Wuya sosai ta sha hannun Abdurrashid har sai da ta fara mishi kuka ya sarara mata.
A jikinsa ya rungume ta hannunsa kan cikinta cikin kunnenta yake raɗa mata zancen cikin Aunty Karima, buɗe idonta ta yi daga lumshe sun da ta yi ko da Aunty Karima ta tashi daga ganin abinci ba ta kawo ciki ne da ita ba ta taya Auntyn murna a ranta.
Hira suke a hankali har sai da aka kira sallar magrib ya raba ta da jikinsa ya shiga bathroom.
Ita ma anan ɗakin ta yi sallah don ba ta gyara ɗakinta ba har sai da suka yi sallar asuba tana ganin Abdurrashid ya fara barci ta zare jikinta, ya buɗe ido ya dube ta sai ya mayar ya rufe, ta fita sai ta ja ƙofar.
Ɗakinta ta wuce ta shiga kakkaɓe kakkaɓe da goge goge ta canza labulayya da zanen gado sai da ta ga ɗakin ya yi mata yadda take so sai ta fita zuwa kitchen, tun a jiya aka kawo mata abin da ta buƙata daga wurin Aunty Karima, Abdurrashid ta haɗa ma abin karyawa ita kunun gyaɗa take sha a Daura don ba ta iya shan madara, ta san Innawuro ta manta ta haɗo mata da markaɗaɗɗiyar gyaɗarta don duk abubuwan da take ci ta haɗo mata su. Tana farawa mai taya ta aiki daga wurin Aunty Karima ta yi knocking ta je ta buɗe sai da suka gaisa Hamida ta ce ta gyara falo.
Lifton ta dafa ma kanta sai ta fita kitchen ɗin, wanka ta je ta yi ta gyara kanta sai ta fita zuwa ɗakin Abdurrashid ta samu ya farka yana kwance yana danna wayarsa ta zauna gefen gadon tana gaishe shi sai ya tashi zaune da ta faɗa mishi ta kammala abin break tare suka fito, motsin mai aikin ta ji a kitchen tana gyarawa.
Abdurrashid yana cin abincinsa yana kallon Hamida da ke shan ruwan lipton tsura ya ce “Ba abin da kike ci ne?
Sai ta yi mishi bayanin kunun gyaɗa take sha kuma babu abin yin, ya ce ta nema yau. Ta ce “To.”
Ya kusa kammalawa aka yi knocking Hamida za ta miƙe mai mata aiki ta fito daga kitchen ta je ta buɗe suka dubi wurin don ganin wanda zai shigo Maman Walida ce, haɗa idon su wani abu Hamida ta ji ya tokare mata ƙirji tuna abin da Walida ta yi mata, miƙewa ta yi ta nufi wurin ta ta ce mata maraba ta nuna mata wurin zama sun gaisa fuskar Hamida ba yabo ba fallasa, ta ce “Taimako na zo nema Haj Hamida.”
Cikin mamaki Hamida ta ce “Wane irin taimako? Sai ta fashe da kuka” Hamida ta danne zuciyarta don ji take kamar Walidar ce gabanta ta ce “Subhanallah ya kuma kike kuka Umma? Ta share hawaye “Ƙawarki Haj Hamida.
yau kimanin watanni biyu kenan ba mu gan ta ba ko sama ko ƙasa.”
Hamida ta ce “Innalillahi, ba ku gan ta ba? Ta fyace hanci “Wallahi tafiya ta yi kwana biyu da tafiyarta mun yi waya, daga nan shi kenan ko an kira wayar a rufe take.”
“Duk kuma an je inda take zuwa? Hamida ta tambaye ta “Ba inda ba a je ba shi ne na zo neman taimako wurin maigidanki ya taimake ni yadda Allah ya taimake shi daga shi Soja ne, ko Allah zai sa in san inda take.”
Abdurrashid ya tashi zai wuce wurin shi ta sauka kan kujera ta soma gaishe shi, shi kuma tunda ya gane uwar Walida ce ya yi matuƙar ɗaure fuska ta soma shessheka”Ka taimaka mini yadda Allah ya taimake ka.”
Amsawa ɗaya ya yi ya shige ciki.
Ta ci-gaba da roƙon Hamida ta ce kar ta damu za ta yi mishi magana za su yi iyakar ƙoƙarin su.
Ta miƙe Hamida ta kai ta zuwa ƙofar falo ta dawo ta zauna tana tuna cin amanar da Walida ta yi mata baƙin cikin abin ta ji ya taso ya rufe ta, tuna Abdurrashid na ɗaki ya sa ta miƙewa zuwa ɗakin, wanka ta samu ya fito yana goge kansa ta samu wuri ta zauna sai ta rasa ta inda za ta fara mishi magana don har ga Allah Umman Walida ta ba ta tausayi za ta saurari maganar ne don ita, amma ta ma fi ƙarfafa zargin Walida yawon barbaɗarta ta tafi.
