Skip to content
Part 11 of 16 in the Series Siddabaru by Muntasir Shehu

“Kana da gaggawa Isah, da za ka yi haƙuri ka bibiye ni sannu a hankali komai zai warware ga fahimtarka… sa’annan ban cika son yawan tambaya ba musamman idan ya kasance ina kan ƙadamin faɗin abu mai muhimanci ne… ka daure ka ci ribar jin wannan labari.” Ta ƙare roƙon nashi tana mai haɗe tafukan hannayenta biyu ta ɗaga sama.

Isah ya yi shiru yana rarraba idanu a tsakanin su Turaki, fuskar kowa ta nuna cikin shakku yake, amma don su ci ribar jin labarin kamar yadda Ishola ta buƙata sai kowa ya kanne neman dalilinsa a zuciyarsa.

Ishola ta koma mazauninta ta zauna, a hankali ta miƙa hannu ta ɗauko wani hoto ta ɗago musu shi.

Fuskar wani kyakkyawan matashi mai ji da gayu suka yi arba da shi, daga gani irin yaran nan ne fitinannu duba da yadda sumar kanshi take a cuccure, wato irin gyaran gashin da ake cewa (dada), sa’annan suturar jikinsa ta yadi mai kauri (jeans) a kekkece da salon da gayu ke cewa (crazy).

Fuskar Ishola cike da murmushi ta nuna ɗan yatsanta ɗaya daidai fuskar saurayin ta ce, “Wannan shi ne Jibson, kuma shi ne mutum na farko da aikin Maryam ya fara hawa kanshi bayan kaɓar umarni daga shugaba Kabasa wanda shi ma ya karɓo daga uwargijiyarsa Munansa… yadda abin ya faru shi ne…

… Bayan an gama bincike Maryam tsaf ba a tarar da wani abin cutarwa a jikinta ba, babu alamun fyaɗe ko wani abu da ya danganci (penetrating) jikinta kamar yadda tun farko aka zata, hasalima bayan ƙarin ruwa da aka yi mata sai ga ta ta warware ta koma tamkar wani bai faru da ita ba.

A hukumance daga makaranta aka saka ta a gaba da tambayoyi kan abin da za ta iya tunawa ya faru da ita, sai dai wataƙila ko tana gudun yaɗuwar labarin a duniya ne sosai ya sa ta ce ba za ta iya tuna komai ba, kuma ta nemi alfarma da a rufe maganar tunda dai babu abin da ya same ta, ko hutu da aka so ba ta na sati biyu ta ce ba ta buƙata, wannan ta sa aka rufe maganar tare da cewa ba za a daina gudanar da bincike ba don yi wa tufkar hanci saboda gaba.

Maryam ta koma gidan da suke, a ɗaki ta zauna jugum, ga dukkan alamu tunani take yi kan wancan lamari da ya faru, babu mamaki ma a cikin zuciyarta tana saƙa wa ne yadda za ta sake haɗuwa da Kabir don ta ji me ya aikata mata lokacin da ta je gidansa.
Habiba ta shigo ɗakin ta same ta cikin wannan yanayi, guri ta nema gefenta ta zauna sannan ta saka hannu ta dafa kafaɗarta.

“Maryam ki yi ƙoƙari ki cire tunani a ranki, ki gode wa Allah ma da ya sa Kabir bai cutar da ke ba, babu mamaki ya yi nufin aikata miki wani mummunan abu ne Allah ya kuɓutar da ke…”

Maryam ta ɗaga kai a hankali, muryarta cike da rauni ta ce, “Wallahi Habiba ban san wace irin makantar zuci ce ta saka na biye wa Kabir ba, kodayake dole in tuhumi zuciyata da ydda ta yi sakakin ba wa Kabir gurbin da har ya so ya yi min wasa da rayuwa… wallahi ji nake tamkar ba a gaske komai ya faru ba, wai ni ce da rawar jiki na ɗauki ƙafa zuwa gidan wani gardi… anma Allah ya isa.”

