Skip to content
Part 12 of 16 in the Series Siddabaru by Muntasir Shehu

Wannan mutuwa ta Jibson ta gigita lissafin Maryam matuƙa, wuni ta yi tana kuka a ƙunshe a ɗaki har sai dai Habiba ta gaji ta da rarrashin ta ta ƙyale ta nufi makaranta don tana da lecture.

Labarin mutuwar Jibson ya karaɗe garin gaba ɗaya kasancewar zamani da ake ciki na wadatuwar kafofin watsa labarai na yanar gizo, amma da yake ba a cikin makaranta abin ya faru ba ya sa babu wani tsaiko da aka samu cikin makarantar.

Habiba ta dawo ta riske Maryam har lokacin ba ta daina kuka ba.

“Maryam zuwa yanzu na fuskanci ba iya kukan mutuwar waccan mutumin kike ba, don kuwa in dai kukan mutuwar sa kike ya ci a ce yanzu kin dangana ko da a ce shaƙiƙinki ne balle ni ban ga abin da ya gama ki da shi ba, ko kuwa kina da wani abu a tsakanin ku ne a cikin mutuwar tashi?”

Maryam ta fyace hanci, idanunta ja zur, ta miƙe daga in da take ta isa ga jakar kayanta ta zuge ta fara zaro kayanta.

Habiba ta tako a hankali ta dafa kafaɗar Maryam.

“Maryam kodayake na san ni ba jininki ba ce, amma na yi zaton zaman da muka yi ya kai taƙin da ba za ki ɓoye min wata damuwa taki ba… ki yi haƙuri zan cigaba da taya ki da addu’a a kan dukkan abin yake damun ki, sannan ina mai shawartar ki da ki sauya shawarar tafiya idan har hakan kika ƙudure a ranki, kwanaki kaɗan ya rage mu cinye wannan zangon karatun, don haka dukkan wani abu da za ki yi kya yi shi idan kin koma gida.”

Daga haka ta miƙe ta koma ta cigaba da sabgoginta ta bar Maryam shanye da hannaye ta kasa cigaba da zaro kayan nata.

Bayan kwana biyu abubuwa suka yi sauƙi, Maryam ta warware ta cigaba da zuwa makaranta cikin ƙoƙarin yakice komai ta watsar na abin da ya shafi Kabasa da shirginsa…”

Ishola ta yi shiru ga bayar da labari, ta miƙe tsam ta isa gaban teburin ta ɗauko wani hoto ta nuno musu shi.

Fuskar wani matashin saurayi ne a ciki wanda ko ba a faɗa ba saurayin zai kasance kamili, karimi, duba da yadda kwarjini ke fita a fuskar tashi.

Ishola ta matse hawaye, muryarta na karkarwa ta ce “Kun ga wannan? Ustaz Jaafari kenan! Na sani tuni zuciyoyinku suka wassafa muku yadda zai kasance kamilalle duk da ma na riga na samar muku da tunani kan hakan da na ce Ustaz Jaafari.”

Babu wanda ya iya magana cikinsu, Ishola ta ajiye hoton ta cigaba da cewa. “Bari ku ji yadda azal ta faɗa masa har shi ma ya rasa nashi ran…”
Isah ya zabura ya katse ta. “Kina nufin ki ce wai dukkan waɗannan hotunan mutanen duk mutuwa suka yi irin ta Jibson?”

“Haka ne!” Ishola ta amsa cikin murmushi.

Isah ya soma birkita hotunan cikin tashin hankali yana babbankaɗo hotunan, ya zaro hoton AbdulNasir, cikin zazzare idanu ya ɗago yana duban Ishola.

“Kenan mutuwar AbdulNasir ta alaƙantu da wannan ƙaddara ta Maryam?”

Murmushi Ishola ta saki, “Sannu a hankali za mu zo wannan gaɓar…”

Ta ɗora cikin labarin Maryam

“…Bayan kwanaki uku da mutuwar Jibson, Maryam na aji suna ɗaukar darasi, hankalinta sam ba ya tare da Malamin nasu, ta lula a duniyar tunani, can ta ji an taɓa daga gefenta, firgigit ta yi ta juya tamkar wadda ta farka daga mummunan mafarki.

Ta sani kafin wannan lokaci a zaune take kusa da wata Shamsiyya abokiyar karatun ta, amma a yanzu Kabasa ta gani a zaune kusa da ita da siffar fuskar Kabir.

Ta zabura a gigice za ta zunduma ihu amma sai Kabasa ya yi caraf ya toshe mata baki da hannu, Maryam ta dinga zazzare idanunta da suke cike da matuƙar tsoro, babu mamaki tsoron kar a ga abin da ke wakana tsakaninta da Kabasa take, sai dai abin da ba ta sani ba ita kaɗai take bidirinta don babu wanda yake ganin Kabasa sai ita.

Kabasa ya saka ɗaya hannun nasa ya kamo hannunta, take madubi ya bayyana ɗauke da fuskar Ustaz Jaafari. Maryam ta ƙara tsorata, ta ƙwace hannunta ta miƙe zumbur tana girgiza kai bakinta na furta “A’aaa! A’aaa!”

