Skip to content
Part 10 of 22 in the Series Sirrin Boye by Halima Zakariyya

Ni dai bin bayan Ammi na yi da kallo har san da ta shige wani ɓangare da ke cikin falon, bin ta nake da idanu da sauyin yanayin da naga ta samu cikin lokaci ƙalilan, jikinta a saɓule hakana walwalar da ta shigo da ita a ɗazun ta ɗauke, a zuciyata na shiga tunanin abun da zai sauyata zuwa wannan yanayi wanda yafi kama da alhini, sai dai mamakina yafi ta’allaƙa akan abun da zai sata a damuwa alhalin tana cikin wannan daular?

Hoto! Kalamar hoton ta sake haskawa acikin kaina ina mai tuna furucinta ga Suhail, lallai ta sami sauyin yanayin ne daga san da ta ɗaga idonta ga jikin bangon gabas sannan tayi furucin ga Suhail, kenan rashin hoton shi ne ya sata a wannan damuwar? to hoton menene?

Na sami katsewar tunani a lokacin da Jakadiyar ke min maganar na gwada takalmin makaranta, kuma ko da na gwada yayi min kaɗan kasancewar ina da doguwar ƙafa, Suhail ya jijjiga kai yana cewa, “ke ko Mairo wace iriyar ƙafa ke gareki haka”. Murmushi nayi kawai idona na kan takalmin da nake jin dama a bar min shi a haka saboda kyan da yayi, sai dai babu batun hakan dan tuni Ashraf yace Jakadiya tasa a kayan marayu.

Suhail ke tambayar lamba nawa nake sawa takalmin nace nima ban sani ba, Ya Kabiru yace masa ai da yake anfi siya mana silifas lambar bai zama lallai tazo ɗaya da irin wannan ba, amma kambas ɗin da ya siyo min kwanaki lamba arba’in ne, to dai da aka rasa lambar da za’a bawa ƙafata ƙarshe sai takalmansu suka ce na gwada, ina gwadawa ina ƴar dariya ganin ƙafata cikin takalmin maza, kuma daga kan takalmin Ashraf har zuwa na Ya Kabiru kowanne yay min kaɗan, sai da Jawad wan da kansa ke kan wayarsa yace nazo na gwada nasa, ina kuwa sakawa tamkar nawa yay min dai-dai, har Ashraf ke zolayata akan ko shi za’a bar min kawai, nace,”tabɗi me zanyi da takalmin Jawad, duk da yayi min kyau amma bana so, a sayo min sabo irin na ƴan’uwana.”

Ni da ƴan’uwana mun yi murna sosai da irin kayan da aka bamu, kayan da bai zama lallai ɗan wani mai kuɗin ma ya mallakesu ba cewar Ya Kabiru, ni a ɓangaren kayan zaƙi da aka haɗa mana ma babu ɗaya da na taɓa cin karo da su a rayuwata, ina jin Ashraf na faɗin ai bamu za muke girki da kanmu ba makaranta ce take dafawa, hasalima ko yaji aka kama mu da shi sai an ƙwace kuma sai an horar damu, saboda haka a kula, ya kuma ƙara jaddada mana da cewar duk wani abu da muke da buƙata ko kuma aka buƙata a makaranta mu kira Suhail.

