Skip to content
Part 34 of 45 in the Series Siradin Rayuwa by Sumayyah Abdulkadir (Takori)

A lokacin ne hankalin ta ya kai ga Hidayah da Hunainah wadanda ke hada komatsansu cikin ‘trollies’ din su basa ko dubarta. Hankalinta ya tashi, ta ji babu dadi ta ce,

“Ku kuma ina za ku?” 

In jakunkunan su sun amsa, to suma sun tsinka mata. Ta ja jiki ta sakko daga gadon fuskarta jike da hawaye taje ga Hidayah da Hunainah, ta kama kowacce da hannu daya ta rungume a jikinta ta cigaba da kuka mai tsuma rai su kansu basu san sanda hawaye ya cika idon su ba. Tace cikin kuka

“Don Allah ‘yan kanne na ba sai jibi zaku tafi ba?” Hidayah ta tureta tana share hawayen ta da bayan hannu.

“Ai zaman mu baya da amfani, tunda ke ba kya jin shawarar kowa kuma ba’ajin damuwarki. Yaya zaki sa Ya Aminu kuka akan idon matar sa?

Mu bazamu iya jurar ganin wannan wulakancin ba, so hauka ne? Kuma idan yanzu ba kya sonsa ba zaki aure shi ba ai ba haka ake abun da wulakanci ba.”

Ta ce, “Hidayah, Kome zan gaya miki a yanzu bazaki gane ba…. Baki san Babar Al’ameen ba ne….” Ta katseta,

“Ba bu abinda na tambayeki, ban kuma ce ki gaya mun ba, ban santa ba ba kuma na so in santa, to amma ta yaya zaki hukunta shi da laifin uwar sa wanda ba nashi ba ai har ga Allah kin dau hakkin shi…” Ta ce,

“Hidayah, ba wannan ne kadai ba….” sai kuma ta kara sa kuka, to tace mata me? 

Bata da abinda zata ce da ita ta fahimta game da Faisal Bello Makarfi, daga Anti sai Daddy ne zasu fahimce ta akan hukuncinta amma su Hidayah baki ne basu san komi ba.

Dai-dai lokacin da Anti ta shigo tana rike da Zarah, tun kan ta zauna Zarah ke mikawa mutuniyar ta Hunainah hannu tana zillo daga jikin Antin, ta amsheta yayinda Antin ta samu gefen gado ta zauna ta dibesu dukkansu tace “duk mi ya janyo wannan?”

Hunainah ta ce,

“Tafiya zamu yi Anti” ta ce, “Ina?”

Su duka suka hada baki suka ce “Can inda aka sauki su Maman mu.” Ta ce,

“Akan me?”  Duk suka yi shiru ta ce,

“Nasan sai jibi zaku tafi Korea, mun yi da Hajiya sai zasu tafi zasu biyo ku tafi, to a kan me yanzu zaku ce zaku tafi, ku bar ‘yar uwarku cikin irin wannan halin da ta jefa kanta don bana ce wani ya jefa ta ba.”

Hunainah ta ce, “To Aunty yaya zamuji dadin zama alhalin tana kuntatawa kanta? A ce mutum bashi da aiki sai kuka kamar wanda ya rasa iyaye da dangi, mu bamu da amfani a gareta kenan. Muna iya kokarin mu don kawo ma Saratu canjin rayuwa amma bata gani. Damuwar ta bamu isa mu ji ba, bamu san hakikanin kuma me ke damun ta ba. Ni ban ga meye abin bakin ciki duk a cikin maganar nan ba, tace ta fasa auren Yaya Al’ameen waye yace dole ta aure shi?

Sai kuma tasa mutane gaba tayi ta kuka in ta canja shawarane ba sai taje ta sameshi ta bashi hakuri ba?”

Ta share hawayenta da yatsunta biyu ta ja ‘tissue’ ta fyace hanci ba tare da ta lura da hararar da Intisar din ta wurgo mata ba, dai-dai lokacin da Najib ya yi sallama ya shigo.

Da ganin yanayin da suke ciki duk ya bi ya rikice, ya zube a gabanta bai ma kula da Anti dake zaune ba ya ce,

“Hidayah, tafiya, why?” Sai ta sake barkewa da kuka.

