Skip to content
Part 23 of 45 in the Series Siradin Rayuwa by Sumayyah Abdulkadir (Takori)

Gabadaya falon ya dauki tsit inka dauke karar bugun dakika na agogon bango mai nuna karfe sha biyu na rana dai-dai sanda Daddy ya kawo karshen labarinsa.

Najib ne ya fara magana yana murmuhi ya ce,

“Wannnan shi ake kira ‘narrow – escape (tsallake rijiya da baya)”

Kowa yayi murmushi mai fidda sauti.

A nan ne aka shiga baiwa Daddy labarin halin kuncin da gidan ya shiga a bayan shi, yadda karatun su ya dinga watangariya da yadda malamai suka rinka cin kudin su na karya dana gaskiya, Hajiya ta ce,

“Wata rana wani mutum yazo mini ya sha farin rawani, ga doguwar tazbaha yana ja yace in bashi dubu arba’in in har ba’a sako ka cikin wannan satin ba zai maido mun kudina. Ni kuma jin haka jiki na rawa na kirgo kudi na bashi ya tafi. Yana fita Khalil ya shigo yace wallahi karen mota ne ya san shi a tasha har yau dinnan kuma ban kara jin duriyar sa ba” Gabadaya aka sa dariya har Daddyn ya ce,

“Dana karyar, dana gaskiyar dai duk sun yi, kuma Allah ya amsa, sai mu roke sa ya kare gaba.”

Faisal ya iso gidan su yamma lis, sanye yake da farar shadda ‘getzner’ babbar data dauki dinkin Mohammed Abacha, kafafunshi sanye cikin budadden takalmi kirar Italy, bakin agogon ‘swiss’ ya lafe cikin lafiyayyar farar fatar hannun shi wadda bakin lallausar gashi ya baibaye. Kamar yadda yake dogo ba can ba, shi kansa ya san shi dan gayu ne na hakika mai ginannen jiki irin na Daddy Makarfi.

Kallo daya zaka yiwa dukkan samarin nan na Brigadier ka amincewa ranka lallai abubuwan nan guda biyu masu tafiya a tare da juna sun masu mayafi wato naira da tsantsar boko.

To haka Faisal Allah ya halicce shi da wasu ilhamomi daya zarta na ‘yan’uwan shi nesa ba kusa ba.

Yana da kakkarfan taku mai jan hankali da idanuwa tamkar maganadisu, da ke fizgar hankula da dama garesa ba tare da shi din ya sani bama musamman ga ‘ya’ya mata. Ta ko’ina, Faisal Bello bai da makusa, shi kansa ya san hakan.

Ma’abocin wani ni’imtaccen turare wai shi 5,000 Doller, inda duk yayi idan mutane sunyi dubu zaka fidda shi da wannan lallausar kamshin koda ya wuni ne da barin wurin kuwa. Don haka kamshin sa kadai daya baibaye ilahirin gidan ya tabbatarwa da mutanen gidan cewa ya zo, musamman Intisar din shi da Hajiyar shi.

Ya sallame dakin Baban su cikin sanyin murya, kamar yana tababar ko karya aka gaya masa, tamkar wani yaro karami, sai ya fada jikin Daddyn hawayen farin ciki na ziraro mishi Daddyn yasa yatsun shi biyu yana share mishi ya ce,

“Komi ya wuce Faisal, Allah shine abin godiya, mu rokesa ya kare gaba.” Abinda yace da shi kenan.

“Daddy wai ya akayi ne?” Ya tambaya a dokance, sai ya sake mayar mai da labarin kamar yadda ya baiwa sauran ‘yan uwan shi,

Faisal kuka yayi sosai na tausayawa mahiafinsa ya ce,

“Na fadiwa Ya Aminu, Daddy ba zai taba aikata abinda a ke zargin shi da shi ba.” Amma a zuciyar shi. Sun dade suna tattaunawa akan al’amarin kamin ya tashi ya nufi sassan Hajiya. Allah-Allah yake ya sallami Hajiyar ya je ga Saratun shi, kanwar da baya da kamar ta duk fadin duniya, ya ji tayo waya ta kuma aje ba tare da ta fadi sakon da tai niyya ba wanda ya tabbata fitowar Daddyn su ne, to akan me ta aje? Shine abinda ke damunsa yake kuma matukar son ya ji.

