Nafisa ta tarar da Maryam a tsaye kan Zainab tana kukan makirci, da sauri ta miƙa mata katin hannunta na rawa.
“Anty Maryam kin san me na gani yanzu a waje yana faruwa?”
Maryam ta dakata da loda katin wayar ta bayar da hankalinta ga Nafisa idanunta a waje.
“Wai wasu yara ne suka tsinci jariri a baƙar ledar an yaddar a bola… sai na ji tsoro na ga kamar jaririn da Anty Zainab ne kikace ta yi ɓari…”
Cikin bayyanannen tashin hankali Maryam ta iso ga Nafisa jikinta na rawar mazari.
“Ke…! Ke ba shi… ba shi ba ne! Ba jinjirin Zainab ba ne… ita ɗanta ai bai zama mutum ba, ba ki ji ma na ce na jefa shi masai ba? Ai dama haka ake yi wa jaririn da aka yi ɓarinsa…” Gaba ɗaya a ruɗe take.
Nafisa ta zabura ta ce, “To ki yi sauri ki saka katin mana ki kirawo Yaya Hashim ɗin kar Anty Zainab ta mutu.”
“Kin ga Nafisa maza je ki kira min Mamanku ta zo, ni ba zan iya ba gwara babba ya zo.”
Tun ba ta rufe baki ba Nafisa ta fice a guje yayin da ita kuma ta soma kai-kawo a ɗakin cikin kullewar kai, babu shakka tantama ce ta sarƙe ta ta yadda za ta gamsar da mutane cewa ɓari Zainab ta yi kuma wai ta saka abin da aka ɓarar ɗin a masai, wannan zance ne da ba kowane mai dogon tsinkaye zai gamsu da shi ba, nan take ta gane babban kuskuren da ta tafka na saka Nafisa ta kira gyatumarta, tabbas tsabar ruɗewa ce ta saka ta yin wannan shirmen. A gefe ma kuma ga wani sabon abin sakawa zuciya ta yi bugun farat ɗaya, wato batun da Nafisa ta zo da shi na tsintar jariri a bola, babu shakka jaririn da ta ciro ne a cikin Maryam…
Kamar walƙiya ta ga bayyanar farar tsuntsuwar nan da ta taɓa ganin ta a ranar farko da aka kai ta fadar tsafi, kafin ta yi wani ƙwaƙƙwaran motsi tsuntsuwar nan ta rikiɗe ta zama zankaɗeɗiyar budurwa cikin shigar da ‘ya’yan sarakunan fararen aljanu ke yi, fuskarta cike da murmushi.
Ta duƙa sosai don nuna girmamawarta ga Maryam, sannan ta yi mata ishara da ta kwantar da hankalinta Duniyar ujosa ba za ta taɓa bari wani hadiminta asirinsa ya tonu a idon duniya ba don haka ita ma ta kwantar da hankalinta wannan matsala dai an gama da ita. Ta runtse idanunta ta soma karanta ɗalasimai, ɓukut! Sai ga jinjirin a hannunta ya bayyana tamkar zuwa aka yi aka ɗora mata a hannun. Farin mayafi ya bayyana a ɗaya hannunta ta sa ta naɗe jinjirin sannan ta ɗaga shi sama cikin karanta ɗalasimai ta cilla shi saman, iska mai karfi ta tashi ta yi sama da shi fuuuu ta ratsa rufin gidan ta wuce.
Maryam ta sauke kanta a gajiye, ta dubi wannan aljana da take ta zuba murmushi.
Cikin karkarwar jiki ta nuna Zainab da ke kwance.
“Wannan… ya… ya zan yi da… da ita?”
“Kar ki damu, an mantar da ita komai, za ta tashi da tunanin ba ta san komai ba na abin da ya faru…”
Sallamar su Nafisa ce ta sa aljanar nan saurin rikiɗewa ta zama hayaƙi ta yi sama ta fice.
Maman Nafisa ta ƙaraso a rikice “Innalillahi… Zainab… subhanallahi… !”
Maryam ta fashe da kuka sosai tana jijjiga Zainab, “Daina jijjiga ta! Ke Nafisa maza fita ki nemo mana mota, wannan ai ba sai an jira mai gidan ya dawo ba… taimakon gaggawa take buƙata…”
Nafisa ta fice da sauri, Maryam ta ce, “Ban kira Hashim ɗin ba, ban ma iya kiran kowa ba wallahi…” Sosai take ambaliyar da hawaye.
“Ba za ki iya ba ai. Ina wayar taki? Nemo min lambar maman taku ni in yi magana da ita.”
Maryam ta nemo lambar ta kira sannan ta ba ta wayar.
Nafisa ce ta dawo a guje tana haki da dafe ƙirji.
“Mama mun shiga uku!”
Cikin ɗimauta Mama ta saki wayar. “Me ya faru kuma Nafi?”
“Wannan jaririn da na ce miki an tsinta a bola wai kin ji guguwa mai ƙarfi ce ta taso ta tayar da hankalin kowa a gurin, babu wanda yake iya ganin na kusa da shi saboda duhu da kuma ƙarfin yadda iskar ke tafiya, ga tulin ƙasa da ta cika idanun mutane, wai kin san me?”
Mama ta gyaɗa kai, muryar tata sarƙe ta cigaba, “Wai iskar ta fisge jinjirin, yanzu an nemi jinjirin ba a gan shi ba kwata-kwata!”
Wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya Maryam ta yi wacce har sai da ta ja hankalin Maman Nafisa ta waiwaya ta kalle ta, sai dai ba ta ce komai ba, hasali ma faɗa ta hau Nafisa da shi.
“Wace irin shashasha ce ke an ce ki je ki nemo mota shi ne kika tafi shirme…”
Umma suka shigo gidan a rikice, suna zuwa shi ma Hashim ya dawo aka taitayi Zainab zuwa asibiti.
Ta sha wahala sosai kafin ta dawo hayyacinta, dayake ta ranta ake babu wanda ya bi ba’asin abin da ya fita daga cikin nata, sai da likita ya yi bayani sosai tare da tabbatar da cewa tamkar da ƙarfin tsiya aka tsige jinjirin daga tushiyarsa, saboda haka mahaifar Zainab ɗin ta samu matsala sosai.
Kuka sosai umma ta dinga yi, ta ƙwallafa rai sosai a kan wannan jika da take saka ran zuwan sa sakamakon yadda ta rasa na wajen Turaki wanda shi har uwar aka rasa.
Mama kuwa kowa ya kalli fuskarta take zai gano zargi kwance lamɓam wanda zargin ba a kan kowa yake ba face Maryam!
Tabbas zargi take yi da saka hannun Maryam cikin wannan lamari, akwai hujjoji bayyanannu da za su tabbatar da hakan, sai dai da yake ba a buɗe ƙofar shigo da zargi ba ya sa ta adana zarginta a zuciyarta, sai dai ta cigaba da tsanar Maryam da kuma ƙoƙarin shiga tsakaninku kai Isah.
Kamar yadda aljanar nan ta faɗa wa Maryam haka ce ta faru, da Zainab ta farfaɗo nunawa ta yi sam ba san ma yadda lamarin ya faru ba, don haka maganar ta bi shanun sarki.
Bayan lafawar wannan lamari uwargijiya Munansa ta sake buƙatar jinin Isah a karo na biyu, sai dai Maryam ta sake kafewa a kan ba za ta bayar da jininka ba. Sun wahalar da ita! Sun gana mata azabobi kala-kala na tashin hankali wanda a lokacin ku kanku kuka rasa abin da yake faruwa da ita, kun sani yadda ta dinga ɗan ƙaramin hauka da tonawa kanta asiri cewar duk ita ce take kashe mutanen da suka ce suna son ta, har jinjirin Zainab ma ita ta ƙwaƙule shi.
Wannan lamari ya tashi hankalin kowa a danginku, har gidan mahaukata kuka kai ta aka tabbatar ƙwalƙwaƙwarta lafiya take, sai dai ƙwaƙwalwar tana fuskantar barazanar samun matsala sakamakon azabtuwa da take da fargaba da tsoro…
Akwai wani lokaci da su Kabasa suka kusa cimma nasara a kanka Isah… Idan ba ka manta ranar da Maryam ta same ka a ɗaki da dare ba, a lokacin saura ƙiris ka faɗa tarkonta, sakamakon addu’ar iyaye ya sa ta kasa samun nasara a kanka… a lokacin da shedan ya rinjaye ka ka biyewa ganin kyawun surarta ka yi gangancin afka mata to da yanzu babu kai ake jin wannan labari… ka ƙara godewa Allah sannan ka ƙara tsananta addu’ar neman tsari da kariya…
Da suka fuskanci Maryam ba za ta bayar da jininka ba Uwargijiya Munansa ta fusata sosai ta ce tun da Maryam ta bijire ta zaɓi jinin Isah a kan farin cikin shugabar duniyar Ujosa to ta buƙaci a ba ta jinin ita kanta Maryam ɗin…
Daga wannan rana suka soma tatsar jinin Maryam, kuma ba ta sauƙaƙkiyar hanya irin wacce aka saba ba, sosai suka azabtar da ita suka dinga zuƙar jininta yadda ko a asibiti suka kasa fuskantar abin da ke faruwa da ita. A wannan lokacin babu wanda bai tauyawa Maryam ba, duk waɗanda suka tsane ta suka dawo tausaya mata ban da Mama da sauran wasu iyayen waɗanda suka rasa ransu dalilinta. RANA ƊAYA TAK zuciyar Maryam ta buga saboda ɗaukewar jini a jikinta, ba ta ƙara ko daƙiƙa ɗaya ba ta shura tana mai cike da neman gafarar Abba….”
Sosai Ishola take share hawaye fuskarta ta yi jage-jage.
“Wannan shi ne labarin Maryam!”
Isah ya zabura cikin fiddo idanu waje. “Me kike nufi yanzu? Ina Maryam ɗin take yanzu kamar yadda kika faɗa mana kin san inda take?”
Da murmushi guntu ta ce “Ka taɓa ganin wanda ya mutu ya dawo?”
Da sauri Kamal ma ya ce, “Kina nufin ki ce da gaske Maryam ta mutu?”
Ta gyaɗa kai, “Tabbas Maryam ta mutu, tana can kwance cikin ƙabarinta, addu’arku kawai take bukata yanzu…”
“Ji nan madam! Kar ki kawo mana wasa da ƙoƙarin yi mana yawo da hankali” Seargent ya faɗa cikin sauri tare da miƙewa yana kashe abin ɗaukar magana.
Turaki ma ya miƙe, “Ki yi mana cikakken bayani da za mu gamsu, ki faɗa mana ina Maryam take yanzu.”
Da guntun murmushi take duban su. “Kamar yadda babu wanda yake da ikon sauya ƙaddara face lillahi, to haka babu wanda zai iya sauya mutuwar Maryam zuwa rayuwa… tabbas Maryam ta mutu…”
“To ke ɗin wace ce a gare ta ne? Ko kuwa ke ma makamancin abin da ya faru da ita ne ya faru da ke? Ya aka yi duk kika san wannan labarin da kika ba mu?” Seargent ya sake katse ta.
Ta tattare hotunan a hannunta, ta dube su sosai ta ce, “Ku zauna don Allah ku ɗan jira ni, zan faɗa muku wace ce ni… har da sauran abin da kunnuwanku ba su taɓa tsammanin ji ba, tunaninku ma bai taɓa hasasowa ba.”
Ta wuce cikin ɗaki ta bar su nan shanye da baki, suna jefa wa juna kallon-kallo.
Jim kaɗan dukkan su suka sake miƙewa a kiɗime cikin maɗaukakin mamaki da al’ajabin abin da idanunsu saka yi arba da su…