Skip to content

Siradin Rayuwa 4 | Babi Na Hudu

2.8
(17)

<< Previous

Hakan kuwa a kayi, ta fito daga jirgin MEA International sanye da doguwar riga kirar Oman, ta yane kanta da kankanin mayafin panorama kalar baki da ratsin toka-toka, yayinda abnormal idanuwanta ke saye cikin farin medicated din ta mai kama da gidan biro sabida sirinta. Kafar ta bakin takalmi ne mai tsayi sosai kuma mai tsari da ban shaawa, babu wani make-up a tare da kasaitacciyar fuskar ta, sai wannan kyawun ziryan mara algus da kyale-kyalen zamani Ta na rataye da matsakaiciyar jakar hannu, siraran labbanta dauke da murmushi kayatacce ga Daddynta data fara yin tozali da shi.

Ranta yayi dadi da ganin wannan taron dangi da aka yi dominta. Ga dai shakikiyarta Hidayah rike da hannun mijinta Najibullahi, ga Antin ta, ga Aunty Ihsan, ga Bello, Nasir, Yasir, Idris, Furkan da Khalil uwa-uba babban Yaya Faisal Bello Makarfi. To amma duk wannan gayya ta hanga, ta duba bata hango zahran cikin taurarin ba, ba ta hango haske maganin duhun zuciyar ta ba (bata hango Alameen din ta ba).

Duk da haka ta daure, ko a fuska bata nuna ba, tabi kowa da runguma, amma data zo kan Ihsan sai da ta dan dakata kadan kamar mai nazarin wani abu, kana ta daure ta rungumeta itama, sai ta ji wani abu mai tsini ya tokare ta wanda babu ko tantama ciki ne mai girma sosai.

Ji tayi wani abu yazo ya tokare a makoshin ta. A yau kam ta samu kanta tana mai kishin Ihsan fiye da koyaushe a rayuwar ta.

Ko kamin ta iso kan Faisal shi har yayi gaba ya bude mota ya shiga yana jiran su, daman shi ya yi driving dinsu cikin babbar mota Jeep baka mai tudu da tsayi. Hannunta cikin na Daddynta, hakannan kujera daya suka zauna. Sai a lokacin ta lura da muguwar ramar da kowannen su yayi, ba kuma wanda ya yarda ya kara hada ido da ita, kai ba ma wannan ya dame ta ba kamar muguwar hararar da Faisal ke jefa mata a duk sanda su kai kuskuren hada idanu ta cikin mudubin motar.

Karewa ma babu mai yin ko kwakkwaran motsi a motar tamkar ruwa ya cinye su. Tun tana kai zuciya nesa tana tausar zuciyar ta da cewa ai koma meye tunda gani a gidan zan ji ne har ta kasa controlling tashin hankalin ta kawai sai ta fashe da kuka, cikin siririyar muryar ta mai tsuma zuciya tace ku sauke ni, ku sauke ni a titin nan tunda duk bakin-ciki kuke da dawowa ta, zan koma inda na fito.

Daddy ya yi murmushi ya kama hannunta na dama yace,

“Waye mai bakin-ciki da dawowar ki Saratu, gayamin sunan shi yanzu in sauke shi, ya nemi wani uban daban amma ba naki ba, umh waye shi Intisar gaya mun ki gani in baa sauke shi ba?”

Ita dai bata bar kukanta ba, haka Ihsan da Hidayah kuka suke cikin mayafansu, kuka mara amo bare sauti sai radadi a zuci.

Koda suka iso gida ma bata sake zani ba, kowa yayi nasa waje, Faisal ya wuce da Daddy office Najib da Hidayah sun wuce gidansu a Maitama, Ihsan ma ta wuce dakinda aka ware mata, inda anan ne take zanan takaba da rainon cikinta don Daddy yace bazata rabu da su ba har sai ta haihu, dan ta ko yar ta yayi wayo daga nan tana da zabi a rayuwar ta. Mahaifinta ya amince da hakan amma Ann cewa tayi wahala ce bata ishe ta ba.

Dawowar Intisar gidan sai ya zama tamkar wani fami ne bisa ciwon da ya fara samun sauki ga kowa a gidan. Wai Antin ta mai tarairayar ta da rasa ina taka saka  ina-taka  aje da ita a duk lokacin da ta dawo hutu, ita ce yau mai kakalo aiki don kawai kada ta zauna da ita ko na minti daya ne a dakin, kai daga karshe ma da taga kukan da Intisar din ta soma na neman karya mata zuciya itama ta fashe da kukan duk irin kokarin ta kuwa, sai ta gudu sassan Daddy Intisar din bata kara ko jin duriyar ta ba.

