Skip to content
Part 14 of 16 in the Series Siddabaru by Muntasir Shehu

Dariya ta ƙwace wa Ishola ganin yadda idanun Isah suka yi tulu-tulu a waje cikin matsanancin tsoro.

Sosai ta dara har ta kusa tuntsirawa, duk sai suka baza mata idanu.

Da ta gama dariya ta nutsu ta ce, “Haba Isah! Wannan tsoron duk na mene ne? Ko ka manta labari ne nake ba ku? Ka manta shekaru nawa rabon ka da Maryam? Da hakan zai faru ai da tuni ya faru

Ta ƙara murmusawa sannan ta ɗora.

“Isah ba za ka taɓa tabbatar da irin matsananciyar ƙaunar da Maryam ke yi maka tun da ba ka ga halin da ta ta shiga ba a dalilin bijirewa umarnin Kabasa na ƙin yarda ta ba da jininka!”

Isah ya buɗe ido sosai cikin mamaki, ya waiwaya ya kalli su Turaki, duk sun yi tsamo-tsamo tamkar waɗanda aka tsamo daga ruwa.

Ishola ta gyaɗa kai ta cigaba da cewa, “Lokacin da Maryam ta ga fuskarka Isah a cikin madubin tsafi zabura ta yi cikin tashin hankali tana girgiza kai tana faɗin; “Aaa’aa! Ba zai yiwu ba! Ba zan aikata ba!”

Fuskar Kabasa ta soma rinewa da ɓacin rai, da kakkausar murya ya ce, “Kar ki yarda ki sake aikata kuskuren bijirewa umarnin uwargijiya a karo na biyu… ruhinki ba zai taɓa zama cikin salama ba!”

Ta cigaba da girgiza kai hawaye na gudu a sararin fuskarta. “Zan iya sadaukar da duk wanda Uwargijiya ta buƙata amma ba zan iya bayar da Isah ba… Isah masoyina ne na ƙwarai, ba a taɓa halittar wanda ya so ni ya ƙaunace ni a rayuwata ba kamar shi, ba zan iya bayar da shi ba ba zan iya ba!”

Hannu ya bayyana a jikin Kabasa ya zabga mata mummunan marin da ya sa ta katantanwa a tsakiyar falon, ƙarshe ta kife a ƙas cikin rishin kuka.

Kabasa ya yi tsafinsa ya mayar da ita hayaƙi, sannan ya buɗe wata ‘yar mitsitsiyar kwalba ya kira wannan hayaƙi ya shige cikin kwalbar, hayaƙin na gama shigewa cikin kwalbar ya sake rikiɗewa zuwa ainahin siffar Maryam ta zama ‘yar mitsitsiya, tana ta fagamniya a cikin kwalbar tana neman hanyar ficewa.

Duk wannan abu da ya faru babu wanda ya sani a cikinku, lokacin kai Isah kana can tare da Mama tana cigaba da yi maka faɗa kan alaƙarka da Maryam.

Idan ba ka manta ba lokacin da ka fito falon ka iske Maryam ba ta nan, haka ka wuce cikin ɓacin rai.

Maryam ko tana can ana gana mata azaba da sinadaran tsafi, an cire ta daga kwalbar aka rataye ta a wata doguwar bishiya aka sanya hadimai suka dinga fyaɗar ta da bulalar tsafi. Tun tana ihu sauti na fita har sai da ta suma ta daina motsi sannan Kabasa ya yi umarni aka ƙyale ta, amma ba a kwance ta daga ratayar ba aka bar ta tana ta reto a jikin igiyar.

Bayan wani lokaci ta farfaɗo don kanta, ta cigaba da kuka, kuna baƙin ciki da nadama, kuka na da-ta-sani… ina ma a ce baya ta dawo! Ina ma tana da damar dawo da hannun agogo baya da ta dawo da jiyan rayuwarta don ta gyara kuskurenta…!

Kabasa ya yi tsafi, igiyar ta tsinke ta faɗo ƙasa tim! Ƙwaƙƙwaran motsi kasa yi ta yi.

