Skip to content
Part 9 of 16 in the Series Siddabaru by Muntasir Shehu

Abubakar Tafawa Ɓalewa University

Burin Maryam ya cika, yau ga ta a jami’a cike da tarin farin ciki da kyakkyawan fata da take da shi a kan wannan karatu nata.

Sai dai tun farkon tafiya ta fara cin tuntuɓe da ƙalubale, domin kuwa a yadda ta yi fata da burin abin ya kasance, saɓanin haka ne ya faru.

Wato ta so a ce matan da za su yi rayuwa tare a hostel gogaggu ne waɗanda suka san kansu, masu aji waɗanda boko ta ratsa, sai ga shi ta ɓuge a ɗakin ustazan mata, yayin da ɗaya daga ciki ma ƙabila ce kirista ‘yar Jihar Taraba, sauran mata biyun ne Hausa-Fulani, ɗaya ‘yar Bauchi ɗaya ‘yar Gombe.

Lura da ta yi da cewa tafiyarsu ba za ta zo ɗaya ba ya sa ma sam ba ta wuni a hostel ɗin, cin abinci da bacci kawai ke kawo ta ɗakin har Allah ya haɗa ta da ƙawa irin wacce take burin samu.

Sun fara ƙawance da Khairat kasancewar kusan komai nasu ya zo ɗaya, sai dai Khairat ɗin ba a cikin makaranta take rayuwa ba, gida ne sukutum ta kama take rayuwarta ita kaɗai.

A yadda ta faɗa wa Maryam ita ɗin ‘yar Jihar Jigawa ce a garin Dutse, mahaifinta ɗan siyaya ne, kuma su ne cikin gwamnati dumu-dumu.

Ba ƙaramin daɗi Maryam ta ji ba da haɗuwar ta da Khairat, da aminci ya yi nisa tsakaninsu ma sai ta tattara komatsanta ta koma gidan Khairat kamar yadda ita Khairat ɗin ta nema.

Ƙalubale na farko da ta fara cin karo da shi shi ne, ta lura duk gayu da ƙaryar aji da Khairat ke nunawa ashe ba ta da kamun kai, tamkar zaman dadiro ma take yi. Jibson wanda a cewar Khairat ɗin saurayinta ne shi ya mayar da ita tamkar matarsa, tare suke kwana kullum, da safe kowa ya kama gabansa.

Da farko jikin Maryam ya yi sanyi matuƙa, don har ga Allah ita ba shashanci ya kawo ta makarantar ba, amma da ta ga har zuwa wani lokaci babu wani abu mai kama da hari da ya taɓa gifta ta, ko kuma ita Khairat ɗin ta yi mata tayin irin lalatar da suke yi a wajen abokan Jibson sai ta fara sakin jikinta.

Abin da ya ƙara kwantar mata da hankali shi ne yadda wata rana wani abokin Jibson ya zo gidan, da ya ganta sai ya fara ƙoƙarin nuna maitarsa a zatonsa ‘yar hannu ce, Khairat ta ɓata rai ta nuna masa ita Maryam ba ta wannan harkar don haka ba ruwansu da ita. Wannan ta sa Maryam jin sanyi a ranta ta kuma saki jiki ta mayar da hankali kan karatunta, karatu ta ke so ta yi irin na bai wa mara ɗa kunya.

Kwatsam wata rana sai ga AbdulNasir, ba ta yi mamakin ganin sa ba don kusan kullum suna tare a waya dama, wannan zuwan nashi a hargitse ya zo, ya ce mata iyayensa sun sako shi a gaba za su yi masa auren dole muddin bai kawo musu mata nan da wata guda ba shi ya sa hankalinsa ya tashi matuƙa!

Kallon shi ta yi cikin ido ta ce, “Dear, yanzu karatun nawa kake so na ajiye in zo mu yi aure ko yaya?”

Cikin girgiza kai ya amsa, “Ba zan hana ki karatunki ba Marry, fatana kawai ki ce kin amince kin fitar da ni a matsayin wanda za ki aure… kin ga hakan zai ba ni ƙwarin gwiwar zuwa in cewa su Dad na fid da zaɓin zuciyata…”

“Maryam ba za ta taɓa zama zaɓin zuciyarka ba Malam, ko ta zama ma to ba za ta taɓa zama mallakinka ba!”