Ta yi ƙarfin halin fuskantar sa, “Kana ji Hamma abin da ta zo da shi? Ka taimaka mata don Allah.”
Wani kallo ya yi mata da ya sa ta kauda kai sai ya ja tsaki “Ki fita harkar mutanen nan na faɗa miki, ko za ta fito ba yanzu ba sai ta gane matar wa ta taɓa.”
Galala ta yi da baki gane da hannunsa a ɓatan na Walida.
“Kai ka ɓatar da ita Hamma? Ƙara ɗaure ya yi sai ta fasa faɗin abin da ta yi niyya illa ta ce mishi za ta dubo Aunty Karima.
Kwance yau ma ta same ta ita ta yi mata gyaran bedroom ta haɗa mata ruwan wanka, da bin bango ta shiga ta yi ta fito ta nuna ma Hamida kayan da za ta ɗauko mata ta shirya sai mai aikin ta ta zo ta ce mata Dr ta zo, tare suka fito da Hamida, Hamida ba ta zauna ba ta ce za ta koma gida.
Sai da ta biya ta gaida Engineer da bai daɗe da dawowa daga Daura ba sai ta koma gida.
Kitchen ta shiga ta fara shirin abincin rana shinkafa ta yi ma Abdurrashid da miya duk son ta da shinkafa da miya yanzu ba ta son ta, ita cikin sai ya cika wata uku sannan ta fara ba ta cin wannan, tana cin wannan kuma ga shi har ya shiga wata na biyar ba ta daina ba.
Ita dambu ta ɗora ma kanta da tsakin da ta taho da shi.
Jin Abdurrashid ya shigo daga sallah da ya fita ta ɗauko abincinsa ta ajiye a dinning sai ta koma kitchen ta fito ɗauke da plate sai ta nufi inda yake tsaye yana tuɓe jallabiyar jikinsa ya juyo ya dube ta, ta ɗan karya wuya “Bari in kai ma Aunty.”
“Me za ki kai mata? Ya tambaye ta yana kallon plate ɗin da ke hannunta “Dambu na yi shi ne zan kai mata ko za ta iya ci.”
Juya kai ya yi yana canza tasha da remote ɗin da ke riƙe a hannunsa ya wuce dinning ɗin.
Ɗaki ta koma ta sanya hijab ta fito kwance ta samu Auntyn a falo ta ba ta ta kuma wuce kitchen ta ɗauko mata cokali, ba ta zauna ba ta koma gidanta.
Ta samu Abdurrashid har ya yi nisa da cin abincinsa, tana yaye hijab ɗin kitchen ta faɗa ta fito da nata danbun,don da ma plate biyu ta yi. Abdurrashid dai bin ta ya yi ta yi da ido ganin yadda take ci, yana kammala miƙewa ya yi ya shige ciki ya fito cikin shiri, ya ce mata zai fita ta yi mishi fatan dawowa lafiya tare da roƙon zuwa La’asar za ta leƙa Gwoggonta.
Ya ce a’a daga dawowa sai yawo?
Bai jima da fita ba ta ji knocking ta tashi ta buɗe sai Gwoggonta ta gani fara’a “Shigo Gwoggo,sannu da zuwa.”
Ta shiga tana faɗin “Tun ɗazu na shiryo in zo in gan ki, sai ga Laila ta yo yaji.”
Hamida ta fidda ido “Yaji kuma Gwoggo?
Ta ce “E wai aure zai yi shi ne suke ba ta kashi.”
“Hamida ta dafe kai “Innalillahi, wayyo Aunty Laila, kishiya za a yi mata?
Ta ajiye ma Gwoggo lemo tana zuba mata “Ke dai bari yau duk hankalina a tashe yake yadda Laila ta fita hayyacinta, ya jikin ke kuma?
Hamida ta ce “Na ji sauƙi.”
Suna ta hirar su har cikin hirar take ba Gwoggo labarin cikin Aunty Karima ta yi ta mamaki ta ce “Ikon Allah kenan, ashe rabon naku a tare yake.”
Sai La’asar ta tashi tafiya Hamida ta yi mata alheri na kuɗi da turare.
Ganin Abdurrashid bai shigo ba ta yi ma kanta tuwon dawa miyar kuka, shi ba ya cin abinci mai nauyi da daddare. Nan ma kallon ta ya yi ta yi da take ci yana shan fruit salad ɗin da ta haɗa mishi.
Da ta kammala ɗakinta ta koma ta yi wanka da duk shirin da za ta yi na zuwa turaka. Ta fito cikin wata yaloluwar rigar barci mai hannun shimi ga cikinta nan ya turo,tsawon rigar iya gwiwa.