Ya fiddo ‘handkerchief’ a aljihun don share mata hawayen da ke zuba ya na tambayar su me ya faru? Aunty ta ce,

“Najib ya zan yi in san damuwan Saratu ne don Allah?”

Ya kai dubanshi ga Intisar, cikin kwanaki kalilan rak wai har tafi can baya sanda take cin bakar wuya lalacewa, yayi murmushi ya ce,

“Aunty, wait a minute” (jira ni minti daya).”

Ya juya ya fita da sassarfarshi, ya fi rabin awa kamin ya dawo Faisal na biye da shi. Idanun shi jazur da gani shi din ma yana cikin tsananin tashin hankali kwatankwacin koma fiye da na Intisar din, don dai shi namiji ne, sannan akwai juriya.

Kallon kyama kawai yake bin kowa da shi da tsanar duk wani al’amari dake cikin duniyar. Najib ya ce,

“Zauna” ya ce,

“Bana bukata.”

Ya tsaya kikam a bakin kofa ya harde hannuwanshi bisa kirji, idanunshi akan Inteesar tamkar mijin da ya kama matarshi da kwarto.

Najib ya zauna jikin Hidayarshi, cikin kwanciyar hankali ya dibi Anti cikin basira ya ce,

“Dibe su Anti.” 

A mamakance Anti ta dubi Faisal, kana ta maida dubanta ga Intisar ya ce,

“Anti me kika fuskanta?” Ta ce,

“Dukkanin su, suna cikin yanayi daya.” Ya kuma cewa,

“Anti ba ki tuno can baya?” Cikin rashin fahimta ta ce,

“Ban gane ba”.

Ya bugi Jakar Hidayah da kafarsa ya ce,

“To cut the long story short! Na fahimci daga Faisal har Intisar suna son junansu ne tunda dadewa, duk wani da ya san kuruciyarsu zai gane hakan sai dai in baya da lura.

Na dade da sanin Intisar kishin Faisal take har zazzabi sai da nayi na kwana bakwai don mamaki. Intisar na cikin damuwar yaya zata bar Faisal akan Al’ameen? Ko da taso Al’ameen ta so shi ne a rashin Faisal, ta so shi ne domin ya mallaki wasu ‘qualities’ da ‘appearances’ na Faisal kaman murya, taku, da sauran su, yayin da Faisal ke jin haushin jinkirin shi na kin fara furtawa cewa…”

A fusace Faisal ya katse shi,

“Dakata don Allah Malam abin naka ya koma sharri, for God’s sake, yaushe na taba ce ma ina son Intessar, irin son da kake nufi? Yaushe ka zama predictor? Zuciyar wa ka shi ga a tsakanin mu har ka gano hakan?”

Najib ya dubeshi a lalace ya ce,

“To canzawa juna da kuka yi na mene ne?”

Kamin ya rufe bakinsa kawai sai suka ji Faisal ya ce,

“Hidayah zaki iya aurena?”

Hidayah ta dago a razane, ta girgiza kai da karfi tace “A’ah, wallahi ba ruwana, ni ina da wanda nake so kada a kara sani a ciki.”

Yadda ta fada da sauri da gigita saida ta ba Najib matsiyaciyar dariya, ya kuma ji nadamar abinda ya jangwalo ga abin na shirin juyewa kansa, shi ko Faisal wani dogon tsaki tsuuu… yaja ya juya ya fita har yana tuntube da dokin kofa.

Hunainah ta sunkuyar da kai cikin alhinin wannan cukurkudadden al’amari. Anti ta dubi Najib ta mike tsaye ta ce,

“Ni dai ina ganin Saratu ki sassautama ranki hakannan, Allah ya zaba abinda yafi alheri gaba daya.” In banda Najib ba wanda ya ce, “Amin.”

Ta fita ta ja masu kofa yayin da Najib ya cigaba dayi mata nasiha mai sanyaya rai. Ya ce,

“In da nine ke, Saratu ba kuma wani abu da zai sake sa ni bakin-ciki. Kamar yau ne nake gaya maki cikin wasikata sanda akai mana katanga dake cewa; ni na tabbata wani babban al’amari ne zai faru dake anan gaba, kuma hakika ke din wata ce a cikinmu.