Gaba ɗayan su suka ɗaga kai zuwa ga inda maganar ta fito, Isah ne, fuskarsa a ɗaure tamau tamkar wanda ke tafe da saƙon mutuwa.

Ya ƙaraso gabansu ya tsaya.

“Maryam ki sallami gayen nan ya koma in da ya fito…”

“Ji nan mr man! Ba ka da wata zarrar da za ka kawo min cikas ko ka katse min hanzari yayin da na ke tare da maɓuɓɓugar farin cikina…” A hasale AbdulNasir ya furta yana zare gilashi daga idonsa.

Daidai lokacin Khairat ta zo wucewa suna tare da Jibson, ta ja ta tsaya tana ƙare musu kallo su ukun.

“Maryam baƙi kika yi haka amma ba ki sanar da ni zuwan su ba.”
“Sorry, zuwan bazata ne suka yi min…”

“Ayya! Amma gaskiya ba ku kyauta min ba… at least ko waya ce ai kwa kira ku sanar da ita sai mu shirya tarbar ku… ga shi ga dukkan alamu kun sha hanya…”

Ta juya ga Maryam, “Ki kai su gida ko… ya kamata a ce sun zauna sun huta ko?”
“Hakan ya yi.”

Duk da fuskokin Isah da na AbdulNasir cike suke da mamaki ba su gaza gurin amsa gaisuwar Khairat ɗin ba, Jibson na tsaye ƙiƙam yana ƙare musu kallo a wulaƙance, ganin su yake kamar wasu gidadawa duk kuwa da irin gayun da suka sha na wankan sukari.

Maryam ta gabatar da Khairat gare su, sannan ta gabatar da su ga Khairat ɗin a matsayin yayyenta, duk da AbdulNasir ya so fasa ƙwai amma ta ɗaure fuska ta aika masa da harara dole ya kame kanshi.

Kafin Khairat ta wuce ta ƙara jadadda mata ta kai su gida su sha ruwa su huta. Bayan tafiyar ta Isah ya kalle ta cikin damuwa.

“Sweety maganar gida na ji kuna yi? Garin ya haka ta faru?”

Ta wulƙita idanu cikin gajiyawa. “E gida fa! Na bar zaman hostel ne.”

“Amma ba ki…” Ta yi saurin dakatar da shi ta hanyar ɗaga masa hannu, sannan kamar cikin ɓacin rai ta ce, “Kar ka faɗa don Allah Ya Khalifa, ka yi min addu’a da fatan alkhairi… wai ma ta yaya kuka haɗa baki kuka yi min zuwan bazata haka?” Ta sauya akalar zancen ta kuma cika fuskarta da murmushi.

Isah ya waiga ya kalli AbdulNasir ya ɓata fuska, shi ma AbdulNasir ya sha kunu ya kawar da kai yana jin ƙunar rai, darajar ‘yan uwantakar da ke tsakanin Maryam da shi ya ke kalla amma ba don haka ba da tuni ya nuna masa iyakarsa, ko kaɗan shi ba ya kallon Isah matsayin abokin takararsa, kallon irin yaya mai matsantawa ƙannensa ya ke don haka gaba ɗaya ya ƙi jininsa.

“Ki fara sallamar shi ya tafi don tafiya zan yi da ke.”

Ta zaro idanu. “Ka kai ni kenan?”
“Ki sallame shi na ce!” Ya ɗan ɗaga sauti.

Sauya fuska ta yi ta ce, “Look Ya Khalifa! Yadda kake ganin ka yo tafiyayya ka zo shi ma haka ne, so cikin ku babu wanda zan kora don in faranta wa wani… though ma ina da lecture ƙarfe huɗu amma zuwan ku ya sa zan haƙura da ita.” Cikin damuwa ta ƙarasa maganar.

Shiru ya gifta tsakaninsu, kowa da abin da yake saƙawa cikin ranshi. Can sai Isah ya duba agogon da ke hannunshi, ya ɗago ya dube ta.

“Na ba ki mintuna ashirin ki saurare shi.”

Ya juya ya koma in da ya ajiye motarsa ya buɗe ya shige, kujera ya kwantar ya kishingiɗa tare da kunna na’urar sanyaya guri.