Dariya ta kama Habiba, amma da yake ba muhallinta ba ne sai ta maishe ta murmushi.
“Komai dai ya wuce sai a kiyaye gaba.”

Ta miƙe ta wuce don gabatar da uzurinta.

Maryam ta cigaba da zama tana karanta wasiƙar jaki.

*****
Cikin dare baccinsu ya yi nisa Maryam ta ji tamkar ana bugun ƙofa, da ƙyar ta yakice bacci ta buɗe idanu a hankali, kasancewar ɗakin babu wadatar haske ya sa ba ta iya ganin komai. Ta ji an sake ƙwanƙwasa ƙofar, ta ware ido da sauri alamunta na nuna fargaba, da sauri ta kai hannu ga makunnar fitilar ɗakin ta kunna. Haske ya wadatu a ɗakin, ta kai duban ta ga shimfiɗar Habiba wacce ta yi nisa a duniyarta ta bacci ba ta san bidirin da ake ba.

Aka ci gaba da buga ƙofar fargabar Maryam na ƙaruwa, ta yunƙura a tsorace ta nufi Habiba za ta tashe ta sai kuma ta sauya shawara ta nufi ƙofar cikin tafiyar sanɗa, da ƙaramar murya ta soma tambayar “Waye?”

“Ni ce!” aka amsa da muryar mace.

Fargabar da take ji ta ɗan ragu ga yadda ta saki uban numfashi da ajiyar zuciya, sannan ta saka hannu a hankali ta zare sakatar ɗakin…

Tun ba ta gama cire sakatar ba wata ƙaƙƙarfar iska ta tunkuɗo cikin ɗakin da ƙarfi ta fara watsi da komai na ɗakin. Cikin abin da bai gaza mintuna biyu ba ta sauya komai na fasalin ɗakin. Maimakon Maryam ta gan ta a ɗakinsu ita da Habiba sai ta gan ta a wani guri mai kama da kogon dutse mai tsananin duhu da ƙaƙƙarfar iskar da ke barazanar zare zumbuleliyar jar rigar da ta ga ta bayyana a jikinta lokaci ɗaya, ba ta gama shanye mamaki ba ta ga komai na jikinta ya sauya, wasu irin suturu na bayyana a jikinta, har da hula irin ta sarauta, ta dinga kallon kanta a cikin hasken wutar da ke jikin bango tsilli-tslli da ba su samar da wadaccen haske ba.

Kafin wani lokaci sai ga ‘yanmata santala-santala cikin shiga ta rashin suturta tsiraici suna fitowa daga wasu hanyoyi na cikin kogon dutsen suna zuwa gabanta suna rissinawa da kawo gaisuwa.

Can kuma sai ga wasu su ma sun bayyana cikin shigar jajayen kaya, a gaban rigar kowa an rubuta S da A (wato tambarin duniyar Ujosa). A hannun kowacce akwai ɗan ƙaramin kofi wanda ke cike fal da jini.

Su ma suka zo gaban Maryam suka sunkuya suka kawo gaisuwa cikin wani irin yare da ita kanta Maryam ba ta san yaushe ta koya ba yadda har za a yi magana da shi ta fahimci me aka ce.

Ɗaya daga cikin ‘yan matan ta kama hannun Maryam ta ja ta suka fara tafiya babu gardama ba tirjiya, a cikin doguwa kuma siririyar hanyar kogon dutsen suka yi tafiya mai ɗan nisa sauran ‘yan matan nan na biye da su ɗuuu kamar ƙuda a kasuwar nama, waɗanda suke ɗauke da kofin jini suka dinga dangwalar jinin suna yarfowa Maryam suna cigaba da karanto waƙoƙin girmamawa na barka da zuwa ga ita Maryam ɗin har suka ida babbar fadar tsafi.

