Skip to content
Part 10 of 16 in the Series Siddabaru by Muntasir Shehu

Cigaban labari

Isah ya zabura ya miƙe a gigice ganin shigowar Turaki, Kamal da kuma ‘yansanda su Sergent. Mamakin ganin su bai bar shi ya iya amsa sallamar da suke dokawa ba.

Suka tsaya a falon cirko-cirko suna wa juna kallon-kallo, dukkan su sararin fuskokinsu nuni suke da bayyanannen mamakin da zuciyoyinsu suke ciki.

Budurwar ta taka a hankali cikin fara’a ta isa ga su Turaki tana faɗin, “Marhabin da zuwan ku… bismillah ku ƙarasa ku zauna mu yi karin gaba ɗaya don na san ku ma ba ku samu sukunin karyawa ba.”

Babu wanda ya tsinka cikin su, maimakon hakan ma nufar tantsama-tantsaman kujerun falon suka yi suka zazzauna.

Isah ya fitar da numfashi mai nauyi, abin da ke ƙasan ransa ya kasa ɓoyuwa. “Ta yaya kuka san ina nan har kuka zo ku ma?”

Kafin wani cikin su ya tanka budurwar nan ta yi caraf ta ce, “Me ye abin mamaki cikin haka har za ka yi tambaya? Ko ka manta cewa na sa an karɓi motarka? To da ita aka yi amfani aka gamsar da su har suka amince suka biyo ‘yan aike.”

Isah ya zuba wa Turaki ido yana neman tabbaci kan wannan magana, gyaɗa masa kai Turaki ya yi, sai ya koma ya zauna yana ajiyar zuciya, take kuma wani tunani ya rikito masa a kan wannan budurwar, ya kamata fa a ce sun san da wa suke tare tun kafin tufkarsu ta warware.

Budurwar ta miƙe ta ce “Ina zuwa.” Ta fice daga falon.

Bayan fitar ta Isah ya yi zumbur ya miƙe daga inda yake zaune ya koma kusa da su Turaki.

“Ku ba ni labarin yadda kuka zo nan.”

Cikin mayar da numfashi Turaki ya ce, “Muna can hotel cikin jimamin inda ka tafi sai muka ji ana buga ƙofa, bayan an buɗe sai muka ga wasu mutane farare kamar larabawa, amma abin mamaki Hausa raɗau a bakinsu, suka ce mana kai ka turo a ɗauke mu wai ka gani inda Maryam take… to abin da ya sa muka yarda da su shi ne ganin motarka a wajensu sannan kuma suka kira ka a waya da bakinka ka tabbatar mana cewa kai ka turo su kuma kana buƙatar mu taho cikin gaggawa…”

Isah ya zazzaro idanu cikin ɗimauta, jikinsa har rawa yake yi ya ce “Ni..? Ni…? Ni ne aka kira? Yaushe kuma? Wayar tawa fa ma an karɓe ta a waje…”

Daidai lokacin budurwar nan ta dawo falon ɗauƙe da ƙaton faranti shaƙe da kayan karyawa. Ta dire a kan faffaɗan teburin da ya ci kusan rabi na kason ɗakin. Ta hau zuzzuba musu tana miƙa musu, sai dai duk wanda ta miƙawa ya karɓa ajiyewa yake, da ta fuskanci haka sai ta dakata ta ɗaga kai ta dube su ɗai-ɗai fuskarta ƙunshe da damuwa muryarta a sanyaye ta ce, “Haba ‘yan uwa! Me ya sa kuke tunanin zan cutar da ku? Don me ya sa ba za ku yadda da ni ba? Me ya sa ba ku gamsu ni ce zan fito muku da hasken da ke cikin duhuwar rayuwar Maryam?”

“Me zai saka mu yadda da ke bayan ko sunanki ba mu sani ba? Sannan kuma…”
“Sunana Ishola! Kar ku ji sunan ya saɓa da yadda kuka saba ji, to ba wani abu ba ne ni ba Bahaushiya ba ce!”

Turaki zai yi magana Ishola ta yi saurin dakatar da shi da hannu, sannan ta ce “Ku karya don Allah! Na sani zai ɗauke mu lokaci mai tsayi ban gama ba ku labarin Maryam ba…”

Ta ɗauki kofin tea ta kurɓa, sannan ta ɗaga kai ta kalli Isah. “Bismillah.”

Isah ya ɗauka ya sha, sannan duk suka fara sha.

