Shigowar Aliyu suka gaisa da Abdurrashid, Innawuro ta shaida mishi abin da kenan.
Ya isa ɗakin ya samu Hamida shi ya yi aikin rarashin da har ta haƙura ta tashi ta yi wanka ta shirya cikin riga da zane da dogon hijab ta fito zuwa cikin gida don ta yi sallama da mutanen gidan, ta wuce Abdurrashid da Aliyu kowanne sashe ta shiga sai Allah ya kyauta gaba ake mata da Allah ya kiyaye hanya ta yi tunanin kowa ya ji maganar kenan?
Sasan su ta shiga ƙarshe Innarta na zaune tana kallon tashar Sunna TV sai ƙannenta su biyu, zama ta yi Innar ta ce “Kin tashi kenan? Ai don mijin naki da ke zaune ya hana in shigo in ci miki, Innawuro ke sangartaki.”
Ta tura baki sai hawaye”Ni Inna ba a ga abin da ya yi min ba?
“In an gani fa rayuwar duka guda nawa take? Babu abin da ke isa sai haƙuri, ki yi haƙuri jarabawa ce.”
Nan dai ta yi ta mata nasiha ta share hawaye sai ta miƙe ta tuɓe hijab ɗin ta yo alwala don ta ji an fara kiran sallah sai da ta idar ta murza farar hoda,ta je ta zauna gaban Innarta, haƙuri ta ƙara ba ta da yi mata nasiha sai hawaye ke zubo mata.
Sallamar da Abdurrashid ke yi daga bakin ƙofa bai sa ta motsa ba ya shigo cikin nutsuwa Innar ma ƙara sunkuyar da kanta ta yi ya gaishe ta tare da ba ta haƙuri kan abin da ya faru duk da bala’in kunyar sa da take ji sai da ta yi musu nasiha da su je su yi ta haƙuri, rayuwar aure yar haƙuri ce.
Da ta gama ta tashi ta shige ɗakinta ya yi mata godiya da bankwana, sunan Hamida yake kira a hankali yana faɗin ta tashi su wuce banza ta mishi tana share hawaye, shigowar ƙannenta ya sa ta miƙe ta bar falon tana goge ido, shi kuma ya ciro kuɗi ya ba ƙanenta Jabir ya ce idan sun wuce ta ba a ya miƙe ya bi bayan Hamida.
Mutanen gidan sun fito suna mata Allah ya kiyaye hanya ƙannenta suka saka tsarabar sauri da Innawuro da Innarta har ma da mutanen gidan suka haɗa mata, ta zauna cikin motar tana mamakin wannan zalama ta Abdurrashid da kamar dole sai ya tafi yau tsoron tafiyar dare take saboda hanya da ba ta da kyau, duk lol maganganun da yake mata ba ta ce uffan ba sai can ta ce “Saboda Allah ka san hanya ba kyau meye na tafiyar dare? Ɗan murmushi ya yi mata yana zaro bindigogin da ke jikinsa”Kuma yarinya ba ki ga motar da na ɗauko ba? Kauda kai ta yi a ranta tana cewa “Ka ji shi waɗannan masu kama mutanen ina ruwan su da wani Soja? Sai ta ji yana kiran wayar Aunty Safiya bayan ya gaishe ta ya ce yana hanya bai daɗe da tasowa ba ta yi haƙuri ya so tsayawa amma yamma ta yi. Faɗa ta yi mishi kan tafiyar dare ta ce maza ya iso Katsina, gobe da safe sai su wuce. Inda Hamida ke zaune ya duba sai ya ajiye wayar a gefensa, ita da ba ta san me aka ce mishi ba har ya canza hanya ba ta ce komai ba.
Ganin sun shiga birnin Katsina ya sa ta mamaki a ranta ta ce da ma Katsina zai tsaya?
Ya shiga masarautar Katsina aka kuma kiran wayarsa, har kuma ya yi parking bai gama wayar ba ya fito cikin motar ya jingina jikinta ya ci-gaba da wayarsa.
Hamida ta fita ta kama ɓangaren Aunty Safiya, tana ta shan gaisuwa daga barorin gidan aka yi mata iso kafin aka zo aka yi mata jagora zuwa wani shiryayyen falo da take hutawa, daga inda take kishingiɗe kan kilishi take ma Hamida murmushi da barka da zuwa,ta zauna gefen ta tana miƙa gaisuwa, aka shiga hidimar kawo mata abin tarar baƙi, Abdurrashid ya shigo apple ɗin da ke gaban Auntyn ya ɗauka sai ya zauna daf da ita sai sannan ta tashi zaune gaisawa suka yi cike da bayyana so da ƙaunar da ke tsakanin su.