Kabir da ta gani zaune a wata a kan wata ƙojalalliyar kujera ya sa ta zabura har ta zame hannun ta daga ruƙon da buduwar ta yi mata.

Kabir ya taso cikin murmushi yana buɗe hannanyensa yana yi mata maraba cikin yaren tsafi. Wata farar tattabara ta taso ta sauka a kan kafaɗarshi.

Maryam dai ja da baya take yi a tsorace, ganin haka ya sa Kabir ya ɓace ɓat a idanunta, sai kuma ta gan shi ya bayyana a gabanta, ya kama hannayenta ya riƙe tare da runtse idanu yana karanto ayoyin tsafi, shikenan sai Maryam ta yi ɗif, duk tsoro da fargaba da ta ke ji suka watse, maimakon hakan ma murmushi ne ya soma malala a sararin fuskarta.

A kan idanunta Kabasa ya ɗaga hannayensa sama ya karanto ɗalasimai na tsafi, take sai ga komai na ɗakin na sauyawa daga kogon dutse mai duhu zuwa wata haɗaɗɗiyar fada mai cike da kyawun tsari, komai na fadar da zallar zinare da lu’u lu’u aka samar da shi.

Ba iyaka nan sauyin ya tsaya ba, hatta ita kanta Maryam suturar jikinta ta sauya daga doguwar jar riga mai ɗigar da jini zuwa fararen tufafi matsattsu da suka kama mata jiki ɗam tamkar wata sarauniya a ƙasashen turawa.

Shi ko uban gayyar girgiza ya yi ya koma ainahin suffarsa ta Kabasa, wannan tattabara ma ta rikiɗe ta zama wata kyakkyawar mace mai kama da mutanen ƙasar Hindu.
Sam babu tsoro ko fargaba a fuskar Maryam, a yanzu ta gane Kabir ba mutum ne tabbatace ba, amfani aka yi da fuskarsa don jan ra’ayinta, wannan ƙyamusasshen tsoho dai shi ne yake zama Kabir don haka babin Kabir dole ya shafe a rayuwarta.
Wasu daga cikin ‘yan matan suka kama ta suka ƙarasa da ita ga wata kujerar dake kusa da ta Kabasa suka zaunar da ita, faruwar hakn ke da wuya fadar ta cika da ihu da sowa da tafi, ‘yan matan nan suka hau rawa suna jinjina ga Maryam a matsayin sabuwar jakada ga duniyar Ujosa wacce ta dalilin ta Uwargijiya Munansa za ta dinga samun abin kalacinta.

A nan aka saka mata kambun girmamawa tare da gabatar mata da dokoki da sharruɗa na uwargijiya Munansa, nan take ta amince, aka ƙara ɗaukar sowa.

Kabasa ya kamo hannunta na hagu ya ɗaga, nan take ta ga tafin hannun nata ya zama madubi, cikin dariyar ƙeta ya sanar da ita cewa wannan madubi shi zai zama abin haska mata dukkan wanda Uwargijiya ta buƙata, sannan ya faɗa mata ya samar da madubin ne daga ruhin mahaifiyarsa tsohuwar matsafiyar da ya gaji komai a wajenta, ya taso kuma ya fi ta taƙadiranci da farin jini gurin manyan Alhazawa da ‘yan siyasa da suke zuwa wajensu neman buƙata. Ganin shahararsa na neman binne ta mahaifiyar tashi ya sa ta fara shirin hallakar da shi a ɓoye, da ya farga sai ya tsafance ta ya mayar da ita karya ya saka ta daga cikin hadimansa masu yi masa bauta.

Ita ko wannan kyakkyawar budurwa ta fito daga jinsin fararen Aljanu ne, ya ɗauko ta ya maishe ta hadimarsa.

