Skip to content
Part 39 of 45 in the Series Siradin Rayuwa by Sumayyah Abdulkadir (Takori)

Bayan Watanni Biyu

Dr. Rehab Mohammed, aboki nagari kuma amini na kwarai ga marigayi Dr. Alameen Bello, ya iso kasar Nigeria a safiyar wata litinin, tuni dama Daddyn ya san da zuwansa, don haka ya tura Yasir ya taho dashi da ga air-port.

Ya samu Daddyn a ofis ne inda suka kara yiwa juna taaziyya. Ya shiga fidda takardu da file-file yana yiwa Daddyn bayanin su dalla-dalla, kama daga takardun gidan marigayin da ke Miami da wani fili daya saya ya fara gini a Florida, shares din shi (hannun jari) na bankuna, takardun asibitin shi Meritime na kwakwalwa da suke kokarin rufewa, zuwa takardu na kananan kadarori kamar bungalows guda biyu daya saya a Vienna, da dakin shan magani cikin meritime da wasu kudade da yake bin Baptist Health Care dake Miami.

Akwai kuma kudi na musamman da suka tasamma naira miliyon goma da su abokanen aikinsa suka bawa iyalinshi sadakah, ba don komi ba sai don dinbin alherinshi da taimakon da yayi masu a rayuwar shi tare da su wanda a cewar su har abada bazasu manta ba.

Daddy ya amsa ya yi mishi godiya mai tarin yawa, yace amma kafin ya tafi, ya jira ya yi shawara da matar shi tunda mahaifiyar shi bata da lafiya.

An zauna da Ihsan a ranar wadda kanta ke sunkuye cikin abaya. Daddy ya shaida mata abinda kenan ya kuma danka mata komi na Alameen ya ce ya bar mata duniya da lahira ita da abinda zata Haifa, illa kason mahaifiyar shi da za a cire. Ihsan na hawaye tace ta amsa, amma itama ta barwa abinda zata haifan, bata son komi na Alameen domin bata taba tunanin ta ci gadon Alameen ba.

Burin ta har kullum shine shi ya bizne ta. Don haka in an cire na Hajiyar Daddy ya cigaba da kulawa da jikarsa ko jikansa dukiyarshi a hannunshi. Alfarma daya take nema su yi mata shine Rehab yayi kokarin maido Meritime cikin Nigeria kamar yadda Alameen ya dade da wannan burin kuma har ya mutu da burin a zuciyar shi.

Tace ya riga ya nemi iznin assasa asibitin daga federal ministry of health tun dawowar su, takardun komi suna nan a gidan su, tuni ginin yayi nisa, haka ko bayan rasuwar shi maaikatan basu daina ba, domin ya riga ya biya su kudin su. Tana so Rehab ya taimaka mata ya cigaba da jagorantar asibitin koda yana can Miami ne. Akwai karatu da zata karo na tsawon shekaru ukku kacal idan ta dawo zata cigaba da jagorantar Asibitin kamar yadda Alameen ke son yayi Allah bai bashi iko ba.

Abinda zata haifa tana da burin in mace ne ko namiji? To zai yi karatu irin na Baban sa, ya jagoraci Meritime, tana fatan ko bayan ran ta Daddy ya taimaka mata wajen cikar barin ta, wanda Alameen ya dade da yiwa rayuwar sa amma rayuwar tayi mishi gaggawa.

Rehab ya daga ido ta cikin farin mudubin idon sa ya dubeta. Yayi mamakin yadda cikin bakar fata aka samu irin wannan soyayya ta tsakani da Allah tsakanin mace da mijinta tamkar a kasar haihuwarshi (India). A da, ya dauki matan bakar fata a matsayin masu kwadayi da son abin duniya kadai; basu san mecece soyayya ta gaskiya ba. Amma a yau Ihsan Abubakar, ta shayar da shi mamaki.