A wannan lokacin hankalin ‘yan ajin ya dawo kanta ganin yadda ta miƙe ita kaɗai tana surutai.

Lecturar ya yi tsaye cikin ɗaurewar kai da mamakin ganin abin da ke faruwa.

Maryam ta kwasa da gudu ta yi waje tana gursheƙen kuka, dukkan ɗaliban ajin fuskokinsu suka cika da mamaki.

Lecturar ya ƙaraso ga kujerar da Maryam ta tashi ya kallai Shamsiyya.

“Me ya same ta ne?”

Shamsiyya ta girgiza kai, “Gaskiya ba na ce ga abin da ya same ta ba, lafiya dai muka shigo muka zauna, ni ma kawai gani na yi ta miƙe tana surutai.”

Ya gyaɗa kai, “Allah ya kyauta.”

Ya cigaba da bayar da darasi.

Maryam na tsaye a jikin wata bishiya tana sharar hawaye, Kabasa ya sake bayyanar mata ciki hayaƙi, iyakar fuskarshi ce kawai take iya gani, sauran duk hayaƙi ne.

Fuskar tashi a ɗaure take tamau, da kakkausar murya ya ce, “Karon farko kar ki saɓawa umarnin Uwargijiya Munansa…”

“Amma me ya sa za a zaɓi wanda bai ji ba bai gani ba?”

“Uwargijiya ba ta buƙatar lalubalanta…”

Ta buɗe baki za ta ƙara magana ya yi zaraf ya turo mata hayaƙi zuwa cikin hancinta.

Ta runtse idanu, jim kaɗan ta buɗe su, sun rine ja zur, fuskar tata ta turɓune tamkar daɗai duniya imani bai taɓa ratsa fuskar tata ba.

Ta matsa daga jikin bishiyar ta nufi ainahin ofishin ƙungiyar ɗalibai musulmi.

Ustaz Jaafari ya kasance shi ne ma-ga-takarda na ƙungiyar, wato (MSSN secretary), kusan kowa a makarantar ya san shi don ba ɓoyayyen mutum ba ne, an san shi mutum ne mai matuƙar ƙokari wajen hidimta wa ɗalibai ta fuskar abin da ya shafi addini, jajirtacce ne da bai yadda da wasa ko ƙoƙarin aikata dukkan abin da ya saɓawa addini ba ga wasu ɗalibai, Ustazu ne gaske. Baya ga haka kuma yana da ƙoƙari wajen fahimtar karatu.

Dukkan waɗannan turaku da Utaz Jaafari ya kafu a kan su ba su hana masa faɗawa mummunan tarkon ƙaddara ba, dama a rayuwa kowa da irin shafin da yake buɗewa na ƙaddara, sa’annan wasu mutane rayuwarsu kan fara da kyau amma su ƙare da mummunan ƙarshe, hakazalika wasu kan fara da farko marar kyau su gama da mai kyau kuma…

Ustaz Jaafari suka haɗu da Maryam suka yi kallon ido cikin ido, sai da dukkan sinadaran tsafi suka gama shiga idanun nashi sannan ta kawar da kanta ta wuce.

Ba ta sani ba ashe yana biye da ita har ta yi nisa da barin makarantar, hakan nan ta nufi titi ta tsayar da mai napep ta shiga, har mai napep ɗin ya kunna zai tafi Jaafari ya ƙaraso da sassarfar shi ya tsayar da mai napep ɗin ya shige.
Mai napep ya waiwayo ya ce, “Ustazu ina za mu je?”

Kai tsaye ya amsa da cewa, “Tare muke da wannan ai.” Ya nuna Maryam.

Mai napep ya waiwayo gare ta ya ce, “Haka ne Hajiya?”

“Haka ne.” Ta amsa.

Ya ja napep ɗin suka tafi.

Wani madaidaicin hotel ta ce a tsaya, ta zuge jaka ta zaro kuɗi wanda lokacin da ta ke cikin hayyacinta ba sanya komai ba ciki sai tarin takaddu, to Kabasa ne ya kawo mata maƙudan kuɗaɗe matsayin tukwicin kyautar jinin Jibson da ta kawo shi ga Uwargijiya, a yanzun ma an yi niyyar yi mata gwaggwaɓar kyauta muddin ta yi nasarar kai musu jinin Jaafari, kamar yadda ake faɗa wa ruhinta da Kabasa ya tafi da shi can duniyar Ujosa aka bar hadimai suna yin tasrifi da gangar jikinta.

Tamkar raƙumi da akala haka Maryam ta kama hannun Jaafari ta shiga da shi hotel ɗin ta biya musu kuɗin wuni sannan suka shige ciki.

Dukkan su ba da ruhin jikinsu suka aikata abin da suka aikata ba, sai da komai ya faru sannan aka bar jikkunan nasu da hayyacinsu.