Aah, wai me ke shirin faruwa ne? Ta kasa baiwa kanta amsa, me ya kawo Ihsan gidan har daki aka ware mata cikin sassan Anti, ina Alameen?

Sai a lokacin ne ta daga idanunta cikin gilashinta, ta kai duba ga katon hoton shi window-size da ke makale a falon tun kamin ta tafi, babu hoton an dauke shi. Ta sunkuyar da kai, haka kawai ta ji mummunar faduwar gaba ta same ta, jinni ya daskare daga gudun da yake yi cikin jikin ta. Kada Allah yasa abinda zuciyarta ta sinsina ya tabbata. Kada Allah ya sa a ce da ita a yau babu Alameen. Ka da Allah ya nuna mata wannan ranar!

Ta kai hannu ta share kwarmin idanunta a dai-dai lokacin da Khaleel ya shigo, daga bakin kofa ya sanar da ita Daddy na kiranta, ba kuma tare daya kara ce da ita komi ba ya juya ya fita.

Ta mike cikin rashin kuzari, tamkar kazar da kwai ya fashewa a ciki ta doshi main falon su. Kowa na zaune, da yawa kansu a sunkuye, kadan ne suka dube ta. Ta yi mamakin duk wannan taron da a kayi mata na menene?

Ta kai dubanta ga Mamarta, domin neman Karin bayani, amma kamar dazu tayi ignoring hada ido da ita. Daddy ya mike da kan sa har inda take ya kamo hannunta, ya zaunar da ita a gefen sa.

Ya ce mu karanta salati goma sha daya ga Annabi (S.A.W), mu karanta kulhuwallahu kafa (3) zuwa makwancin sa, mu kara godiya ga Allah da yayo mu Musulmi maabota Imani da yadda da Kaddara.

Bayan sun shafa ya dubi Intisar da tashin hankali ke zane baro-baro bisa kyakkyawar fuskar ta tamkar ta daura hannu a ka ta ce wayyo Allah! Ya dubeta da sassamyan duba mai sa nutsuwa ga dan adam ya ce,

“Saratu!”

Ta dago ta dube shi da dukkan idanu amma bata amsa ba, idanunta fiki-fiki a warwaje. Ya yi murmushi yace zaki iya gaya mun me da me Ubangiji Allah yayi miki a rayuwarki, kama daga lokacin haihuwar ki zuwa yau da kika dawo? 

Ta shiga girgiza kai da sauri, hawayen ta na zuba bisa cinyar ta ta ce,

“Aah! Ba zan iya ba, domin baiwar sa da fadhalolin sa masu yawa ne a gareni. I can’t express his infinite mercy! An yar da ni a daji amma bai bar ni na tozarta anan ba, bai ba wani mugu iko a kaina ba. Ya hada ni da uba nagari, mai so na da kauna ta tare da jin ciwo na kamar, ko ma fiye da uban da ya haife ni. Ya bani wata irin uwa, mai kyautayi da alheri, wadda a kullun burin ta shine farin-ciki na. Bakin-cikin ta shine bacin rai na. Ya bani yan uwa ba jinni na ba, amma masu jin kai da matukar kyautayi a gare ni.

Ya yi mun rai, lafiya, ji da ganin da bai raba ni da shi kwata-kwata ba. Ya kuma bani lafiyayyun kafafun da na ke takawa da su a doron kasa in nemi Ilmi..ya yi mun komi.. ya yi min kowa, I can’t explain his abundant blessings, ai abubuwanda ya yi min baiwarwaki dasu ba zasu fadu ba.”

Ta yi shiru cikin sheshshekar kuka da Imani da ya kara ratsata. Ya girgiza kai cike da gamsuwa da kalamunta ya ce,

“To a yau idan aka ce Allah ya jarrabce ki da wani bacin rai, domin jarraba imanin ki da godiyar ki gare shi bisa wadannan niimomi da ya yi miki, ta hanyar dauke abinda kika fi so a duniya me zaki yi? Ya ya zaki karbi alamarin kuma me zaki ce da shi?”

Cikin yankewar burin duniya bakidaya, kuma cikin matsananciyar kauna da bege ta ce,

“Sai in yi tawakkali in gode masa! Hakan ba zai sa in fita daga Imani na ba.

Ba tun yau nake haduwa da jarrobawoyinsa ba, ba kuma wadda na taba faduwa. Duk wadda yayi min in nayi hakuri daga baya alherin sa na ke gani.

Ya ce madallah da wanda zuciyar sa ta kasance maabociyar bakin ciki guda daya. Abinda ya gani da idanunsa, ko ya ji da kunnuwansa (na wannan bakin-cikin) bai shagaltar da zuciyar sa daga rahmomin Ubangiji a gare shi ba. Intisar, Alameen ya amsa kiran mahaliccinsa, ya tafi ya barmu da kewa da ciwon rashin sa, ya bar mana gibin da mun tabbatar cike shi abu ne da bazai taba yiwuwa a gidan nan ba, kamar yadda mance shi ko shafe tunaninsa, wani abu ne da ba zamu taba iyawa ba!.

