Skip to content
Part 3 of 16 in the Series Siddabaru by Muntasir Shehu

Kamar daga sama sai ga su Alhaji Tukur (babansu Isah) sun bayyana a cikin maƙabartar, har da Alhaji Ahmad mahaifin marigayiya Maryam da kuma su Turaki da Munkaila duk yayyun Maryam.

Gaba ɗayansu suka yi cirko-cirko a tsaye a gaban ƙaburburan da ke gurin cikin matuƙar ɗimuwa da tu’ajjibi.

Da gaske ne fa babu ƙabarin Maryam babu alamarsa, kuma tabbas babu tantama ko shakkar lallai a nan ne aka haƙa rami aka binne ta, a yanzu kuma babu, don haka lamarin yanzu ya shallake hankalin kowa, dole kuma a yi wai-wai-da-baya a koma a bi diddigin mutuwa da dalilin mutuwar tata.

Cikin matuƙar gigita Isah ya yi baya yana sambatu, “Tun farko sai da na faɗa cewa Maryam ba mutuwa ta yi ba, akwai abin da aka ɓoye, tabbas Maryam tana Lagos tana shirye-shiryen aure”
Ya fashe da kuka tare da juyawa ya nufi hanyar fita daga maƙabartar yana cigaba da sambatu. Me ya sa Maryam za ta yi masa haka? Me ya ta zaɓi wannan hanyar don gujewa ƙaddararta? Me ya sa ta kasa gasgata sadaukarwarsa gare ta? Ga shi yanzu hanyar da ta bi ba ta ɓulle mata ba.

A ɓangaren Babansu kuwa salati da sallallami suke zuciyoyinsu a tsinke, bayan kaɗuwa har da tsoro a tattare da su. Daga lokacin zuwan su duniya zuwa lokacin a ƙalla shekaru sittin da ɗoriya amma ba su taɓa ganin abin ɗaure kai da tsinka tunani irin na wannan lokaci ba.

“Malam kai ne mai gadin maƙabartar nan, garin yaya haka ta faru babu ƙabarin ɗiyar nan tamu.”
Cikin rashin hayyaci Alhaji Tukur ya fara tuhumar Mal. Hashimu.

A ɗan rikice Mal. Hashimu ya fara inda-inda. “Ammm. Alhaji… ummm wallahi… Wallahi ko jiya na ga ƙabarin nan, yanzu zuwan wannan yaro muka ga babu shi wallahi..”

“Malam dole kana da masaniyar faruwar wannan lamari in dai har da gaske gadin maƙabartar kake yi…” Cewar Kamal ƙanin Isah.
Da sauri kuma Alhaji Ahmad ya tare shi, “A’a Kamalu! Kar wannan tunani ya zo ranku, wannan ba lamari ne na saurin yanke hukunci da ɗora zargi ba, nutsuwa muke buƙata a halin yanzu don tantance gaskiyar abin da ya faru.”

Malam Hashimu mai gadi ya gama rikicewa gaba ɗaya, babban abin da yake tsoron faruwarsa shi yake shirin faruwa, hanyar kuɓutarsa kawai yake hange idan har maganar ta yi tsananin da za a dangana ga hukuma, hakan na nufin tsananta bincike a kansa har a gano rashin gaskiyarsa, nan take nadama mai girma ta cika masa zuciya, cikin ƙanƙanin lokaci gajimaren hawaye ya tattaru a idanunsa ya tarwatse.

“Ni fa ko kaɗan ban kawo a raina cewa tone ƙabarin nan aka yi aka cire gawar Maryam ba don babu wata alama ta an tone ƙasa a nan, yadda gurin nan yake tun fil’azal haka yake a yanzu, na tabbata kuma ko ƙarshen watan nan Isah ya zo maƙabartar nan don mun yi maganar zuwa tare amma ban samu dama ba, don haka ma mu canza tunanin ko sace gawarta aka yi.” Dogon sharhin da Munkaila ya ɗauko kenan, yana direwa kuma Turaki ya karɓe.

“Dama ai babu wanda ya yi tunanin haka, ni kawai da aikin jinnu na ta’allaƙa hakan duba da abin da Isah ya gano a facebook, kawai Malamai ya kamata a saka su duba lamarin.”

Kowa ya yi shiru, duk da cewa ba rasa abin faɗa suka yi ba, kawai dai harsunansu sun yi nauyin da ba za su iya fitar da sauti ba.

