryam Ibrahim Litee

Duk da lugude da ƙirjinta ke yi bai hana ta isowa gaban shi ta zauna a ƙasa ba.

Irin Video da aka tura mata shi aka tura mishi “Ranar wanka ba ɓoyon cibi Hamma, yau zan gaya maka abin da na daɗe ina ɓoye maka.”

Ta yi shiru, bai ko motsa ba ballantana ta sa ran zai tanka ta ci-gaba ta ba shi labarin tun farkon abin da Usman ya yi mata a haihuwar yar shi Hamida, har zuwa wanda Brigadier ya yi mata har kawo yaudarar da Walida ta yi mata ta kai ta Hotel da ganin da ta yi musu su uku Usman Walida da Brigadier a ɗakin Hotel har kare tan da Allah ya yi tana period a ranar, sai saƙon da aka turo mata yanzu fitar shi.

Wayarta ta buɗe ta ajiye mishi kusa da shi ɗaukar wayar ya yi ya tashi zuwa ɗakinsa.

Ta ɗauki awanni a wurin har lokacin sallah ya yi, Abdurrashid bai fito ba ta je ta yi sallarta ta shiga kitchen ta gama girkin ta je tana ƙwankwasa ƙofarsa shiru bai buɗe ba ta gaji ta koma ta zauna jugum har La’asar Abdurrashid bai fito ba ta miƙe ta sake komawa ta buga ya fito bai ko kalli inda take tsaye ba ya raɓa ta ya wuce.

Sai tara na dare ya shigo shi ɗin ma bai saurare ta ba ɗakinsa ya shige ya datse, tashin hankalinta ta ji ya nunku me Hamma ke nufi da ita shirin kwanciya ta yo ta zo ta murza ƙofarsa a datse take ta buga ta koma ta tsaya jin shiru ta gane ba shi da buƙatar ta, ta ja ƙafa falo ta koma ta zauna kan carpet nan ta kwana.

Da ya fito sallar asuba nan ya wuce ta inda ta ɓingire bayan raba dare da ta yi a zaune.

Tana farkawa ta miƙe zuwa ɗakinta sallah ta gabatar ta san ba za ta zolayi kanta ba ta ce za ta kwanta ta yi barci daga ta san ba ɗaukar ta zai yi ba, samun kanta ta yi da yin wanka ta gyara jikinta wata doguwar rigar material ta saka wayarta tana hannun Abdurrashid sai ta rasa abin da za ta yi ya ya ɗan ɗauke mata tunanin halin da take ciki.

Motsin ƙofa da ta ji ya sa ta ɗaga kai “Ina kwana? Ta ce tana duban sa.

“Lafiya, ki shirya mota za ta iso ta kai ki gidanku, ki je ki zauna har sai na gama yanke hukunci kan wannan abun.”

Wani irin duka ƙirjinta ya yi ta sunkuyar da kai ya juya sai ya bar ɗakin wasu hawaye suka fara gudu kan kuncinta, ta daɗe zaune tana kuka shi kenan sun ja mata sun kashe mata aure.

Ta jima cikin halin zubar hawaye ƙarshe ta miƙe ta shiga tattara kayanta duk wani abin amfanin ta ta ɗauka ta fito falo ta samu mai aikinta ta zo, sallamarta ta yi da alheri mai yawa ta ce tafiya za ta yi, haka ta juya cikin alhini don ba ƙaramin daɗin Hamida take ji ba.

A hankali ta janyo akwatunan da ta sanya kayanta, waɗanda za su yi tafiyar tare sojoji ne guda biyu suka riƙa ɗauka suna sakawa a boot suka shiga gaba tana baya direban ya ja motar suka bar barrack ɗin.

Lokaci lokaci tana share hawaye wayar da ta ji ɗaya daga cikin su na yi yana faɗin ya yi tafiya zuwa Kano ya sa ta gane Kano Abdurrashid ya ce su kai ta. Sai ta ce Daura za su.

Daga Abuja zuwa Daura tafiya ce doguwa don haka kafin isar su gajiya liƙis Hamida ta yi.
Ko da suka isa ba ta yarda ta furta komai ba ɗakin Innawuro ta sauka kamar yadda ta saba sai washegari suna karyawa da safe ta kwance wa Innawuron komai, tsananin tashin hankali Innawuro ta shiga ta sa aka kira iyayen su Hamida cikin su har da baban Hamida, ta kwance musu abin da ya kawo Hamida daga mai salati sai mai riƙe kai sun kiɗime sosai da wannan masifa da ta faru da ita.

