Skip to content
Part 2 of 16 in the Series Siddabaru by Muntasir Shehu

“Da gaske kai kake wannan furucin Alhaji? Na yi mamaki matuƙa! Ko a labaran almara ban taɓa jin inda aka yi haka ba kuma a kalli hakan a matsayin abin da zai faru a gaske, sam!”
Cewar Mama cikin bayyana takaicinta.

Umma Fatima abokiyar zaman Mama ce ta tsinka cikin maganar Maman.

“Gaskiya abin dai akwai ɗaure kai da kulle zuciya matuƙa, wannan ya wuce a kira shi da tsananin kama, domin duk wanda ya san Maryam idan ya kalli waɗannan hotunan ko a ransa ba zai kawo cewa mai kama da ita ba ce, kai tsaye ita ɗin ce zai ce!”

A karo na biyu Baba ya sake magana da cewa “Babana ba na ko tantama wannan Maryam ce, kuma tabbas na fara ji a jikina akwai wani ɓoyayyen al’amari cikin mutuwarta…” Ya ɗan ja numfashi.
“Ta yaya ka samu ganin waɗannan hotunan ma?”

Har yanzu babu nutsuwa a tare da Isah, don haka harshensa cikin rawa ya soma fitar da hargitsattsun kalmomi.
“A… Facebook… Facebook ne, a facebook na gani an watso… An watso sanarwar shagulgulan biki…”

“Amma Alhaji dogon nazari ya kamata a yi, kar mu mata mu fi ka zuzzurfan tunani kan wannan lamari… Ka duba fa da kyau, bayerabe ne zai aure ta, kuma a Lagos, ta yaya Maryam da ta kai a ƙalla shekaru biyu da rasuwa za a ce ita ce wannan?
Akwai kama fa Alhaji? Akwai cewar fa duk mutum ɗaya zai iya samun masu kama da shi kwabo-da-kwabo har mutune bakwai, to don me ya sa ba za mu yi tunanin ita ma wannan kama ce kawai suka yi da Maryam?” Cikin ƙunar zuciya Mama ta yi maganar.

Da sauri Isah ya isa gabanta, “Sunan fa Mama? Sunan ma fa iri ɗaya ne.. Ki duba ki gani wallahi wannan Maryam ce…”

“Kai shashasha sakarai mara lissafi! Idan ita ɗin ce ya za ka yi to? Wace irin baƙar masifa ce wannan haka! Yarinya ta mutu amma ba ta bar min zuciyar ɗana ba, na shiga uku ni Rahma so zai zautar min da yaro” Ta fashe da kuka.

Jikin Isah ya ƙara rikicewa, Babansu ya yi saurin duban sa.
“Babana dare ya yi sosai yanzu, ya kamata ku koma gida a bar wa gobe komai, ka nutsu ka kwantar da hankalinka tun da ka ga har mahaifiyarka ta shiga damuwa… Ka ja matarka ku koma inyaso gobe a yi maganar ciki nutsuwa.

Isah ya kasa tsinkawa kuma ya kasa takawa, Jalila ce ta isa gare shi cikin mutuwar jiki.

“A mota ɗaya kuka zo ne?” Baba ya tambaya.
Jalila ta gyaɗa kai “A’a Baba, daban-daban muka zo.”
“To ki bar taki motar a nan ku tafi a tashi, idan kin fuskanci ba shi da nutsuwar tuƙi to ke ki ja ku.”

Ya dafa Isah, “Babana ka nutsu ka ji, ka bi komai a sannu, ka tabbatar ka yi addu’a kafin ka kwanta ka ji.”

Gyaɗa kai kawai ya iya yi, ya juya ga mahaifiyarshi wacce ke sharar hawaye hannu bibiyu.
“Ki yi haƙuri Mama, addu’arki nake buƙata ba ɓacin ranki ba, dukkan abin da ke faruwa ba ina yi ne don raɗin kaina ba sai abin da zuciyata ta umarci gangar jikina da yi, ban isa in hana zuciyata yin…”

“Ya isa haka Babana, ka kama hanya ku tafi na ce ko?” Cikin ɗaga murya Baba ya katse shi tare da sa hannu ya fara tura shi a hankali.

