Skip to content
Part 4 of 37 in the Series Shirin Allah by Maryam Ibrahim Litee

Jin ya sake ta yasa ta bude ido tana kallon kofar. Wani matashin saurayi ne tsaye ya harɗe hannayensa yana duban su waige -wangen inda za ta ga gyalenta ta kama yi takalmanta ta fara gani ta wawuro su kafin ta ga gyalen ta hada da shi ta nufo kofa matashin ya ba ta hanya duk abin nan kuma kuka take tana fita ya mara mata baya yana duban yadda take tafiya tana kuka sai da ta yi nisa ta tsaya ta sanya takalmi da gyalen tsirarun ma’aikatan da ke bin ta da kallo ba ta ko san suna yi ba.
Maimakon shago gida ta wuce ƙwanƙwasa get din ta yi ta yi duk da ba ta da yaƙinin akwai mutum, sai kuma ta ji takun tafiya an zo an buɗe , Malam Buhari ne wanda shigowar sa kenan daga wurin aiki, ganin ta a birkice yasa ya tambaye ta abin da ya same ta ta ce ba komai, ciki ta wuce ta haye saman katifarsu tana kuka tana kullawa da kwancewa yadda za ta koma Daura.

Muryar Gwoggo Indo da ta ji ba ta sanya ta ɗaga kai ba har ta dafa kafaɗarta “Me zai sanya ki yi mini haka Hamida? Me ya faru kika taho ban sani ba? Shiru ba ta ba da amsa ba tsawa ta kwatsa mata “Tashi zaune mu yi magana! Ba shiri ta tashi don ko banza ba ta taɓa yi mata tsawar ba “Na ce “Me ya same ki? Ta fada cikin zare ido cikin inda inda ta bata labarin sama sama. Wayarta da ke hannunta ta shiga latsawa “Sannu tsohon banza mai kokarin ɓata ƴaƴan jama’a.” abin da ta fara cewa kenan tana huci, da alama shi ma tsiyar ya tarbe ta da ita. “E ko da nake kwaɗayayya ban zama fasiƙa ba, ka gode wa Allah da ya ce ce ka ba ka ɓata mini yarinya ba, da Kano sai ta yi maka kaɗan.”

A takaice dai tsiya suka kwasa ta sauke wayar tana ci gaba da masifa, bala’inta ya shigo da Malam Buhari yana tambayar abin da ya faru ba ta saurara ba da ƙyar ya lallashe ta suka bar falon.

Tun daga ranar Hamida ba ta kuma yarda ta je kai abinci kowanne Office ba.

Kuma ta rage walwala, abin da ya damu Gwoggo Indo kenan ta shiga tambayar ta abin da yake damun ta ta ce ba komai. Ranar da ta rutsa ta sai ta faɗi mata damuwar ta sai ta samu kanta da cewa ita makaranta take so a sanya ta. Lallaɓa ta ta yi ta ce akwai shirin da take yi, lokaci na yi za ta kaita makaranta, makarantar ma ba ta kowa da kowa ba ta yayan masu fada aji za ta kaita tana sane ba mantawa ta yi ba.

Dadi ya kama Hamida hakan ya sa ta maido da walwalarta ko don ta faranta ran Gwoggonta ta da kullun take tattalin farin cikin su ita da Aina, duk da kasancewarta mace me zafi su kam ba ta yi musu.

Sati uku da afkuwar abun Hamida na zaune a shagon su na provision wani matashi ya shigo ya ce ta ba shi tissue gudar dubu daya ya miko mata ta ba shi ta juya dauko masa canji, juyowarta ya fice, bin bayansa ta yi da canjin cikin sauri ta hango shi yana tafiya kamar zai kifa ita ma ta daga kafa ta bi bayansa da kyar ta kamo shi sai da ya shiga wata kwana ta ba shi sai ta juyo daidai wata mota da ta wuce a yayin tafiyarta ta gan shi tsaye gabanta ya buga tuna a inda ya fara ganin ta da abin da ya faru a ranar.

Ya za a yi ta manta da mutumin da ya tseratar da ita daga shaiɗani Alh Ɗanlami? Wani irin kallo yake jefa mata da ya sanya ƴan hanjin cikinta hautsinawa, don yadda ya yi mugun ɗaure fuska da sauri ta wuce shi kamar ana hankaɗata ta shige shago.

A ranar kuma da daddare sai ga Laila da mijinta wai sun zo roƙon Gwoggo ta basu Hamida mai aikinta ta koma garinsu kafin ta samu wata.

Da ƙyar Gwoggo Indo ta yarda shi ma saboda tana jin nauyin mijin Lailan don yana matukar yi mata alheri.

Sun taho bisa hanya yana ta nuna mamakinsa kan Hamida, wai shi bai taɓa sani tana nan ba don bai ma san ta ba.