Zama suka yi suka tattauna kan wannan magana su bar ta iya nan ko iyalansu kar wanda ya faɗi ma wa, sai Gwoggo Indo ita kaɗai za a yi ma waya ta zo a shaida mata a kuma faɗa mata ta kama bakinta don ba zancen da za a bari wani ya ji ba ne, yadda za a yi shi daban yadda za a juya shi daban ƙarshen ta a ɓata sunan Hamidar, su zauna su saurare shi har san da zai gama binciken in kuma Malam ya dawo sai su saurari abin da zai yanke.

Saboda idon Baban Aina kowa ya yi shiru kan abin da Brigadier ya yi sai shi ya ɗauki waya zai kira Aina ya faɗa mata yan’uwansa suka hana shi.

Haka taron ya tashi kowa jikinsa a mace ran shi a ɓace.

Suna fita Innawuro ta aika kiran Innar Hamida sai da ta zauna ta kwance mata abin da ya faru da Hamida, duk da tashin hankalin da ta ji ɓoye komai ta yi a ranta ta jajanta.

Innawuro ta tashi ta ɗauko kuɗaɗe ta dawo kusa da Hamida ta zauna “Ki yi haƙuri kin ji Hamida? Jarabawa ce kowane bawa da ta inda ake jarabtar shi ki koma wancan ɗakin ki yi zaman ki.”(Da yake an mayar musu Three bed bedroom flat bayan tanƙamemen falon da aka zuba musu komai na more rayuwa Malam an mishi bedroom ɗinsa Innawuro an mata two bedroom).

Ba tare da mun zauna ɗaki ɗaya na takura miki ba. Wannan kuɗin Muzanbilu zan kira a zo a gyara miki Ac da aka sanya a ɗakin, a lokacin Muzanbilun ya ce ko me za a yi mata ta fara bada sanyi ba mu koma ta kanta ba ni da Malam.”

Nan ma ta sa aka kira mata Muzanbilun a waya abin da Hamida take ci da sha ta matsa mata ta faɗi ta bayar aka sawo.

Zuwan Aliyu shi ma lallashi sosai ya yi wa Hamida ya fita ya yo mata sayayya mai yawa kafin ya yi musu sallama don shi ya koma gidan da Engineer ya gina ma Malam.

Gatan da aka nuna mata ya sanyayar da ranta tafiyar Aliyu sai ta shiga ɗakin da Innawuro ta ce ta zauna gado ne da mirror da wardrobe yan waje sai tafkekiyardardumar da aka shimfiɗa saman tayels, labulayen ma na alfarma ne.
Ta fara tuɓe kayan ta ji kaya-kaya ana sallama da shigo da wani abu ƙannenta ne da ƙaramin fridge wai Babansu ya sawo mata suka juya suka shigo da ruwa da drinks ɗin da Innawuro da Aliyu suka sawo mata. A sanyaye ta ce su ce ma Baban ta gode.

Bayan fitar su ta kwanta bisa gadon tana tuna rayuwa, Hamma bai yi mata adalci ba. Ta janyo pillow ta rungume ta daɗe cikin tunani na baƙin cikin halin da take ciki kafin barci ya yi awon gaba da ita.

Washegari sai ga Gwoggo Indo da aka yi ma waya aka ce ta zo.

Zuwan ta zama suka yi ita da yan’uwanta aka kuma tusa maganar a gabanta, ranta ya yi mummunan ɓaci ta dinga surfa faɗa ana tausar ta ta ce “Aikin banza aikin wofi da zai turo yarinya gida bayan ya san ba laifin ta ba ne, in ma rabuwa zai yi da ita ai ba haihuwa ta yi ba miji wanda ya fi shi za ta samu ta aura.

Da ma ni tun auren shi da ita haƙuri nake me yake ba ni?

Innawuro ce ta taɓo ta sai ta waiwayo tana duban ta “Ke me batun raba aure tun da ba ki raba ba sai yanzu da abin nema ya samu.”

Kallon rashin fahimta ta yi wa Innawuron “Ban gane ba? “Ki kalli yar taki da kyau, ba ki ga addu’ar mu ta ci ba?

Gaban Hamida ya buga me Innawuro ke nufi?

“Kar dai ki ce min ciki gare ta? Gwoggo ta tambaya tana fidda ido.

“Ya wuce wai da kin dube ta kin san ba ita kaɗai ba ce.”

Gwoggo ta miƙe har tana neman yadda zane “Shi ne ba ki faɗi ba Hamida, Wannan abin farin ciki haka?

Kunya ta lulluɓe Hamida cikin ƙarfin hali ta ce ita wallahi ba ta sani ba.