Ko da aka zo ɓangaren cike takardun makaranta Suhail yace sam ba za’a saka min Mairo Adamu ba kamar yanda Ya Kabiru ya faɗa, yay ta masa tsiyar idan shi ɗan kauye ne sai akace masa kowa ma zai zauna a irinsa ne, dan haka ya maida min da Maryam Adam Bichi, Adawiyya ma Jakadiyya tace ai Rabi’a ne asalin sunanta, dan haka ita ma Suhail bai sanya mata Adawiyya ba, Rabi’a Adam Bichi shi ne sunanta kamar yanda ya faɗa, Habiba kuwa sunanta ne dama aka saka mata. Na ɓata fuska na tubure akan cewar ni dai a maida min da sunan da Babana ya raɗa min, bana son wani Maryam, Ashraf yace to ai ko wurin Baba akaje zai ce Maryam shi ne usulin sunana ba Mairo ba, Jawad da ke gefe yana aikin latsa waya yake faɗin haka za’a kaini makarantar ƴan gayun ina masu ƙauyanci, Na harare shi ta ƙasan ido nace ina ruwansa, ni kaina daga irin kayan da naga an haɗa mana da irin yanda Ashraf ke lissafowa Ya Kabiru doka da ƙa’idojin makarantar nasan cewar ba irin gajigari-gajigari bace, makaranta ce babba.
Bayi huɗun da Jakadiya tasa aka kira mata su ne suka ɗebi akwatunnan kayan da bakko suka fita da su zuwa mota.

Naso ace kamin fitowarmu na ƙara ganin Ammi, dan lokaci ɗaya naji matar ta shiga raina, ina kuma sonta da tausayinta tare da son kasancewa tare da ita, dan wallahi duk wannan murna da zumuɗin da nake akan nuna mana kayanmu gaba ɗayan hankalina yana can kanta da son sanin yanayin da take ciki ayanzu, da kuma son ƙara ganin fuskarta dan tabbatar da ganina wanda nake jinsa matsayin hasashe ko gizau.

Lallai Masarautar bichi da girma take, dan baki ma yayi kaɗan ya misalta girmanta saboda gari ce guda. Tun da muka fito haraba nake bin masarautar da kallo da burgewa, komai nata mai kyau ne da ƙawa, tsaruwarta har ɗaukan ido yake. Jefa idanuna nake ta ko’ina ina duban Bayi da Kuyangu da ke kai komo a ayyukansu, ƙwarai ne tun daga waje zaka gane tabbas an narka dukiya wajen tsara masarautar balle kuma ka shigo daga cikinta, idan ma ka shigo matsayinka na baƙo zaka kasa tantance wacce ƙofa zaka sada kanka saboda yawan ƙofofinta.

Muna nan tsaye a inda su Suhail suka barmu suka dawo muka ɗau wata doguwar hanya mai cike da shuke-shuken fulawowi masu ƙamshin gaske da sanyaya wuri, a lissafin da nai bayan ƙofar Ammi ta biyu da muka fita wannan da muka shiga itace ta shida, tafiya muke muna wuce fadawa da ke tsaitsaye tun daga shigowar get ɗin da kuma tsirarrun bayi dake kai komo, duk kuma ta inda muka gimla sai an duƙa anyi gaisuwa da kirari ga Suhail da Ashraf. Mun yi tafiya me nisa naja na tsaya dan tun ɗazu ƙafata ta gaji, nace da Suhail”Buzu wai ina zaku kaimu? ko Anan makarantar ta ke ne?”. Ya waigo ya dubeni tare da bani amsar,”a’a ba nanne makarantar ba, nan ɓangaren Kakarmu ne Bella, zan kai ku ku gaisheta ne, kiyi haƙuri ai an kusa zuwa?”

Na gyaɗa kai kawai Ya Kabiru ya kama hannuna yana ce min raguwa.
a yanda na sani tuta a makaranta ne ake dasata, tun da akwai tutar najeriya a makarantarmu, to amma isowarmu gejin da zai sadamu da wata ƙatuwar turaka sai naga dashen tuta a ƙofar wurin daga ɓarin dama, ƴan sanda biyu na gadinta kowannensu riƙe da bindiga a hannu sun ƙame tamkar dasa su akayi, kalar tutar kore da yelo da ja, tare da kwalliyar tauraro a tsakiya me kalar yelo da shuɗi, na ɗauka tsawon daƙiƙa biyu ina kallon tutar da son sanin ko tutar wacce ƙasa ce, sai dai duk nacina na kasa saboda bata ɗaya daga cikin tutocin da aka koyar damu a makaranta.

