Skip to content
Part 13 of 45 in the Series Siradin Rayuwa by Sumayyah Abdulkadir (Takori)

Juma’a 21 Jumada Thani

Abinci ake ci bisa dining table kamar yadda yake a al’adar gidan. Furkan ne tsakanin Intisar da Aminu, Hajiya ta kiftawa Aminu ido za a yi mugunta kenan, ya ce da Idris ya miko masa ketch-up (tumatirin kwalba) sai ya faki idon kowa ya janyo har da kwalbar pepper irin attaruhun nan da Larabawa ke sarrafawa cikin kwalba ya zazzaga ketch-up kadan kafin ya zazzaga yajin pepper din kusan rabin kwalbar a plate din shi ya cakude shinkafar ‘fried-rice’ din shi, yau kam ya kudire Saratu ba za ta ci abincin ranar nan ba.

Hankalin ta na kan T.V inda ake watso shirin da take matukar so na Tom & Jerry, ya faki idon kowa ya sauya masu plate ya janyo nata ya ci gaba da ci hankali kwance, ta cika cokali ta kai bakinta ba tare da ta dubi abincin ba ta tauna ta hadiye, ba shiri ta furzo shi waje cikin plate din Daddy da Hajiya ta zazzaro ido abin dariya ta ture plate din ta mike tana tsalle da ihu.

Daddy ya mike ya kamo ta ta fincike ta yi bandaki da gudu, ji take tamkar ta tsige fatar bakinta ta huta da wannan azaba da ba ta taba ji ba.

Hajiya ta fusata da abincin da aka furzo mata ta ce, “Dubi sangartar banza don Allah, yarinya ba kwaba ba tsawatarwa da can tunda ta fara cin abincin ba ta ji yajin ba sai yanzu da ta koshi?”

Ba wanda ya tanka mata sai Anti da ta mike ta bi bayan Intisar din ta, Faisal ya janyo plate din Saratu ya dibi kadan ya kai bakin shi, ba shiri shi ma ya furzar ya ce,

‘Wuh! Allah masifar yaji, ci ka ji Daddy?”

Aminu ya harare shi ya ce,

‘Wa ya sa ta ta zuba? Ina kallonta tana ta zazzagawa kamar ‘yar kauyen da bata san mene ne a ciki ba”

Daddy ya dago a hankali ya dube shi na dan lokaci, kamar mai son fahimtar wani abu a tare da yaron, bai ga komai ba illa tarin kuruciya fal a cikin kan shi. A yau kam ya nuna masa bacin ran shi a fili ya ce,

“Ko kadan bana jin dadin yadda ka ke mu’amala da kanwar ka Aminu, kai ba ka ganin Saratu karamar yarinya ce ne? Kai da ka ke babba da ya dace a ce ka hada kan dukkan kannen ka ka rungume su, sai ya zamo kai ne ka ke nuna bambanci? To su kuma kannnen na ka su koyi me kenan daga gare ka?

Jiya ina ji fa kana tsula mata carbi wai ba ta iya karatu ba, to ba haka ake koyar da karatu da azaba ba, idan har ba za ka koya mata yadda ka ke koya wa sauran ba, ka bari na gode.

Amma daga yau sai yau, kada ka sake taba lafiyar Saratu da sunan duka, don uwar ta na maku kawaici ba zan zuba maku ido ku illa ta yarinya ba, once and for all, ka kiyayi Saratu Ameenu!.”

Hajiya ta aje cokalin da yake hannunta ta dubi Daddy a yatsine kamar za ta yi magana, ko me ta tuna? Oho! Ta maida bakin ta ta tsuke, can kuma ta ja wani dogon tsaki tsuuu! Ta ce,

‘‘Tashi mu bar wurin nan Aminu, maigida ya zo mai tabarma a bakin kofa ai sai ya nade kayarsa, mu nan ba wurin zaman mu ba ne na masu uban ne.”

Ta fada cikin yi wa Daddyn gatse, amma shi din bai tashin ba, kwantar da kai ya yi ya yi ta bai wa Daddyn hakuri har da kwallah. Sai da ya tabbatar masa ya yafe masa tukunna.

Wannan na daga cikin halayyar yaron da har kullum take sayo masa mafificiyar kauna a zuciyar mahaifin shi. Zai yi komai, zai bata wa kowa, amma ban da wadannan mutanen guda biyu; Daddy da Hajiya.