Ga shi a yau kin zamo mabudi kuma sityari mai juya zuciyoyin ‘ya’yan Hajiya, sai inda ki ka garasu. Duba ki ga nima shakikiyarki bata barni ba. Kun zamo mana barin jiki, bango abin jinginar mu mu ji sanyi sai yadda kuka yi da mu. Don a yau Hidayah tace bata so na, ina jin haukacewa zanyi.

To haka daga Ya Aminu har Ya Faisal na tabbata babu mai tsira daga takobin kaunarki, duk da nasan Al’ameen bai san Faisal na sonki ba da duk matsalar ta warware.

Duka wannan matter bai yi kamari yadda kika daukeshi ba, don Allah, ki maida walwalarki ki, ki bude sabon shafin rayuwar farin-ciki da ‘yanci tamkar kowa, ina kara gaya miki ba fa mai yi miki dole kan abinda ba kya so.”

Tasa gefen dankwalinta ta share idon ta tas, eh, gaskiya Najib ya fada, yanzune ya dace ta budewa kanta sabuwar rayuwa mai ‘yanci, tamkar sauran ‘ya’yan gata, ciki kuwa har da neman ‘yancin kanta na rama abinda uwar su ta shekara yi mata!

Wasa farin girki! Tun kowa na tsammanin Intisar wasa take maganar rashin amincewar ta kan aurenta da Al’ameen har suka tabbatar da gaske take. Duk wasu hanyoyin sadarwa tsakanin su ta toshe su, bata daukar wayar shi hakannan in zai wuni cikin gidan bazata bari ya ganta ba, ko dai ta kulle kanta a (toilet) ko ta shige cikin (store) har ya gaji ya tafi haka Anti tace ba ruwan ta, ta tsame hannun ta a al’amarin duk abinda Intisar din ta zabawa rayuwar ta tayi dai-dai.

Al’ameen duk ya sukurkuce ya rasa inda  zai tsoma ransa, bashi gaban Daddy bashi gaban Anti, wurin Hajiya Hadiza kadai yake samun sanyi to ita din ma mijin ta daga baya ya gargadeta ta fita harkar su, tunda  tare ta gan su, bata da wata (power) in dai akan Intisar ne.

Su Hidayah kam bakin-cikin da suke ji kan Yayar su da hukuncin ta har kuka suke tausayin Al’amen kadai ya ishe su, duk ya rame ga wata kasimba ta babu gaira babu dalili ta cika kyakkyawar fuskar sa, duk son gayu da kwalisa irin na Al’ameen Bello, a yanzu babu ya kau. Babu komi gaban sa kamar Intisar din da ke neman kufce masa karfi da yaji yana ji yana gani.

Babban abinda yafi damun sa shine wani kululu ko katutu dake tokare shi a kahon zucci, in ya tuna wai yau Halimar sa ce ke gudun sa sabida Hajiyar sa? Yayi dakacen kasancewar sa Al’ameen dan Hajiya Nafi, ba tun yau ba, a yau ma yana karawa.

Ya kuma tabbata wannan tabon data yaba masu har abada bazai gogu a zuciyar yarinyar ba. Yayi ban hakurin, yayi ban bakin yayi lallashin duk a banza. Yo ina ya ganta ma?

Ta haramta masa ganin kyakkyawar fuskarta da ke sa shi nutsuwa balle dan murmushin ta dake gigita shi, duk sun zama tarihi, na wani zamani can daya shude, zamanin da yake ganin ba zamanin da ya samu gata a cikin sa kamar sa, wato zamanin rayuwar ta a Kitchin.

Ya kan zauna yayi tunani, iya kokarin sa ya rasa mafita cikin al’aamarin sa, karewa ma, bai san me take nufi da shi ba; tana son sa ko ta daina son sa?

Kai bashi kadai ba babu wanda ya san nufin da ke kunshe cikin zuciyarta a gidan. Cikin wannan halin Faisal ya samu Daddy ya gaya masa ‘transfer’ da ya dade yana nema zuwa NNPC na Lagos ya fito. Daddy ya nemi dalilin ‘transfer’ din yace hakanan yake son yanayin garin Legas, ya kuma dade da burin aiki a nan to sai ga yadda al’amarin ya kasance, wato samun aikin da yayi da wurwuri anan Abj.