Cikin makeken falo na gaske muka sanya ƙafafunmu, falo me ɗauke da kayan sarauta ta ko’ina, ni da ƴan’uwana da muke baƙi muka shaƙi ni’imtaccen ƙamshin da ko a gidan waziri da suke gidan turare babu irinsa, da ace zan sami dama da babu abunda zai hana ni roƙar a sammin turaren, nima na kaiwa Gwaggona da Innata suke sawa a ɗakinsu, saboda duk wanda yaji wannan ƙamshin yasan ƙamshi ne na musamman, yanda nake ta zuƙar ƙamshin a hancina yasa na tuna da furucin Sadiya a wata rana, tace ke dai Mairo idan ba’a saceki a ƙamshi ba to za’a saceki a kyau, nai ƴar dariya kawai.
A irin yanda kuyangun falon ke nutse da takatsan-tsan ɗin ganin sun cimma ayyukansu zaka fahimci cewar me ɓangaren bata wasa bace, wata tsohuwar mata ce zaune kan kujera irin ta sarauta me shilla mutum a hankali, tana kishigiɗe a jikin kujerar yayin da hannayenta duka biyu ke kan hannun kujerar ta ko wanne ɓari, idanuwanta na ɗauke ne da siririn farin gilashi, yayin da bayi kusan shidda ke tare da ita, biyu na tsaye ta bayanta su na mata firfita, biyu kuma na duƙe ne a ƙasa suna matsa mata ƙafafu, sauran biyun kuma na daga tsaye a gefen hannun damarta, ɗaya acikinsu tana riƙe da ƙaton faranti me ɗauke da kayan marmari, ɗayar kuma ita ce me ɗauka tana sakawa tsohuwar a baki wadda ke ci a hankali. lallai anan ake sarauta me cike da ƙarfin izza da ƙasaita, anan kuma usulin kyan halitta yake da ido ba zai so ɗaukewa daga kansu ba, gabana ya faɗi a san da muka haɗa ido da ita ta cikin gilashinta, na saurin ɗauke idona ina ambaton innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, yayin da kuma hoton fuskokin mutum uku suka shiga haskawa a cikin idona, na haɗiye guntun yawu a maƙoshina sannan na nemi wurin da Suhail yay mana nuni na zauna.

“Ranki ya daɗe barka da wannan lokaci”. Ashraf da Suhail suka ce da ita bayan ta baro kan waccen kujerar da take ta dawo ta zauna akan wata kujerar ta daban, ta mayar masa da magana acikin yaren da ban san wane yare bane amma yana shige da larabci, sun daɗe su na magana da ita acikin wannnan yaren kamin Suhail yace,”Bella wannan sunansa Kabir abokina ne, waɗan nan kuma ƙannensa ne, sun shigo masarautar ne shi ne nace bari na rakosu wurinki ku gaisa, su na da mutunci sosai domin a gidansu muka sauka ranar da muka shigo cikin garin nan, an karramamu an mutuntamu a gidansu ba kaɗan ba”. Suhail na rufe baki daga Ya Kabiru harmu muka rissinar da kai muna miƙa mata gaisuwa, bata buɗe baki ta amsa ba illa iyaka ɗaga mana kai da tayi, sannan naga tayi nuni wa Suhail da hannu, shi kuma ya dubemu yace an bamu izinin zama kan kujera, to a raina saina kawo ko tsohuwar bata magana ne, bebiya ce.

