Skip to content
Part 13 of 16 in the Series Siddabaru by Muntasir Shehu

Ishola ta zaro hoto ɗaya ta juyo musu fuskar ta ce, “Wannan shi ne Dr. Hadi Daura, sunanshi ba ɓoyayye ba ne a faɗin jami’ar a dalilin kasancewar shi fitinannen mutum mai masifar son ‘yan mata. An kai jallin da duk yarinyar da aka gan su tare ana yi mata kallon ba mutuniyar arziƙi ba.

Cikin haka ne wata rana Habiba sun fito daga ɗakin karatu, gwaji (test) ce suka yi don haka a jigace ta fito ta nufi wani sashe da yake da yalwatattun bishiyu masu kaɗa sassanyar iska. Ba ta jima da zama kan kujera ba ta ga tsayuwar mota nesa kaɗan da inda take zaune.

Jim kaɗan ta ga Maryam ta fito daga motar tana ƙyaƙyata dariyar farin ciki, shi ma ya fito, caraf ta gane Dr. Daura ne, nan take gabanta ya faɗi, ta dafe ƙirji da zaro idanu. A fili kuma ta shiga tuhumar kanta, “Me ya haɗa Maryam da wannan shaiɗanin mutumin kuma?”

Ta cigaba da kallon Maryam dake ƙarasowa gare ta tana zuba murmushi har ta zo ta zauna kusa da ita.

“Ya ake ciki ne ƙawas?”

“Meye haɗin ki da Dr. Daura ke da ba department ɗinku ɗaya ba?”

“Ina ruwan alaƙa da department?”

Cikin takaici Habiba ta kawar da kai, “Gaskiya ba zan ɓoye miki ba Maryam sam ban ji daɗin ganin ki da Dr. Daura ba, yaya mutane za su dinga kallon ki a yanzu idan suka fuskaci kina alaƙa da shi?”

Maryam ta haɗe rai, “Ni kallon da mutane za su yi bai dame ni ba, ba kuma zai dame ni ba don ba a kan wani nake rayuwa ba.”

Cike da mamaki Habiba ke kallon ta baki buɗe. “Da a ce wasu ƙawaye kike bi sai in ce suna neman gurɓata miki hali, amma na san ke ba mai biye-biyen ƙawaye ba ce ko a ajinku… na yi mamaki da na ga lokaci ɗaya kin sassauya halayenki Maryam…”

“Kin ga Habiba! Don Allah idan ba za ki yi wa rayuwata fatan alkahiri ba to ki shiga sahun masu zuba min idanu.” Ta ja dogon tsaki ta miƙe ta bar wajen.

Ko a gida ma kowa sabgar gabansa ya dinga yi, sosai Maryam take fushi da Habiba, ita ma sai ta share kawai, ta san fushin nata na ɗan lokaci ne.
Babban abin da ya ƙara tayar wa da Habiba hankali shi ne yadda bayan wasu kwanaki sai ga Maryam na shiri da dare za ta fita, kwalliya sosai ta yi kamar mai shirin zuwa gasar fidda gwanar kyau.

Habiba ta kasa haƙuri sai da ta tanka, “Wai Maryam ina za ki je da daren nan haka?”
Murmushi kawai ta yi madadin bayar da amsa, sai da ta gama shirinta tsaf ta ɗauki jaka sannan ta dubi Habiba da ke shanye da baki ta ce, “Unguwa zan je Habiba, idan dare ya yi sosai kawai ki rufe gida…”

Ba ta ba wa Habiba damar yin tuhuma ba ta fece, dafe ƙirji Habiban ta yi tana zazzare idanu tamkar wacce aka ce ta zagi sarki. Wani abu da ya zo ranta ya sa ta yi zumbur ta miƙe ta bi bayan Maryam, lokacin da ta isa ƙofar tuni har an yi wa motar key, amma da yake akwai haske cikin motar ya sa ta gane fuskar Dr. Daura.

Nan take ta ji kanta ya soma juyawa, ta dinga karanta Innalillahi tana maimatawa.
“Yaushe Maryam ta lalace ta fara bin maza? Ko kuwa dama can halinta ne hakan?”

Abin da ta dinga juyawa a ranta kenan har lokaci mai tsawo ya shuɗe, har bacci ya yi awon gaba da ita ta manta ba ta sakawa gidan sakata ba, sai motsin mutum ta ji sama-sama ya sa ta farka a gajiye.

Kiraye-kirayen sallar asuba aka fara don haka ta girgije baccin da ke kawo mata wafta ta miƙe ta kai dubanta ɓangaren makwancin Maryam.