Cikin kakkausar murya Kabasa ya ƙara jaddada mata umarnin uwargijiya Munansa na buƙatar jininka Isah, tare da albishirin mummunar azaba idan ta sake bijirewa, idan kuma ta cika umarni aka yi mata kyakkyawan alibishiri da samun maɗaukakiyar dukiya mara yankewa. Kabasa ya sake jaddada masa a gobe uwargijiya take buƙatar jinin Isah don haka ta tabbatar ta haɗa idanu da kai a wannan rana! Daga nan ya sake yin tsafinsa iska mai ƙarfi ta tashi ta sure ta ta yi sama da ita.

A cikin ɗakin da take kwana a kan gado aka watso ta ta faɗi tim, ta rushe da kuka har da birgima.

A fili ta dinga sambatu da faɗin sai ta tona asirin duk abin da ke faruwa da ita ko me zai faru sai dai ya faru, ya kuma faɗa cewa za ta je ta ƙara neman yafiyar Abbansu da Umma da kuma ‘yar uwarta Zainab da kowa ma!

Ranar ba ta runtsa ba saboda tashin hankali, don Kabasa bai saurara mata ba, ya dinga aiko mata da abubuwan ban tsoro da rikita ƙwaƙwalwa da gargaɗi mai zafi a kan tona asiri da ta kudiri niyyar yi.

Washegari saboda kar ta ma haɗu da kai Isah balle tsautsayi ya faɗa maka shiryawa ta yi ta tafi can gidansu duk da cewa a cikin jikinta azaba kawai take sha daga Kabasa don kar ta samu damar zuwa gidan amma duk da haka da ƙyar ta samu ta je.

Kuka sosai ta dinga yi a gaban Abba tana ba shi haƙuri da neman gafarar shi, sosai ta ba shi tausayi ya ƙara tabbatar mata da ya yafe mata tare da yi mata kyakkyawar addu’a.

Wannan addu’a da ya yi mata ita ta sa ta ji salama a ranta, hankalinta ya ɗan kwanta, ta samu ‘yar nutsuwar da ta buɗe baki da niyyar faɗa masa duk abin da ya faru da ita a ƙaddararriyar makaranta tun daga haɗuwar ta da Kabasa da duk abubuwan da suka faru bayan nan, amma me?

Kabasa ya sa aka ɗaure mata harshe ta kasa furta komai, ƙarshe haka ta huƙura ta dawo gida.
Tun daga wannan rana kuma ba ta sake yadda kun haɗu ba in za ka iya tuna haka, kullum tana ƙunshe a ɗaki, idan ma ta gaji ta fito falo to da zarar ta ji gilmawar ka za ta tashi a guje ta shige ɗaki. Tare da cewa kullum dare sai Kabasa ya zo ya ɗauke ta ya kai ta duniyar tsafi sun gana mata mummunar azaba wacce a ruhinta kaɗai take ji, dalilin da ya sa ma babu wanda zai iya fahimtar abin da ke faruwa da ita, sai dai ramar da kullum take ƙara zabgewa tamkar sigarin da ake zuwa.
Kabasa ya kafe a kan dole sai ta kawo ka, ita ma ta kafe kan za ta iya jure kowace irin azaba amma ba za ta bayar da jininka ba.

Dole ita uwargijiya ta haƙura ta ce a sauya mata da jinin AbdulNasir.

A lokacin tuni AbdulNasir ya yi aure, amma bai daina bibiyar lamarinta ba sama-sama, faruwar wannan lamari sai ga shi ya dawo a haukace da soyayyarsa mai zafi. A ranar da suka haɗa idanu tsafin jikinta ya shige shi ranar ƙin barin gidan ya yi har ka dawo ka iske shi. Na san ba za ka manta d wannan rana ba da har rigima kuka yi da ka ga yadda ƙiri-ƙiri AbdulNasir ke kama jikin Maryam, kamar ma zai far mata a cikin mutane…”

“Tabbas an yi haka! Wallahi an yi haka, kuma bayan kwana biyu ne da faruwar haka muka ji labarin mutuwarshi… amma don Allah kar ki ce min shi ma ya kwanta da Maryam ne…” Hawaye sosai a fuskarsa.

“Sai dai ka yi haƙuri Isah, abin da ya faru kenan, washegari AbdulNasir ya dawo ba tare da ka sani ba ya ɗauki Maryam ya kai ta hotel…”

“Don girman Allah ki tsallake gurin nan ba na son ji, tamkar zuciyata za ta fashe nake ji… su ma duk waɗancan da na iya jure jin labarinsu na yi ne don babu wani abu da ya taɓa shiga tsakaninmu ne… amma ba na son jin abin da ya faru tsakanin Maryam da AbdulNasir please!”