Daddy yace ya je Allah ya sanya albarka amma yayi kokarin zuwa ya ga lafiyar gida duk karshen sati ko bayan sati bibbiyu. Ba kuma tare da ya kara bi ta kan kowa ba ya yai tafiyar sa, inda ya rungumi aikin sa cike da karfin zuciya.

Yau kam Al’ameen ya kudurce bai barin gidan sai yaga Intisar ko da hakan na nufin ya kwana a gidan ne. Yana ta zarya falon Anti zuwa sassan Daddy har dare bata ba alamarta.  Shi kam duk ya fi daura laifin komi akan Anti don a tsammanin sa da sanin Antin Intisar ke yi masa duk abinda ta ke yi.

Bai sani ba, Antin ta fishi takaicin abinda Intisar ta yanke a kansa, don dai bata son matsanta mata ne. Ta tabbata ita yarinya ce, amma mai sahihin tunani da hangen nesa, tabbas tana da kwakkwarar hujjar ta ta yin hakan. Ita kadai tasan azabar da ta kwankwada a hannun Hajiya, sai dai tana matukar tausayin Al’ameen har hawaye take masa kamar su Hidayah amma a bayan idon sa.

Karfe daya da rabi na sulusin dare ta fito daga maboyar ta, wato cikin store, ta san dai duk nacin sa zuwa yanzun ya hakura ya tafi amma me? Ta zauna gefen gadon ta kenan ya murdo kofar ya shigo.

Ba karamar razana ta yi ba amma sai ta cije, ta yi kamar bata gan shi ba.  Ta cigaba da kokarin gyara wajen da zata kwanta. Hakikah zuciyar ta ta girgiza da ganin muguwar ramar da yayi fiye da sanda ya kwanta ciwo, ga sumar da ta cika kyakkyawar fuskar sa kamar ba Al’ameen din da ta sani ba, mai tsananin kwarjini, gayu da kwalisa, ilhama da cikar zati. Fuskar shi ba annuri sam kamar yadda zuciyar sa ke wani irin zazzafan bugu da sauri da sauri.

Ya dubeta da lumsassasun idanun sa cikin fidda rai da al’amarinta, ya karisa har gaban mudubin ta ya ja (stool) ya zauna yana fuskantar ta, cikin raunanniyar muryar da bata taba ji daga gare shi ba yace

“Inteesar!”

Ta dago ta dube shi, amma ta kasa magana, sabida zuciyarta dake neman bayar da ita. Ji ta ke kamar ta ruga ta rungume shi tayi kukanta mai isar ta, ta gaya mishi tayi kewarsa ita ma fiye da yadda harshe zai iya furtawa, fiye da yadda kwakwalwa zata iya fassarawa kuma fiye da yadda tunani zai iya kintatawa.

Ta ji ta a marainiya, duk kuwa da tarin iyayen da suka zagayeta a yanzun. Ta fi jin ta a mai cikakken gata, a sanda suke tare a (kitchen) fiye da yanzun da take da Daddy da mamar ta. Ta azabtu da rashin ganinsa fiye da yadda shi yake tunani.

Ya dubeta ya gani, ta fi shi ramewa da lalacewa, ta fi shi ciwon zuciya illa ita mai iya ‘controlling’ zuciyanta ne ba kamar shi da zuciya ke juyawa ba.

Ta fishi jin ciwon abinda take masa da hukuncin da ta yanke masu, kuma ta fishi azabtuwa daga hukuncin. Ta fi shi tunanin yaya rayuwarta zata karasa batare da shi ba? Ya fiye mata duk wannan gayyar dangin da suka zagayeta! To amma wannan alkawari ne, alkawari ne tsakanin ta da zuciyar ta da Ubangijin da ya halicceta ta yaya bazai gane ba ya taimaka mata wajen cikar alkawarinta da burin da ta dade tana ciwa zuciyarta….

Sheshekar kukan Al’ameen ya katseta da digar zafafan hawayenshi bisa tafin kafarta, dubawar nan da zatayi sai taga Al’ameen ne durkushe a gabanta, yama rasa kalmar da zai yi amfani da ita wajen rarrashinta da nuna mata muhimmancinta a gareshi.