“Allah ya kyauta.”

Cewar Alhaji Ahmad lokacin da ya juya ya fara takawa da nufin fita daga maƙabartar. Da sauri Alhaji Tukur ya dafa masa, su ma sauran suka rufa musu baya suka bar Mal. Hashimu a nan tsaye cikin matuƙar taraddadi da tashin hankali.

“Ahmadu wannan fa ba abin da za a ce Allah ya kyauta kaɗai kuma a kau da kai ba ne, dole a tsananta bincike tun daga dalilin mutuwar yarinyar nan har zuwa kan wannan mai gadin, sa’annan dole mu gaggauta yin report wa jami’an tsaro don gudanar da abin da ya dace.” Abin da Alhaji Tukur ke faɗa wa Alhaji Ahmad kenan yayin da suke ƙoƙarin barin maƙabartar.

“Ni fa wallahi Baba ban yadda da mai gadin nan ba sam, na kasa yadda da kare shin da zuciyata ke yi daga zargin da na ɗora a kanshi, zamanin nan ya gama lalacewa, komai kuma zai iya faruwa, tsaf za a iya haɗa baki da shi a aikata wani mummunan abu wallahi.” cewar Kamal.
Turaki ya karbe, “Tabbas ni ma ina jin haka a raina duk da cewa wasu dalilai na kore hakan da haifar da shakku a zuciyata.”

“Koma dai yaya ne idan aka tsananta bincike za a gano.” cewar Alhaji Tukur.

Ba su iske motar Isah ba a gurin, hakan na nufin ya tafi kenan, don haka cikin sauri Turaki ya lalubo wayarshi ya kira Isah.

“Hello! Ina kuma ka tafi ne Isah?”

“Ina gida.” Isah ya amsa.

“Ok ga mu nan mun fito mu ma, za mu taho gidan.”

Ya kashe wayar ya shige motar da suka zo cikinta, dama shi ya tuƙo motar don haka duk suka shige motar ya tashe ta suka nufi gidan Alhaji Tukur.

****

Dukkan manya daga cikin iyalin sun hallara a babban falon gidan, fuskar kowa cike da shakkun wannan ruɗaɗɗen al’amari.

Isah a zaune yake amma zuciyarsa a tsaye take cak, tana aikin saƙe-saƙe da haifar masa tunani kala-kala, dukkan wasu jawabai da aka yi kan faruwar wannan lamari bai tsinci komai ba illa gaɓar ƙarshe wacce ita ma don ta zo daidai da shawarar zuciyarsa ne.

Wato za a shigo da hukumar tsaro cikin lamarin sannan a faro bincike tun daga asibitin da Maryam ta mutu da likitan da sauran ma’aikatan lafiyar da suka kula da ita har zuwa kan mai gadin maƙabarta.

Abu ɗaya ne bai ji an yi magana a kanshi ba shi ne batun zuwa a taho da Maryam daga Lagos kafin nan da cikar kwanaki uku, wato ranar da aka rubuta za a yi aurenta a jikin katin gayyatar da ya gano.

Miƙewa ya yi zaraf ya fara magana, “An faɗi komai amma ba a yi maganar zuwa a taho da Maryam ba, ko kuwa har yanzu zukatanku ba su yadda Maryam tana Lagos ba?”

Kowa ya yi shiru, aka shiga kallon-kallo har zuwa wasu ‘yan daƙiƙu kana Babansu ya ya katse shirun.

“Za a yi hakan Babana, amma sai bincike ya tabbatar da cewa lallai Maryama ba ta mutu ba an kuma ji dalilin yadda ta fita daga ƙabarinta ta tafi Lagos.”

“Hakan zai ja lokaci Baba idan har sai an gama bincike, saura kwanaki uku fa a ɗaura mata aure da bayerabe…”

“Idan kuma ba ita ba ce ba fa? Me ya sa kai ka cika gaggawa ne Baba?” Alhaji Ahmad ya katse shi. Da sauri shi ma Isan ya amsa, “Ita ce ma, wallahi ita ce Baba… Ni kam yau zan shirya in tafi Lagos in taho da ita….”
Cikin faɗa Alhaji Ahmad ya dakatar da shi
“Babu inda za ka je! Babu kuma wanda zai ɗauki kafa ya je, mu ba sakarkarun mutane ba ne ka ji ko!”