Ba shakka rayuwa ta kada Ihsan ta shigar da ita taitayin ta, ta yarda ita din ba komi bace face kyal-kyal banza, da zaka tafi ka barta ka shirya ko baka shirya ba. Ta zama mai tsoron Allah da gudun duniya abinda Alameen ya dade yana nusar da ita bata gane ba sai da ta faru a kanta.

A karshen satin Faisal ya iso daga Lagos, sanye yake da kufta da wando na bakar lallausar shadda getzner. To tabbattaccen kamshinsa na (5,000 Doller) kadai daya gauraye ilahirin gidan ya sanar da mutanen gidan isowarsa as usual. Ya saya kwayar idanuwan shi cikin bakin dark glasses ta yadda baka iya ganin halin da kwayar idon shi ke ciki.

Babu shakka mutuwar dan uwansa ta dokeshi inda duk ya dauki laifin ya daura akan baiwar Allah da bata ji-ba-bata gani ba, itama ta kanta ta ke Intisar.

Inda abinda ya tsana da gani a rayuwarshi a yau to Saratu Intisar ce. Yana ganin ta as a wicked lover kuma har abada baya jin zai yafe mata.

Baya ga tagayyara tashi zuciyar tare da daidaita farin cikinsa, ba kuma tare data kara waiwayar shi a rayuwarta ba don sanin shi din a mace yake ko a raye? Ta koma ga zuciyar dan uwan sa, ta illata ta gabadaya da ciwon da har abada bazai warke ba. Duk hakan bai ishe ta ba, sai da ta yi sandaiyyar danganar shi da karkashin kasa, inda baa dawowa.

A yanzu kam ya na mai tantama da alamarin ta, tare da furucin da nahaifiyar su ta dade ta nayi a kanta na cewa, shin ko ita din, mayya ce?

Ya samu Daddy zaune bisa kujera yana nazarin labarun da ake watsowa daga tashar CNN a akwatin talbijin din jikin bango (plasma) dake falon. Yar lelen na gefe rike da karamin Alkurani izfi sittin bugun Misra tana karantawa. Kallo daya ya yi mata ya kawar da kanshi haka itama, da ganin mugun ramar da kowannen su yayi. Zuciyar ta ne ya bata wani irin bugu, don sai ya zamo mata Alameen sak a ranar bankwanar su illa shi din yafi Alameen haske da kauri kadan.

Tamkar bai taba sanin ta ba, bashi kuma da masaniyar kasancewar ta a wajen ya doshi Daddy suka gaisa, suka shiga hira ta abinda ya shafe su. Cikin karfin hali ta juyo tace ina wuni Ya Faisal? Da sauri ya amsa sabida dukan da zazzakar muryarta ta yiwa zuciyarsa, ba tare daya dubeta ba ya ce lafiya, yaya gida? Da haka ya maida hankalin shi kan zancen da suke da Daddy cewa ranar litinin zai tafi da Hajiya asibtin Meritime da ke Miami domin har zuwa lokacin babu wani cigaba akan alamarinta a asibitin kwakwalwa na Kaduna.

A lokacin Daddy ya ji matukar kunyar dan nasa kan biris din da yayi da alamarin mahaifiyarsu, ko ya ta ke bai taba tambayar wani a cikinsu ba. Ya sadda kai ya ce

kun yi maganar da Dr. Rehab ne? Ya ce Eh, shi da kansa mun je ya ganta, shi ya kawo shawarar mu tafi da ita can din in Allah ya yarda zasu yi iyaka kokarinsu. Daddy ya ce Allah ya taimaka, in akwai wani matsala sai kayi gaggawar sanar dani, ya ce babu wata matsala don shi Rehab din ne ya dau nauyin komi daga aljihunsa. Ta tashi ta bar masu falon cike da tukuki da kunar da zuciyar ta ta shiga yi kan irin wulakancin da Ya Faisal ya tsiri yi mata ba tun yau ba.