Me zai gaya mata ta yarda bazai iya jinyar zuciyar nan ba… me zai gaya mata ta san ya manta komi, ya manta kowa, ya manta ko shi wanene saboda rashin soyayyar ta?

To itama kukan take mai tsima zuciya an rasa wanda zai rarrashi wani a tsakanin su.

Ta ga dai inta biye masa zasu kwana ne a hakan, wanda ita bata fatan hakan. Ita kadai ta san yakin da take yi da zuciyarta a duk sanda take tare da Al’ameen, balle a irin wannan halin da zuciyoyinsu ke gab da narkewa saboda azababben son da fada ma bata baki ne.

Ta sauka daga gadon  itama tayi tsugunne bisa carpet a gabansa  tamkar yadda yayi, don tana ganin it’s a disgrace agareshi ya durkusa mata, cikin muryar kuka da nadama tace

“Ni, ni… dama cewa nayi sai in har Hajiya ta rokeni gafarar abinda tayi mun, ta kuma furta amincewa da ni a matsayin matar ka, sannan ne zan yarda.“

Ya dago a hankali ya dubeta, yayi tsai da ransa yana nazarin zancenta. Tamkar kuma wanda aka yiwa allurar kuzari kuma sai ya mike tsaye, ya zauna a gefenta yace

“Har ga Allah Saratu wanan shine uzrin ki?” Ta gyada kai tana hadiyar zuciya. Yayi murmushi, ya ce,

“Intisar, idan na kawo Hajiya na gaban ki da Daddy da Aunty, ta nemi gafararki, ta kuma ce ta amince muyi aure, shikenan?”

Ta kara gyada kai da sauri. Ya sake yin murmushi ya mike, jikinsa ba inda baya rawa ya ce,

“Keep your promise.”

Ya soma ja da baya-da-baya har ya tadda kofar fita idon shi na kanta, yana mata murmushin da har abada ba zai gushe daga zuciyarta ba, cikin karfin hali itama ta mayar masa, sai kuma duk suka kyalkyale da dariya ga hawaye sosai a fuskar kowannen su. Ya daga hannunshi ya sumbata kana ya huro mata iskar. Da haka ya bar dakin gudu-gudu sauri-sauri, zuwa inda ya adana motarsa. Akan idon Daddy dake kallonshi ta taga ya ja motar ya bar gidan.

Daddy da Aunty Saratu suka yi ajiyar zuciya a tare. Duk kawaici irin nasa a yau ya yanke shawarar dosar Intisar a washegari don jin inda ta sa gaba, abin ya isa.

Washegari ta je gaida Daddyn da safe kamar yadda ta saba a ‘main’ falonshi, yana rigingine cikin kujera da ‘yar karamar rediyon shi inda yake sauraren ‘Voice of America’ shigowar ta yasa ya kashe rediyon kwata-kwata ya bata hankalinshi yana murmushi tun kamin ta zauna ya ce,

“Saratu, gobe fa in Allah ya kaimu tare da su Hunainah zaku tashi, daga Korea zasu rakaki makaranta don duk wasu shirye-shiryen komawar taki ban san sanda Al’ameen yayi ba. Dama abinda yasa aka daga tasu tafiyar kenan nima ban sani ba sai jiya yake gaya mun. Sai dai kuma naga alamar bakya son sakin jiki da Haj. Hadiza, Why?”

Ta yi shiru, yayi zaton bata ji ba sai ya sake maimaita tambayarshi. Ta dan kada kafadu alamun zancen bai dameta ba ta ce, “ba komi” ya ce,

“Ba komi, na nufin komi. Duk inda kika ji ance ba komi, to anan koman take”.

Ta ce, “To Daddy itama bata kula ni sai ‘ya’yanta (Su Hidayah) to ni ma ba sai in zauna inda na fi wayau ba?” Ya girgiza kai cikin murmushi “a’ah, ba zaki zauna inda kika fi wayau kadai ba. Uwa-uwa ce, matsayinta ya wuce duk yadda kike tsammani, ko ita bata kula ki tilas kuma wajibi ne ke ki kulata, ki dinga nuna mata kauna.