Ta runtse idanuwanta da karfin gaske, runtsewa irin wadda bata taba yi masu ba, yayinda wasu hawayen suka kwararo da gudun gaske daga kyawawan abnormal idanun ta. To haka kowa a wajen kifa kai yayi a inda yake zaune ya shiga fidda nasa hawayen da ya dode bai fitar ba. Suna jiran wannan ranar.

Ranar da zaa gayawa Inteesar Alameen ya rasu! Su kam basu ji dadin hukuncin Daddy ba da yace kar a daukota tun a wancan lokacin gashi yanzu ta dawo masu da mutuwar danya shakaf. Abinda ya riga ya faru watanni uku da suka gabata.

Jikinta ne ya kama kaduwa, ta soma rawar dari duk kuwa da zafin da ake a lokacin. Kafin wani dan lokaci zazzafan zazzabi ya rufeta haka gabobin jikinta babu inda bai girgiza haka hakoranta ba wanda bai haduwa da dan uwansa ji kake kaf-kaf-kaf. Ta mike da gudu ta je ta rungume Mamar ta. A sannan ne ta samu damar yin kuka mai sauti. Kuka mai girgiza zuciya, kuka irin wanda bata taba yi ba a tsayin rayuwarta.

Kuka na rasa abu mafi muhimmanci kuma mafi soyuwa ga rayuwarka. Kuka na nadama da da na sani mara amfani! Bata tabayin da na sani a rayuwar ta ba sai yau!! Bata taba tsanar kanta a duniya ba sai yau. Ba abinda ta ke tunawa illa irin rabuwar da suka yi da Alameen din ta. Ashe dama rabuwar kenan? Wannan murmushin, wannan, wannan hawayen nasa da dariyar da suka yi duk na bankwana ne, Allah Sarki!

Ta tashi daga jikin Maman ta rarrafa ga Daddy, ta kama kafarsa cikin raunanniyar murya ta ce,

“Kada ka taba yafe mun Daddy. Domin ni ce silar shigar Alameen cikin halin kuncin da ya shiga.

Ai na gaya maka hukuncin yayi masa tsauri bazai iya cikashi ba. Da nasan hakan ne zai kawo ajalin sa, wallahi dana amince masa koda bata amince ba, ko da hakan zai zamo karshen abinda zanyi a rayuwa ta, koda zata haka rami ta bizne ni ne da raina.

Nayi kuskuren hukunta soyayyarshi gareni a matsayin laifin da ba nashi ba! Na kasance azzaluma ga dimbin soyayyar da yake mini. Ban yi maka adalci ba ko kadan Daddy domin da da halacci, da duk wani jinin ka ma yafi karfin yarjejeniya a gareni.

Da ni din mai halarci ce da ko kare ka haifa kace in aura, zan yarda ba tare da wani ja-in-ja ba. Balle shi mai kirki ne, kyautayi da soyayyah irin wadda ban taba gani ba.

Yayi kokarin inganta rayuwata ta hanyoyi da dama, ta duk hanyar da ya san zai bi ya fidda ni daga halin da yazo ya sameni a ciki; da yawun bakinsa, da aljihunsa, da zuciyarsa da komi daya mallaka!

Amma sakamakon sa, wani hukunci tsatstsaura, da nake da yakinin ba zai taba yiwuwa ba! Ba zai taba samo shi gare ni ba. Ban maida martanin soyayyata gareshi ba koda kashi talatin cikin dari (30%) na dimbin soyayyar dake tattare da ni.

Maimakon haka, sai nayi amfani da matsananciyar soyayyar da yake yi min wurin hukunta shi da laifin da ba nashi ba…” Ta ci gaba da rera kuka mai matukar motsa zuciyar duk wani mai sauraron ta.

Ita ba mutuwar Alameen tafi daga mata hankali ba, kamar irin rabuwar da suka yi, da kin amincewar ta da auren su, bayan ba haka bane zahiri a zuciyar ta. Ba don komi ba sai don sanin cewa irin su basu da kaico, mutuwa ba komi bace face hutu a gare su, halayen sa da dabiunsa duka masu kyau ne, tsarin rayuwar shi da muamalar shi da kowa mai kyau ce. Duk wanda ya san shi idan ya budi baki alkhairi zai fada a kan sa.

Bata taba ganin mutum mai kirki da jin kai irin Alameen ba, don haka bata kokamawa mutuwar sa, sai rashin soyayyar sa, da rashin maida martanin tata soyayyar a gare shi, kuma a ganinta ta zalince shi, har abada Daddyn ba zai yafe mata ba.