Muna zama kan kujerar nayi zumbur na miƙe a zabure ina aikin zare idanu ina mammatsa hannuna tamkar mara gaskiya, nan kuwa tarin kunya ce ta lulluɓeni duba da yanda aka zuba min ido, Suhail da Ashraf suka haɗa baki wajen tambayata,”lafiya?”. Ban basu amsa ba sai dana kalli su Adawiyya da ke kan kujera zaune lafiya, na mayar da kallona ƙasan ƙafata a san da wata baiwa tazo gabana tana tambayata,”me ya faru?”. Nace musu,”babu komai, da na zauna a kujerar ne sai naji kamar zan faɗa ciki, laushinta yayi yawa”. Takaici ya kama Adawiyya da Habiba dan ina kallo suka harareni, su a yanda suke zaune kamar ma sun saba da zama akan irin kujerar ne, akayi-akayi kuma na koma na zauna naƙi nace ni dai ba zan iya zama akai ba. “ƙaraso da ita nan”. Cikakkiyar muryar tsohuwar ta ambata a lokacin da ta ɗago da dubanta kaina, tsoro da fargabar abun da zai faru ya kamani, nai saurin zube gwiwoyina ƙasa na shiga bata haƙuri. “dan Allah ranki ya daɗe kiyi haƙuri ki gafarceni, wallahi ba da gangan nayi ba, ban taɓa zama bane akan irin wannan kujerar mai kamar auduga, su kansu ƴan’uwan nawa sunyi ƙarfin hali ne, kiyi haƙuri dan Allah kar a hukuntani, ni ɗin ƴar ƙauya ce ɗiyar talaka.”

Sai dai kuma me, duk magiya da ban haƙurin da nake Bella bata ji ba, hasalima kanta na kan wasu takardu ne da rubutun ciki ke kamar jagwalgwalo, haka Baiwar ta kamo hannuna ta kawoni har gaban Bella, nasa hannu na goge ƴar guntuwar ƙwallar da ta sakko min, nayi wurƙi-wurƙi da idanu ina jiran tsatstsaraun hukuncin da za’a yanke min, dan na taɓa jin labarin gidan sarauta basa yin da sauƙi, tausayin iyayena ya kamani saboda halin da za’a jefasu aciki idan suka ji cewar masarautar ta kamani da aikata wani laifi.

Bata ɗago ba har tsawon daƙiƙa biyun dana ɗauka gwiwona zube a gabanta, sannan ta kuma kallona muka haɗa ido gabana ya kuma faɗuwa saboda kamanninta, muryar nan tata me baƙuwar hausa tace da ni,”zauna akan wannan”. Ta faɗi hakan tana min nuni da tum-tum ɗin da ke ƙasa gefen ƙafafunta, hannu na rawa na janyo shi na zauna ina rumtse ido, dan shi ma taushi ne da shi sai dai bai kai kamar kujerar ba. Wannan lokacinma ba da hausa ta yiwa Suhail magana ba, da yarensu ne. “taya ka san Kabir?”. Yace da ita,”zuwan da muka yi ƙasar nan a wancan shekarar, muka raka Madaki masallacin liman a ƙauyen Saye. To anan muka haɗu da shi har muka taɓa hira dan mun jima tare, kyawun hali da nagartarsa dana karanta a lokaci ɗaya yasa nayi sha’awar haɗa alaƙa ta abota da shi, hakanne yasa a wannan zuwanma na kai masa ziyara, saboda lokacin da muka baro airpot Sarkin gida ya biya damu ta gidan Liman dan isar da saƙon Me Martaba, shi ne a lokacin tahowarmu nace da Sarkin gida ya tafi kawai zamu iso, da taimakon wani yaro ɗan gidan Ladan muka sami kwatancen gidansu, dalilin da ya sa ma muka kwana acan gudun faɗan Ammi kasancewar dare yayi, Bella su ɗin mutanen ƙwarai ne domin sun karramamu ba tare da sanin su wane mu ɗin ba”. Bella ta jinjina kai sannan tace da Ya Kabiru,”na gode da karrama min jikoki da gidanku suka yi, haƙiƙa ina mutunta duk wanda ya karrama jinina, ina kuma kyautatawa agare shi, saboda haka ku saki jikinku daga yau ɗin nan acikin masarautar bichi ɓangaren Bella ku ƴan gida ne ba baƙi ba”. Ta juya ta dubi kuyangar da ke tsaye kaina sannan tace da ita,”ace Jakadiya ta haɗo musu abun sakawa a baki”. da sassarfa Kuyangar ta juya domin cika umarnin shugabarta. Bella kuma taci gaba da magana da Suhail, “kai kuma wane irin tukwici ku ka yi musu game da karramawar da suka yi muku?”