Falon ya yi tsit kowa ya mayar da hankali gurin take cikinsa har zuwa wani lokaci.
Sai da suka kammala karyawa suka gyatse sannan Ishola ta tattara komai ta kawar, ta dawo ta samu guri ta zauna gaban teburin, ta sake baje musu hotunan Maryam da sauran hotunan wasu mutane.

Ta ɗago ta kalle su ta sauke numfashi, sannan ta gyara murya ta ce.

“Zan mayar da ku baya ne cikin labarin Maryam da zan ba ku, sa’annan za ku iya jin wasu kuramen baƙi waɗanda sun keɓanta ne kawai gare mu, idan kuma kun bi ni da kyau za ku fahimci ma’anoninsu.”

Ta yi shiru tana mayar da numfashi, tana ganin yadda Sergent ke mutsu-mutsu ta fahimci maganganun nasu yake naɗa a ɓoye, ta saki murmushi. “Ka fito da recorder ɗinka ka ɗauki komai, don hakan shi zai zama hujja gare ku da ni kaina…”
Ta gyara zama ta fara,

Ƙaddarar Maryam (Siddabaru)

Labarin zai datsa ne daga ranar da Kabasa ya bayyana ga Maryam a jami’a yana mai amsa sunan Kabir, babu mamaki Allah ya ƙaddara cewa sakamakon taƙadiranci da kangara irin ta Maryam da kuma yadda ta ƙuntata wa iyayenta ya sa ta faɗa tarkon Kabasa…

Ranar da ta ke zaune a makaranta tana cin abinci cikin damuwa, a ranar Kabasa ya fito shawaginsa tare da ‘yan aike kamar yadda ya saba lokaci zuwa lokaci.

Hango Maryam da ya yi a zaune tana cin abinci sai ya ji a ransa ita ɗin wani ɓangare ce ta nasararsa a DUNIYAR TSAFI, don haka nan take ya bayar da umarnin a jirkita masa halittarsa zuwa ta saurayin da aka saba mayar da shi a duk lokacin da ya so ɗana tarkonsa a jami’ar. Ba tare da ɓata lokaci ba kamanninsa suka sauya daga yadda yake tsoho tukuf mai cike da ƙazanta zuwa kyakkyawan saurayi mai ji da aji, aka kuma samar da tsadaddiyar motar da zai hau, sannan aka sauke shi daga kan iska da ya saba tafiya a kai.

Babu wanda zai kalle shi bai ji ya burge shi ba, mata kuwa tamkar su sace shi su gudu.
Kai tsaye wajen Maryam ya nufa yana mai bayar da umarnin a samar da dukkan wani nau’i na abin sha a ajiye a gaban teburin da ta ke zauna, shi kuma ya zauna a kujerar da take fuskantar ta.

A kallon farko da suka yi wa juna wani abu mai haske ya fita daga idanunsa ya faɗa nata, wanda wannan ba komai ba ne face wani dafi da zai kanainaye zuciyarta ya dinga haifar mata da jin tsoron sa da kuma kasa ƙetare umarninsa.

Duk ɗago kan da za ta yi sai sun haɗa idanu, idan sun haɗa idanun kuma sai ya watsa mata wannan dafi wanda shigar sa jikinta ya sa ta dinga jin faɗuwar gaba, ƙarshe da ta ga ba za ta iya jurewa ba ta tashi ta bar wajen.

Bayan barin ta wajen suka tuntsire da dariya shi da sauran muƙarrabansa, dariya suke yi ta farin cikin samun nasarar cafko Maryam zuwa duniyarsu ta tsafi. Abu ɗaya ne ya rage shi ne yadda za a sanya mata sinadarin aiki a jikinta, wanda haka shi ya sa Kabasa cigaba da zuwa gurinta a matsayin mai neman soyayyarta, tasirin dafin tsafi ya sa ta kasa bijire wa karɓar soyayyar.

A cikin sati biyu rak Kabasa ya gama da zuciyar Maryam yadda ta dinga jin duk duniya babu wanda take tsananin so da ƙauna face Kabir (Kabasa), kuma za ta iya yin komai a kan soyayyarshi. A washegarin ranar ne ya nemi da ta zo ta ga gidansa, babu musu ta amince.

Habiba wacce suke ɗaki ɗaya ta so kawo tarnaƙi ta hanyar nusar da Maryam ɗin illar kwasar jiki ta bi Kabir da sunan za ta ga matsugunninshi.