Da suka isa Laila ta nuna ma Hamida dakin da za ta zauna sama sama ta gyara dakin ta kwanta.
Da asuba har ta gama abin da take ta fito ba ta ji motsin kowa ba.

Sai karfe goma LailDuk a fito, Hamida ta gaishe ta sai ta tambaye ta ta karya? duk da Hamida take karamar yarinya sai da ta ji mamakin tambayar ita bakuwa ita ake tambaya ta karya.

Ta dai ce a’a kitchen ta wuce ta ce Hamida ta zo ta mike ta bi bayanta, tea ta haɗa sai ta dubi Hamida “Ki duba akwai komai ki dafa abin da kike so, daga yau ma kar ki kara jirana ki shigo ki nemi abin da za ki ci in kin tashi. Hamida ta ce to ta dauki tea dinta ta fice. Ita ma tea din ta haɗa sai ta fito ta sha. Ba ta zauna ba aikin tsaftace wuri ta kama da ta gama ta riƙa jiyo kukan yaron Laila kamar ta share sai ta kasa, ta isa har bedroom dinta, ta shiga da sallama kwance take kan gado riƙe da wayarta yaron na gefenta yana kuka. Daukar shi ta yi tana tambayar me ya same shi? Ta ce “Rigima ce kawai yake ji.” Hamida ta juya dauke da shi, ta kai ƙofa ta ji muryarta “Ki shiga kitchen ki duba abinci me sauki ki ba shi.” Da “To. Ta amsa.

Indomie ta dafa mishi ya ci sosai daga nan ya kama wasan sa. Ganin ba alamar matar gidan za ta fito don ɗora girkin rana sai ta bi ta dakin ta tambaye ta ce mata ta yi ta je ta dora da ta kara tambayar me za ta dafa ta ce komai ya yi mata ta dafa, ta fito cike da mamaki, ganin akwai komai yasa ta yi niyyar yin fride rise wanda ta koya wurin Aina da take yawan yi musu. Ta yi ta gama ta shirya musu nasu a dinning, duk kuma abin nan Amir yana tare da ita sai da ta ba shi abinci ta ga yana lumshe ido sai ta kwantar da shi. Shigowar maigidan yasa ta tattara ta koma daki.

Sai La’asar ta fito ta tambaye ta abin da, za ta dafa a matsayin abincin dare kai ta girgiza ta ce ita sau daya take shiga kitchen. Hamida dai ta ce bari ta yi ta fita cike da mamaki idan ta tuna a gidan su na Daura, to ya ma za a yi iyayensu maza su dawo a ce ba a yi girki ba, ita kam bata taɓa gani ba.

Kitchen din ta shiga ta yi tuwon shinkafa da miyar kuɓewa ɗanya wanda ta iya su tun a Daura. Da ta gaya wa Laila tana son kuɓewa ɗanya mai mata wanki ta aika gidan Gwoggo ya karbo tana kammalawa ta shige daki

Da safe ma ita ta fito ta yi musu abin karyawa. Ta koma daki ta ji tana kiranta ta fito, sai da ta gaishe su Laila ta ce ta shiga ta dauko Amir ta yi masa wanka ta ba shi abinci.

Sai da ta yi mishi yadda duk aka ce mata sai ta goya shi ta gyara wa Auntynta ta daki. Ta fito goye da shi ganin babansa wanda ke kokarin fita yasa yaro soma zizzillewa sauke shi ta yi ya isa wurinsa, sai ta wuce daki, sai da ya fita laila ta kira ta ta bata Amir din.

Haka rayuwar Hamida ta ci gaba da gudana a gidan laila, ita ta zama tamkar matar gidan don ita ke gudanar da komai duk da ƙarancin shekarunta.

Laila irin matan nan ne da suke ɗaukar ragamar gidansu su damƙa wa masu aiki, abin da suka sani su mike kawai mai aiki za ta tsaya kan komai. Hamida dai don ta horu da aikin tun tana Daura, sannan zamanta gidan Gwoggo Indo ta kara koyon girke girke na zamani don nan din ma bata zauna ba, hakan ya bata damar iya riƙe gidan Laila wadda kodayaushe za ka samu mike tana charting.

Wata ranar Asabar masu gidan suna zaune a falo, Hamida na ɗaki tare da Amir wanda ya yi matuƙar sabawa da ita. Jan rigarta yake yana faɗin Daddy ta dauke shi don miƙa shi sun zo kofa sai ta ji kamar suna fada. Yadda take jin tashin muryoyinsu sai ta tsaya Laila ta fara ji tana cewa “Ni dai ban ce ka kawo mini kowa ba, abinci ka je Restaurant ku ci.” Shi ma ya karɓe da “Nan na yi niyyar kawo su, kuma tilas a girka abincin tarar su, manyan abokaina ne za su taso su ziyarce ni ina da iyalin, sai in kai su Restaurant? Zan fita za a kawo cefane.”