AbdulNasir cigaba ya yi da dabaibaye kunnuwan Maryam da kalaman da yake zaton suna ratsa zuciyarta, sama-sama take biye masa har ya gaji suka yi sallama bayan ya sauke mata niƙi-niƙin kayan tsarbar da ya taho mata da su.

Kafin ya wuce sai ya da aikewa da Isah saƙon harar mai cike da gargaɗi sannan ya wuce. Ko ta kanshi Isah bai bi ya ja motar zuwa gurin Maryam ɗin.

Shi ma dai ba yabo ba fallasa, haka hirar tasu ta tafi duk da bakinsa cike yake da maganganu amma ya kasa ganin fuskar da zai tuhume ta musamman a game da gidan da ya ji ta ce ta koma can, da kuma ita kanta Khairat da bai gamsu da tarbiyarta ba, tare da cewa yaron da ya gan su tare ko ba a faɗa irin yaran nan ne lalatattu, abin da yake tsoro shi ne kar tarayyar Maryam da su ta sa su gurɓata mata rayuwa, dama yaya yunwar kare balle ya samu ƙashi!

Sannu a hankali suka cinye zangon karatu na farko, suka sami hutun mako biyu don haka ta tattaro ta dawo gida.

Abin mamaki sai ta tarar da Zainab na fama da cikinta da har ya fito sosai, da ta je gidan Turaki ma ta tarar da Khalisat na fama.

Ta dinga girgiza kai tana taɓe baki, a ranta take ayyana cewa dama fa abin da ake yayi kenan yanzu, daga an yi aure sai ciki, kamar a ruwa ake sha… kamar kuma dama jira ake a shiga gidan a ɗauki cikin… da a ce har ita aka yi auren ds yanzu ita ma tana nan tana fama da wannan kayan, da yanzu kuma ana nan an fara yi mata lissafin watan haihuwa…

A ɗan zaman hutun da ta yi ta ga naci iya naci daga AbdulNasir zuwa kan Isah, don dukkansu iyayensu sun sako su gaba da fushi ba na wasa ba, shi ya sa su ma suka sako ta a gaba kan ta watsar da batun karatun a yi auren. Dalili kenan da tun saura kwana uku a koma hutu ta tattara ta koma makaranta, don kar su dame ta ma sai duk ta kulle layukansu, wayar tata ma ta dinga nesa-nesa da ita.

Karatunsu na zango na biyu ya fara nisa, wata rana saƙo ya shigo wayarta na mutuwar Khalisat matar Turaki, cikinta wata shida ta dinga zubar da jini, sai da aka yi mata aiki aka cire cikin bayan nan kuma ta ce ga garinku nan.

Mutuwar ta gigita ta matuƙa, sai ga shi ta tsinci takanta da yin hamdala a zuciya, gani ta yi da a ce ita ma ta yi auren abin da zai faru da ita kenan.

Duk da cewa ana tsakiyar karatu haka ta dawo ta yi ta’aziyyar kwana biyu ta koma.
Ba ta jima da komawa ba mai afkuwa ta afku.

Haɗuwar ta da Kabir kamar shiryayyen abu, cikin ƙasa da mako biyu ya gama kanainaye mata zuciya, ba ta taɓa jin so a cikin ruhinta ba sai a kan Kabir.

Ya zo mata da wani irin salon soyayya da duk rintsi ba ta iya ƙetare umarninsa.
A cikin makaranta suka haɗu wata rana tana zaune a capteria ita kaɗai tana cin abinci kasancewar sun samu saɓani da Khairat, don har sun rabu ma, inda ta gane ashe ƙarya kawai Khairat ɗin ta shisshirga mata, ba ma sunanta Khairat ba, sunanta ashe Ladidi, kuma iyayenta talakawa ne tulus, sanan an daɗe da korar ta daga makaranta, duk fafar da ta ke yi ta ƙarya ce Jibson shi ya ke mata komai, kuma daga baya ya kama ta da cin amanarsa ta satar masa maƙudan kuɗi don haka ya kore ta ya wulaƙanta ya kuma ya ƙwace gidansa wanda dama nashi ne ta yi mata ƙaryar ita ta kama haya, tana kallo kuma ya kawo wata sabuwa fil ya saka ta gidan.