Above all, Hadizah bafillatana ce usul fillanci take maki, wannan kunyan na dan fari na nan tattare da ita ga kuma rashin shakuwarku, wanda wannan sai a hankali. Ke zaki taimaka ku shaku. Idan bakya kusantarta yanzun ba zaku taba sabawa da juna ba tunda yake ke mace ce, gidan aurenki zaki cikin dan lokaci, ki daure kiyi hutun karshen wannan shekarar tare da su.  Don ba mamaki kamin ku dawo an daura auren ku duka.”

Ta cira kai a hanzarce tana yi mai duban mamaki kana tayi saurin sadda kai, cikin siyasa irin tasu ta manya ya ce,

“Wai yayane? Ke da mutumin me kuke ciki ne, na ganshi yana ta mana zarya kamar marayan da ya rasa uwa, me kuka yanke ne? Su Najib fa ku suke jira don tuni sun gabatar da bukatarsu suna son asa masu rana da wuri.”

Yayi shiru yana nazarin irin karbar da tayi wa zancensa.

Tayi lamo da wuyanta a masangalin kujera abin tausayi. Idonta ya kawo ruwa raw-raw cike da nadamar hukuncin da ta yanke akan Al’ameen, wanda tasan abinda bazai taba yiwuwa bane. Tayi kokarin maida hawayen don bata son Daddy ya gani.

To amma shi Daddyn duk tsawon lokacin idanunshi na kanta, tsoron shi Allah, tsoranshi kada Intisar tace bata son Aminu. Da ina zai sa kansa da rigimar Al’ameen yadda jiya ya sashi gaba da magiyar a daura musu aure koda tace bata son shi!

Abinda shi kuma ba zai taba Iyawa ba wato danne mata hakki don farin cikin nashi? To amma shi kansa yakan so kasancewar al’amarin ba don komi ba sai don cigaban zumuncin bangarorin guda biyu, hakannan zuri’arshi kadai ya taba yiwa sha’awar auren kamilallar mace irin Intisar! Balle gudan jinin sa Ameenu?

Kwata-kwata tarbiyar Ihsan bai mishi ba, tun haduwar su na farko. Hakannan banda mutuncin Dr. Argungu da yake gani da tun zagin da Ann Hathaway taje ta yi mishi har ‘office’ kan wai Al’ameen ya ci mutuncin Addininta don kawai ta bashi shawara kan zaman shi da Ihsan gaba daya suka sire mishi.

Haka shigowa da Ihsan ke yi rungume da Al’ameen har cikin dakinsa abin na damun sa kwarai, don dai ba yadda zai yi ne. Cikin murya mai sanyi ya ce,

“Saratu, ki gaya min saboda Allah ba kya son Al’ameen ko?”

Ta shiga girgiza kai da sauri alamun ba haka bane, hawaye suka soma biyo kumatun ta. Tsohon Brigedier Bello Makarfi, ya mike zaune daga kishingiden da yayi, ya daura hanunshi na dama a kanta, ya ce,

“Wannan hawayen da kike kwarararwa a kullum yana damuna, sai in ga ni ban kai ga taka rawar uba har yau a gareki ba. Bayan ukubar da na sanya ki cikin gidana, still na kasa share miki hawaye a shekarun farin – cikin ki, na kasa tsayawa in gina maki rayuwa ta kwarai tamkar yadda na gina ta ‘ya’yana, na zalunce ki, na bautar dake, ban baki kwakkwaran ilimi ba har yau, ban idasa da zaba maki miji na gari a girman ki ba.

Idan bakya son Al’ameen kada ki ji nauyi na, ki kawo ko waye ni kuma mai share hawayen ki ne, in har ya cancanci ya amsheki daga hannuna, zan bashi.

Ki bar la’akari da kasancewar Aminu da a gareni, ni duk daya kuke, sai ma in ce kin fi shi. Domin ke ‘ya ce da ban taba ganin mai biyayyar ta da son iyayenta tamkar ke ba. Na rantse, a cikin ’ya’yan da na haifa bakidaya babu wanda ya ji kai na ya ke kuma kaunata tamkar ki.

Don haka don baki son Aminu baya nufin bakya son Daddyn Aminu, Illa shi Aminu ne ba kya so saboda wani aibinsa ko wani kuskure daya aikata miki kika kasa yafewa! 

