Skip to content
Part 1 of 16 in the Series Siddabaru by Muntasir Shehu

Shimfida

Ana bikin duniya akan yi na ƙiyama…
Wayar gari da mutuwar matshiyar mace wadda ba ta haura wa shekaru ashirin da huɗu ba abu ne mai dukan zuciya kai tsaye, duk abin da ya taɓa zuciya kuma dole gangar jiki ta nuna. Wannan ta sa tun da aka sanar da mutuwar wasu daga cikin ‘yan uwa suka dinga rufsar kuka ba ji ba gani.
Koda dai a gefe akwai masu farin ciki da mutuwar, suna ganin mutuwar tata kamar wata rahama ce Ubangiji ya saukar musu ko kuma ace yayewar annoba mutuwar ta zama.

Iyaye mata da suke da matasan ‘ya’ya samari su suka fi jin hakan a zuciyoyinsu, don haka farin cikin su ma gagarar ɓoyuwa ya yi a allunan fuskokinsu.

Isah Tukur Isah shi ya zama mutum guda ɗaya tilo da mutuwar Maryam ta fi jijjigawa zuciya, don labari na ishe masa ya yanke jiki ya faɗi bakinsa ɗauke da wasu maganganu na ƙaryata mutuwar, lokacin kuma da ya farfaɗo an riga an sada Maryam da gidanta na gaskiya.

A kan kabarinta ya tsaya yana kuka, kuka irin wanda duk taurin zuciyar mutum sai ta rusuna ta samar wa da ƙwaƙwalwarsa dalilin jin tausayi a gare shi.

Babu irin rarrashi da ban-baki da ba a yi masa ba, amma ko kaɗan ba su shiga kunnuwansa ba, to wanda zuciyarsa ta toshe ta yaya ake saka ran sauran sassan jiki za su zama a buɗe!

Da ƙyar mahaifinsa da mahaifin marigayiya Maryam suka janye shi daga kan kabarinta lokacin da yake tsakiya da yi mata dukkan addu’ar da ta zo kan harshensa cikin nema mata Rahamar Ubangiji bisa dukkan ta’asar da ta aikata a ban ƙasa lokacin da ruhi ke zaga gangar jikinta.
Yana roƙon Allah ya sassauta mata cikin tarin zunuban da ta tafi ta bari a doron duniya.
Ba shi kaɗai ba, kowa ma ya yi wa Maryam addu’ar dacewa da Rahamar Allah, babu wanda ya isa shiga tsakanin bawa da mahaliccinsa don haka babu wanda ba zai saka wa Maryam samun gafara ta Ilahu ba, waɗanda haƙƙoƙin rayukansu suka hau kanta kuma Allah ya nufe su da su yafe mata, sannan gaskiyar da ke binne cikin al’amarin rayuwarta Allah ya bayyana ta, ya kawo haske da zai bayyana ainahin dalilin faruwar dukkan abin da ya faru…

Babi Na Daya

Fuskarta babu walwala ta shigo falon, duk da kasancewar ta ɗanɗansa kwalliya da ado na kece raini, ƙamshin daddaɗan turare ke fita daga jikinta a duk sa’ilin da ta motsa.

Ɗan ƙaramin faranti ne wanda ke ɗauke ƙaramar moɗa ta ƙashi a hannunta.
Cikin moɗar kuwa zazzafan shayi ne wanda ke ta hucin tururi.

Bayan ta yi sallama ya amsa ta taka cikin nutsuwa ta isa gare shi, ya ajiye komai da yake yi ya barbaza mata lafiyayyun idanunsa yana ƙare mata kallo cikin yaba irin tsarin kwalliyar da ta yi, tuni zuciyarshi ta kuɓuce ta samar da murmushin gaggawa a kan fatar fuskarshi, yayinda wasu zantuka suke maimata kansu can cikin ƙoƙon ranshi.
Ina ma… Ina ma…

Ta ajiye masa kofin shayin a kan teburin da ke gabansa gefen na’ura mai ƙwaƙwalwa wacce ita ma take ajiye a kan teburin.