Ita kuma Hajiyar da ta fahinci a cusgune yake hirar da ita, ji yake kaman yayi fiffike ya fice sai tayi ta jan hirar da tsawo, tace kuma bai fita dakin sai ya cinye tarin abinciccikan data sa aka shirya dominsa tunda ta san inda za’ayi mai barbade-barbade zai je yaci sai yayi murmushi.

Yana ci yana shan zagi da alkaba’I iri-iri daga bakinta wanda in har da sabo ya saba da jin ire-iren su, har ya zamanto basa damunsa a yanzun ta ce,

“Na taba ganin maye irin ka Faisal? Shin me Saratu da Saratu ke baka ne da kake tarewa a gindin su?”

Yai murmushi sosai da ya motsa dukkannin (beauty-point) din shi hagu da dama, yana taunar abincin yana cigaba da murmushin ya ce,

“Hajiya, maita kuma? To a ina na tsotso?” Ta ce “a nonon Ubanka, can nonon su Saratu, in banda maita kai kenan baka da burin komi daya wuce Saratu da Saratu kai!

Allah ka raba ni da irin maita, wannan alaka Allah Ka wargaza ta, shin uwar me kake daukowa ne jikin su Saratu?”

Ya ce cikin muryar nutsuwa da rashin jin dadin kalamunta,

“Hajiyar mu, kina bani mamaki. Bana dauko komi sai dai kar ki manta jinin mu ke gauraye da na juna, kenan ko ban bi su ba, wannan jinin na bibiyar jinin jikina?”

Ta ce, “A gidan uban wa jinin naku ya gauraya?” Kome ta tuna?

Tayi saurin fizgo dankwalin ta ta toshe bakin ta da karfi, yayinda shi din ya bita da idanun mamaki, a ransa yana cewa ko sai yaushe Hajiya zata girma? Ko sai yaushe bakin Hajiya zai iya magana? Ita kam babba  ce, amma tunanin ta da maganganun ta na kananan yara ne, abin nufi, babu kawaici da jan girma a cikin su.

Ta yi fatali da tebirin abincin komi ya kwankwatse, ya wanke masa jiki, ya rine farar sassalkar shaddar dake jikin shi ta soma nuna shi da yatsar ta sabbab, tana ja da baya tace a kaurare,

“Wata rana zaka yi nadamar cewa da kake kun hada jini da Saratu!”

Ya so yace da ita “irin wadda Aminun ki yayi akan ta ya nisanceki shekaru goma sha biyar?”

Sai kuma ya tuna wannan uwar sa ce, da ta dauke shi cikin mahaifar ta tsayin watanni tara cif, ta haifeshi bayan nakuda da wahalhalun da harshe ba zai iya bayyanawa ba, ta raine shi shekaru dai-dai har ashirin da bakwai bata taba gazawa akan hidimomin shi ba.

Kenan ko ba komi tana da wannan matsayin, amma da ba ita bace, a yau da ya gaya mata bazai taba nadamar hada jini da ko mai gugar takalmin Saratu ba balle ita, kuma har gobe zai cigaba da kaunar ta, tun kaunar nan da yake mata a sanda take a tsumman goyonta; ba mayya ba, ko ‘yar mafiya ce…

Tayi mamakin yadda har ya kwana ya wuni cikin gidan bai nemeta ba, duk da tasan ba zai wuce ya gamu da fushin Hajiyar su bane a kanta, kamar yadda ta saba a duk zuwansa garin, to itama dama haushin sa take ji don haka bata ko nemeshi ba.

Washegari da safe tana dakin da su Goggo ke sauka tana kintsawa Goggon kaya don a ranar ne zasu koma Makarfi, ta dibeta cike da tsantsar kulawa da kauna irin ta kowacce kaka ga jikanyar ta, tace cikin zolaya

“Saratu Baba ya dawo, mu da ganin ki kuma sai Baba ta gani” tayi ‘yar sassanyar dariyar ta ta ce,

“Kai Goggo, yanzu sabida Allah  sai ba Daddy nake zuwa Makarfi?