Tun daga nan Maryam ta fara tsorata da lamarin jami’a da mutanen da ke cikinta, yanzu ƙawarta ɗaya, wata Habiba ita ma kuma nesa-nesa suke ƙawance kasancewar ɗaki ɗaya suka kama a wani gida na ɗalibai kusa da makaranta.

Tana nan zaune jigum tana cin abinci amma kamar magani take ci, kawai sai gani ta yi ana ajiye kayayyakin abinci a kan teburin da nata abincin ke kai, kafin ta kai ga yin magana ya ƙaraso ya ja kujera ya zauna. Kallon farko da suka yi wa juna sai da gabanta ya yi mummunan faɗuwa har sai da ta saka hannun ta dafe saitin zuciyarta.
Murmushi yake jifan ta da shi wanda yake ratsa har ƙwaƙwalwarta. Tun da ya zauna bai yi magana ba, sai dai duk lokacin da za ta ɗaga kai ta kalle shi sai sun haɗa idanu, idan idanun nasu suka haɗu kuma sai ta ji faɗuwar gaban da ta fi na baya. Da dai ta ga ba za ta iya jura ba ta tatare komatsanta ta bar wajen ba tare da ta kammala cin abincin ba.

Zuwan sa gidansu da daddare ya ƙara shayar da ita ruwan mamaki, ya zo mata da batun neman soyayyarta, abin kamar wasa sai ga shi babu wani ja ta yi amanna, komai ya faɗa mata nan take take gamsuwa.

Sai bayan ta koma gida ne take ta jin haushin kanta da yadda ta kasa sarrafa kanta da harshenta a gabanshi.

Duka satin su biyu da haɗuwa ranar Asabar ɗin cikar kwana na goma sha biyar da haɗuwar su ya zo mata da buƙatar son su je ta ga gidanshi, ba ta musa ba ta amince, don haka ta koma gida ta fara shiri.

Habiba ta so hana ta zuwa tare da ankarar da ita cewa babu wanda ya san Kabir, kuma an ce an daɗe ana ganin shi yana gilmawa a makarantar amma babu wanda ya taɓa cewa ya san shi ko ya san department ɗin da yake.

Duba irin tafka-tafkan motoci da muma tsadaddun kaya da ya ke sakawa wanda abu ne kuma mai wahala a ce in dai kana hawa manyan motaci a makarantar a ce ba ka yi fice ba, don ga ire-iren su nan birjik a makarantar ‘ya’yan masu kuɗi da masu mulki, sai dai shi babu wanda ya taɓa ganin shi tare da wani balle a ɗorar da wani abu a kanshi.
Maryam ta ƙeƙashe ƙasa ta ƙi yarda da duk wata togaciya da Habiba ta kawo mata, ta shirya kwalliyarta mai tsada ta bi shi suka tafi.

A ganin idanunta tafiya suka yi mai ɗan nisa a kan titi suna tafe suna hira har suka zo gidan cikin jerin rukunin gidajen masu kuɗi, duk da cewa ba ta san sunan unguwar ba amma za ta iya shaida manya-manyan gidajen da ke unguwar…

Abubuwan da suka biyo baya ba za ta iya ɗorar da su ba tun bayan wani irin lemo da Kabir ya saka aka kawo ma ta ta sha. Ganin idanunta ba lemo ba ne JINI ne amma sai ta kasa ƙin sha, abin mamaki kuma sai ta ji jinin na da zaƙi cakwai, daga nan kuma ba ta ƙara sanin me ya faru da ita ba sai hayaniyar mutane ce ta ke ratsa kunnuwanta tana shiga ƙwaƙwalwarta. A hankali kuma ta buɗe idanu da ƙyar, dishi-dishi ta fara ganin mutane.

Ihun da aka ƙara sakawa ya sa ta buɗe idanu tangararan inda ta tsinci kanta gaban wani kafcece kogon wata shirgegiyar bishiyar tsamiya da ke can cikin dajin bayan makaranta. Da sauri ta kai hannu ta murje idanu ta kuma yi yunƙuri a ƙoƙarinta na miƙewa amma sai ta ji wani azababben zafi da ya taso daga mararta ya ratsa har ƙwaƙwalwarta, ba ta iya jurewa ba sai da ta saki ƙara.