A kishingiɗe Maryam ɗin take da waya a hannunta tana daddanawa. “Yaushe kika shigo Maryam?”

“Ban jima da shigowa ba, na yi mamaki da na ga ba ki kulle gida bayan na ce miki ki kulle in ban dawo da wuri ba.”

Takaici bai bar Habiba ta sake tsinkawa ba ta nufi banɗaki ta yo alwala ta zo ta fara nafila, aka kira sallah ta tashi ta gabatar. Bayan nan ta ɗauko littafinta ta fara nazari kasancewar tana da jarabawa a wayewar garin ranar.

Suna cikin gudanar da jarabawar labari ya fara yawo na mutuwar da Dr. Daura ya yi a gidansa, mai gadinsa ya tabbatar da cewa tare shi Dr. ɗin ya shigo da wata, bayan sun gama abin da za su yi yarinyar ta fita, ba ta daɗe da fita ba ya fara tsandara ihu yana murƙususu, da aka kira likitansa bai kai ga yi masa komai ba ya fara zubar da jini ta gabansa, bayan lokaci kaɗan ya mutu.

Habiba ta gigice ta kiɗime da jin wannan labari, a take a nan ta soma girgiza kai, wanda babu ko tantama zargin da ke cikin ranta take son tabbatarwa, don haka jikinta har rawa yake ta fice daga makarantar zuwa a gidansu inda ta iske Maryam da tuhumar zargin kisan Dr. Daura bayan ƙiyasi da ta gama yi da lissafin salon mutuwar Dr. da ta Jibson da Jaafari da yadda duk salon ya zo ɗaya, sannan kuma da yanayin damuwa da Maryam ɗin take tsintar kanta duk bayan mutuwar. Tabbas dole a ɗora wa Maryam karan zargi!”

Kamal ya ja numfashi ya ce, “Har Dr. Daura ya mutu amma ban ji kin faɗi lokacin da Kabasa ya bayyana ga Maryam ya ba ta umarni kamar yadda ya saba ba?”

Ta yi murmushi, “Na ɗauka kun fahimci haka ai, babu buƙatar a yi ta maimaita abu ɗaya, muddin dai Maryam za ta wayi gari ta kalli hannunta ta ga madubi ɗauke da fuskar wani, to fa ko waye sai ya faɗa tarkon tsafin Kabasa, don haka na san kun fahimci shi ma Dr. Daura nuna mata fuskarshi aka yi a madubi ta je ta haɗu da shi ta kawo ƙarshen numfashinsa.”

“To bayan mutuwar Dr. Daura sai me ya faru kuma?” wannan karon Turaki ya tsinka da tambaya.

Ishola ta mayar da hankali kansu, “A ranar Maryam ta tattare kayanta ta bar gidan bayan Habiba ta yi mata fata-fata, ta kuma tabbatar mata in har ba ta bar gidan ba sai ta tona mata asiri. Cikin tashin hankali Maryam ta tattaro ta nufo gida cike da tsoron kar a biyo sawunta da zargin mutuwar Dr. Daura duk da cewa tana da sauran jarabawa guda biyu da ba ta yi ba amma ta haƙura ta watsar da su, ta gwammace a saka mata (absent) da dai ta tsaya har bincike ya biyo ta kanta.

Dawowar ta gida akwai abubuwa da yawa wanda kai Isah za ka iya ɗorar da su tun da a gidanku ta sauka. In har za ka iya tunawa daidai lokacin da ta dawo ana tsaka da dambarwar son haɗa aurenka da Jalila ɗiyar ƙanwar Mama kai kuma ka kafe a kan muradinka na auren Maryam…”

Isah ya gyaɗa kai, “Tabbas an yi haka!”
“Sannan kuma dai har ila yau in ba ka manta ba dawowar ta gida babu daɗewa Yasir ɗan maƙwaftanku ya tayar da guguwar son ta lokaci ɗaya har da iƙirarin kashe kai in bai same ta ba?”
Isah ya sake gyaɗa kai na tabbatar da zancen Ishola.

Ta cigaba da cewa, “To duk wannan sharrin Kabasa ne, an nuna mata hotonsa a cikin madubin hannunta, aka kuma ba ta umarnin haɗuwa da shi, shi ne ta taka takanas ta shiga gidan da zummar gaishe da mahaifiyar Yasir ɗin, Allah kuma ya ƙaddara ƙaddarar Yasir ɗin shi ma ya faɗa tarkon… Ku da ba ku san shi ba bari in nuna muku fuskarshi…” Ta ƙare maganar da zaƙulo hoto ta nunawa su Sergeant hoton.
Ta cigaba da cewa. “Saboda masifa ta tasirin sihiri sai da Maryam ta hilaci Yasir suka keɓe a shagonsa a wani dare, wanda a washe garin ranar ya tashi da mummunan ciwon ciki, da aka kai shi asibiti ma ba su iya yi mishi komai ba saboda jinin da yake ambaliyarwa daga gabansa, kafin wani lokaci ya shura takalmansa.