Mutum ne da ya iya takun rayuwar shi, da wuya ka fahimci abinda yake ciki. Yana da taka-tsantsan cikin dukkan al’amuran shi mawuya ci ne ka ce yau ga ta inda ya kuskuro ka, sai dai da yake an ce wai zuciyar mutum birnin sa.

Haka ne Al’ameen mugun mutum ne na karshe ga wanda ya tsana, sai dai muguntar sa tafi yawa a kan Intisar.

In kin san wata kalma wai ita ‘yan-ubanci, to Al’ameen Bello ne shugabanta. Yana son uwarsa, yana son kannensa, baya son kowa ya rabe su saboda matsananciyar kaunar da yake wa Daddyn shi. Yana da ra’ayin rikau na Malam Bature kan single nuclear family life, bai ga dalilin da Daddy zai bata masu family ba ta hanyar kawo wasu can.

A da, kafin Dady ya auri Saratu yana matukar shiri da ita, haka ko san da take karatu a Edeter musamman ya kai mata ziyara har sau biyu a matsayin ta na kanwar ubansa, yana jin dadin mu’amala da ita, kasancewarta mace mai ilimi irin yadda yake so, kuma wadda ta rage masu cikin dangin ubansu kaf, sai Baffa da Goggo.

Amma tunda ta zabi zaman kishi da mahaifiyar shi shi ma ya ce to mu buga, in ya so mai sa’a ya kwaci Daddyn.

To haka Aminu ke ta azabtar da baby Intisar kullu nau’in azabar yau daban ta gobe daban. Har sai da ya zamanto Baby in ta hango Aminu a bakin gate a guje take komawa dakin Mamarta tana haki kamar ranta zai fito, ko kuma wadda ta ga dodo, sai dai ta bude baki ta ce ga abin da yake mata ina! Tana masifar tsoron sa, tun Anti Saratu ba ta ganewa har ta fahimci baby na gigicewa in ta ga Aminu, haka ko muryar shi ta ji daga waje ta nutsu kenan, tun kuma ranar da ya hana ta shan majina ba ta kara ba, majinar ma kanta tsoron ta take ji, bini-bini tana yawo da tissue tana cewa da ‘yan uwan su goge mata, kada Ya Aminu ya yanke mata hanci ko ya ba ta fitsarin Bombino.

Shi ko in ya ga Anti Saratu a wuri ya soma yi mata wakar come on beautiful baby kenan ko taso tambayar baby sai ta fasa, ta kan dauka don yana matsanta mata wurin karatu ne.

Ranar wata Asabar ba aiki daga Aunty har Daddy suna gida ba su je ko’ina ba. Hajiya ce dai ta tafi Cape-Town can South Africa harkar gwala-gwalan su, kafin ta tafi sun shirya a nakasta Intisar yadda mutane za su daina sha’awar ta ta hanyar gurgunta wadannan kafafun nata ta zama gurguwa ta daina wannan tafiyar tata kamar ta mage, ita kuma za ta taho mai da mota End of Discussion (da ‘ya’yan gata ke yayi a lokacin) da ta yi masa alkawari. Aminu yana matukar tsoron Babansu yana kuma masifar son Hajiyar shi ta yadda duk abin da ta nuna ba ta so shi ma daga ranar ya tsane shi kenan.

Rashin imanin da yake ganawa diyar Aunty Saratu ba wai halin shi ba ne domin dai shi mutum ne mai son kananan yara da son wasa da su shi yasa yake son Khalil.

Komai yake yi yana yi ne don farin cikin Hajiya, don Hajiyar shi ta ji dadi, domin ta ce da shi ba irin wulakanci da tozarcin da Daddy bai mata ba a kan Intisar lokacin yana makarantar kwana shi yasa shi ma ya tsane ta, don komai yake so ita ma Hajiyar naso, komai yake so ta na yi masa, ko damuwa ya shiga Hajiya ba ta kuma samun kwanciyar hankali ba kuma za ta huta ba sai ta ga ta gusar masa da wannan damuwar.

Abu daya ne har zuwa yanzun ta ki mara masa baya wato ra’ayin shi na son tafiya karatu Miami (Miami gari ne na ‘yan hutu cikin U.S.A) don tana ganin duk cikin ‘ya’yanta ya fi sonta, ya fi su kaunar ta, ya fi kaunar abin da take so. Idan ya tafi wa zai taya ta kiyayyar su Saratu?