Kin san ma yanzu ba zai yi wata bai aiko mu kawo maku kayan amfani ba musamman yanzun da ya san kun wahala kwatankwacin mu?” Goggo tace “hakane, wai ke sai yaushe zaki kawo min maigidanne?”

Ta tintsire da dariya tace,

“Kin san Alllah Goggo bani da saurayi.”

Ta ce, “Haba dai, bari fadar haka, maza bari, babu ko dadin ji. Duk kyawun nan naki kaman aljana, ki ce baki da masinsini? Ki ce zama bai samemu ba, sai mu fara yo miki rubutun farin jini, watakila duk farin nan naki jinin ki bakikkirin yake a idanun maza.”

Ta sake sakin dariya  har da dan guntun hawaye, dai-dai lokacin da Faisal ya yane labulen dakin ya shigo  tare da sallama.

Bai zauna ba sai da ya dauki (remote) ya  kunna A/C yana hararar Intissar ya ce,

“Shin kema ‘yar kauyen ce ne Goggo da ba zaki kunna A/C ba duk uban zafin nan da ake?” Ya samu kujerar zaman mutum daya cikin (cushion) farare sol da suka mamaye dakin, ya zauna ya harde yana karkada ‘yan mukullayen shi dake like jikin wani ‘key-holder’ mai tsinannen kyau, ta tura baki gaba yadda take mai in ya bata haushi, ta mike zata fice sai ya dan zamo daga cikin kujera, ya mika dogayen kafafun shi suka tadeta ta fadi kif, bisa kafet da baka, ya ce,

“Good, gobe ma ki kara zumburan baki, Allah Goggo Intisar ta raina ni.” Goggo ta ce,

“Wa ya janyo? Duk ba ku kuka so ba.”

“Da muka yi me?”

“Kun fini sani ai don Allah shashashun wofi.”

Intisar ta mike tana karkade kayan jikinta tana yatsuna kamar wadda aka tura cikin yumbu, ya ce

“To Goggo bakya yi mata fadan turan bakin da ta ke yi?”

A hasale kamar ta rufe shi da duka ta dago daga gurzar goron ta data keyi tace

“Bana yi din, nace baku kuka so ba? Tana ganin ku kai daya har marin ku bazata yi ba, shin in tambayeka, sai yaushe kuka shirya kawar da Saratu ne?”

Faisal yayi wani iri da fuska alamun bai gane hausar ba.

“Ban gane mu kawar da ita ba Goggo don Allah yi min bayani, mu kawar da ita sai kace wata kaya? Ko mu kasheta kike nufi?”

Intisar bata san lokacin da ta saki murmushi ba, wasu al’amuran na Faisal kan bata dariya, yafi kama da dan fari fiye da da na biyu, Goggo ta kara gyara bayanin ta da cewa,

“Ina nufin sai yaushe ne zaku yi mata aure? Ga yarinya kafada daya da uwar ta, amman har yanzu kun taru kuna ta wani lailayarta Baby-Baby (tana yi tana kyabe baki irin yadda suke yi din) nan ko uwar mata ce. Wai naga kai ne na hannun daman ta shiyasa na tambayeka don ita uwar har da yi mun fuskar shanu don nace a yi mata aure. Kuna nufin saka muku ido za’ai kuyi ta ajiye yarinyar sai ta zama kwantan ‘yammata tukunna?”

Intisar daga inda take tsaye ta dinga dariya ta ce, “Goggo menene kuma kwantan ‘yammata, ai mace bata kwantai komi girmanta, zata samu kato dai-dai girmanta” Faisal sai ya juyar da kai, bai san san da yaja tsaki ba, yayi kicin-kicin da fuska, ya ce,

“Wai ke Goggo baki da zance sai aure-aure, to har nawa Babyn take? Ko sakandire bata gama ba fa, ita wannan kifin rijiyar ma tana fita ne balle wani mummunan ya ganta yace yana son ta?”

