Yamma liƙis suka fito tare da Gwoggo. Ƙin zuwa ta yi gidansu ta sauka wurin Aunty Karima, yau dai ta same ta da ɗan sauƙi sai da Engineer ya shigo duba Auntyn ta tashi don komawa gida sai ga Abdurrashid ya shigo ta raɓa shi ta wuce.
Da ta koma ba ta yi tunanin yin girki ba don ta gaji, turare ko’ina ta yi da turarukanta masu ƙamshi sai ta yi wanka ta yi sallah sannan Abdurrashid ya shigo, a falo suka zauna tana ta sauraro ta ji ya yi mata faɗan daɗewar da ta yi sai ta ji shiru har suka kwanta.
Washegari da daddare sai ga Ahmad mijin Laila, anan gidansu ya yi hira ta zubo mishi jallop ɗin da ta dafa ma kanta don Abdurrashid ba zai ci ba.
Ya kuma cinye tas sauka ci-gaba da hirar su tana sauraren su har ta ji barci ɗakinta ta miƙe ta shiga brush ta yi sai ta yi alwala ta yi turarukanta sai ta sanya riga da wando masu taushi sun lafe a fatarta sai ta ɗaura dogon hijab ta fito ta yi mishi sai da safe ta wuce ɗakin mijinta, gado ta hau ta karanta falaƙi da nasi, da Suratu Ikhlas, da ayatul kursiyu sai ta rufe da Amanar rasulu.
Ta rufe idonta ta shiga barci, cikin barcin ta ji an birkito ta ana shafa cikinta ba ta buɗe ido ba don ba abin da take so irin ta yi barcin, a kunne yake raɗa mata “Jibi fa za mu wuce Abuja, gobe ki fara shiri.”
Ai gaba ɗaya ta buɗe idonta “Ni Hamma na gama zama garin nan.”
Ya ce “Saboda ke ke iko da kanki?
Ta ce “Garin ya fita a raina ba za ni ba.”
“Ai ba shawara na ce mu yi ba, ki shirya gobo jibi in sha Allah za mu wuce. “Ta tashi a jikinsa ta koma kan pillow”Ni na faɗa maka Hamma ba za ni ba.”
Ƙwafa ya yi ya kwanta don bai saba tana musu da shi ba.
Har washegari ya ga ba ta da niyyar soma shiri, ya kai ta asibiti don ta mayar da awonta anan har Scanning ya sa aka yi mata don ya ga lafiyar abin da ke cikin.
Sun dawo ya kuma mata zancen shirin tafiya, ta ce ita fa ba za ta ba ita Islamiyyar ma take son shiga
Ya ce “A’a ba yanzu ba sai kin haihu.”
Ta ce “Islamiyyar nan cikin Estate ɗin fa shi ne sai na haihu.”
Ya ce “Haka na ce. Ya miƙe sai ya fice.
Jin wayarta tana kuka ta duba sai sunan Aunty Karima ta gani ta ɗaga ta ce ta zo part ɗin Engineer ta same ta. Ta sanya dogon hijab ɗinta sai ta fita.
Har Abdurrashid a falon ta same shi ga Engineer zaune, kusa da ƙafar Aunty Karima ta zauna ta gaishe da Engineer sannan Aunty Karimar fuskarta na ƙasa.
Engineer ya ce “Ya aka yi ɗiyata, Mijinki ya ce kin ce ba ki bin shi Abuja? Shiru ta yi don ba za ta iya magana gaban shi ba “Ki yi haƙuri ɗiyata, ki shirya ki bi mijinki kamar yadda yake so ba ma daɗewa zai yi ba ai Abujar bai fi saura wata biyu ba ya dawo nan ɗin.”
Ita dai ko motsi ba ta yi ba har ya ƙare maganganun lallashin ta ya sallame ta.
Ta ce musu sai da safe ta tafi ba ta tsaya ko’ina ba sai ɗakinta, hijab ɗin jikinta kawai ta yaye ta haye tsakiyar gadonta ta fara kuka a haka ya shigo ya same ta tsaye ya yi yana kallon ta kafin ya ce “Duk maganar da aka yi miki ba ki haƙura ba kenan? Ba laifi.”
Ya sa kai ya fita ta share hawayenta ta tashi ta soma haɗa kayan da za ta tafi da su, ba ta kwanta da wuri ba sai sha biyu, hakan ya ja mata makara don ba ta tashi buɗe idonta ba sai da haske ya fara shigowa ta window ta ta tashi da sauri tana salati sai ta dubi agogo, bakwai tuni ta wuce cikin matuƙar baƙin cikin rasa sallar asuba da ta yi ta shiga bathroom, ta fito ta kabbara sallah tana idarwa ko azkar da karatun Alƙur’ani da ta saba yi ba ta tsaya yi ba ta tuɓe hijab ɗin ta nufi wurin Abdurrashid tsaye ta same shi cikin shiri ya waiwayo ya amsa sallamarta a hankali ta ce mishi “Ina kwana? Tana kaiwa zaune bakin gado amsawa ɗaya ya yi ta ce “Na makara, shi ne ba ka tashe ni ba? Ya noƙe kafaɗu “Na san don in yi fushi in tafi in bar ki ne kika ƙi tashi, kuma kin samu nasarar yin hakan zan tafi in bar kin sai dai ki sani ba ƙaramin cutar da ni hakan zai yi ba, tsawon watanni biyu muka ɗauka ba kya tare da ni yanzu daga dawowar ki ki guje min, sai dai kar ki ga laifina idan ban zo ba don sai kin neme ni.”
Hawaye Hamida ta ji suna zubo mata na baƙin cikin juya maganar da ya yi ta sauko gadon ta durƙusa ƙasa ta shiga kuka sosai.
Ya dubi inda take sai ya ajiye jakarsa da ya ɗauka ya tako zuwa inda take tsugune ya kamo ta ta ƙwace ta ci-gaba da kukan ƙarfi ya sa mata ya ɗago ta sai ya haɗe ta da jikinsa tana sane ta shiga goga fuskarta a jikin fara ƙal ɗin shirt ɗinsa, duk ta goge masa hawayen da ya damalmale fuskarta.
Zuwa bakin gado ya ja ta ya zauna tare da ita tana cikin jikinsa da dukkan hannayensa ya rungume ta.
“Me ya sa kike so ki yi ta ɓata ranki alhali kin san ba ke kaɗai ba ce? Ya shafa cikin “Me kike ma kuka? Ta ƙi magana ya kuma maimaitawa nan ma ba ta ce uffan ba.
“To ki yi haƙuri daga ba ki son zuwa zan ƙyale ki.” Da sauri ta ce “Daddy zai ga na raina maganarsa.”
Ya zare hular kanta ya soma shafa calabar kanta “Ba zai ce ba zan mishi bayani.” Ganin ya zare rigar barcin jikinta ya soma tube tashi ta san abin da kenan, zagewa ta yi ta faranta mishi tana mishi kukan shagwaɓar ɓata mishi rai da ta yi daren jiya ya yafe mata.
Bai raba jikinsu ba bayan kammala komai barci ya ɗauke ta shiru ya yi yana duban fuskarta, a hankali ya zare jikinsa sai ya miƙe zuwa bathroom wani wankan ya sake ya fito ya sake shiri cikin wasu ƙananan kayan sai ya ɗauki jakarsa ya dubi inda Hamida ke barci sai ya dubi agogonsa lokaci ya fara tafiya, ya fita ya ja ƙofar.
Sai da ya zauna a motar ya zaro wayarsa ya tura ma Hamida saƙo, ya tayar da motar mai gadi ya wangale gate yana wa mai gidan nasa fatan sauka lafiya.
Wayar Hamida da ke kan gadon ta tayar da ita da rurin da ta ɗauka, ta buɗe idonta tana duban ɗakin da yadda suka yamutsa shimfiɗar gadon sai dai ba Abdurrashid, tunanin ko ya tafi ya bar ta ne ya sa hankalinta tashi ta gaza ɗaukar wayar har ta tsinke.
Ta rafsa tagumi tana duban agogon bango sha ɗaya saura, wayar ta kuma ɗaukar ƙara a karo na biyu cikin sanyin jiki ta miƙa hannu ta ɗauko ta, Ahmad ne mijin Aunty Laila, cikin mamakin kiran ta yi picking sai ta soma gaishe shi cikin girmamawa kamar yana ganin ta, ta tambaye shi su Aunty Laila da yaran ya ce duk suna lafiya.
Ya ƙara da tambayarta “Oga ya wuce ne? Ta amsa da “E.” Ya ce “Da ma wata magana nake so mu yi da ke saboda yaba hankalinki da nake yi da ɗabi’unki.”
Ya ɗan tsahirta ko za ta ce wani abu, jin ta yi shiru ya cigaba “Game da zamantakewa ta da Laila ne tun kina ƙarama na san kin san komai ina zaune da Laila ne don ina son ta, shi ya sa nake haƙuri da ɗabiunta, amma yanzu an kai lokacin da dole ina buƙatar sama ma kaina mafita shi ya sa na nemi ƙarin aure, Laila ta dira ta yi tsalle ba za ta yarda ba.
Me Laila ta riƙe wanda zai hana a yi mata kishiya?
A ran Hamida ta ce “An zo wajen.” Ta daɗe tana ma yar’uwar ta ta fargabar ranar da za a zo haka. Ta ja ajiyar zuciya ta ci gaba da sauraren shi.
“Komai da ake wa miji ban san shi ba daga Laila ba abin da ta sani sai ta ci ta kwanta ta ɗauki wayarta, yarana su za su yi ma kan su komai har ni ma su yi min, wanka da kwalliya su kaɗai nake samu daga Laila su ma ɗin ta watsar ta rungumi waya. Ni dutse ne da ba zan buƙaci inda zan samu kula ba? Don haka na kawo koke na gare ki, kina da hankali da sanin ya kamata ki yi mata nasiha ta nutsu ta gyara aurenta.”
Jin ya yi shiru ta ce “Ka yi haƙuri Baban Amir.”
Ya ce “To na gode.”
Suka yi sallama ta ajiye wayar ta zauna shiru cikin tunani ita ya ma za a yi ta fuskanci Aunty Laila da zancen za ta yi mata nasiha duk girmanta? Amma tsakani da Allah ta san Laila tana da buƙatar a zauna a yi mata nasiha ta gyara yadda take tafiyar da rayuwar gidanta, in kuwa ba ta gyara ba aka auro mata wadda ta san kanta Aunty Laila ta kaɗe har ɗan ganyenta.
Ta daɗe cikin tunanin ƙarshe ta miƙe zuwa ɗakinta, wanka ta yi ta gyara jikinta sai ta gyara ɗakin.
Ta fita zuwa dakin Abdurrashid ta gyara nan ma sai ta fito don barin gidan suka yi kaciɓis da mai yi mata aiki sai da suka gaisa ta ce ta ce ta zo ta yi ta knocking ba a buɗe ba. Ta ce barci take.
Tare suka tafi wurin Aunty Karima can Hamida ta wuni har girki ta yi mata ta ci kuma ya tsaya mata ba ta yi amai ba.
Yamma sosai ta koma gida.
Washegari ta nemi iznin Abdurrashid ta je gidan Laila, zagewa ta yi ta yi mata gyaran gida amma ta kasa ce mata komai domin dai Laila ba sa’ar ta ba ce ko da wasa. Sai da La’asar ta yi mata sallama ta koma gida.
Har Abdurrashid ya yi sati biyu bai zo ba, tuni zaman ita kaɗai ya gundure ta.
Suka sha bikin Ahmad mijin Laila yan Daura sun zo sosai cikin su har da Innarta wadda ta ji daɗin ganin ta sosai.
Ranar wata Laraba da hantsi ta shiga wurin Aunty Karima Auntyn ke faɗa mata Mami ba lafiya kan dole ta tashi ta tafi gaishe ta ba dan ta so ba.
Su uku ta samu falon Mamin, Mamin sai Haj yar Yaya sai wata mata da ba ta san ta ba. Su biyun suka yi mata caa! Da ido, don duk da ƙaton hijabin da ta sanya cikin ya turo ya fito.
Wuri ta samu ta zauna tana gaishe su da tambayar Mami jiki Haj yar Yaya ta taɓe baki “Bikin Anisa kafin ta haihu za a yi shi.” Mami ta ce “Da an bari in ta haihu sai a haɗa da suna.”
Suka cigaba da zancen auren Anisa da Abdurrashid kamar ba ita ce a gaban su ba. Ta miƙe ta yi musu sallama sai ta bar sashen zuciyarta na mata zafi jin waɗannan mutanen ba su haƙura ba da ƙarin auren Abdurrashid.
A falonta rasa inda za ta zauna ta yi tana cikin haka kiran Abdurrashid ya shigo wayarta, ta ɗaga sai ta kama mishi kuka hankalinsa ya tashi don tunanin ko wani abu ya faru, ya shiga tambayar ta ta ce ita dai yaushe zai dawo? Ya ce ba yanzu ba ta ci-gaba da kukanta tare da magiyar ya zo ya ce to zai dawo da ƙyar suka rabu.
So take ya dawo don idan yana can gani take za su yi ta soyayya da Anisa hankali kwance ita tana nan.
Tashi ta yi ta rufe ƙofar falon ta dawo ta baje a falon cikin damuwa a taƙaice kasa shiga ɗakin ta yi a falon ta ƙaraci damuwar ta barci ya yi awon gaba da ita.
Cikin barcin ta ji ana shafa ta ta tashi a razane sai ya riƙe ta “Ke ni ne.”
Ta buɗe idonta da ta rufe don tsoron da ya rufe ta ta gan shi tsugune gaban ta, tare da ita ya miƙe hannunsa na kan cikinta suka nufi ɗakinsa.
Sai da ta wartsake ta tambaye shi hanya har yake gaya mata ko lokacin da suka yi waya ya shigo garin yana barrack ɗin da ya bari, ta nemi ta yi masa girki mai sauƙi ya ce a’a dare ya yi bai tare da yunwa.
Ba su jima ba suka kwanta don dare ya fara nisa.
Kwana biyu kawai ya yi mata ya koma.
Rayuwa tana ta tafiya cikin Hamida yana ta girma da na Aunty Karima.
Nata ya kai watanni takwas na Aunty Karima shida Abdurrashid ya dawo Kano da aiki, wai sai ga Anisa ta dawo gidan tunda Hamida ta gan ta hankalinta ya tashi don ba ta san da zuwan ta ba sai wani dare suna zaune a falo ita da Abdurrashid ita tana zaune kan Sopa ta bubbuɗe ƙafafu shi kuma yana zaune a ƙasan carpet kusa da ƙafafun nata yana cin apple ta yi knocking shi ya amsa yana duban agogo cike da mamakin waye me zuwa musu yanzu, Anisa ta shigo cikin karairaya.