Mutuwar ta gigita mutanen unguwa, kun dai san yadda mutuwar yaro matashi take rikita zukata, to haka aka yi jimamin mutuwar shi aka gama, yayin da a ɓangaren Maryam kuma take cikin matsanancin tashin hankali da damuwa gami da tsoro a kan wannan mutuwa ta Yasir. Isah na san za ka iya tuna halin da Maryam ta shiga a lokacin.”

Isah ya gyaɗa kai, tabbas Maryam ta tashi hankalinta a kan waccan mutuwa ta Yasir, don kuwa har shi kanshi sai da ya shiga damuwa da kishi saboda a ganin shi kukan da ta ringa yi na son da take wa Yasir ɗin ne, ashe ita ta san dalilin kukanta!

Ya saka hannu ya matse hawayen da suka tarun masa a kurmin idanu, yana ji Ishola ta cigaba da cewa.

“Bayan mutuwar Yasir samari uku ne suka ƙara rasa rayukansu a dalilin wannan siddabaru na duniyar Ujosa, kuma dukkansu suna fara kamuwa da zazzafar soyayyar Maryam ne wanda hakan ke tasiri wajen su biyewa Maryam ɗin su aikata masha’a, hakan kuma ya zamo silar salwantar rayukansu.

Hankalin mutane ya fara dawowa kan Maryam na ganin duk wanda ya ce yana son ta sai ya mutu, mutuwar kuma duk iri ɗaya, nan da nan aka fara fitar da ƙananan maganganu a kanta, wasu su ce baƙin Aljani ne ya aure ta ya ke kashe duk wanda ya ce yana sonta, amma kuma sai togaciya ta zo na ganin Isah da AbdulNasir har gobe suna son ta amma kuma ga su a raye. Wasu su ce farar ƙafa ce da ita, wasu su ce kambun baka ne. Kowa dai da abin da yake zato.

Daga cikin gidanku ma Mama tana cikin masu zargin baƙin Aljani ne ya auri Maryam a makaranta shi ne yake kashe duk masu cewa suna son ta. Wannan zargi ya tashi hankalinta matuƙa, hakan kuma saka ta ƙara matsa maka lamba kan ka auri ɗiyar ƙanwarta Jalila…

Samari suka cigaba da rasa rayukansu a dalilin Maryam, hankalinku kuma a nan duk ya tashi kuka fara yadda da baƙin aljani ne ya aure ta, kuka shiga nema mata magani ba ji ba gani amma babu nasara. A wannan lokacin Abbansu ya sauko daga fushin da yake da ita har yake ɗan taimakawa cikin neman maganin nata, dama tsakanin ɗa da mahaifi sai Allah.

Bayan maƙudan kuɗi da suka salwanta kan nemo maganin baƙin aljani, karshe dai aka tabbatar babu baƙin aljani a tare da ita, sai kuma zargin kasancewar ta mai farar ƙafa ya taso, aka dinga lugwigwita maganar yadda har sai da kowa ya dinga ƙyamatar Maryam, duk uwar da take da ɗa saurayi takan guji haɗuwar ɗan nata da Maryam ciki har da Mama da babu yadda ba ta yi ba don Maryam ta bar gidan amma Babanku bai bayar da dama ba.

Ana cikin haka wata ranar litinin Maryam ta farka da matsanancin ciwon kai, Isah ka zo ka tarar da ita a kwance a falo tana ƙananan hawaye, da ka tambaye ta lafiya ta ƙi faɗa maka, ana cikin haka Mama ta shigo falon ta same ku, ta balbale ka da masifa sannan ta ja ka ɗaki, to bayan wucewar ku caraf sai ga hayaƙin bayyanar Kabasa ya soma tashi a saman kanta, bayyanar shi ta matuƙar tsorata ta saboda yadda kwana biyu babu abin da ya faru na lamarin duniyar Ujosa. Tun daga yadda yake ɓaɓɓaka dariyar ƙeta ta san cewa mugunta ce fal yau zai aikata, wannan ta sa hannunta na karkarwa ta ɗago shi ta duba don ta ga wa za a buƙata.

Kun san fuskar wa ta gani?

Isah! Fuskarka ce ta bayana a madubin tsafi….”
Ba Isah kaɗi ba, dukkan su suka zabura a gigice.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Siddabaru 12Siddabaru 14 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.