Hankalin Kabasa ya ɗugunzuma ainun, ba zai taɓa bari Habiba ta watsa masa garinsa ba don haka nan take ya yi umarni da a far mata, sai dai ‘yan aiken sun kasa kataɓus ɗin komai a kanta sakamakon yadda ta kasance abida mai yawan ibada, sannan ba ta wasa da azkar.

Kabasa ya ƙara wa ‘yan aike ƙarfi amma duk da haka ba su iya komai ba, don haka da kanshi ya rikiɗe ya zama iska ya je ya shige jikin Maryam ya toshe mata kunnuwan zuciya yadda ba za ta ji duk wata nasiha ko kafa hujja ba, zuciyar tata ya janye gaba ɗaya ma ya tafi ya kai ta duniyar tsafi ya ajiye, don haka lokacin da ta shirya ta bi Kabir ma a makance take ba ta ji ko ganin komai sai yadda ya yi da ita.

Ganin idanun Maryam a cikin mota suke tafiya ita da Kabir, sai dai baɗini cikin iska suke tafiya tare da Kabasa.

Da a ce Maryam na nan za a tambaye ta, to da tabbas cewa za ta yi wani wani tafkeken gida mai cike da kayan alatun rayuwa suka nufa, sai dai saɓanin ganin ta fadar tsafi aka nufa da ita.

Koda suka shiga gidan ta ga yadda aka zuba daula a gidan sai duk ta kiɗime, ta zama ‘yar ƙauye. Murmushi Kabir ya saki tattausa a lokacin ya ce da ita.

“Ya kika ga ɗan akurkin nawa?”

Cikin zari idon mamaki ta riƙe baki, “Akurki? Yanzu in ban da neman magana wannan danƙararen gida za ka kira da akurki?”

Yana cigaba da murmushi ya zauna, “Akurki ne mana, ni ba na kallon sa a wani babban gida idan na yi la’akari da maƙwaftana.”

“Hmmm! Haka ne kuma.” Ta ce ita ma sannan ta samu guri a kujerar kusa da shi ta zauna.

“Yanzu a fara kawo miki abin taɓawa ki fara da shi ne ko kuwa tashi za mu yi mu zaga gidan ki ga tsarin ginin?”

Kanta a sunkuye ta ce, “Duk yadda ka ce shi ne daidai.”

Bai yi magana ba ya janyo wayar tafi-da-gidanka da ke ajiye a falon ya kira ya yi magana sannan ya dawo ya zauna yana cigaba da jan ta da hira.

A takure take sosai, ta kasa sakin jiki, yayinda ta ke ta son saƙa zaruruwan tunani tsakanin ƙwaƙwalwarta da zuciyarta amma sai komai ya gagara, jin ta take tamkar wata gunki ce ita, tamkar babu wani abu da ke sarrafa kanshi a jikinta.

Aka turo wata ƙofa aka shigo falon, wata matashiyar budurwa ce kyakkyawa son kowa ƙin wanda ya rasa ta ƙaraso ta ajiye ƙaton farantin da take ɗauke da shi a kan teburin tsakiyar falo. Bayan ta ajiya ta je gaban Kabir ta rankwafa kanta a ƙan kafarsa sannan ta ɗago ta miƙa masa hannunta ya sumbata daga nan ta miƙe ta fice daga falon.

Komai a kan idanun Maryam ya faru, ya kamata a ce ta ɗisa ayar tambaya a kan wannan lamari in da a ce a cikin hayyacinta ta ke, sai dai inaa sam ba ta ji komai ba cikin ranta koda na kishin yadda ya kama hannun budurwar ya sumbata…

Kabir da kanshi ya tsiyaya mata jan lemon a kyakkyawan farin kofin gilashi ya miƙa mata, babu musu ta karɓa ta kai bakinta, sai dai karaf idanunta suka gane mata jini ne cikin kofin ba lemo ba, gabanta ya yanke ya faɗi, ta ɗago da sauri ta kalle shi, ya kanne mata ido ɗaya tare da girgiza kai, don cire mata shakku ma sai shi ma ya tsiyaya a kofi ya sha, kawai sai ta tsinci kanta da kafa kai ta shanye jinin, nan take jikinta ya soma wani irin yammmn kamar ƙuda na bin bayan gida, kafin wani lokaci hajijiya ta fara yawo da ita.