Uwargijiya Munansa ba kowa ba ce, face gangar jikin matarsa wacce ya tsaface tun kafin ya gama zama taƙadarin matsafi, ya sanya wani rukuni na jinsin baƙaƙen aljanu suke tasrifi a a gangar jikinta…”

“Za ku sha matuƙar mamaki idan na fayyace muku yadda ‘yan uwanku masu kuɗi da ‘yan siyasa da matayensu ke cincirindon zuwa ga Kabasa yana cika musu ayyukansu… Kabasa ya wuce duk yadda kuke tunani, taƙadarin shu’umin matsafi ne da shahararsa ta sa Ajanu ke shakkar zaluncinsa har suke ƙasƙantar da kai a gabansa suna yi masa bauta…”

Ishola ta yi shiru ta ɗauke ƙwallar da ta taru a idanunta, ba Isah kaɗai ba, dukkanin su hankulansu sun yi mugun ɗugunzuma da jin inda Maryam ta kai kanta… ba su da hurumin da za su karyata wannan labari tunda sun gagga abin da ya faru kafin mutuwar Maryam, su Sergent ne dai suke jin labarin irin jin tatsuniyar gizo da ƙoƙi, babu abin suke aiyyanawa a ransu face wannan rainin hankali ne kawai wannan budurwar ta zo musu da shi, amma dai za su bibiya su ji ƙarshen labarin ƙanzon kuregen.

Ishola ta ajiye hoton da ta ce Jibson ne a jiki sanan ta ɗora cikin labarin.

“Kabasa ya gama sanar da Maryam komai na abin da ke cikin duniyar Ujosa, bayan nan aka raɗa mata sunan da Uwargijiya Munansa ta zaɓar mata wato ZUBESA… nan take kuma Kabasa ya saka allurar tsafi ya zana mata sunan a dantsenta na dama… wannan ƙa’ida ce ta duniyar Ujosa dukkan wanda ke cikinta sai an sauya masa suna, kuma dole sunan sai ya ƙare da S da A wato (SA) sannan a zana masa a dantsen dama, dantsen hagu kuma a zana tambarin duniyar (SA) da wani irin birkitaccen salo wanda sai mutum ya yi amfani da madubi sannan zai fahimci (SA) aka zana…”

Isah ƙwaƙwalwarshi ta ɗau zafi zau… duk waɗannan abubuwan zai iya ɗorar da su a tattare da Maryam domin ba sau ɗaya ya ga zane a dantsenta ba, hatta yadda aka rubuta ZUBESA a dantsen ta na dana ya taɓa gani a wata rana da ba za ta taɓa goguwa a ƙwaƙwalwarsa ba… sannan kamar yadda Ishola ta faɗa tabbas wannan tambari na duniyar Ujosa da ya gani a dantsen Maryam na hagu ya kasa karantawa a kwai ranar da ta taɓa tsayawa a gaban madubi zanen ya bayyana raɗau har ya karanta amma aka ɗaure masa harshe ya kasa cewa komai kan abin duk kuwa da yadda abin ya dinga cinye zuciyarsa… kenan dai dole ya gasgata labarin da Ishola ke bayarwa… Kenan Maryam ɗinsa ƙungiyar tsafi ta shiga… Nan take sai ga hawaye shaaa na gudu a sararin kumatunsa.

Ishola ta cigaba da labari, “Kabasa da kanshi ya kama Maryam ya kai ta ga Uwargijiya Munansa ta miƙa gaisuwa, a yadda take a sunkuye kanta a saitin ƙafar Uwargijiya Munansa Kabasa ya yi tsafi ya yanki hannunsa jinin ya dinga zuba a kan Maryam yana gangarawa kan ƙafar Uwargijiya.

Nan take sai ga magana ana yi wa Zubesa (Maryam) jinjina da fatan ta cika dukkan buƙatun uwargijiya.

Abu ɗaya ya rage shi ne wanka a kogin jini. Wani ɗan ƙaramin kwatamin ne da ke cike fal da jini, haka Kabasa ya kama hannun Maryam ya kai ta ga kogin ta tattaka har ta nutse a ciki, jim kaɗan ta ɗago ta fito.