Ta lura tunda ta fito Abdurrashid yake kallon ta ta zauna tana taya shi kallon film ɗin da yake kallo, sosai take son shirin series Film ne kuma ta yi sa’a ana farawa ta fito
Miƙewa ya yi sai ya soma kashe duk kayan wutan da ke falon ganin ya kashe TV ta ɓata fuska “Haba mana Hamma,ina son shirin nan.” Ya ce “Kwanciya zan yi.”
Ta dube shi “Zan taho idan an gama.”
Ya girgiza kai ” A’a, a jikinki zan yi barci, ina jiranki.”
Ya wuce ta bi shi da kallon takaici ya hana ta ta kalla.
Ta miƙe ta mara mishi baya, yana shiga tana shiga, ganin ya hau gado ita ma ta haye ya janyo ta ya sa jikinsa tana jin ajiyar zuciyar da yake fiddawa.
Sai da suka yi nisa da wasanni ta yi mishi tambaya kan batun Walida, take ya amsa da cewa shi ya sa a ɓoye ta amma bai ce a mata komai ba yana so dai ta ɗauki darasi. Ajiyar zuciya ta fidda sai ta cigaba da abin da take masa wanda ya ƙara rikita shi sai ta kwantar da murya ta roƙe shi ya saki Walida kawai ko dan uwarta, ya ce zai yi hakan.
Washegari ta kammala shiri da hantsi za ta gidan Gwoggonta sai ga Maman Walida ta kuma dawowa.
Wata magiyar ta dasa mata a taimake ta a nemo mata Walida.
Hamida ta ce Kar ta damu ganin Hamida cikin dogon hijab da Safa ta ce “Hala fita za ki yi na tsare ki?
Murmushi Hamida ta yi ba ta yi magana ba ta ce “To mu je, ni ma gida zan koma.”
Tare suka fita a ƙafa ta yi niyyar tafiya amma saboda Maman Walida ta janyo motarta ta buɗe mata gaba ta shiga suka tafi.
Suna tafiya tana faɗi ma Hamida tashin hankalin da take ciki wanda ko barci ba ta iyawa.
Sun zo gidan Gwoggo Hamida ta tsaida motar, Maman Walida ta ce”Ni ma zan shiga mu gaisa da Haj Indo.”
Hamida sai fargabar haɗuwar Maman Walida da Gwoggonta take don ta san sam ba za ta yi daɗi ba.
Suka sauka tare tana kulle motar Gwoggo ta turo ƙofa ta fito, ganin Hamida da Maman Walida ya sa ta ƙara buɗe idonta, tabbatar da abin da idon ke nuna mata ya sa ta balbale Hamida da faɗa “Wane irin rashin hankali ne haka kuma?Me ya kuma haɗa ki da mutanen nan Hamida ko sharrin ne bai ishe ki ba? Maman Walida ta matso “Gwoggon yara ina kwana? “Riƙe gaisuwar ki Marka, ban da buƙatar ta, me ya kawo ki wurin Hamida?
Ko yar ki bata faɗa miki tarwatsa rayuwar Hamida da ta tashi yi sai dai ta Allah ba ta ta ba? Cikin rashin fahimta Uwar Walida ta ce “Wai me ya faru Haj Indo? Ta yi ta ba Gwoggo haƙuri kan ta faɗa mata abin da ya faru. Gwoggo ta gaya mata saƙare ta yi kunya ta baibaye ta da takaici kafin ta shiga ba Hamida haƙuri da rantsuwar ba ta sani ba.
Nan dai ta wuce a sanyaye, Gwoggo da Hamida suka wuce ciki sai surfa ma Hamida faɗa take da ta tsaya sauraron uwar Walida.
Ganin Laila Hamida ta yi duk ta yi wani firgai-firgai, ta matsa kusa da ita tana gaishe ta suka ji sallamar Ahmad ya shigo, sai da aka gaisa ya bada haƙuri tare da cewa Laila ta tashi su tafi ta yi funfurus, sai Gwoggo ce ta ce ya yi tafiyar sa za ta maido ta da yamma.
Cikin damuwa ya tashi ya tafi.
Sai kuma bayan tafiyasa Hamida ta ji duka-duka auren saura sati biyu.
Tana zaune tana cin kwakwa tana sauraron Gwoggo na ba Laila shawara. Ƙarfe uku ta yi shirin komawa gida Gwoggo ta ce ta bari su kintsa sai ta sauke su.
Sai da Laila ta yi wanka ta shirya suka tafi Gwoggo sai mita take a mota “Don za a yi maki kishiya sai kuma ki zama ƙazama, tunda kika zo fa Laila ba ki yi wanka ba meye haka?
Sun samu gidan Laila kaca-kaca don ba ta da mai aiki sai yaranta su hudu, Amir shi ke komai na aikin gida.
Hamida ta cire hijab ɗinta ta shiga kintsa wurin a ranta kuma tana fargabar haɗuwar ta da Abdurrashid don ta daɗe.