Isah ya sunkuyar da kai yayin da ƙwalla masu zafi suka cika idanunsa, yadda yake jin ransa na tafasa zuciyarsa na taurara ba ya jin akwai wanda ya isa hana shi zuwa Lagos a yau ya taho da Maryam, ya tabbatar ba za a fuskance shi ba har sai an gan shi tare da ita sannan za su tabbatar da gaskiyarsa.

Miƙewa ya yi zai fice daga ɗakin.

“Ina za ka je?” Babansu ya katse shi da tambaya, cak ya tsaya ba tare da ya tsinka ba.
“Wato so kake ka koyi gaddama kan wannan al’amari ko? Kana so ka rufe idonka ka ce ba za a saka ka ba, ba za a hana ka ba ko? To ka dawo ka zauna a ƙarƙare magana.”

“Ka bar ni da shi Yaya, babu in da zai je har sai an gama bincike.” Cewar Alhaji Ahmad.

Kasancewar Turaki yana da aboki jami’in tsaro don haka ta hanyar shi aka bi aka shigar da report, nan take kuma aka fara gudanar da bincike a asibitin da Maryam ta mutu.

Babban asibiti ne na kuɗi, kuma an yi matuƙar sa’a likitan yana nan har lokacin yana aiki, sai dai wasu daga cikin nurses da suka canza asibiti.

Kwatsam Likitan ya ga Sufetan Ɗansanda tare da Isah, Turaki, Kamal da kuma Alhaji Tukur, babu mahaifin Maryam don ya ce ba zai zo ba.

Nan aka tsiye Likitan da tambayoyi kan dalilin mutuwar Maryam ɗin, kasancewar ba abu ne da ya faru a jiya ko shekaran jiya ba, dole akwai halin mantuwa, don haka sai da aka tafi binciken fayil ɗin waɗanda suka rasa rayukansu a asibitin, da ƙyar aka lalubo nata, don har an fidda ran ganin shi duk da yadda aka birkice komai na ɗakin ajiyar takaddun aka tayar da hankalin komai na ɗakin.

Rashin ganin takardar a farko ba ƙaramin ƙara dasa tubalin zargi ya yi ba a zukatan su Isah, har ya fara wassafa irin mugun hukuncin da za su yi masa kafin a kai ga yi a hukumance, sai kuma aka ci sa’ar ganin shi.

Bayan dogon nazari da likitan ya yi kan fayil ɗin ya ɗago ya sharce gumin da ya tsatssafo masa a goshi na fargaba, ya zare gilashi da ke maƙale a saman karan hancinsa ya yasar gefe, kana ya fitar da nannauyan numfashi.

Ya nisa ya soma koro bayani daga kan waɗanda suka yi aiki a kanta kafin mutuwar tata inda ya karanto sunayensu, nan take Sufeta ya bayar da umarnin su ma kawo su ofishin, daga ciki guda ɗaya aka samu wacce ta rage, sauran duk sun canza gurin aiki.

Bayan an gurfanar da nurse ɗin mai suna Ummi, likitan mai suna Doctor Mansur ya soma jawabi kan lalurar da samu Maryam har ta yi ajalinta.

“Yallaɓai Maryam ta rasa ranta ne sakamakon bugawar zuciya da kuma tsotsewar jini a jikinta.”

“Me kenan hakan yake nufi a likitance?”

“E to, kai tsaye dai ba lalura ba ce wacce za a ce ga sunanta, hasali ma ni dai ban taɓa ganin lamari makamancin wannan ba, don kuwa dai an kawo ta ne tana fama da matsalar ciwon ƙirji wanda a lokacin bincike ya nuna Ulcer ce take ɗauke da ita, amma daga baya sai ta samu bugawar zuciya da kuma ɗaukewar jini a jikinta don a lokacin na tabbatar ko wuƙa aka sa aka yanka jikinta ba za a samu jini ko ɗigo ɗaya ba wanda hakan kuma ya saɓa ɗa ƙa’idar jikin da rai bai jima da fita daga cikinshi ba.”

“Wane tabbaci kake da shi a lokacin da ka bayar da sanarwar mutuwarta?”

Doctor ya gyara zama yana fuskantar Sufetan.

“Yallaɓai kar ka manta fa ni likita ne, ina da ƙwarewa a kan aikina kamar yadda kake da shi a naka aikin.”

“Na san da haka”

“To shakkun me kake yi cikin aikin?”