Lokacin da ta ke gani dishi-dishi ta ga san da Kabir ya miƙe yana tsallen murna, daga bisani duhu ya mamaye ganinta, komai ya tsaya mata cak!

Cicciɓar ta Kabir ya yi ya nufi ɗaki da ita ya watsar da ita kan gado, ya yi girgiza ya koma siffarsa ta tsoho tukuf sannan ya soma surutai irin na tsafi, nan take wani irin ruwa mai yauƙi da wari ya soma zubowa daga sama, ya tara bakinsa ruwan na shiga cikin yana zarcewa cikinsa. Ya ɗauki a ƙalla mintuna ashirin yana shan wannan ruwa na tsafi sannan ya ɗauke kai, ya soma ambaton wata Kalma “Basasa! Basasa!”

Wata shirgegiyar karya ta faɗo daga sama bakinta na dalalar da yawu mai shegen yauƙi, ya tara hannunsa yawun karyar na zuba a ciki, sai da ya tara da yawa sannan ya ɗauke hannun ya isa ga Maryam da ke yashe a kan gadon, wata iska mai ƙarfi ta bayyana wacce ta kwaye dukkan suturar da ke jikin Maryam ta yi watsi da su, wannan yawun karya da ke hannunsa ya watsa a gabanta sannan ya bi ta ya haike mata.

A cikin wannan saduwa da yayi da ita ya zuba mata dukkan tsumin tsafin da ya haɗa a kanta, ya kai a ƙalla awa biyu yana zuba mata mugunyar tsafin kafin ya ɗaga ta ya koma da baya ya zube a kasa sharab, ko ina jikinsa ruwan gumi ne ke fita.

Har lokacin karyar nan na nan a tsaye hawaye na fita a idanunta, lura da hakan da Kabasa ya yi ya daka mata tsawa, nan take sai ga ta ta girgije ta zama wata tsohuwar mata tukuf wacce ko tsayuwa ba ta iya yi, idanun tsohuwar cike da hawaye.

“Kukan me kike yi tsinanniyar uwa….?” Ya runtse idanu, “…samun ki a matsayin uwa asara ce! Zamowar ki uwa a gare ni masifa ce! Ƙaddara ce! Tashin hankali ne! Saboda haka yau za ki bar duniya… amfaninki gare ni ya ƙare yau, don haka za ki bar duniya ki je ki girbi abin da kika shuka…!”

A yadda idanun nashi ke rufe ya soma karanto ayoyin tsafi, nan take jikin tsohuwar nan ya fara karkarwa tamkar wadda inji ke jijjigawa. Ta soma ƙaraji tana roƙon sa “Kar ka kashe ni ɗana! Kar ka…..” Da ƙyar take furtawa.

Ya buɗe idanunsa, ya sa hannu ya wanka mata mari, take ta kife a ƙas. Wasu irin hallitu masu kama da kunama suka dinga rikitowa daga sama suna zuba a kanta suna gasa mata cizo, ta dinga malelekuwa a ƙasa tana ihu da ƙaraji, tun tana motsi har ta daina, sai kuma ƙwarin suka ɓace ɓat! Kamar ɗaukewar ruwan sama. Jikinta ya soma fitar da hayaƙi.

Kabasa ya sake runtse idanunsa yana karanto ayoyin tsafi hannunshi na nuni da gawar tsohuwarshi, nan take sai jikinta ya fara zagwanyewa yana zama wani irin farin ruwa mai malalewa a ƙasa, Kabasa bai gushe ba yana cigaba da karanto ayoyin tsafi idonshi a rufe har sai da jikin tsohuwar ya gama zagwanyewa sannan ya buɗe idanun, ya zame ya faɗi ƙasa a matuƙar galabaice yana mayar da numfashi, kowace kafa a jikinsa ruwan gumi ke tsiyaya. Ya tuntsire da dariya yana mai zazzare idanunsa, idan ya yi dariyar sai ya yi ɗif ya ɓata fuska, sai kuma ya ƙara rushewa da dariya, haka ya yi ta yi har zuwa wani lokaci.