A washegari takardun ta na karatu suka fito suka tadda Daddyn a ofis, sabida kyawun sakamakonta hade yake da gurbin karatu daga Jamioi har ukku sai wanda ta zaba. Jamiar (Ummul-Kura) da ke Madinah sun bata gurbi a fanning pure and applied chemistry yayin da (King Abdul-Aziz University) da ke Riyadh suka bata biochemistry inda (Al-Azhar) da ke Egypt suka bata (doctorate) gurbi a medicine and surgery. Duka cikin ukun nan babu na yarwa babu kuma wanda ba raayin ta ba. Don haka da Daddyn ya bata zabi tace ta bar mishi wuka da nama ya zaba mata wanda duk ya ga ya dace da ita.

Ranar da Faisal ya daga da mahaifiyarsa kasar Amurka nema mata maganin tabin kwakwalwa data samu. Ranar ne itama ta daga Egypt tare da Najib da Hidayah da Daddyn ya wakilta suyi mata rakiya, bayan sun kammala duk wani shige da fice da ya kamata aka bata lokacin da zata fara shiga aji, wato daya ga watan Junairu na sabuwar shekara mai kamawa, kimanin watanni biyu kenan kamin lokacin.

Sun hadu da Hunainah a can wadda tuni ta zama yar gari, don haka ita ta nuna musu garin suka ci shi. Najib da Hidayah kam wani sabon honey moon din aka bude. Yayinda ita kuma ke tare da Hunainah kodayaushe, tana koka mata rayuwar ta da ta ishe ta, komi bakikkirin take ganinsa, bata jin dadin komi.

Ta gaya mata ita ta yanke rai da samun farin-ciki a rayuwarta, komi da ta ke yi tana yi ne cikin karfin hali da inganta Imani. Babban abin da ya dameta ya kuma kara dagula lissafinta da jin dadin ta shine gabar da Faisal ya daura da ita, ita ba yarinya ba ce, ta tabbata Faisal ya daura alhakin mutuwar dan uwansa da baya da kamar shi a duniya ne a wuyan ta. Ta ce cikin karyayyar zuciya da radadin zuci mara misaltuwa.

“Hunainah a da na so Faisal, na so shi a cikin rashin sanin shi din ko me nene a gareni. Hakannan dai nike son shi sabida shi mai kyautayi ne da tausayi, kuma gwani wajen nuna kulawa da nuna kauna a gareni.

To kin san zuciya an halicce ta ne a bisa kaunar mai kyautatawa a gareta, to hakan ne ya faru da ni a lokacin. Na so shi a sailin da ban san ma menene son ba, son shi nake, amma ban san son shin na ke ba, kawai na san ni mai tsananin kishi ce a kanshi ta yadda bana son ko da wasa in ji ko in ga wata mace ta rabe shi.

Babu ranar da ta fiye min tashin hankali tamkar ranar da ya ke yi mun hirar budurwar sa Ronke Adeyemi. A ranar na tabbatarwa kaina ina son Faisal, so na soyayya a matsayin yana yayana da muke uba daya?

Don haka na kalubalanci zuciyata na gargadeta da kakkausar murya a kan haramci da rashin dacewar abinda ta ke so! Haka na samu taimakon kiyayyar da mahaifiyarsu ke mun ya zagwanyar da 50% na soyayyar, kawai dai na bashi matsayin wani mutun precious a zuciyata (wato mai darajjah) kuma har yau, har gobe hakan ne ba abinda ya canza. Domin in har zan manta Faisal wanene a gare ni? To kuwa zan manta wane ne Daddy Makarfi.

Yayi min dimbin alheri kwatankwacin na Daddy na, tun ban san kaina ba. Kawai na budi ido na gan shi tare dani, cikin karimci da ingantacciyar kulawa.

Ko a sanda uwarsu ta yi min shamaki da su, na kuma alkawarta ma raina na rabu dasu har abada, na tambayi kaina a lokacin anya zan iya rabuwa da Faisal? Na bawa zuciyata amsa nan take da cewa, aah! Faisal wani mutum ne mai muhimmanci, kima da daraja a zuciyata da bazan taba iya rabuwa da shi ba. Haka lokacin da ya bar ni ba zato ba tsammani, na yi kuka nayi kewa na shiga kunci mara misaltuwa.