Suna nan zaune har aka kira sallar magrib, Aunty suka tashi ita da Hamida maimakon inda take saukar baƙinta bedroom ɗinta ta kai Hamida ta yi sallah, ƙaramar yarinyarta ta shigo ta ce mommynta ta ce ta fito su ci abinci, ta ɗaga mata kai sai ta miƙe da hijab ɗin ta fito wani wuri na musamman da aka shirya don cin abinci ta gano su zaune Aunty Safiya da Abdurrashid, ta isa ta zauna kan tattausar shimfiɗar sai ta ƙara gaida Aunty Safiya.
Kowannen su ya zuba abin da yake so amma Hamida ƙamshin da suke fitarwa ma tayar mata da hankali yake saboda Aunty Safiya ta zauna suka zuba har sun fara ci Abdurrashid dai ganin idon Auntyn ya hana shi mata magana sai Aunty Safiyan ce ta ce “Yaya dai Hamida ki zuba mana.”
Ta ce “To.” Ta zuba kaɗan sai dai cin ya gagara ta ce “Ko akwai abin da kike so a yi miki?
Da sauri ta ɗaga kai “Idan akwai tuwo ina so Aunty, na dawa ko na Semo.”
Take Auntyn ta zargi wani abu wanda take fatar ya tabbata.
Kira ta yi ta sa a tuƙa ma Hamida tuwon Semo, suna kuma gama cin nasu abincin ana kawo tuwon su Auntyn suka koma falo ita kuma ta zauna ta ci tuwonta wanda ta ji daɗin shi, da ta gama ba ta zauna inda Abdurrashid da Auntyn ke hira ba wuce su ta yi ta je ta hau gado ta yi kwanciyar ta ba ɓata lokaci kuma barci ya yi awon gaba da ita.
Sama sama ta ji muryar Auntyn tana cewa “Anya Hamida kwanciya da wannan dogon hijabi.”
Ba ta yi magana ba ta gyara kwanciya, kukan wayarta ya tashe ta ta ɗauka ta kai kunne Abdurrashid ne ke faɗa mata ta zo ta same shi cikin muryar barci ta ce ba ta san inda yake ba. Ya ce ta fito za ta gan shi. Ta ce “Haba ga Aunty ya za a yi in fito?
Ya ce “Ba Aunty daga ta bar miki ɗakin, da asuba sai ki dawo.” Ta ce ita dai ya yi haƙuri tana jin kunyar Aunty ta gane ta kashe wayar ya sake kira bai shawo kanta ba ƙarshe ya turo mata text ƙyale shi ta yi ta sanya wayar a silent ta tura ta ƙarƙashin pillow ta shiga barcinta.
Da asuba ko da ta farka sallah ta yi karatun Alqur’ani don akwai complete Quran a wayarta, da azkar da yanzu ya fara zame mata jiki. Sai ta koma saman gado ta koma barcinta.
Ƙarfe takwas ta shiga bathroom ta yi wanka ta yi kwalliya wata doguwar riga ta sanya ɗinkinta mai girma ne don haka ya ɓoye cikin da ba ta so a gani, tana fesa turare Aunty Safiya ta shigo ta ɗan ranƙwafar da kai ta soma gaishe ta ta amsa cikin fara’a ta ce ta zo su je ta gaida mai martaba, suna dawowa suka samu Abdurrashid ya shigo cikin shiri yake Aunty Safiya ta ce “Duk saurin ka dai ka tsaya ku yi break past.”
Kamar jiya ma tare suka yi zaman karyawar cikin ya sa Hamida ba ta iya shan madara sai Lipton ta sha ta ci wani Farfesun kaza.
Suna gamawa Abdurrashid ya ce za su wuce kyautar wasu turaruka Aunty Safiya ta yi wa Hamida.
Sun ɗauki hanya babu mai magana duk da mamakin canjin da ya gani tattare da Hamida na mu’amala da dogon hijab da Safa bai mata magana ba.
Ƙarfe Sha biyu suka shiga Kano. Suna shiga Estate ɗin ta kira Gwoggo Indo ta waya ta ce ta dawo, yana sauraren ta har ta ƙare wayar sai ta dube shi “Ka fara sauke ni wurin Aunty Karima.” Jin bai tanka ba ta ce “Don Allah.”
Can ɗin ya yi horn aka wangale gate ya cusa hancin motar.
Masu aiki na ta mata barka da zuwa ta isa falon Aunty Karima Abdurrashid masallaci ya wuce ta tambayi Aunty Karima suka ce tana bedroom ɗinta.
Can ɗin ta isa ta yi knocking ta ji muryarta ta ce a shigo ta shiga da sallama kwance ta samu auntyn ta tashi zaune da ƙyar, cikin mamaki Hamida ta ce “Ba ki da lafiya ne Aunty?