Sannan ya miƙa hannunsa sama ya yi kira da cewa… “Usshhah… baba maaagaaa…!”
Sanda ta bayyana a hannunsa ya riƙe ta ya yunƙura ya miƙe zuwa kan zagwanyayyen ruwan jikin tsohuwar ya dinga zagaya ruwan da sandar yana cigaba da karanta ayoyin tsafi. Ruwan ya soma cakuɗewa yana dunƙulewa har ya haɗe ya zama kyakkyawan ɗan ƙaramin farin madubi, ya sunkuya ya ɗauki madubin ya dinga juya shi yana dariyar farin ciki, ya taka da ƙyar ya isa ga Maryam da ke yashe a kan gado har yanzu ba ta farko ba. Hannunta na hagu ya kamo ya ɗora madubin a kai, a hankali madubin ya soma zama hayaƙi yana shigewa cikin fatar hannunta har ya gama shigewa gaba ɗaya sannan ya ɗaga ɗanyatsanshi ɗaya ya yanki fatar jikinshi da kakkaifan zallaƙeƙen farcen da ke jikin yatsan, jini baƙiƙƙirin ya yi tsartuwa, ya dangwali jinin da yatsan ya kama dantsen Maryam na hagu ya zana mata harrufan da suka zama tambari na duniyar UJOSA duniyar tsafi, wato (SA).

Daga nan ya ɗaga bakinsa ya busa iska, iskar ta fito da ƙarfi ta dinga bajewa tana hautsina komai na ɗakin, cikin haka dukkan kayayyakin jikin Maryam suka daddawo inda suke tamkar wani abu bai faru a jikinta ba.

Ya sa aka ɗauke ta cikin iska aka kai ta bakin ƙatuwar bishiyar tsamiyar da ke dajin bayan makaranta aka yasar ta a nan.

Allah ya kawo wasu ɗalibai suka zo wucewa suka gan ta a gurin, sai suka yi tunanin ɗaliba ce wani abu ya faru don haka suka gaggauta koma wa makaranta suka kai rohoto.

Nan da nan labari ya cika makaranta, Habiba na cikin makaranta a lokacin, tana jin labarin gabanta ya faɗi, zargi ya kama ta na tunanin ko Maryam ce don haka cikin damuwa ta fice ta nufi gurin, tana zuwa ta ratsa da ƙyar ta cikin dandazon mutane har ta isa ga inda Maryam ke a yashe, kuka ta fashe da shi ta faɗa kan Maryam, da ƙyar aka janye ta ana ba ta haƙuri da yi mata tambayoyi. Ba ta iya amsa ko tambaya ɗaya ba ta bi ayarin masu kai rahoto zuwa ofishin kula da walwalar ɗalibai da kuma ofishin jami’an tsaro aka zo aka ɗauke Maryam.

Dayake Kabasa ya riga ya gama shu’umancinsa a jikin Maryam ya sa duk binciken da aka yi ba a tarar da komai ba kamar yadda aka dinga zaton ko fyaɗe aka yi mata….”

Dukkan su wani irin kallo suke wa Ishola, koda dai akwai alamun sanyayar jiki a tattare da su. Isah shi ya fi kowa shiga ruɗu, akwai abubuwa da yawa da suke ƙoƙarin hautsina masa lissafi cikin wannan labari da Ishola ta fara ba su… Can cikin sashen adana bayanai na ƙwaƙwalwarshi yake ƙoƙarin lalubo tabbaci na yadda wata rana ya taɓa ganin wani zane a dantsen hannun Maryam a lokacin ta dawo gida hutu, zanen a jujjuye yake amma tabbas ya yi kama da (SA), a lokacin kuma ya so ya yi mata magana kan wannan zane mai kama da tattoo amma sai ya ji tamkar an ɗinke masa harshensa ne.

Kenan akwai damshin gaskiya cikin wannan labari na bakin Ishola?

Dole suna buƙatar su san wace ce ita kanta wannan Ishola ɗin da yadda ta alaƙantu da Maryam har take bayar da labarin da babu yadda za a yi ta sani in dai har ba a kan idanunta aka yi ba. Wannan ta sa Isah muskutawa ya nisa ya watso tambayar.

“Wai tukunna ma shi wannan Kabasan wanene shi? Ke ma ta yaya duk kika san an yi waɗannan abubuwa da kike labarta mana su…?”

Murmushi Ishola ta saki tare da miƙewa ta zo gaban Isah ta tsaya, hannayenta ta rungume a ƙirji tana cigaba da aika masa da saƙon murmushi da ya sa ya dinga jin ƙirjinshi na bugawa dif! Dif! Dif!

Ishola ta kada baki ta ce….

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Siddabaru 9Siddabaru 11 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.