Komawa Hamida ta yi ta zauna sai da Amir ya dame ta ta fito, Laila kadai ta samu mike kan sofa tana danna wayarta.

Zama Hamida ta yi tana kallon Tv da ke ta aiki. Wanda aka aiko ya kawo cefane ya yi sallama ya miko, Hamida ta karba ta kai kitchen Laila kuma ta tashi ta yi ɗakinta.

Wurin awa daya da kawo cefanen Hamida ta gane Laila ba za ta yi girkin ba, sai ta tashi ta shiga kitchen iya ƙokarinta da wayonta ta yi kuma cikin ikon Allah ta yi abinci kala biyu masu dadi ta shirya komai kan tebur ta koma daki ta dauki wani littafin hausa da ta samo dakin Laila ta ci gaba da karantawa.

Karfe hudu ta ji hayaniyar bakin da basu wuce su biyu ba.

Yamma likis ta ji shiru alamar sun tafi ta fita ta kwashe komai ta kai kitchen ta wanke.

Sai zuwa dare ta ji an turo kofarta. Kai ta ɗaga sai Ahmad ta gani ta maida kanta kasa ta soma gaishe shi ya amsa da yi mata sannu da aiki, cikin ransa kuma yana mamakin yarinya ƙarama kamar wannan ta iya fitar da shi kunya. Ya ce “Ina ɗan naki? A ɗarare ta ce “Yana wurin Aunty Laila. ” ledoji guda biyu da ya shigo da su ya ajiye mata, ba tare da ta ɗago ba ta yi godiya ya juya sai ya bar ɗakin. Ƴan mintoci ta ba shi sai ta dauki ledojin zuwa dakin Laila, tana knocking ta ce ta shigo, zaune take gaban mirror tana ma kanta wankan turare, don ta sha kyau har ta gaji, wata haɗaɗɗiyar rigar barci ce mai kwalliya a kirji ga fuska ta sha make-up. “Ya a ka yi? Ta tambayi Hamida sai da ta ajiye ledojin bakin gado ta ce “Baban Amir ne ya bani.” ta ce “Kwashe ki je da su kin gode, ki dauki Amir ya kwana wurin ki.” kai ta ɗaga tana kai dubanta inda Amir din ke barci, ta ƙarasa ta dauke shi, sai da ta sanya mishi pamfars sai koma dauko ledojin babu Laila, ta san ta wuce dakin maigidan, ta koma sai ta koma dakin maigidan.

Washegari da La’asar zafin da ta ji tana ji yasa ta watsa ruwa. Da ta fito kwalliya ta yi cikin riga da zane na atamfa tana fesa turare Laila ta shigo cikin “Ki zo Gwoggo ta zo.” Da murnarta ta ajiye kwalbar turaren ta bi bayanta.

Kamar yadda take cike da zumuɗin ganin Gwoggon ita ma Gwoggon haka, kasa ta zube kusa da ƙafafunta, Gwoggo ta shafa sumar kanta “Na yi kewar ki ɗiyata, kuna nan lafiya? “Lafiya lau Gwoggo ina Aunty Aina? Ta ce “Tana gida.” Ta dubi Laila “Wai har yau ba ku samu mai aikin ba? Ta ce “Ba a kawo ba Gwoggo, da ma za ki bar mana ita.” Saurin girgiza kai da hannu ta yi “Sam! Ku nemo mai maku aiki zan ɗauki ɗiyata, nan da wasu kwanaki ko kun samo ko baku samo ba.”

Ta shiga bude ledar gabanta “Yanzu Gwoggo iyakar kudin kenan ba a ragi? Gwoggo Indo ta dube ta da mamaki “Ragi kuma Laila? Wadannan fa ba irin na gama gari ba ne, wannan na manyan mata ne. Daga ke sai Haj Mariya na daukar ma ma, don ke duk tsada na san ba ki ƙyashin saye ki gyara kanki.”
Ta jinjina kai “Zan bayar da rabi yanzu, cikon kuma sai nan da kwana biyu.”

Gwoggo ta yi fara’a “Yawwa ko ke fa? Allah ya kaimu. Ta maida dubanta ga Hamida “Tashi ki yi mini rakiya mu je mu dawo? Laila ta yi saurin cewa “Ina za ku Gwoggo? “Gidan mai gayya mai aiki, oga kwata kwata.” “Waye mai gayya mai aiki Gwoggo? Hamida ta tambaya murmusawa ta yi “Mai wannan Estate din, gidansa za mu maza sanya lullubinki mu je ki kashe kwarkwatar ido.” hijab ta sako sai suka bar gidan.

<< Shirin Allah 3Shirin Allah 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×