Da Jaafari ya farga da abin da ya wakana tsakaninsu sai hankalinsa ya yi mummunan tashi, ya kasa yarda shi ne ya aikata zina a rayuwarsa, ya dinga girgiza kai yana runtse idanu, Maryam ita ma da ke can gefe tana sanya tufafinta hawaye kawai take zubarwa dayake ita ta riga ta san abin da ya wakana, fuskarta babu abin da take nunawa face tausayawa ga Jaafari, shikenan ta jefa rayuwarsa cikin masifa.

Jaafari ya miƙe da ƙyar yana duban ta, “Wace ce ke? Me ya kawo ni nan? Me muka aikata da ke? Don Allah kar ki ce zina ce na aikata…!”

Ya rushe da kuka tare da gwara kanshi a ƙasa, Maryam ta kasa jurewa ta yi saurin zarar mayafinta ta yafa, ko jakarta ba ta tsaya ɗauka ba ta fice daga ɗakin ta hau titi ta dinga tafiya cikin kuka, ta yi nisa sosai cikin tafiyar tata ta ji tashin ƙaƙƙarfar iska, kamar sillen kara haka ta ji an sure ta an danna ta a mota, ba a dire ta a ko’ina ba sai ƙofar gidansu, abin mamaki jakarta da ta bari a hotel ta iske har ta riga ta zuwa ɗakinsu.

Kan katifa ta faɗa ta rushe da matsanancin kukan nadama, tana yi tana buga kanta a ƙasa.

A yanzu ko ta ƙi ko ta so cikin da-ta-sani take, cikin nadamar bijewar umarnin mahaifinta take, ayyukan da ta aikata a baya su ne yanzu ta fara ganin sakamako. Ta dinga surutai a kan nadamar zuwan ta makarantar nan, da a ce ta bi umarnin mahaifinta da yanzu tana can gidan aurenta cikin kwanciyar hankali kamar yadda ‘yar uwarta Zainab ta ke can cikin zama lafiya. Haka ta dinga sambatu har Habiba ta shigo ta iske ta.

A daren wannan rana sai da Kabasa ya sake zuwa ya tafi da Maryam zuwa duniyar tsafi, babban abin da ya tayar mata da hankali shi ne ganin yadda aka rataye kuruwar Jaafari a jikin wata dirka jininsa na ɗiga a ƙasa yana gangarawa cikin kogin jini, gefe kuwa hadimai ne ke ta rawa da ihun murnar Uwargijiya ta samu zazzaƙan jinin matashin saurayi, wanda hakan ya sa aka shirya walima don karrama ita Maryam ɗin.

Aka sanya mata wani jan zobe na sirrin samar da kuɗi, yadda aikin shi yake kuma, shi ne da zarar ta zura hannunta cikin jaka ta ƙudire a ranta akan ko nawa take so to za ta zaro su ne daga cikin jakar kodakuwa ba kuɗin ƙasar nan ba ne, wannan shi ya zama tukwici na kyautar jinin Jaafari da ta kawo.

Bayan kwana biyu labarin mutuwar Ustaz Jaafari ta karaɗe makarantar, a yadda aka ce mutuwar tashi ta kasance shi ne ya wayi gari da mummunan ciwon ciki wanda sai da aka ɗauke shi aka mayar da shi gidansu dayake ɗan garin Bauchi ne, aka ce cikin daren ranar da zai mutu ya dinga zunduma ihu yana tumami a ƙasa, daga bisani kuma jini ya ɓalle daga gabansa kwatankwacin yadda ya faru ga Jibson. Kafin a tafi ga kai shi asibiti gaba ɗaya jinin jikinshi ya ƙare tsaf, take ya amsa kiran mahaliccinsa…”

Ishola ta sharce hawaye a karo na ba adadi, ta tattare hotunan gaba ɗayan su sannan ta koma ta zauna ta haɗe rai sosai ta cigaba da cewa.

“…Suna gab da kammala zana jarabawar ƙarshen zangon, ranar wata Asabar tana zaune a ɗaki ita kadai tana karatu sama-sama kwatsam ta ga Habiba ta faɗo ɗakin a hargitse cikin tashin hankali.

“Maryam! Maryam wallahi zargina ya gama tabbata a kanki… tabbas da sa hannunki a mutuwar Dr. Daura… ke ba shi kaɗai ba hatta Jibson da Ustas Jaafari ina zargi kin san komai game da mutuwarsu… ki faɗa mini gaskiya Maryam wace ce ke? Me ya sa ma na ja ki a jikina ba tare da na san ke kara da kiyashi ba ce? Wayyo na shiga uku!”

Ta ƙare da ɗora hannunta a ka. Maryam ta yi zumubur ta miƙe a gigice, bakinta ya soma rawa tana so ta yi magana amma ta kasa…”
Isah ya yi saurin ɗaga wa Ishola hannun dakatarwa.

“Wait! Ya za ki jirkita mana labarin ki kawo mana ƙarshe a farko? Wane ne kuma Dr. Daura? Shi ma sun haɗu da Maryam ɗin ne…?”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Siddabaru 11Siddabaru 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.