Ta harare shi a ranta tace bari in tura ma haushi nima, kaima ba kana da budurwa ba? Ta ce a ladabce.

“Wa ya ce ma bani da saurayi Ya Faisal?” Faisal ya fiddo ido cikin barazana ya ce,

“Eh, Baby kin san abinda kike fada kuwa?” Ya kara bude baki kaman zai kara cewa wani abu, kafin ya bara cikin kada ido ta sake cewa,

“Allah Goggo ina da saurayi, amma balarabe ne mutumin Turkey, shine malamin chemistry din mu a Riyadh sunan shi Dr Alhassan, ya taba zuwa nan ma kuma ki tambayi Mama.” Ta kara duban Goggo da dukkan idanu, tana murmushin da ke kara mata kyau da kwarjini, lokaci daya tana satar kallon Ya Faisal da wutsiyar abnormal (marassa lafiyan) idanunta don ganin irin sukar da kalamin ta ke yi.

Ba shakka ta ga sauyawar fuska da idanuwan shi bakidaya irin yadda bata taba gani ba, taci gaba da cewa,

“Baki gan shi ba Goggo, dogo kyakkyawa jawur da shi, idanun nan kamar na Ya Najib, hancinsa zirit irin na Ya Faisal, muryar shi.”

Haba! Faisal ya gama zuwa wuya tun kamin ta karasa, tun can fa sauraron ta yake ‘absent-mindedly’ da tunanin ba Saratu-Intissar ke wannan maganan ba, yarinyar da har kullun yake gani ‘as a kid’ bai san yaushe bakin ta da idanun ta suka bude har haka ba, ita ce har take yabon kyawun namiji, abin mamakin ma har a gaban sa!

Bai san sanda ya cafko hannayen ta duka biyu ba ya yana kallon ta cikin ido da idanun shi da suka rine ‘completely’ har wani (blue-blue) suka koma suka rine da abin da bata taba gani ba, ya durkusar da ita gaban Goggon, shima binta yai suka durkushe yana huci kaman yunwataccen zaki ya ce,

“Maimaita abunda kika fadi yanzun Intisar, Goggon bata ji sosai ba” ta tsorata, ta razana kwarai da yanayin sa haka tsatstsauran rikon da yayi mata ya gigitata, sai tasa kuka. Goggo ta yi salati ta ce,

“Sakar ta, sakar mata hannu, sake ta nace, idan ka karyata fa?”

Da alama bai jin ma abinda Goggon ke fadi domin gabadaya baya a hayyacin sa yace

“In an karya ta sai me Goggo? Yanzu wannan tsakuwar yarinyar ce take yabon kyawun maza, ina ta koyo wannan fisarar?” Ta ce,

“Na fada din, Goggo shekaran jiya waya na yi mishi, in gaya mishi Daddy ya dawo, wata Inyamura ce ta dauka  tace min wai…” ya kara tsananta matsar da yayi wa hannun ta tare da murje yatsun kafar ta da karfi da nashi yatsun, ta saki kara don zafi amma bakin ta bai mutu ba, hakannan bata yi shiru ba da gaya wa Goggon yadda sukai da yarinyar shi a waya. Ya ce,

“Nace da ke na santa?”

“Ya santa mana Goggo, cewa tayi fa wai ya shiga wanka, idan bai san ta ba, ya za ai har ta san inda yake wanka? Wa ya sani ma,…”

Faisal ya soma daldalle mata baki da yatsun shi da karfi nan da nan dan bakin ya haye, dai-dai lokacin da Najib ya shigo, koda yake ya dade yana kallon su yana son tirsasawa zuciyar shi rashin amincewa da abinda kwakwalwar shi ke son fahimtar da shi, ya shiga tsakani  ya janye kanwarsa ya ce,

“Wonderful! Abin mamaki, abinda cikin gidan nan ba wanda ya taba gani, abinda ko a tunani ba’a taba kuskuren tunanowa ba, wai Faisal da Intisar yau aka gani a rana?”