Da ta ajiye kofin sai ta juyar da kanta gefe cikin matuƙar jin haushi da takaici.
Da ace faɗa mata aka yi ba za ta taɓa yadda ba, ko kuma za ta kalli abin kallon shiryayyen labari da marubutan Hausa ke tsarawa ko wasan kwaikwayo, wai ace waya ko kwamfuta su zama kishiyar mace?
Ace idan miji ya shigo gida ba shi da lokacin matar gida sai lokacin danne-danne da bincike-bincike a waya ko kwamfuta, wa ya sani ma ko da wasu matan yake hira ita ya mayar da ita hoto abin kalla a yi nishaɗi!
Wace sauran dabara ce kuma ta rage mata a yanzu da za ta gwada ko za ta ci sa’ar raba kanta da waɗannan gumakan kishiyoyi nata?

Ya ajiye cokalin da kai bakinsa bayan surɓe shayin da ya ɗebo, a hankali ya mayar da dubansa gare ta.

“My dear, shayin nan ya fi na kullum daɗi… Zuciyata har ta fara zargin ko zumar ƙaunarmu ta ƙarshe ce kika zuba ciki.” Ya ƙawata fuskarshi da murmushi.

Ba ta saki ranta ba ta juyo ta watsa masa wani kallo mara ma’ana sannan ta sake kawar da kai.

“Wani abu da ba ki sani ba shi ne, gwargwadon yadda za ki ɗaure fuska ki ɓata rai, gwargwadon yadda kyawunta yake ƙaruwa a idanuna, don haka ni ba komai fuskarki ke isar min ba face saƙon tsantsar soyayyata da ke maƙare a ƙasan zuciyarki…”

Abin da ta lura da shi shi ne, idan har ta cigaba da zama kusa da shi to tabbas zai cigaba da jiƙa mata zuciya da zantuttukan da ta ke kallon su a matsayin na zaƙin baki, don haka ba tare da ta yi wani dogon tunani ba ta miƙe fuu a fusace ta yi hanyar ɗakin baccinsu tana mai cin laya a ranta na ko ta halin ƙa’ƙa sai ta karkato da hanalin mijinta zuwa gare ta.

Ajiyar zuciya ya yi, wannan ba sabon abu ne cikin rayuwar aurensu, a karan kansa ya san yana shiga haƙƙin baiwar Allahr nan da yawa, kullum yana tuhumar zuciyarsa da kasancewar ta mai tsananin son kanta da abin da duk ya ɓoyu cikinta, fatan sa a kullum yadda zai koyi kyautatawar rayuwa ga wannan mata tashi wadda har lokacin ba ta taka koda matakalar farko ba cikin birnin zuciyarsa sashen adana soyayya…
Ina ma wadda ta taka wannan matsayin na nan a bisa doron duniya… Da tuni ya daɗe da nuna wa duniya amsa sunansa na BABAN SOYAYYA!

Ya ƙara sauke ajiyar zuciya, sannan a hankali ya miƙa hannu ya ɗebo ruwan shayin wanda zuwa lokacin ya fara hucewa, da ya sha sai ya ji sam shayin babu ɗanɗano tamkar ba wanda ya sha a baya ba yake zuba santin ƙauna.
Ya mayar da cokalin ya ajiye tare da tura kofin shayin gefe, kwamfutarsa wacce tuni haskenta ya ɗauke ya danna da niyyar ya kashe komai ya je ya lallaɓi matarsa ya kwantar mata da hankali ko ya samu ya kwana lafiya ba tare da ya kwan da haƙƙinta ba.