A hankali na dinga sanyawa zuciyata salama tare da kokarin yakice shi a raina amma na kasa, sabida wata ingantacciyar kauna ce nake yi masa ta daban a zuciyata.

A sailin ne kuma Alameen ya shigo cikin rayuwata. A lokacin da zuciyata ta rasa aboki, take cikin kadaici. Lokacin da nake mai tsananin bukatar taimako. Sai ya zo da wata irin soyayyah mai shiga rai ya shimfidata a zuciyata, irin wadda ban taba ji ba. Irin wadda ko a mafarki ban taba yin na tsintar kaina cikin ta ba.

Soyayya ce irin wadda ko muryar sa na ji, sai na ji gabban jikina, zuciya zuwa kwakwalwata gabadaya sun amsa! Idan dosowa yayi inda na ke, babu inda baya girgiza da kadawa a jiki na. Na tambayi kaina ashe dai wannan itace soyyar ta hakika, waccan da nayi duk a cikin gigin kuruciya ne kuma sabo da shakuwa sune tubalan da suka ginata a birnin zuciyata.

Wannan ita ce natural love kuma love at first sight wadda daya bazai iya rayuwa mai dadi ba tare da soyayyar dan uwansa ba, wadda kobo ko sisi ba zai iya sayen ta ba; saukakka ce daga indallahi!

Kwatsam, kaddara da mutuwa suka yi mun yankan kauna, a lokacin da muke gab da cikar burin zuciyoyin mu. Duk da cewa ta wani bangaren zan iya cewa ni na jawo amma na amince kaddara gaba take da komi.

Na ji ciwon rasa Alameen yadda harshena bazai iya furtawa ba, zuciyata bazata iya kwatantawa ba, ba don na yi imani da Allah da duk abinda ya saukar a gareni, mai dadi ne ko mara dadi? Da na tabbata babu abin da zai hana ni fita daga hankalina, sai dai komai ina dangantashi daga Allah ne.

A duk sanda na tuna Alameen ina yi masa adduar neman rahma kuma na tabbata wannan ita ce kauna ta karshe da zan nuna masa. Ni kadai na san ciwon da zuciyar nan ke mun Hunainah, ni kadai na san kadaici da maraicin da nake jin ya sameni.

Na dauka wannan ne lokacin da Faisal zai tausaya mun, ya waiwaye ni ya rungumeni, ya bani soyayyar da na rasa ta dan uwan sa mu debewa juna kewar Alameen, to amma abinda na fahimta shi a yanzu kiyayyar da yake mini da da hali, da ya koreni daga gidansu, da da hali, da ya dauki fansar dan uwansa a kaina. Yana gani na muguwa mayaudariya kuma maciyiya amanar soyayya.

Na rasa yanda zanyi da zuciyata Hunainah, na rasa wanda zan fadi wa abinda ke damuna idan ba ke ba. Na san ke kadai kika san irin ciwon da nake ji ke kuma ce kawai zan iya gayamawa na ji sanyi a zuciyata Hunainah.”

Hunainah kuka yar uwar ta Intisar ma kuka. An rasa mai rarrashin dan uwansa. Ita Hunainar da aka gayawa labarin don neman kwarin gwiwa da shawararta sai tafi victim din ma karaya da zub da hawaye. An rasa mai lallashin wani. Hakika tafi yar uwarta jin ciwon wahalolin da take fuskanta a rayuwarta. Tunda uwarsu ta haifeta kawo girmanta bata taba hutawa ba.  Bata taba ganin mai SIRADI iri-iri a rayuwa irin Saratu-Inteesar ba. Daga wannan bakin-ciki ya gushe sai wannan ya bullo. Gaskiyarta ne tabbas ba don ta kasance yarinya mai karfin imani ba da ta fita a hankalinta. Kalaman Hunainah ga yar uwarta shine;

“Ni na tabbata Ya Faisal na son ki. Wannan son da yake miki tun kina tsumman goyo ba abinda ya canza domin soyayya ta gaskiya bata taba gushewa kamar yadda bata tsufa, saidai masoyan su tsufa. Balle ku da yanzu nema kuke kan ganiyar kuruciyarku.