Ishola ta jijjiga kai, “Duk yadda kake tunanin irin matsanancin son da kake mata to tabbas zan iya tabbatar maka son da ita take maka ya zarce naka… don dai kawai ido bai gani ba, zuciya kuma sai dai ta hasaso amma babu damar dawo da bara bana da ka gani da idanunka irin azabar da Maryam ta fuskanta a kan ƙin bayar da jininka ga duniyar tsafi duk don saboda son da take yi maka.”

Ta ja dogon numfashi ta fitar sannan ta cigaba. “To dai shi ma AbdulNasiy haka ya rasa ransa, jininsa ya sadaukantu ga uwargijiyar tsafi, sai dai ba a yi wa Maryam kyautar komai ba don ba wanda uwargijiya ta so tun farko ba ne aka kawo mata, abu ɗaya dai aka yi mata shi ne ɗaga mata ƙafa da aka yi da sake buƙatar jinin wani har zuwa tsawon lokaci.

Lokacin ana gab da komawa makaranta, sai dai in ba ka manta ba ƙiri-ƙiri ta ce ba za ta koma ba, har faɗa Babanku ya dinga yi mata amma sai ta dinga kuka, da ranshi ya ɓaci kawai sai ya share lamarinta ya zuba mata idanu.

Kai ma babu yadda ba ka yi ba don ka ji abin da yake damunta amma ta ƙi faɗa maka, haka kai ma ka haƙura ka zuba mata idanu.

Wata rana ta wayi gari da ganin bayyanar Kabasa, da ta duba hannunta sai ga madubi ɗauke da fuskar jariri.

Tabbas ta samu faɗuwar gaba a lokacin don yadda ta dafe ƙirji har da ranƙwafawa.
“Jariri!”

Ta furta a fili.

Kabasa ya gyaɗa kai cikin dariyar ƙeta, “Tabbas jinjiri uwargijiya take buƙata!”

Hawaye suka soma gudu a kundukukinta. “Ina zan samu jariri ni?”

Kabasa ya haska mata fuskar ‘yar uwarta Zainab, wato jaririn cikinta ake buƙata!

Ta so yin gaddama amma Kabasa ya sa aka riƙe mata zuciyarta gam ta ji ba za ta iya ketare wannan umarni ba.

Sai ga ta washegari ta shirya ta ce za ta je gidan ‘yar uwarta su gaisa, Umma Fati ba ta kawo komai a ranta ba ta ba ta kuɗin mota tare da miƙa saƙon gaisuwa ga Zainab ɗin. Mama kuwa taɓe baki ta yi cikin nuna tsanar Maryam.

Maryam ta je gidan Zainab ta iske ta tana tuƙawa da ƙyar da tsohon cikinta na kusan wata takwas.
Sosai Zainab ta yi farin cikin ganin ‘yar uwar tata, ta dinga ina-ka-saka ina-ka-aje da ita saboda tsawon lokacin da suka ɗauka ba su haɗu ba.

“’Yar uwa na ga duk kin rame tamkar wacce ta daɗe a gadon jinya… ke da kika dawo hutu ai kamata ya yi a ce an gan ki kin yi ɓul-ɓul abinki” ta ƙare maganar tata da sigar ban dariya.

Maryam ba ta yi dariyar ba, maimakon haka ma kawar da kai ta yi cikin murmushin takaici.

Zainab ta kawo mata ruwa da lemo da kuma ɗan abin taɓawa kafin ta gama girki, ta umarci wata yarinya Nafisa ‘yar maƙotanta da ta ke shigowa kullum tana taya ta aikin gida da ta je kicin ta kula mata da girkin, ita kuma ta zauna gurin ‘yar uwarta don su yi hirar zumunci.

Sai dai sam Maryam ta ƙi bayar da haɗin kai, sai fuffuzga take tana neman hanyar da za bi ta ƙwakulo jinjirin da ke cikin Zainab…

Kamar wadda aka tsikara da tsinke ta yi zaraf ta miƙe ta nufi uwar ɗakan Zainab, cikin mamaki Zainab ɗin ta miƙe ta bi bayan ta da ƙyar.