“Na faɗawa Ammi sai tace babu wani tukwicin ban girma da za’ayi musu har su kasa mantawa damu sama da ɗaukar nauyin karatun ƴaƴansu, yanzu haka zuwan nan da suka yi sun zo karɓar kayansu ne na tafiya makarantar kwana, shi kuma Kabir ta ba shi ɗaya daga cikin shagunanta dake cikin gari”. “shagon ɗauke yake da kaya?”. Ta tambaya, Suhail ya kaɗa mata kai,”a’a Bella, babban shago ne dai, zai nemi jari ya zuba”. “zancen banza kenan, mutumin da ya bawa naka makwanci, ci da sha, ba kyara ba walaƙanci ai yafi ƙarfin wannan ƙaramar kyautar a wurinka…a yau ɗin nan a nemi kaya masu kyau da inganci a zuba masa a shagon, sannan a mallaka masa maƙullin gidan Hauwa’u da yake Estate ɗin Madaki, dama na gaji da ganin gidan a haka, idan auransa ya tashi ayi min magana…yayi karatun boko?”. “ehh yayi yana da certificate na diploma akan aikin wutar lantarki”. “masha’Allah, duk da su ɗin mutanen ƙauye ne amma basu bar kansu da duhun jahilci ba, Allah yaywa iyayenku albarka…Suhail a sama masa addmission a ƙasarmu abar tunƙahona”. Ta dubi Ya Kabiru tace, “za ka iya zuwa ethopia kaci gaba da karatu?”. Kan ya bata amsa Suhail ya amshe da cewar, “ai Bella burinsa kenan yaci gaba da karatu sai dai rashin dama”. Tace, “to a mayar da gurbin addmission ɗin da Fawwaz ya samu a matsayin nasa, ina so jirginsa ya ɗaga a ƙarshen wannan watan.”

Ya Kabiru bai san sanda ya zube gwiwoyinsa ƙasa ba ya shiga jero tarin godiya gareta, Sai dai baija da nisa ba Jakadiyar da ta shigo kamar an jefota ta zube tare da dakatar da shi, “Bella tana yi ne domin Allah, bata son godiya, kayi shiru da bakinka a wurin nan idan kuma baso kake ka fuskanci wani hukuncin ba”. Ya Kabiru ya jinjina kai alamar yaji, farincikin da yake ciki na daɗa bayyana a saman fuskarsa, kamin ya kada baki yace,”tabbas duk wani me aikin alkhairi domin sarki rabba baya son godiya sai adu’a”. Aiko nan ya shiga yiwa Bella adu’oi ita kuma tana mai murmusa fuskarta da alama tana jin daɗin adu’ar.

Ta ɗau tsayin wasu daƙiƙu tana kallona ba tare dana sani ba, sai a yanzu dana bar kallo ga Ya Kabiruna na dawo da shi gareta, muka haɗa ido da ita ta sakar min siririn murmushi ni kuma nai saurin sauke kai ƙasa ina wasa da yatsuna.

Na jiyo muryarta tana cewa,”Ashraf ba dan na san duka ahalina ba, da sai nace Maryam jinina ce”. Taci gaba da kallona tana ci gaba da faɗin,”idan kayi mata duban tsanaki akwai wasu kamanni sirrantattu irin na jinina a tare da ita”. Ta sauke numfashi kana tace,”ina ma ace ke jinina ce Maryam da naji daