Skip to content
Part 37 of 37 in the Series Shirin Allah by Maryam Ibrahim Litee

Ta zauna tana facing ɗinsu, ba ta damu da kallon da suke mata ba ba wanda ya yi mata magana sai ita ta gaida Abdurrashid.

“Ba ka shigo ba.” Ta ce da ta ƙare gaisuwar, ƙara ɗaure fuska ya yi bayan shakkar Haj yar Yaya da yake da tuni ya kore ta ya yi mata fata-fata.

“E ban shigo ba. Ya amsa mata a taƙaice.”

Ta ci-gaba da zama tana jan shi da magana, Hamida ta ƙi magana don tana son ta ga ƙarshen rashin kunyarta, idan ma ta yi magana tana ganin ta mayar da kanta baya. Ta gama firiritarta ta tashi za ta tafi ganin Abdurrashid ya yi banza da ita daga inda yake ko motsi bai yi ba ta fice. Hamida ma ta cicciɓa ta miƙe tsaye ta fara takawa ya kira sunanta ba tare da ta waiwayo ba ta amsa “To zo mana.” Ya ce mata.

Nan ma ba ta tsaya ba ya miƙe taku ɗaya ana biyu ya cim mata, hannu ya riƙe mata sai ya janyo ta suka koma kan kujera “To fushin na mene ne? Uhm na ce na mene ne? Ta turo baki “Wallahi wannan ne na ƙarshe da za ta shigo min wuri wai ta zo wurin ka.”

“Ina ce yanzu ba za ta dame ki ba? Ya na faɗi yana shafa cikin ta.

Hamida dai ba ta samu sukuni ba sai da Haj yar Yaya ta zo kan batun auren Abdurrashid da Anisa ya basu tabbacin ba zai auri Anisa ba don dama an ce don ya samu haihuwa to shi yanzu ba shi da wannan matsalar.

Da Mami da Haj yar Yaya ba a san wanda ya fi shiga tashin hankali ba da wannan hukunci da Abdurrashid ya yanke.

Hamida ta ziyarci Asibiti a hanyarta ta dawowa ta yi karo da baban Amir mijin Laila ya ce ta ƙi zuwa ta ga amarya ta ce za ta zo. Don haka da ta tashi zuwa gidan Gwoggonta sai ta fara biyawa ta can part ɗin yar’uwarta ta fara shiga ba ta nan sai yaran, da yake Weekend ne.

An gyara wurin don ta yi sabuwar mai aiki, yaran suka kewaye ta ta raba musu Chocolate ɗin da ta ruƙo musu har da abin wasa ta sawo ma ƙananan su biyu, ta kama hannun ƙaramar daya ta bi ta a baya zuwa part ɗin amarya.

Da ta yi knocking aka amsa shiru ba a zo an buɗe ba sai da ta ƙara yaran ma suka ƙara ta ce su bari sai ga wata mata ta buɗe cikin matuƙar kwalliya take tana ganin yaran ta ɗauki ƙaramar ta kama hannun ɗayar ta yi ma Hamida maraba da tayin shigowa ta bi bayan ta ta zauna kan ɗayan daga cikin kujerun falon da ya sha gyara yana fitar da ni’imtaccen ƙamshi.

Baban Amir da ke zaune kan dinning ya ce “A’a ƙanwata ke ce a gidan? Barka da zuwa.” Ta ce “E tana gaishe shi matar ba ta zauna ba sai da ta kawo ma Hamida abinci ta zubo ma yaran ta sanya ƙaramar a cinya tana ba su tana gaishe da Hamida.

Kaɗan kaɗan Hamida ke amsa hirar da baban Amir ke mata, da yaran suka ƙoshi ta shiga ciki ta kwaso musu kayan wasa ta basu tana taya su wasan Hamida tana karantar su, awa biyu ta yi ta miƙe ta ce “Na ga amarya baban Amir, Allah ya sanya alheri.”

Ta yi ma amaryar sallama wadda ta ce ta bar mata yaran.

Ta fita ya raka ta har waje ta tafi.

A gidan Gwoggo ta samu Laila tana ta razgar kuka wai yanzu baban Amir bai son ta amaryarsa mai shegen sanabe nema take ta karɓe shi ita kaɗai.

Duk da nauyin ta da Hamida take ji zama ta yi ta faɗi mata gaskiya yadda za ta yi mu’amalarta da mijinta,tun kafin a karɓe mata shi gabaɗaya.

Ta yi mata alƙawarin turarukan ɗaki da Lailan ta ce tana so ina Hamidar ke saye.
Sai La’asar Abdurrashid ya zo suka koma gida.

Washegari tana zaune a falonta ta ji ana knocking daga inda take zaune ta bayar da izinin a shigo, aka buɗe aka shigo.

Ƙura wa wadda ta shigo ido ta yi don son tuna inda ta san ta. Ta tako cikin falon sai ta zauna a ƙasa “Barka da hutawa Haj.”

Ta furta cikin sunkuyar da kai “Rabi! Hamida ta ambaci sunan cikin wani irin mamaki da ya rufe ta “Na’am Haj Hamida.”

Hamida ta yi murmushi “Da ma Rabi kina duniyar nan?

“Ina nan Haj Hamida, bayan tafiyar da aka yi da ni aka yi min aure, auren ne ba daɗi shekara guda kenan da mutuwar shi, zaman ƙauye sai a hankali shi ne na yanke dawowa wurin Haj (Gwoggo Indo) sai kuma na iske ta bar sana’ar, da na tambaye ki sai ta bani labarin kina nan shi ne na taho ki taimaka min ki bani aiki a wurin ki kowane iri ne.”

Hamida da ke ta kallon Rabi cike da tausayawa don ganin yadda ta koma gabaɗaya ta rafke ta yamutse saboda wahala.

Ta ce “Ina da mai aiki Rabi, sai dai hakan ba zai hana in ɗauke ki ba.”

Ta cicciɓa ta miƙe Rabin na mata sannu ta isa kitchen abinci ta zubo mata ta fito ta kawo mata ta amsa tana godiya tana ci suna ɗan taɓa Hamida ta tambaye ta ba ta da yara ne ta ce haihuwa shida ta yi ukun da ta haife su suke mutuwa saura uku yanzu suna gidan uban su.

Sai da ta ƙare cin abincin Hamida ta shiga ciki yan suturu daga cikin nata ta zaɓo mata don ganin tana buƙatar su, da sabulai da man shafawa har da kuɗi dubu uku ta zo ta ba ta ta ce ta koma gidan Gwoggo za ta sanar da mai gidan idan ya dawo. Ta yi ta godiya ta tashi ta tafi.

Da Abdurrashid ya dawo ta faɗi mishi bai ƙi ba don haka ba ɓata lokaci Rabin ta tare a gidan ɗaki ta ware mata can ta baya tana taimakon ta ƙwarai musamman da cikinta ya tsufa sosai, zuwa yanzu duk sun gama sayayyar kayan haihuwa sai jiran haihuwar kawai inda Hamida ta dage da roƙon Allah ya sauke ta lafiya.

Innawuro ta zo daga Daura Daada ma ta zo daga Yola.

Ana gobe babbar Sallah kowa ya ɗauki azumin arfa Hamida ma duk da faɗan da Abdurrashid ya yi kan ta bar azumin hakuri kawai ta ba shi ta ci-gaba da azuminta.

Bayan Rabi wadda ke mata aiki kafin zuwan Rabin ta shigo suka haɗu suka yi mata aikin sallah zuwa yamma sun kammala komai.

Ta yi wanka ta ɗauki kunun ayan da ta yi da cincin ɗin da suka yi su take so ta fara buɗa baki da su idan an kira Sallah,ɗakin su Daada ta nufa ta zauna kan carpet ta buɗe ƙafafuwanta suna mata sannu, ba ta fi minti biyar da shigowa ba aka fara kiran sallah ta ɗaga kofin kunun tana ta addu’a ma fi yawan addu’ar ita ce Allah ya raba ta da cikin nan lafiya, sai ta kafa kofin ai kam tana shanyewa mararta ta amsa da ciwo ta miƙe ta kabbara sallah a ɗakin, har ta idar marar tana ɗan taɓa ciwon tana bari sai dai duk yadda ta so ta yi buɗa baki kasawa ta yi har suna haɗa baki wurin tambayar ta lafiya dai ta ce lafiya lau, Abdurrashid ya yi sallama daga bakin ƙofa saboda Innawuro ya ƙi shigowa ya gaishe su da yi musu barka da shan ruwa sai ya juya ta samu ta miƙe ta bi shi a baya, ba su hawa dinning saboda halin da take ciki ledar cin abincin da aka shimfiɗa suka zauna nan ma kasa cin komai ta yi da ya tambaye ta ta ce ta ci wurin su Daada,yana gamawa aka kira Isha’i har ya fita sallar ya dawo tana nan zaune ya kama ta suka tafi ɗakinsa.

Wasu dogayen riguna ya sawo mata ya ce ta gwada ta gwada ta farko ba ta gama sauka ba ko dan saboda cikin, cikinta ta ji ya yi wata irin murɗawa ta saɓule rigar da sauri sai ta juya ta bar dakin dakinta ta isa ta hau gado tana ta jin ciwon da mararta ke yi, a haka ya shigo ya same ta yanzu kam yana tambayar ta ta ce mararta ke ciwo ya ce ta tashi su je hospital shi ya ɗauki kayan da ta shirya sai da ta zauna a mota ya koma ciki don sanar ma su Innawuro da suka ce ba su ga ta zama ba Asibitin su na sojoji ya nufa da ita cikin sauri suka karɓe ta aka shiga ba ta kulawa Abdurrashid na tare da ita, har sai ƙarfe sha biyu na dare ta haiho santalelen ɗanta mai kama da uban shi sai da aka gyara su aka canza mata ɗaki su Daada sun shigo baki har kunne don Daada ma har da kuka.

Zuwa safiya kowa da ya kamata ya ji ya ji har Engineer da safen ya zo shi da Mami da Aunty Karima wadda ta yi matuƙar nauyi.

Kwana biyu ta yi suka sallame su suka koma gida inda suka shiga karbar jama’a daga ko’ina da ke ta zuwa barka da murna, suna aka yi na ji da gani da ya tara dubban mutane.

Ta samu saƙon Jamilar Usman da ta ce ta kasa zuwa ta yi mata barka amma tana mata fatan alheri.

Ta ci-gaba da kula da ɗanta wanda ya ci sunan Engineer suna kiran shi Affan duk safiya Engineer ke aikowa a zo a ɗaukar mishi shi haka ma idan ya dawo Office, kwanan su arba’in da biyar Aunty Karima ta haihu ta samu budurwa sunan mahaifiyar Abdurrashid aka mayar mata tare suke renon yaran da suka zama kamar yan biyu.

Sai da suka yi watanni biyu ta samu tafiya Daura tare suka tafi da Innawuro a can ta haɗu da Aina wadda kunyar abin da mijinta ya hana ta je wa Hamida sai dai saƙo ta tura mata.

Haƙuri ta yi ta ba Hamida wadda ta ce ba komai Aunty Aina,sai dai ina fatan hakan ba zai raba zumuncina da ke ba.
Tana can ta samu labarin rasuwar Haj yar Yaya dole daga yin sati ta juyo maimakon kwanaki goma da ta samu Abdurrashid ya ba ta da ƙyar.

A gidan mutuwar ta ga su Anisa daga zuwa daya ba ta kuma yarda ta koma ba sai ranar bakwai.

Sannan ta bi gidajen su Momi Binta ta kai musu Affan.
Wata uku da haihuwarta ta shiga Islamiyar da take ta burin shiga ta cikin Estate ɗin.

Rayuwa ta yi wa Hamida daidai don tsakanin ta da Ubangiji sai dai godiya bayan Affan ta kuma haihuwar Abubakar Siddiq sannan ta haifi Fatima sunan mahaifiyar Abdurrashid Aunty Karima dai daga fatimarta ba ta ƙara ba.

Alhamdulillah
Sai Allah ya haɗa mu a book dina na gaba idan mai kowa da komai ya raya mu mai suna Mutum da ƙaddararsa

Labarin Bilkisu mai gadon zinare.
Maryam ɗinku ce.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Shirin Allah 36

1 thought on “Shirin Allah 37”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.