Dariya ta ƙwace wa Ishola ganin yadda idanun Isah suka yi tulu-tulu a waje cikin matsanancin tsoro.
Sosai ta dara har ta kusa tuntsirawa, duk sai suka baza mata idanu.
Da ta gama dariya ta nutsu ta ce, “Haba Isah! Wannan tsoron duk na mene ne? Ko ka manta labari ne nake ba ku? Ka manta shekaru nawa rabon ka da Maryam? Da hakan zai faru ai da tuni ya faru
Ta ƙara murmusawa sannan ta ɗora.
“Isah ba za ka taɓa tabbatar da irin matsananciyar ƙaunar da Maryam ke yi maka tun da ba ka ga halin. . .