Kasancewar kafin shigowar matar tashi a kan manhajar _facebook_ yake don haka yana shafa masarrafin na’urar sai shafin facebook ɗin ya ƙara bayyana, sabbin labarai suka ƙara bayanna wanda ya dinga yin ƙasa-ƙasa a hankali yana duba su har zuwa in da ya ci karo da wasu zafafan hotuna da aka watso nan take.

Nan take shi ma ya zabura cikin bugawar zuciya da ƙarfi, a gaggauce ya shiga hotunan don ya tabbatar wa da kanshi saƙon da ƙwaƙwalwarsa ke karɓa daga madubin idanuwanshi idan har ba ƙarya suke hasko masa ba…
Hotuna ne irin waɗanda ake yi kafin biki ɗin nan wanda a turance ake kiran su (pre wadding pictures), kuma wacce ke jiki ba kowa ba ce face Maryam ɗinshi Maryam Ahmad Isah domin ga sunan nan an rubuta raɗa-raɗa da manyan baƙi, nata da na angon nata wanda ko daga shigarsa da ya yi take za a gane Bayerabe ne. Sunanshi Abdul-Lateep Adebayo.

Yawan hotunan sun kai aƙalla kala talatin, yayin da hoto na ƙarshe kuma ya zama na gayyatar shagulgulan da aka shirya yi a bikin, wanda suka haɗa da na al’adar Bahaushe da kuma tasu ta Yarbawa…

Idan har ya ce zai tsaya ɗora tantama kan kasancewar wannan Maryam ɗin ba Maryam ɗinshi ba ce to tabbas yana son yaudarar kanshi ne, kowace hujja ta bayyana kanta, saura ya rage ga mai shiga rijiya…

Kullewar da kanshi ya yi ne ya tilasta masa ƙwala wa matarsa kira.

“Jalila! Jalila! Jalila! Fito don Allah, zo ki ga me idanuna suke gane min… Jalila!”

Tana can cikin ƙuryar ɗaki ta gama cika fam tamkar fulawar da ta ji wadataccen yis, jin kiran nashi bai sa ta yi ko tari ba balle ta motsa, tana jin shi kuma yana cigaba da ƙwala mata kiran ta yi mursisi ta ƙi motsi…

Ganin shi ta yi ya faɗo ɗakin tamkar wanda aka cillo, hakan ya sa ta zabura a ɗan firgice.

“Jalila duba ki gani! Maryam ce ba ta mutu ba wallahi… Dama na faɗa Maryam ba mutuwa ta yi ba, mutuwarta shiri ce ba ta gaske ba, ga ta nan yanzu a hoto za su yi aure da bayerabe a Lagos…”

Kallo ta ke auna masa mai ma’anoni biyu, tana masa kallo irin wanda ake yi wa wanda ya fara zarewa ko kuma wanda ya yi shaye-shaye ya fara buga tumɓule, sannan tana yi masa kallon wani wahalalle mai dakon soyayyar mataciyya!

Gefe guda kuma gagarumin hadarin kishi da ya haɗo ya tarwatse a birnin zuciyarta, sai ta ke ji tamkar ta fizge kwamfutar ta yi jifa da ita yadda za ta kwarankwatse ta daina aiki, ko ba komai ta rage wa kanta kishiya guda ɗaya da ta addabi rayuwarta.

“Jalila, ki fuskance ni don Allah! Ki taimake ni mu ceto rayuwar Maryam daga halin da ta ke ciki… Ni na tabbatar dama Maryam ba mutuwa ta yi ba, ta shirya haka ne don ta yi nisa da rayuwarmu a ganin ta hakan shi zai zame mata masalaha a rayuwarta… Don Allah Jalila ki taimake ni ki ce wani abu… Wallahi gani nake yi kamar mafarki nake…”

“Anya ban yi kuskuren jefe maka ƙwayar bugarwa ba cikin tea ɗin da na kawo maka? Zuciyata ta fara tantamar haka…” Karon farko kenan da Jalila ta yi magana, sai dai tun kafin ta ajiye numfashi ta ga ya juya a gaggauce ya fice daga ɗakin.

