“Kana da gaggawa Isah, da za ka yi haƙuri ka bibiye ni sannu a hankali komai zai warware ga fahimtarka… sa’annan ban cika son yawan tambaya ba musamman idan ya kasance ina kan ƙadamin faɗin abu mai muhimanci ne… ka daure ka ci ribar jin wannan labari.” Ta ƙare roƙon nashi tana mai haɗe tafukan hannayenta biyu ta ɗaga sama.
Isah ya yi shiru yana rarraba idanu a tsakanin su Turaki, fuskar kowa ta nuna cikin shakku yake, amma don su ci ribar jin labarin kamar yadda Ishola ta buƙata sai kowa ya kanne. . .