“Me zai saka ba za a yi shakku ba tunda an je an nemi kabarin Maryam an rasa babu shi babu alamunsa? Maimakon hakan ma sai aka jiyo ɗuriyarta a Lagos ana shelar aurenta da Bayerabe.”

Zuciyar Doctor ta buga da ƙarfi, maganar ta matuƙar girgiza shi, shi kwata-kwata bai taɓa kawo wa a ransa wannan shi ne dalilin binciken ba, don haka nan take gumi ya soma tsattsafo masa ta kowace ƙofa a jikinsa.

Sufetan ya yi murnushi mai kama da na mugunta, ya yi tsai yana nazarin Doctor har zuwa lokacin da ya samu ‘yar nutsuwar da ya tattara ‘yan ƙwayoyin kalamai da yake ganin za su kore waccan tuhuma.

“Idan na fahimta kamar ana zargina ne akan cewar Maryam ba ta mutu ba na ce ta mutu?”

“Ba ana zargin haka ba ne, tabbacin hakan kawai ake buƙata, faƙat!”

Doctor ya sake buɗe fayil ɗin marigayiya ya turo gaban Sufetan,
“Wannan shi ne tabbaci, cewa ta mutu sakamakon bugawar zuciya da ƙafewar jini.”

Sufeta ya kalli fayil ɗin a lalace, ya ture shi gefe, sa’annan ya juya ga nurse Ummi wacce jikinta ke ta rawa tamkar mai zikiri.

“Amm Ummi kike ko?”

Da rawar baki ta soma inda-inda “E.. E.. Ummu sunana.”

“To malama Ummi a matsayin ki na ma’aikaciyar jinya wacce ta jinyaci Maryam har ta mutu wane ƙarin haske za ki yi mana a kan abin da Likita ya faɗa?”

Duk yadda ta so ta samar wa kanta nutsuwar da za ta yi jawabin da ta ke saka ran zai bayyanar da cewa ita mai gaskiya ce sai hakan ya faskara. Ta kwashi rawar laɓɓa ta soma faɗin, “ummm… Ammmm Ranka ya daɗe.. Yallaɓai ai.. ai Doctor ya gama bayani… Mu kawai aikinmu mu ba ta magani ne da saka mata drip da yi mata allura in ta kama…”

“Allura? Kamar wace irin allura kenan?”

“Akwai duk bayanai a cikin fayil ɗin ranka ya daɗe.”

“An ce ku uku ne nurses ɗin da kuka kula da ita, sa’annan an ce yanzu biyu ba sa aiki a wannan asibiti sun canza gurin aiki, ko meye dalilin barin su wannan asibiti?”

“E to, akwai sister Hafsa wacce ita sun tashi daga gidansu ne sun bar unguwar gaba ɗaya kasancewar a gidan haya suke dama, sai… sai… sai sister Asabe wacce ita kuma ban san dalilinta ba, amma daga baya na fuskanci sun ɗan samu saɓani da mai asibitin ne.”

Ta ajiye zuciya yadda kowa sai da ya sake kallon ta, dole za a yi mata kallon mara gaskiya duba da yadda fuskarta ta gama rinewa da gumi, wanda da za a duba cikin hijabinta tuni ta jike sharkaf, ita a duniyarta abu na farko da yake matukar gigita ta da tayar mata da hankali shi ne titsiye, bare kuma ace ga ɗansanda, don haka ko tana da gaskiya ba lallai kalamanta su ƙwace ta ba.

Sufeta ya ɗago ya dubi sauran jama’ar da ke cikin ofishin, fuskar kowa ɗauke da saƙon da zuciyarshi take dako, ya yi guntun murmushi ya mayar da kanshi ga Likita wanda tuni ya sake mayar da farin gilashinsa mazauninsa, ya soma tattare takaddu duk don ya samar wa da kanshi nutsuwa.

“Doctor, muna matuƙar godiya da waɗannan jawabai da muka samu daga gare ka, abu na gaba shi ne akwai yiwuwar mu sake waiwayar ka don cigaba da gudanar da bincike ina fatan za ka ba mu haɗin kai kamar yadda ka ba mu a yanzu.”

Da murmushi guntu iyakar fatun baki ya amsa “In sha Allahu.”