Ni dai hakannan nake son ki da Al’ameen, ba don komi ba sai don masifaffen son dana lura yana yi miki mai gigigatarwa, mai neman fitar da shi daga hayyacinsa, mai neman raba shi da rayuwarsa.

Duk kuma bakomi ba ne face sakayyar Allah garemu a kan ki. Ina son inda za’a so ki ne, har illa masha Allahu, ba inda za’ayi miki son wanin ki ba. Abin nufi, masu aurenki domin wani naki, kyawu ko dukiyarki.

To sai naga Al’ameen ne irin mijin da ya dace da ke, irin mijin da na dade ina yi miki burin samu, zai kuma rike mana ke da dukkan kauna irin wadda muke so ki samu a gidan aurenki.

Na kuma dade ina sha’awar yiwuwar hakan a raina tun kamin shi ya furta, tun a sanda yake cin zalinki naga abubuwa dayawa cikin kwayan idanun sa, na kuma san ko ba dade ko ba jima Allah na nufin wani babban al’amari a tsakanin ku. Amma in kina ganin na so kaina ne Saratu fada mini?”

A gaggauce ta rarrafa gareshi ta gurfana a gabansa, ta girgiza kai da karfi ta ce,

“A’ah! Har abada Daddy nasan babu mai kaunata a duniya tamkar kai, har kuma iyayen da suka haife ni. Ba kuma zaka taba yin wani abu da sunan son kai a gareni ba. Kuma ni baka taba bata min ba, dai-dai da rana daya balle ka sa ni cikin ukuba.

Bana kuka domin kiyayyar Al’amin, kuka nake don so da kaunarsa, da suka yiwa zuciyata katutu. Allah Daddy, ban taba fada ba, amma Aminu na taba ji har ruhi da bargon jikina, nake kuma azabtuwa a zuci da gangar jiki domin kaunar sa!

Kuka nake domin nadamar tsatstsauran hukuncin da na yanke a gareshi wanda na zauna nayi tunani akai na tabbatar ba zai taba yiwuwa ba, domin kiyayyarta gareni ba karama bace, da kiyayyata aka halicceta baza ta taba yin abinda na kudurta ba.

Kuka nake domin sanin cewa na jefa Al’ameen dina cikin halin kaka-ni-kayi, halin da bazan iya fitar da shi ba, halinda zai iya janyo muguwar gaba tsakanin sa da wadda ta haifesa, ta shayar da shi mamanta, ta raine shi har ya girma ya kai munzalin da har na gani na ke bege,  take kuma son sa fiye da kowa a duniya.

Dama tace ni din mayya ce, yanzu zata kara tabbatar da zarginta cewa na mayancewa ‘ya’yanta, bayan ni kullum kokarina shine in nisance su, in yakice su daga cikin rayuwata amma na kasa!

Ko nayi kokarin hakan bana cin nasara, ba don kaunar jini ba sai don cewa su wani bangare ne daga jikin Daddy Makarfi. Jinin da yafi karfin wulakanci da tozarci a gareni. Ina tsoron hukuncin da zata yanke masa, wanda ko menene ni ce zan zamo sanadi.”

Daddy ya yi murmushi, yace “Gaya mun hukuncin da ki ka yankewa Al’ameen din ki?” Cikin hawayen dai tace

“Cewa nayi yaje yazo da Hajiyar sa, ta nemi gafara ta kan kiyayyar da ta wanzar da rayuwarta nuna mini, ta kuma furta amincewa da auren mu da bakinta, sannan ne zan maido soyayya ta, in rungume shi matsayin miji na uban ‘ya’yan da nake burin samu daga tsatson Daddy Makarfi.” Ta cigaba da kuka sosai, ta ce,

“Daddy daga baya nasan ban kyauta ba, nayi nadama, hukuncin yayi masa tsauri, don bazata taba amincewa ba, shi kuma ba zai dawo gareni ba sai da amincewar ta, tunda hakan muka yi alkawari. Ni kuma ba don komi nayi hakan ba sai don kwatarwa kaina da ‘ya’yan da zan haifa a gaba ‘yanci daga gareta.