Gwoggo ta tafa hannu “Ba ki sani ba sai ka ce wata yarinya? Bari in je a nemo mota mu je asibiti a gwada.” Gwoggon ta faɗi tana ficewa ɗakin.

Ba a jima ba ta dawo ta ce Hamida ta ɗauko mayafinta.

Wata asibiti mai zaman kanta suka je don haka ba wani ɓata lokaci suka ga likita gwajin jini aka yi mata inda aka tabbatar musu tana ɗauke da ciki har ya shiga wata na uku. Ai kuwa suna dawowa tun daga tsakar gida Gwoggo ke rafka guɗa abin da ya ja hankalin mutanen gidan, kafin ka ce me zancen ya je kunnen kowa har na gidan ma’aura,wasu ba su bari an kwana ba sai da suka dangano da gidan, ana ta murna iyayen su maza ma sai da suka dawo suka ji Gwoggo ta so kiran Abdurrashid aka hana ta aka ce ta bar shi har ranar da zai zo.

Hamida ba ta samu keɓewa ita kaɗai ba sai da ta zo kwanciya, kayanta kaf ta tuɓe ta tsaya gaban mirror tana ƙare wa kanta kallo ƙwarai akwai canji a tare da ita wanda rashin sa rai bai sa ta taɓa maida kai ba komai nata ya daɗa cika musamman ƙirjinta, al’ada kuwa tun wadda ta yi gamuwarta da su Brigadier har yau ba ta ƙara ba rashin kwanciyar hankalin da take ciki sai ya ɗauke mata hankali ya hana ta tunanin ko ciki ne.

Ta sa tafukan hannayenta ta rufe fuskarta “Allah na gode maka.” Ta furta cikin siririyar murna.

Da gari ya waye ta bada aka sawo mata sabuwar waya da layi sai layinta da take jin alert ta yi welcome back ɗinsa.

Samun cikinta ya ɗauke mata kowanne baƙin ciki ga iyaye da yan’uwa da ke kewaye da ita suna taya ta farin ciki, Aina ma wadda ta yo waya ta yi nauyi sosai a yanzu ta kusa haihuwa.

Ta sa aka kawo ma Hamida waya sai faɗa take mata tahowar da ta yi ba ta sanar mata ba da aka ce matsala suka samu da Abdurrashid da ta zo gidanta ko Brigadier ba zai sasanta rikicin ba sai ta kama tafiya gida.

Hamida ta ba ta hakuri cikin ƙarfin hali don wani mugun takaicin Brigadier da take ji yana taso mata.

Zaman Hamida gida a wannan lokacin ya kusanta ta da Innarta, duk safiya can take tafiya. Mahaifiyarta ba ta da tashar kallo sai su Sunna TV Africa TV 3 inda za su yi ta saka wa’azizzuka na malamai daban-daban anan za ta tafi Islamiyya ta bar Hamida wa’azin za ta yi ta ji, yawan jin wa’azin har ya kama ta ko ta dawo wurin Innawuro shi ta kan kunna.

Watarana aka saka Sheik Aminu Daurawa wa’azi yake kan shigar mata da yadda suke fita a wannan zamani. Jaddada duk matar auren da ta shafa turare ta fita har wani namiji ya ji ƙamshin, to idan ta dawo ta yi wanka domin tamkar ta yi zina ne ya sa Hamida tashi zaune, duniyar tunani ta faɗa ba ta dawo ba sai da ta ji yana faɗin yawaitar zinace-zinace a yanzu mata sun bar hijabi ana shiga ta son rai, domin Ubangiji cewa ya yi mu nisanci zina, shigar bayyana tsiraici kuma tana cikin kusantar zina, kallace-kallacen fina-finan batsa da karatun labaran batsa suna daga cikin manyan fadadi a wannan lokaci da muke ciki.

Tsaye Hamida ta miƙe don jin da take tamkar zazzaɓi zai rufe ta can ƙuryar Innarta ta shige ta haye gado tana jin nadama na rufe ta a rayuwar ta bari boko ya rinjaye ta ta saki komai na koyarwar addininta in banda sallah da ta riƙe.

Take ta ɗora ma kanta laifi kan abin da ya faru da tsakanin ta da Usman da kuma Brigadier tana yarinyar mace kyakkyawa mai cikakkiyar sura mai ɗaukar hankali ga shiga wadda mijinta kaɗai ya halakta ya gani sai muharramanta amma za ta yi ta shiga ko’ina, ga ƙamshi mai tsayawa a rai da ba ta tarar yaushe ya kamata ta sanya.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Shirin Allah 30Shirin Allah 32 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.