Ɗansanda ya miƙe tare da duban su sauran yaransa ya ba su umarnin tafiya.
Su ma su Isah suka fice ba tare da sun waiwayi likitan ba wanda a halin yanzu sun gama ɗora masa zargin da haɗin bakinsa cikin al’amarin Maryam, ba don ma gudun shiga aikin hukuma ba da take za su ce Maryam ta haɗa baki da shi ne ya yi mata allurar bacci sannan ya ce ta mutu, daga baya kuma suka je suka tone ta ta gudu Lagos don ta yi nisa da su.

*

Isah ya kafe kan a bar shi ya tafi Lagos ya ɗauko Maryam, yadda yake zubar da hawaye abin zai matuƙar ɗaure zuciyar duk wanda ya san shi, babu shakka ƙaunar da Isah ke wa Maryam ta fi gaban dukkan kwatance, alamu sun nuna tabbas wannan karon zai iya samun babbar matsala a rayuwarshi muddin bai samu yadda yake so ba, nan take tsoro ya fara ɗarsuwa a zuciyar mahaifinsu, ya soma ji a ransa gwara ya bar shi ya je ɗin, inyaso idan ya je ya ga ba ita ba ce dole ya sake haƙura da ita a karo na biyu.

Sosai cikin kuka yake roƙon Baban ya amince masa su tafi tare da Ƙaninsa Kamal da kuma Turaki yayan Maryam ɗin.

“Baba kar ka biye wa Abbansu Maryam, kasan rashin kyawun alaƙar da ke tsakaninsu, na tabbatar kuma har yanzu bai huce da lamarinta ba shi ya sa ya ce ba zan je ba don bai so ta dawo rayuwarsa, na sani ba ya son ta…”

“A kul Babana! Kar in sake jin haka daga bakinka, me ya sa kake son yin abu kamar ɗan ƙaramin yaron goye?” Baban ya katse shi.
Ya yi shiru yana sharce hawaye, Baba ya sake cewa, “To kai duk da kake ta wannan gaggawar son zuwa ka taho da Maryam a ina kake tunanin kai tsaye za ka same ta?”

Kai tsaye ya amsa, “Akwai adireshi na gurin da za a yi party gobe, sannan kuma zan turawa wanda ya ɗora hatunan saƙo tun da Allah ya sa na yi adding ɗin shi cikin friends ɗina na facebook ɗin.”

Baba ya yi shiru, har yanzu fuskarshi ba ta nuna alamun ya gamsu ba.

Isah ya miƙe ya tafi wajen Sufeta Usman ya soma yi masa bayanin da yake ganin zai gamsar da shi.

“Inspector, shin ba ka yi tunanin cewa a je a taho da Maryam ba tun ga shi an san a inda take? Ba ka yi tunanin hakan zai sauƙaƙa bincike ba?”

Cikin nuna gamsuwa Sufeta Usman ya soma gyaɗa kai, “Tabbas ka ce wani abu, sai dai kuma tafiyar ka kai kaɗai akwai hatsari.”

“Ba ni kaɗai zan tafi ba, akwai ƙanina Kamal da kuma Turaki.”

“Good, amma duk da haka akwai buƙatar mu haɗa ku da jami’ai koda guda biyu ne da za su taimaka muku, sannan za mu tura saƙo ga division ma fi kusa a can da za su ba ku gudunmawa.”

Cikin matuƙar jin farin ciki Isah ya saki ajiyar zuciya, nan take kuma fuskarshi ta cika da walwala.

“Ban san da kalmar da zan gode maka ba Inspector, iya yau kaɗai na ƙara gamsuwa da aikin ɗansanda, na tabbata ba mu da wani gata mafi kusa da mu da ya wuce ɗansanda, na gode na gode sosai Inspector.”

“Babu buƙatar godiya Isah, wannan aikinmu ne sadaukar da dukkan lokacinmu don karewa al’umma haƙƙoƙinsu da tabbatuwar zaman lafiyarsu, kuma ko ba haka ba ai Turaki aminina ne, zan iya komai dominsa, balle kuma a kan haƙƙin ran ƙanwarmu.”

Suka yi musabaha, Isah na jin kogin farin ciki na kwararar da ruwan nishaɗi a birnin zuciyarsa.

Sufeta Usman da kanshi ya yi wa Babansu Isah bayanin da ya gamsar da shi ya aminta su Isah su je Lagos ɗin tun da tare da jami’an ‘yansanda za su tafi amma ba yau ba sai dai gobe.

<< Siddabaru 2Siddabaru 4 >>

1 thought on “Siddabaru 3”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.