Jalila ta karɓe makullin motar hannunshi ta riƙe ta wuce gaba, Baba sa wasu daga cikin ƙannen Isah suka biyo su da rakiya har gaban mota yayin da Mama ta koma ɗakinta cikin matuƙar baƙin ciki. Abubuwa marasa iyaka ne suka soma yi mata zarya a ranta, babban abin da ya fi ɗaga mata hankali shi ne halin da ɗanta zai sake faɗawa bayan yadda aka samo kanshi da ƙyar ya dawo mutum a dalilin mutuwar Maryam. Idan kuma har ta tabbata Maryam ba ta mutu ba ita ce wannan a hoto hakan na nufin za koma ‘yar gidan jiya kenan?
To ta yaya ma za a ce Maryam ba ta mutu ba, abin da ba zai taɓa yiwuwa ba ne!
Ta jijjiga kai “Maryam ta mutu! Maryam ta mutu! Maryam ba za ta sake dawowa cikin rayuwar ɗana ba, ba za ta dawo ta halakar min da yaro kamar yadda ta halaka wasu ta so ta halaka shi ba shi ma! Maryam kin mutu! Kin yi ƙarya ki sake dawowa cikin wannan duniyar tamu! Na yi alƙawari zan yi duk yadda zan iya don tabbatar da cewa kin mutu da gaske ba za ki sake dawowa cikin wannan duniyar tamu ba, zai fiye miki kwanciya cikin kabarinki akan yin gangancin sake dawowa duniyarmu!!!” Idanunta a warwaje kuma sun rine tamkar jini….

*****

Sannu a hankali Jalila ke tuƙa motar, lokaci-lokaci tana karkata kai ta dubi mijin nata. Gabaɗayan shi a firgice yake bayan damuwa da ta samu makwanci kan fuskarshi.

Sosai take jin rashin daɗi a ranta, ta ji tana son ta yi masa magana amma tana tsoron ƙara dagula lissafi, shawarar da zuciyarta ta ba ta shi ne lallaɓa shi za ta yi idan sun koma gida yadda za ta mantar da shi komai har su samu damar yin bacci cikin salama.

Koda suka isa gida sai ta raina wayonta, don kuwa duk yadda ta kai ga iya tsari da jan hankali ta kasa sama masa nutsuwar da hankalinsa zai ɗan kwanta koda kuwa na taƙaitaccen lokaci ne, ƙarshe ma fice mata ya yi a ɗakin ya shige ɗaya ɗakin ya kulle kanshi ya bar ta nan shanye da baki.
Kuka ta fashe da shi “Allah ya isa Maryam tsakanina da ke! Kina cuta ta kina zalunta ta, kin raba ni da samun farin ciki daga mijina kin hana mu zama lafiya… Kin mutu kin tafi masa da zuciya gangar jikinsa kaɗai kika bar min… Wallahi Maryam koda ace kina raye ni da kaina sai na raba ki da ruhinki… A kan me? A kan me za ki tafi ki bar tarnaƙi tsakanina da mijina… Wallahi wallahi Maryam ki kwanta a ƙabarinki shi zai fi miki kwanciyar hankali akan dawowarki duniya… Matuƙar ta tabbata ba ki mutu ba kina raye to ni da kaina zan kashe ki kisan gaske sannan in ƙwace zuciyar mijina daga hannunki yadda zai manta da ke har abada!”
Ta ƙara tsananta kukan ta tana cigaba da sambatu.

A nashi ɓangaren shi ma sambatun yake ta afkowa tamkar wanda ya sha ƙwayar doki, sai safa da marwa yake a ɗakin yana kai wa iska duka tamkar ba a tsakiyar dare yake ba.
Sunan Maryam kawai yake ambata yana jadadda rashin mutuwarta da ƙara tabbatarwa da kanshi cewa lallai Maryam ce wannan, kuma zai yi duk yadda zai iya don ganin ya sake dawo da ita cikin rayuwarsu duk irin tarnaƙi da ƙalubalen da zai fuskanta a wajen mahaifiyarsa da sauran masu ƙin jinin Maryam kuwa! Ya yi wa kanshi alkawari ba zai bari ya sake rasa Maryam a karo na biyu ba!