Ina guje masu halin da zasu iya fadawa a gaba daga ukubar ta. Ni kadai nasan ita ko wacece? Ku bar ganin wai don iyayena sun bayyana zata daina ki na, a’ah, kiyayyar ta gareni a cikin jinin jikinta take, bazata taba dainawa ba. Koda kuwa a ce ni ce mafi rinjayen iyaye a duniya.

To amma ai shi Al’ameen na zalunceshi, na hukuntashi da laifin da ba na shi ba ko Daddy?” Tayi shiru tana maida lumfashi cikin zargin kanta.

Ga Mamakin ta sai yayi murmushi, ya dora hannu bisa kafadarta, ya ce,

“A’ah, ba ki zalinceshi ba, kin yi dai-dai. Ban taba ganin yarinya mai tunani, hazaka da hangen nesa irin ki ba Intisar! Ina ma a ce sauran yara mata zasu yi koyi da dabi’un ki da an daina wulakanta su a gidan aure.

Soyayyar dake zuciyar ki bata rufe maki ido ga hango gaba ba, da abinda gobe zata iya haifarwa ba. Sadaukarwar ki da sanin ciwon kan ki bazasu tashi a banza ba!!!

Abu ne da bazan iya gaya miki ba, Illa ni ma Haj. Nafi ta cuce ni ba kadan ba, wanda hakki ya koma mata. Ban saketa ba, amma ga gidan, ga ‘ya’yan nata kiri-kiri ta kasa zama a cikinsa, to tun a duniya kenan wata shari’ar sai a Lahira!

Komi za kiyi Saratu ki sa Allah a gabanki, bayanki, hagunki da damanki. Kar ki ji tsoron mutum domin shi ba komi bane face abin halitta daga yunbu, mai yin komi daga kudirah da Iradar Ubangiji kuma bisa nufi da yardar sa.

Magana ta karshe shine ina bayanki akan kudurinki na cewa sai Aminu ya kawo mahaifiyar shi nan a gabana ta nemi a fuwarki, bisa dimbin azabobin data gana miki, wanda ko Allah baya yafe hakkin wani kan wani. In kuma har baki yafe mata ba ai Allah ma bazai yafe mata ba.

Ta kuma furta da bakinta cewa ta amince ki zamo mata a gareshi wannan tunani ne mai kyau. Ni kuma alkawari daya nake so ki min shine, daga yau bazaki sake zubda hawayennan haka kawai bada kwakkwaran dalili ba muddin ina raye”  

Ta sa hannuwanta duka biyu tana sharewa tace

“Na daina Daddy, kuma in har hakan ta faru ni kuma na amince da auren Al’ameen koda a gobe ne, kuyi duk abinda kuke ganin ya dace.” Ya ce,

“Ubangiji yayi miki albarka Saratu, ya zama jagoranki a rayuwa, ya baki aljannah mafificiya sakamakon biyayyar nan da kike yi mun a gidan duniya. Kada Allah ya nuna min ranar da Ameenu zai tozarta ni a idonki.”

Ta sunkuyar da kai cike da kunya, a ranta ko cewa take ai ko Aminu kullum yankar tsokar jikinta zai ke yi yasa a miya, zata daure ba tare data gayawa Daddyn ba. Ya ce,

“Abinda nake so dake a karshe shine ki ji abinda na ce da ke, ki bi mahaifiyarki su rakaki makaranta, ki maida hankali kan abinda ya kai ki, muma insha Allah zamu ke zuwa dibaku a kai-akai, in kun samu hutu ki zauna tare da su har mu ji me Al’ameen da Mamar sa suke ciki a san abin yi.

Da dai za’a hada auren ku da na su Najib ne amma ina ga yanzu za’a fara yin nasun, har sai tazo tukun (Hajiyar), kuma ki saki jiki da ‘yan uwanki don Allah.”

Cike da murmushi tace ‘I can do anything for your sake, Dad (zan iya yin komi domin ka Babana)” ya ce,

“To Allah yayi miki albarka.”               

Mu karasa a littafi na hudu kuma na karshe insha Allahu. Taku har abada,   

–  Sumayyah Abdulkadir.

<< Siradin Rayuwa 33Siradin Rayuwa 35             >>

6 thoughts on “Siradin Rayuwa 34”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×