Maryam ashe tsugunnawa ta yi ta laɓe a gefen ƙofar shigowa, Zainab na sako kanta ciki Maryam ta kwarfe ta, sai da Zainab ta yi sama ta yi juyi sau uku sannan ta faɗo ƙasa nik! Tana faɗuwa kuwa ta baje a kas bayan ta saki razananniyar ƙara wacce ta sa Nafisa yin cilli da tukunyar girki ta sheƙo a guje, sai dai kafin ta ƙaraso tuni Maryam ta mayar da ƙofar ɗakin garam ta rufe.
Nafisa ta dinga bubbugawa tana faɗin a buɗe! A buɗe!

Maryam ta na ji ta yi mirsisi ta soma gudanar da aikinta na ciro jinjirin cikin Zainab.

Bakinta ta saka a bakin Zainab ɗin ta dinga hura iska, in ta hura sai ta ɗago ta karanta ɗalasiman tsafi sannan ta mayar da kai ta sake hura mata iska cikin baki tana kuma jijjigata da matse mata cikin tana tura shi ƙasa.

Nafisa kuwa a bakin ƙofa cigaba take da bugawa tana kwala kiran Anty Zainab!

Ta gigice sosai yadda ko tunanin ta fita ta nemo agajin wani ba ta yi ba, ita dai kawai a buɗe ta ga me ya samu Anty Zainab.

Maryam ta cigaba da siddabarunta, jini na ɓulɓula daga jikin Zainab tamkar bakin indararo. Can kuma sai ga mataccen jinjiri ya faɗo,

Maryam ta zabura ta ɗauke jinjirin ta ɗaga shi sama ta runtse jajayen idanunta tana karanta ɗalasiman tsafi, sannan ta miƙe ta isa ga jakarta ta zuge ta zaro baƙar leda viva ta cusa yaron a ciki da sauran tarkacen haihuwa sannan ta ƙulle ledar ta ajiye gefe.

Sai a lokacin ta je ta buɗe ƙofar idanunta fal da hawaye ta ce wa Nafisa, “Faɗuwa ta yi! Kuma ta yi ɓarin abin da ke cikin ta… bari in ba ki kuɗi ki siyo min katin waya in kira mijinta…”

Ta juya da sauri cikin ɗakin, Nafisa cikin zare idanun tsoro da dafe ƙirji ta bi bayanta cikin karkarwar jiki bakinta na maimaita kalmar ɓari! ɓari!

Hankalin Nafisa ya yi mummunan tashi da halin da ta ga Anty Zainab a ciki, sosai jikinta ke ɓari, ta rikice ta gigice.

Maryam ta goge hannunta da wani zani na Zainab sannan ta zaro kuɗi a jakarta ta miƙa wa Nafisa.

“Maza ki siyo katin kin ji…”

Cikin rawar murya Nafisa ta ce, “Ko… ko dai… ko in kira Mamanmu?”

“A’a kar ki kira ta, ki fara siyo min katin.”
Nafisa ta karɓi kuɗin ta fice da sauri, ita kuma Maryam ta jawo wannan leda da ta ƙunshe jinjiri a ciki ta yi hanyar waje.

Ta na leƙawa ta ga wasu yaran almajirai ta kira su ta miƙa musu ledar ta ce su zagaya bayan gidan su jefar a bola. Yaran suka karɓa suka tafi, ita kuma ta koma ta soma tattare jinin da ya zuba a ƙasa duk ya daskare ta kwashe ta nufi toilet ta juye a ciki, duk ta yi faca-faca da ɗakin.

A can waje kuwa Nafisa ce ta dawo cikin sauri-sauri bayan ta siyi katin, a daidai wani guri ta ga cincirindon yara da baƙar leda wai sun tsinci jariri a leda an yaddar a bola kuma ba a san wanda ya ajiye ba, nan da nan gurin ya ɗinke da mutane…
Nafisa ta leƙa ta ga yadda aka zaro mataccen jinjirin face-face da jini take ta razana, ta tuna abin da ke faruwa a can gidan Anty Zainab, ta kwasa a guje ta nufi gidan har tuntuɓe take a hanya.

Tabbas duk ƙanƙantar shekarunta alamu sun nuna ta ɗisa ɗambar zargi kan wannan jariri da kuma abin da ke faruwa a gidan Anty Zainab.
Me za ta je ta cewa Maryam?

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 2 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Siddabaru 13Siddabaru 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.