Kawai dai zan iya cewa yana jin zafin ki wanda na san as time goes on zai daina ne, ki fidda damuwar komi a ranki, domin karatun ki bana wasa bane in bah aka ba zaki sha mamakin mugun kayen da zaa dinga yi miki.

Ki bar komi a hannun Jallah mai kowa mai komai, wanda Ya halicci Faisal, Ya halicci Alameen, Ya halicci Inteesar ya sanya soyayyar juna a zukatan su. Ki bashi ikon zaba miki abinda ya san shi ne mafi alkhairi a rayuwarki.”

Hakika nasihar yar uwarta ta nutsar mata da zuciya. Tayi damarar karfafa zuciyarta da kokarin yakice duk wata damuwa da ke damunta, tareda daura aniyar fuskantar karatun ta da dukkan iyawarta. Gabadaya daga Alameen har Faisal ta sanyasu cikin wani fai-fai na tarihin rayuwarta ta baya inda ta budewa kanta sabuwar rayuwar data tarar a gaba.

Duk dai a lokacinne kuma tabi jirgi zuwa kasar Korea domin gano mahaifiyarta kamin lokacin da aka diba musu na fara karatun ya cika. Inda ita Hunainah hutu ne zata je na karshen semester wanda daga shi in ta koma zata shiga mataki na uku. Hidayah da maigidanta Najib sun koma gida Nigeria inda Hidayar zata fara karatu a jamiar Enugu inda mijin ta ke aiki kenan.

Daddy ya zaba mata Al azhar dake Egypt ne sabida dadadden burin da ya dade dashi kan son Saratun ta zamo mai amfani ga dumbin alummah da fasahar da Allah Ya bata, wannan shine dalilinsa na zabar mata Medicine and Surgery.

Hakika sun ji dadin hutunsu a Korea tareda mamarsu. Duk wani daddaurewa da takewa Inteesar a da, yanzu ta daina jan ta take a jiki fiye dasu Hunainah. Ita kadai tasan dimbin tausayin da yarinyar ke bata wanda ita din bazata iya maganta mata matsalolin da Allah Ya daura mata a rayuwarta ba.

Gabadaya ta kare, sai tsayinta da farin kadai dama jikin ba wani jiki na azo a gani ba. Ta kan yi mata nasiha da ta kara dayanta Allah a alamuranta yana sane da ita, ba wai mancewa yayi da ita ba.

Da sannu zata samu madawwamin farin-ciki a rayuwarta kamar kowa. Hakurin ta da kudurin ta na alkhairi a kan kowa, ba zai tashi a banza ba.

A lokacin Haj. Hadiza cikin ta ya tsufa sosai, haihuwa yau ko gobe. Zahrah an sanyata a nursery tayi wayo sosai ba abinda bata cewa. Ta gaya musu Daddyn su Hunainah yayi retire suna jiran kwanakin da aka deba musu su cika su koma gida bakidaya. Su Inteesar sun ji dadin hakan sosai.

Daya ga watan Junaiuru na sabuwar shekarar suka koma makaranta. Inteesar ta samu sauyin rayuwa ta fannnoni da dama, haka tsarin karatun Al-azhar yana burgeta komai cikin nutsuwa babu takurawa. Suka durfafi karatu babu kama hannun yaro, balle data fahimci abin na yi ne, mai wasa sai ya kwashi kashinsa a hannu sai ta kara dagewa tareda bada himma sosai.

<< Siradin Rayuwa 38Siradin Rayuwa 40 >>

7 thoughts on “Siradin Rayuwa 39”

  1. Takori na baki kwangilar samo min 5,000 dollars din Faisal please nima in shiga layi ko miyake na Hasib za a samo? . Ina jiran ganin wannan soyayya mai fadi da tarihi kar su saka mu manta da yiwa babban yaya dua

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×