Cikin farin ciki Kabasa ya kama ta ya sumbace ta a goshi sannan ya ya soma karanta ɗalasiman tsafi. Kayan jikinta suka sauya zuwa ainahin yadda suke a da, wata irin iska ta ɗauke ta ta yi sama da ita, sai ga ta a bakin ƙofar ɗakinsu…

Cikin tsoro da ɗari-ɗari ta tura ƙofar a hankali, ta dafe ƙirji da hakan ke nuni da faɗuwar gaba. Ba komai ne ya saka mata wannan ɗimaucewa ba face ganin Habiba zaune kan sallaya ta haɗe tafukanta tana addu’a. Fargabar Maryam ba ta wuce ta amsar da za ta ba wa Habiban ba idan ta titsiye ta da tambayar inda ta je cikin wannan dattijon dare.
Tana nan tsaye tana shawara irin ta mai shiga rijiya ta hangi Habiba ta shafa addu’ar kuma ta waiwayo ta ce.

“Kin fito kenan?”

Maryam ta daburce, “E… e… daga… daga..”

Habiba ta yanke mata wahalar fargaba da cewa “Ai na tashi na ga kin shiga toilet… ina ta jira shiru-shiru kin ƙi fitowa, da na matsu sai na tsugunna a bakin toilet ɗin na yi abin da zan yi na miƙe…” Ta ƙare cikin ƙaramar dariya.

Maryam ta sauke bayyananniyar ajiyar zuciya tamkar wacce aka zarewa ƙaya, sai ta taka ta shige ɗakin ba tare da ta sake magana ba tana tsoron kar rashin gaskiyarta ya bayyana, ba ta yi mamakin kuma abin da Habiban ta ce ba kan maganar shiga toilet, ta gane aikin Kabasa ne ya kawar da komai.

Ganin ta zarce katifarta za ta kwanta Habiba ta ce, “Ba za ki yi nafila ba?”
“Ba na sallah.”

Ta ba ta amsa tare da faɗawa kan katifarta ta kwanta.

Washegari dukkan su suna da lecture ta ƙarfe takwas, don haka da wuri suka tashi suka fara shiri. Habiba na toilet tana wanka Maryam na zaune ta shirya takaddu a jakarta.

Daga saman kanta ta ga hayaƙi na tashi don haka ta ɗaga kan da sauri, Kabasa ya bayyanar mata da fuskar Kabir, da wani irin sauti ya soma magana.

“Ki kalli madubin hannunki ki karɓi umarnin uwargijiya…”

Da sauri ta ɗaga tafin hannunta ta ga fuska ta bayyana kamar a madubi, take ta shaida fuskar Jibson tsohon saurayin Khairat tsohuwar ƙawarta.

Ta ɗaga kai a gigice tana duban fuskar Kabir, ya gyaɗa mata kai sannan ya ce, “Haɗa idanunku kawai ake buƙata, sauran aikin na hadimai ne su za su sarrafa komai…” yana gama faɗar haka ya ɓace ɓat. Hoton jikin hannunta ma ya ɓace.

Nan ta ji komai ya daina yi mata daɗi, jikin ya nuna alamun sanyaya har Habiba ta fito daga wanka ta tarar da ita a wannan yanayi. Ba ta yi mata magana ba ta cigaba da shirye-shiryenta, sai da ta kusa gamawa sannan ta dubi Maryam ɗin.

“Wai lafiya kuwa Maryam na ga jikinki duk ya sanyaya? Ko waya aka yi miki bayan fita ta?”

Girgiza kai Maryam ta yi ta mike ta fice zuwa toilet ta yi wanka ta fito ta shirya suka karya a gurguje suka fice zuwa makaranta.

Habiba tana kula da canjin yanayin Maryam sai dai ba ta cika matsanta mata jin damuwarta ba tun da ta fuskanci ita Maryam ba son haka take ba, tana ɓoye mata abubuwa da dama don haka ita ma take baya-baya.