Ta janyo tissue ta zubar da yawu sai ta yi murmushi “Ai na kwana biyu.”
Hamida ta nuna damuwarta ta yi mata fatan samun sauƙi.
Anan ta yi sallah suka fito falo ana kawo abinci Hamida na buɗewa Aunty Karima ta tashi da sauri tana toshe hanci ta ɗan jima ta dawo Hamida ta yi mata sannu sai ga Abdurrashid ya gaishe da Aunty Karima ya ce Hamida ta zo su tafi, ta miƙe ta yi wa Auntyn sallama da addu’ar samun sauƙi sai ta bi shi a baya, part ɗin Mami da ta ga ya nufa ya sa gabanta bugawa tunawa da Anisa.
Fara’a sosai Mamin ke yi da suka shiga, da suka gaishe ta ba su jima ba ya miƙe sai suka bar part ɗin.
Ba ta yi mamakin ganin falonta fes ba don ta san Abdurrashid na zuwa, a hand bag ɗinta ta ciro keyn ɗakinta sai ta nufi can ya yi ƙura sosai ta fara gyarawa Abdurrashid ya shigo “Ki bari a kira masu aikin Aunty mana su gyara “Ta ce “Zan iya.” Ya ce “To zo mana.”
Ya juya ta ɗan bi bayansa da kallo sai ta taka ta rufe ƙofar bunner ɗinta ta jona sai ta ɗauko turare ta ɗan turara gabanta, ta shafa wata humrarta sai ta fito.
Tana tura ƙofarsa ta hango shi ya yi ɗaiɗai bisa gadonsa, a bakin gadon ta zauna sai hannunsa ta ji ya janyo ta, yana samun nasarar kai ta gado sai ya ɗora mata nauyinsa “Wayyo numfashina.” Hamida ta ce cikin haki, jin nunfashin da take ya sassauta dannetan da ya yi sai ya fara ƙoƙarin raba ta da rigarta, bai sha wahala ba ya cire ta sai bin ta yake da kallo ganin ainahin canjin da jikinta ya samu ba kamar tana da kaya ba, yana zuwa cikinta wani abu ya ji ya buga a ƙirjinsa, hannayensa duka ya sanya kan cikin “Faɗi min da bakinki Hamida, alherin da na daɗe ina roƙon Allah ya ba ni shi na samu kika ɓoye min.
Sai ya sake ta ya sauka gadon ya yi sujjada, ya daɗe kafin ya ɗago ya dawo gadon ya rungume ta tsantsan har sai da ta ƙara cewa numfashina sai ya sassauta mata “Gaya min Hamida tun yaushe ne, wata nawa kenan? Da hannunta ta nuna mishi ya shiga wata na biyar mamaki ya kashe shi yadda aka yi ya kasa ganewa tun tana Abuja. “Me ya sa ba ki kira ni kin faɗa min ba? Ya ce yana kafe ta da ido ta ɓata fuska “Ka kore ni sai in kira ka? Yar dariya ya yi wadda bai faye yin ta ba sai ta ƙure “Korar ki ma na yi? Kunnenki na ja.” Ya faɗi yana jan hancinta.
Tambayoyi ya ci-gaba da yi mata kan cikin tana ba shi amsa abin da ya shagaltar da shi bai samu yin abin da yake ta kwaɗayi ya samu su keɓe da matar ta sa ba, sai kiran sallar la’akari suka ji, tilas ya janye ta daga jikinsa ya shiga bathroom ɗauro alwala.
Ita ma ta tashi ta yi ta ta sallar.
Yana fitowa sallah yan’uwan mahaifiyarsa suka soma kiran sa suna tambayar ya Hamida ba wata dai matsala kansa ya ɗaure bai samu amsa ba sai da Daada ta kira shi hamdala take ta yi da Allah ya sa tun tana raye za ta ga wannan rana Karima da matarsa na da juna biyu tana ta addu’ar Allah ya sauke su lafiya.
Abdurrashid da ya yi shiru yana sauraren ta ya ce “Wai Daada wa ya gaya miki Daada? Ta ce “Karima ta kira ni ta ce yanzu mahaifinka ya kira ta ya ce shi ma yanzu ya samu labari a Daura, Karima kuma jiya ta faɗa mata na ta, yana shiga falo Hamida ma wayar take da su mimi suna murna don gaba ɗaya labarin cikin ya karaɗe family ɗin su har sai da Abdurrashid ya gaji ya ce “Wayar ta isa ina jiranki.” Ya faɗi yana wucewa “Mijina na kira na sai anjima. Ta ce wa Hanan da suke waya a lokacin ba ta saurari sharrin da take mata ba ta bi bayansa.