Tunda duk kawaici irin nasa, sai da ya zaunar da ita ya nuna mata kwadayin sa a fili kan son ta da auren Alameen, shin Daddyn da Aminun sun cancanci hukuncin da ta yanke masu? Wanda ya zamo karshen rayuwar Alameen din ta?

Ta sunkuyar da kai cikin matsanancin tashin hankali, ji take har abada bazata kuma iya hada ido da Daddyn ba. Daddy Makarfi sai ya yi murmushi. Ya sa hannu ya dago ta daga durkuson da ta yi na mai neman gafara, kamar koyaushe ya aza ta a gefen shi ya ce,

“A kan me zan ki yafe miki? Me kika yi mun? Ki daina cewa kin zalinceshi domin baki da hakkinshi. In ma da wanda ya zalinceshi to uwar da ta haifeshi ne. Ya tafi ne cike da kewa da begen ki. Ya tafi ne a bisa kudirinsa na son ki da kaunarki, a bisa son ki da ke neman tagayyara shi da tarin kaunarki daya illata zuciyar sa.

Ki bar ganin kan ki a matsayin mai laifi illa masoyiya tagari, mai son fidda masoyinta daga kuncin da fushin uwa ka iya jefashi a rayuwarshi.. Albarkar Allah ta tabbata a gare ki.

A wannan daren mai cike da sauyin sabbin alamura da dama cikin rayuwarta, ta kasa runtsawa, hakannan ta kasa tsaida hawayenta kamar yadda ta kasa yiwa Alameen addua. Har yanzu ta kasa daina ganin kanta a matsayin azzuluma a gare shi. Ta ma kasa gasgata alamarin kwata-kwata.

Ta dauki komi as an optical illusion, Delusion… Wai Alameen din ta? Ya rasu! Duk burin da suka ci wa rayuwar su, duk farin-cikin da take hangowa rayuwar aurensu ya zama tarihi? Shi kansa Alameen din wai a yau ya zama sai tashin zance?

Ba zata kara jin daddadar muryarshi da ke gigita ta ba, sai a mafarki! Ba zata kara jin daddadan kamshinsa da duk duniya bata taba jin mai irin sa ba. Wannan korafin da ban dariyar sa, ba zata kara jin ko daya ba cikin kiran “Halima dube ni!” Wasu hawayen suka kara shararowa a kundukukinta zuwa cikin kunnuwanta, kasancewar a kwance ta ke rigingine bisa niimtaccen gadonta, tana mai tuna ranar da suka rabu a dakin, yana durkushe a gabanta yana kukan da bata son tunawa, domin ta yarda kawai da dimbin soyayyar shi gareta. Ta yarda shi din ba zai iya rayuwa ba tare da ita ba.

Ta kai tunaninta ga alamuran ubangiji masu juyawa tamkar tayar mota ko gare-gare abin wasan yara. Ita kan ta rayuwar haka take; yau fari gobe baki. Ta na tunanin shin wace rana ne zuciyarta zata huta da bakin ciki a duniya? Wane lokaci ne zata samu dawwamammen farin-ciki a rayuwar ta? Wace rana ce zata tsallake SIRADIN RAYUWAR ta?

Tamkar kuma wadda aka tsikara da allura sai ta mike ta doshi kofa. Karfe ukku na sulusin dare. Ta sanya takalminta ta dauki filo da gilashinta, kana ta yane kanta da yalwataccen mayafi, ta dauki tocilan tana haskawa, kasancewar an kashe dukkan fitilun gidan sai na cikin dakunan barci, ta doshi hanyar sassan Hajiya. Daga nan kuma ta nemi hanyar kitchen din ta.

Ta murda kofa ta kunna fitila, komi yana nan yadda yake, illa kura da koina yayi. Ta koma dakin su da Dela wadda tuni ta dade da barin gidan, tun dawowar Antin ta sallameta. Tabarmar ta da Hajiya ta bata na nan a bayan kofa, ta fiddota ta karkade ta dawo kitchen din ta. Ta shimfida a inda ta saba ta daura filon, ka na ta kwanta. Sai ta ji wani sanyi ya sauka a zuciyar ta.

Filla-filla tana mai tariyo rayuwarta da Alameen ta dan lokaci a cikin kitchen, wadda tafi tsayin shekaru a idanunta.

Kalaman sa masu dadi da sanyaya zuciya na dawo mata tar-tar a sharp kwakwalwar ta, haka hoton kyakkyawar fuskarsa garai-garai a idanunta. Ta san idan ta ce ma ta yi barci a wannan daren, to karya ne. Ta kuma yaudari kanta.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

6 thoughts on “Siradin Rayuwa 4 | Babi Na Hudu”

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×