Maryam ita ta riga fitowa daga lecture kasancewar lecturar ya nemi su yi masa uziri kan kiran gaggawa da ya samu don haka ya fita tun lokacinsa bai cika ba.

Maryam ta taho a kasalce, ga dukkan alamu tunani take kan lamarin da zai faru a gaba kaɗan a kan Jibson da aka buƙace shi, ba ta san me zai faru ba, ba san hanyar da za ta bi ta kai shi ga duniyar tsafi ba, an ce haɗa idanunsu kawai ake buƙata, ba ta san me zai faru ba idan idanun nasu suka haɗu.

Kai tsaye ƙarƙashin wata bishiya ta dosa wacce suka saba zama, kafin ta isa ga bishiyar kuma sai ta biyo ta wata siririyar hanyar bayan wani dogon gini, don haka a kan wannan siririyar hanyar suka yi kicuɓus da Jibson yana tare da wata fitsararriyar yarinya duba da yadda take shisshige masa.

Carf idanun Maryam cikin na Jibson, ita ba ta gani ba, amma wani haske ne ya fito daga idanun nata ya faɗa na Jibson.

Ta kawar da kai ta cigaba da tafiya tana dafe ƙirjinta wanda ko ba a faɗa ba yanayinta ya nuna faɗuwa gaban nata yake yi.

Tana nan zaune a kan kujera ƙarƙashin bishiya sai ga Jibson a rikice ya zo gare da da wasu ruɗaɗɗun kalamai.

Abin da yake furtawa ya yi matuƙar saka ta shiga damuwa da tashin hankali, duk iskar da bishiyar ke bugowa amma ita gumi ne ke karyo mata ta ko’ina.

Tamkar zai ɗauke ta ya tafi da ita haka yake ta magiya kan ta zo su je, ba ta san kuma inda za su je ba!

Mutane suna ta wucewa suna kallonsu suna mamakin yadda Jibson ya mayar da mata tamkar rigar sakawa, yau a gan shi da wannan gobe a gan shi da waccan.

Aikin Duniyar Ujosa ya fara tasiri a jikin Maryam don haka cikin fitar hayyaci ta miƙe ta bi Jibson zuwa gidansa.

Tamkar mayunwacin zaki ya samu nama haka mummunar alaƙa ta shiga tsakanin su.
Bayan komai ya lafa Maryam ta tashi ta tafi gidansu cikin kukan tashin hankali ta bar shi a nan lulluɓe da bargo fuskarsa cike da farin cikin samun biyan buƙatarsa.

Babu yadda Habiba ba ta yi ba don ta ji abin da ya faru da Maryam ɗin ta wuni tana kuka amma ta kasa yin magana har ta gaji ta ƙyale ta.

Washegari aka tashi da labarin mummunar mutuwar da Jibson ya yi, yarinyar da ya ɗauka don taya shi kwana a daren ta bayyana yadda komai ya faru cikin tsananin tashin hankali saboda kai tsaye an ɗora alhakin mutuwar tashi a kanta.

Yarinyar ta ce “Cikin dare muna bacci ya tashi yake ta ihu da zambarwa yana riƙe ciki yana cewa cikin nashi na yi masa ciwo, jim kaɗan kuma sai ya fara cire kayan jikinsa yana watsi da su yana ihu da kururuwa yana sosa jikinsa da ya yi tamkar wanda ake zanewa da bulala…

Hankalina ya yi matuƙar tashi da yadda na ga jini na kwarara daga gabansa tamkar an buɗe bakin famfo, jinin kuma shi ya cigaba da zuba yana malelewa a ƙas har sai da ya durƙushe ya faɗi ƙas… daga nan kuma ya ɓigire ya kwanta jinin na cigaba da tsiyaya har komai na jikinsa ya daina motsi…”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 2.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Siddabaru 10Siddabaru 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.