Da sauri wasu daga cikin ‘yan matan da ke tsaitsaye a gefe suka ƙarasa gare ta suka daddafe ta suna aike mata da saƙon sannu-sannu.

Daidai lokacin motar makaranta ta iso gurin, motar na tsayawa sai ga Habiba ta fito daga ciki a guje ta isa kan Maryam ta rushe da kuka.

Maryam a kiɗime take matuƙa, sambatu kawai take tana faɗin. “Habiba me ya faru da ni? Waye ya kawo ni nan? Ina Kabir? Me ya aikata min ne?”

Kuka kawai Habiba ke yi, ita ma Maryam zuciyarta ta karye ta fashe da kuka.
Matan da suke gurin suka taimaka mata ta shiga mota aka nufi babban asibitin makaranta da ita.

An bincike ta tsaf ba a ci karo da wani abu a tare da ita ba wanda ya danganci fyaɗe ko saduwa da ita ba, lafiya ƙalau take sai ciwon jiki.

Wannan shi ya taƙaice tsawaita bincike musamman yadda ita ma ba ta da abin ɗorarwa, kodayake an so ba ta hutu ta koma gida amma sai ta nemi alfarmar tun da babu abin da ya faru da ita kawai a bar ta ba sai ta koma gida ba, ba ta son karatunta ya samu tasgaro.

An cigaba da bincike kan Kabir wanda ba a ƙara ganin giccin shi a makarantar ba, hakan nan tun daga waccan ranar Maryam ba ta ƙara samun nutsuwa da kwanciyar hankali ba.

Kabir ne ya cigaba da zuwar mata akai-akai da wata siga wacce ita kaɗai ke iya ganin shi. Duk zuwan shi kuma ya kan zo mata da umarnin da ba ta iya ƙetarewa duk a bayan umarnin akwai faruwar wani mummunan al’amari. Sai bayan komai ya faru ta shiga tashin hankali da baƙin ciki da kuka da nadama. Gaba ɗaya ma sai karatun nata ya shiririce, a daddafe ta ƙarasa zangon suka samu dogon hutu na tsawon watanni uku ta tattara ta dawo gida.

Ƙaddararta da ta ɗauko a makaranta ta biyo ta har gida, domin kuwa Kabir ya cigaba da zuwa mata a sigar da ya saba zuwa tare da umarninsa mai wahala a gare ta.
Cikin umarnin aka yi ta rasa rayuka musamman na matasan samari wanda shi kanshi AbdulNasir bai kuɓuta ba sai da ya rasa nashi ran, shi ma Isah da ƙyar ya tsallake rijiya da baya ba tare da ya sani ba.

Tun mutane ba su farga da lamarin Maryam ba har suka farga suka sako ta a gaba da karan tsana da ƙyama amma ban da Isah wanda shi babu wanda zai iya iyakance adadin yawan son da yake wa Maryam.

Cikin haka aka wayi gari Maryam ɗauke da larura birkitacciya wacce aka rasa sanadinta, larurar da ta zamo sanadin ajalinta ta mutu tana mai nema wa kanta gafarar kura-kuran da ta tafka a iya tsayin rayuwar da ta yi a doron duniya…

Bayan mutuwar ta tilas Isah ya haƙura ya auri Jalila ɗiyar ƙanwar Mama, ya aure ta ne auren cike gurbi ba don ta samu koda taku ɗaya daga cikin filin zuciyarshi ba, shi Maryam kaɗai ya so, a kanta ya koyi so, a kanta ya fara so, saɓanin ita bai san yadda zai so wata ba, don haka Jalila ke fuskantar tarnaƙi a gidanta; na auren gangar jikin Isah yayinda zuciyarshi take gurin mataciyya!

Turaki ma tun bayan rasuwar matarsa Khalisat bai sake marmarin aure ba don mikin rashin ta na nan ɗam a zuciyarshi.

(Wannan ita ce Maryam da yadda rayuwarta ta gudana a baya. Yanzu za mu koma kan labarinmu mu ɗora don mu ji labarin Maryam da za a ba wa su Isah, duk da cewa ga dai Maryam nan mun san ta mutu!)

<< Siddabaru 8Siddabaru 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.