Tsaye yake jikin Volvos 6 din Hajiyar shi, yana ta faman murza ‘yar karamar kwamfutar aljihu pocket computer, sanye yake cikin Kaftani na wata jikakkiyar shadda-rini ‘yar Mali. Sai ga Intisar da Khalil tana rungume da ribdediyar teddin ta, daga inda yake tsaye yana iya jiyo muryar Khalil na cewa, “Baby ki je ki kwantar da ita a karkashin mota zan je in dauko mata filon ta.”

Ya juya ya koma cikin gida yayin da ita kuma ta nufi karkashin motar da Al’ameen ke tsaye ba tare da ta lura da shi ba, domin ya ba su baya ne. Sojojin da ke gadi a harabar gidan ba wanda ya ba su hankalin shi kasancewar sun riga sun saba wasansu a wurin kullum ta Allah.

Ta sunkuya za ta shimfide teddin kenan, sai ya sa kafa iya karfin shi ya yi (bull) da ita, ta hantsila ta wulwula har sau uku, kafin idanunta da goshinta su hadu da wani karfen pipe ta gigice ta dimauce ta saki wata irin razananniyar kara da amsa kuwwar ta ya ratsa illahirin gidan, gaba daya ma’aikatan gidan har shi Aminun suka yi kanta a guje.

Jikinsa ya yi sanyi da ganin jini na gudu daga idanun yarinyar hade da wani irin ruwa. Ya saki Computer da ke hanun shi ya dauke ta a gigice yana.

‘Emma bude mini mota, wayyo Allah na shiga uku! Na yi kisan kai!”

Abin da yake ta nanatawa kenan, har suka isa asibiti. Mummunan labarin ya riski Aunty Saratu ne tana cin abinci, ta saki cokalin ta ce, ‘Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un….” Don Khalil da ke bayar da labarin cewa ya yi idanun Baby sun tsiyaye.

Shi kan shi Daddy jikin shi babu inda baya rawa, da kyar ya kulle Aunty Saratu yabi bayan su saboda yadda ta fita daga hayyacinta cewa kawai take, ‘Yanzu baby shi kenan idon ki ya tsiyaye?’

Likitocin ido kwararru uku ne a kan Intisar suna kokarin ceton ‘eye-bulls’ dinta (kwayar idonta). Sai bayan awanni uku babban likitan ya nemi ganin Daddyn a ofis din shi, ya fara da kwantar masa da hankali, don ganin yadda duk ya fidda rai ya kuma ba shi shawarar a kai baby asibitin kwararrun ido na Kaduna, in an yi sa’a a ceci lafiyar idonta, amma he’s sorry to say, ko da Saratu ta warke ba za ta ci gaba da gani da naked-eyes dinta ba.

Inda duk hankalin Daddy yake in ya yi dubu to ya tashi, bai tausayin Baby kamar Aunty Saratu, da ta ci duk wani buri da fatan ta a kan Inteesar! Amman a yau a ce ta makance! Duk kwazon ta, duk himmar ta da ke sawa ana yi mata hangen zama wani abu a gaba. Bai san san da wasu zafafan hawaye suka shiga yi masa lugulgude a fuska ba tamkar ba Brigadier na soja ba.

Yasa habar babbar rigar a ya share kafin ya sa hannu a tura su Kadunan.

A jirgin (bell-view) da suke ciki, Aminu Bello, tafukansa yasa ya rufe kyakkyawar fuskarsa. Ya sha jin Malamin su na Islamiyya na cewa, ‘Ku roki Allah ya kare ku daga nadama mara amfani.”

Bai taba sanin mene ne nadama mara amfani ba sai yau. Tausayin mahaifin su kadai ya ishe shi na wahalar da ya jawo masa. Ya san Daddyn na son shi, amma a yau yana shakkar, idan son da Daddy ke wa Inteesar diyar Aunty Amarya bai dame wanda Daddyn ke masa ba.

A asibitin Kadunar ma sun ce ne idan Daddyn na da hali to ya gaggauta fitar da diyar sa asibitin kwararrun ido da ke Jiddah, nan suka bar Intisar karkashin matsananciyar kulawar likitoci su suka tafi neman visa. Masu abu da abin su nan da nan suka samu. Karfe tara na dare an shigar da Baby tiyatar ido.

<< Siradin Rayuwa 12Siradin Rayuwa 14 >>

6 thoughts on “Siradin Rayuwa 13”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.