“Zan ce wajen likita! Tabbas zan je asibiti! Dole in tuhumi likitan da ya tabbatar da mutuwarki Maryam!”
Ya jinjina kai, ya dunƙule hannu ya kai wa iska duka, sannan a zabure kuma ya nufi ƙofa ya buɗe ya koma ɗakin da Jalila ke zaune dirshan tana gursheƙen kuka.
Tsulum! Ta gan shi ya faɗo ɗakin, kai tsaye inda ya ajiye wayarsa ya nufa ya ɗauko ta ya kunna ya lalubi wata lamba ya kira, bayan an ɗaga kiran ya soma magana.

“Hello Turaki kana ji na… Kana da labarin Maryam na raye…?”

“Maryam guda nawa muke da ita? Maryam da ka sani tana nan a raye a halin yanzu ma tana Lagos wai za a yi auren ta da wani bayerabe!”

“Ohhh kai ma kallon mahaukaci kake min kenan? Kai ma ba za ka yadda tana raye ba ta mutu ba? ‘yar uwarka ce fa…”

Ya kashe wayar ya jefar, hawaye masu ɗumi suka fara sunturi a dakalin fuskarkashi, ya ɗora duka hannuwa biyu aka kamar mai shirin hawa bori, sai kuma ya sake zabura ya jawo wayar ya sake nemo wata lamba ya kira.

“Hello Ɗanladi, don Allah ka yi haƙuri na tashe ka a bacci, don Allah ka shirya gobe da sassafe za ka rakani maƙabarta…”

“Ina saka ran za ka fahimce ni ne kai shi ya sa fa na neme ka, ka taimake ni Ɗanladi mu je mu duba ƙabarin Maryam don in tabbatar da zargina…”

Ya kashe wayar ya cillar, ya jingina da bango cikin runtse idanu.

Jalila dai na zaune ta daskare tamkar dasasshen gunki, komai na jikinta ba ya motsi face ƙwayoyin idanunta da ke bin duk motsin sa da kallo, idan an ce suman zaune ta yi ma ba abin musu ba ne, kalamansa sun girgiza zuciyarta matuƙa yadda har wani ciwo-ciwo take ji a ƙasan ƙirjinta…
Ita kam ko a tarihi ba ta taɓa cin karo da irin wannan jidali na bautar so haka ba, wane irin so ne haka Isah ke wa Maryam yake barazanar kashe kanshi da damuwa da tashin hankali?

Ta lallaɓata ta sauko daga kan gado ta tako a hankali ta tsaya a gabanshi, a yadda idanunsa suke a rufe ta ɗaga hannu da niyyar taɓa shi, ya yi zaraf ya buɗe idanun, ta zabura ta ja da baya, ya baza mata idanunsa da ke aiken saƙon tuhuma.

“Me kike shirin aikatawa?”

“Ba komai.” ta faɗa cikin girgiza kai tana ƙara ja da baya don yadda ta ga idanunsa suka sauya launi sun komai kamar gaushin wuta.

“Isah! Me ke shirin faruwa da kai ne haka?”
Leɓunanta na dukan juna ta yi furucin, bai tanka mata ba ya yunƙura ya sake ficewa daga ɗakin ya koma ɗayan, koda ta bi bayanshi ba ta ci nasarar cim masa ba ya mayar da ƙofar ya murza mukulli, ta dawo ɗakinta ta ɗauki waya jikinta na ɓari ta kunna, lambar Mamanta ta tafi lalube ta kira, sai dai wayar a kashe take, ta sauke wayar daga kuncinta ta zuba mata idanu tana nazarin wa za ta ƙara nema ta kira?
Zuciyarta ta ba ta shawarar neman wayar Mamansu Isah, sai dai ita ma a kashe, ta yi jifa da wayar cikin sakin dogon tsakin da ba ta san ma ta ja shi da tsayi har haka ba.