Su kan su sun ji kunya ba kadan ba, don haka ba wanda ya amsa mishi kowanne sai huci yake kaman ya cinye dan uwan sa, Goggo Jummai ta kyabe baki ta sunto wani goron a habar zanin ta, ta kwashe wanda ta gurza a magogi da farko ta hambuda a baki tana mamulawa ta ce,

“Ai kai kadan ka gani, baka ji ba har tonon asiri sukewa junan su,” Faisal yayi tsaki ya fice har zuwa lokacin idanuwan nan suna rine a (blue) kamar na wanda ya kama matar shi da kwarto, ita kuwa ta cigaba da gaya masu yadda suka yi da yarinyar shi a waya bata ko sanya comma, (wakafi) balle fullstop (aya) zuba kawai take kaman ‘ya’yan kanya  Najib ya daga mata hannu “wait, excuse me please Inteesar, for Allah ’s sake, ina ruwan ki da budurwar Faisal, kin isa ki hana shi yin budurwa ne?”

Ya zazzaro mata manyan idanun shi, ta sunkuyar da kai cike da matsananciyar kunya kafin ta daure ta ce,

“To Ya Najib shima ina ruwan sa don nayi maganar saurayina sabida Allah sai ya murmurde ni yana neman balballa ni?”

Najib yayi murmushi ya juyar da kai, kwakwalwar shi kaman ta tarwatse, yanzu kam ya tabbatarwa kansa abinda tun shigowarsa zuciyar shi ke gaya mishi yana karyatata da gangan, amma sai ya basar tunda mai ilmi ne, ya juya ga Goggo da son wanke mata nata zargin ya ce,

“Goggo da ganin Saratu kin san anyi irin kannen mijin nan ne, masu kishin son da Yayun su ke nunawa matansu, masu so a raba musu kauna da matan Yayyunsu ‘equal’ (dai-dai wa daida) wanda kuma wannan ba zai yiwu ba. Mata fa matsayin ta a zuciyar mijin ta ya zarce yadda duk kike tsammani, kasancewar ta wani bangare na gangar jikin sa, zuciyar sa da hutun sa, zata bashi abinda ke kanwa bazaki taba bashi ba, zata kula da shi da rayuwar sa ta hanyar da ke kanwa baza ki taba yi ba.

Hakannan daga jikin ta ne zai sami ‘ya’yan da zai yi alfahari da cewa nashi ne,  mallakin shine, ta yaya  matsayin ku zai zo daya? Kazalika shima Faisal yana tsananin kishin ki so wani fiye da wannan ingantaccen son zumuncin da kukewa juna, yaya za kuyi rayuwa da haka?

Don haka dole ya ji zafi da farko, amma daga karshe dolen shi ya dangana ya danka ragamar rayuwar ki ga abokin rayuwar ki na har abada bayan shi, don kuwa shi ba auren ki zai yi ba ko a garin gaba-gaba muke bare gari na Addinin muslinci, so kusa ranku a inuwa sassanya, ku yayyafawa zuciyoyin ku ruwan sanyi, dole kowannen ku zai sami abokin rayuwa na daban. Ba rarrashin ki nake ba, gaskiya kawai nake gaya miki. Do u get me (kin fahimce ni?)”

Sai ta mike tana kunkuni na alamun rashin yarda, sai dai wannan Yaya Najib ne bai yuwuwa ya fadi ta fadi, yanada wata kima mai yawa a idonta, amma da ba shi ba ne da tace da shi;

Idan har auren kowannen su na nufin kawo sauye-sauye da canje-canje ne cikin rayuwar so da kauna, shakuwa da ingantaccen son zumuncin da suke wa juna ne ita da Faisal, to ita ta yafe nata! Zata zauna haka tare da Ya Faisal a gida daya, a gaban Daddy Makarfi, matsayin yayanta kuma nata abokin rayuwar har abada!! Ita dai bata son zancen budurwar Faisal ko kadan, za kuma su ci gaba da fada har da ba hammata iska idan ta sake jin zancenta.

<< Siradin Rayuwa 22Siradin Rayuwa 24 >>

3 thoughts on “Siradin Rayuwa 23”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×