Kafin ta yi wani ƙwaƙƙwaran motsi ta ji tashin motarsa.. Rass ta ji gabanta ya buga da ƙarfi, zuciyarta ta yi tsalle ta kusa rabuwa da muhalinta.

A kan agogon bango ta fara ɗora idanunta inda ta yi arba da ƙarfe ɗaya har da kusan rabi na dare.

Take ta shiga tuhumar kanta kan inda mijinta za shi a wannan saurayin daren, ta zargin kanta da duk abin da zai same shi a wannan fitar tashi to tana da kamasho…
Tuni sai ga ta ta dire daga gado ta yi waje a guje, sai dai ina kafin ta isa ga ƙofar fita falo ma tuni maigadi ya wangale masa shirgegen gate ɗin gidan ya fice a tamanin.

Ta tsorata matuƙa kamar yadda shi ma mai gadi ya tsaya sororo yana kallon ta, yana son tambayar lafiya yana jin shakka.

Kawai ita ma sai ta bi shawarar da zuciyarta ta ba ta shige tata motar ta take masa baya, duk tsananin tsoron dare da take da shi sai ga shi babu shi a wannan lokacin.

Tseren gudu suka kasa a titin wanda babu wucewar ababen hawa kwata-kwata, yadda yake ba wa motarsa wuta haka ita ma take kwararawa tata motar wuta tamkar dai suna da burin zuwa ƙarshen bangon duniya ne cikin ƙayyadajjen lokaci.

Duk inda ya nufa nan ita ma take jefa tata motar har a hankali ta fara fahimtar gidan iyayenshi ya nufa.

Har suka isa gidan ba su samu tsaiko ba koda na jam’an tsaro ne, yana isa ya fara sakin hon, take mai gadin gidan ya wattsake daga gyangyaɗin da ya soma ya miƙe da sauri ya leƙa, wadatar haske ta sa ya gane motar ba baƙuwa ba ce a gidan don haka take ya kawar masa da gate ɗin, yana shiga ita ma tana jefa tata, shi ya yi hagu ita ta yi dama kowa ya faka.

Babu wanda ya tsaya rufe motarsa cikin su, sai a yanzu ita Jalilar ta fara ɗaukar haske kan abin da ke shirin faruwa ma da ta ga ya fito da Kwamfutar a hannunsa.

A ƙofar falo ya tsaya yana bubbugawa da hannu don gani yake ƙaraurawar jikin kofar ba ta isa isar masa da saƙon da yake buƙata da gaggawa ba.

Ana buɗe ƙofar ya afka.. Mamansu ce ya fara cikin karo da ita tana murje idanu, da alamu ta yi nisa cikin duniyarta ta bacci wannan bugun nashi ya katse ta.

Da ƙarfin sauti ta dakatar da shi.

“Kai lafiya! Me ya faru haka ne ka taso cikin daren nan? Ko wani abu ne ya samu Jalilar?”

“Mama kalli! Maryam ce, na faɗa muku Maryam ba mutuwa ta yi ba aka je aka binne ta, to yanzu ga ta a Lagos ana watsa hotunan aurenta…”

A rikice yake maganar yana nuna wa Mama fuskar kwamfutar.

Daidai lokacin Jalila ta ƙaraso cikin falon, sauran mutanen gida ma duk suka firfito, kowa cikin firgici yake musamman ganin yanayin da ya shigo da shi, ita Maman ma kasa kara yin magana ta yi sai Babansu ne ya karɓe kwamfutar ya duba ya gani.

“Tabbas Maryam wannan ce ba ko tantama! Amma ta yaya wacce ta mutu muka saka ta a ƙabari da hannunmu za mu gan ta a hoto haka ga shi da cikakken sunanta da komai?”

Furucin da Baban ya yi kenan.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.5 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Siddabaru 2 >>

2 thoughts on “Siddabaru 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.