****

A cikin wannan hali suka wayi gari, don duk cikinsu babu wanda ya iya runtsawa, to ina ma suka ga kwanciyar hankalin yin bacci musamman ma shi Isah?

A nan ciki ɗakin da yake ya yi sallahr asubahi, yana idarwa ya cire kayan jikinsa ya mayar da jallabiya ya fice daga ɗakin.
Bisa sa’a sai ya yi arba da mukullin motarshi a yashe a kan teburin tsakiyar falo inda Jalila ta cillar da shi, ya suri mukullin ya fice daga ɗakin.

Mai gadin nasu ba ya nan ya tafi masallaci don haka da mukullin wajensa ya yi amfani ya buɗe gate ɗin gidan ya kunna motarsa ya fice.

Kai tsaye hanyar maƙabarta ya yi wa tsinke zuciyarshi na luguden duka, tamkar ya yi tsuntsuwa ya isa maƙabartar haka yake jin shi don haka yake ta alla-alla.

Da ya isa maƙabartar ya ci sa’ar tarar da mai gadi dawowar sa kenan daga sallah, suka gaisa sama-sama kasancewar farin sani da mai gadin ya yi masa na yadda duk ƙarshen wata yana zuwa ya yi wa mamata addu’a sannan ya fuskanci wani ƙabari ya yi ta addu’a yana sartun hawaye.

“Alhaji kai ne haka da asuba ko rashi aka yi ne?”

“Ba rashi aka yi ba, na zo duba ƙabari ne.”

“Ikon Allah! To kuma Alhaji ba ka iya bari gari ya waye sosai sai ka zo? Kuma na ga duka ai ba za ka wuce kwanaki goma sha uku da zuwa ba, na san kuma sai duk ƙarshen wata kake zuwa.”

“Bukatar hakan ce ta kama a gaggauce Malam Hashimu, ka yi haƙuri ka buɗe min don Allah.”

Ba tare da Malam Hashimu mai gadin ya ayyana komai a ransa mara kyau daga gare shi ba ya zura hannu a aljihu ya lalubo tarin makullai na ƙofofin maƙabartar ya zaro ɗaya daga ciki ya buɗe ƙofar, tun ƙofar ba ta gama buɗuwa ba Isah ya afka ciki ko addu’ar shiga maƙabatar bai samu sukunin yi ba.

A yadda ƙabarin marigayiya Maryam yake an masa gini gefe da gefe, sa’annan an sanya kafcecen allo a gaba wanda ke ɗauke da bayananta da ranar mutuwarta, duk da haka gefe akwai tafkeƙiyar bishiyar kuka wacce ta ranƙwafa ta samar wa da ƙaburburan ƙasanta inuwa. Dukkan waɗannan shedu ne da suka isa a yi wa wanda bai taɓa zuwa ƙabarinta kwatance ba da su ya gane, amma sai ga shi a tsaye a wajen ya nemi ƙabarin Maryam sama ko ƙasa ya rasa….

Wani irin dum! dum! Yake ji cikin kanshi yayinda wata shegiyar hajijiya ta soma barazanar tiƙashi da ƙasa.

Da ƙyar harshensa ya iya riƙe kalmar Innalillahi wa inna’ilair raji’un!

Ya dafe saitin zuciyarshi, sannan da ƙyar ya iya ɗaga murya ya kira Malam Hashimu.

Da sauri sai ga shi ya iso gurin.

“Malam Hashimu ina kabarin Maryam?
Ban ga kabarinta ba ina yake? Ko kuwa dai da gaske ba ta mutu ba ne?
Ni kaɗai nake ganin haka ko kuwa kai ma ba ka ga ƙabarin ba Malam Hashimu?”

Shi ma Malam Hashimun ya rikice, me ya ke shirin faruwa ne?
Ko shi kanshi a yammacin jiya ya biyo ta ƙabarin lokacin da yake zagaye a ciki, kuma tabbas ya ga ƙabarin, amma yanzu ga shi babu shi babu alamarshi, to ina ƙabarin ya tafi kuma?

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Siddabaru 1Siddabaru 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.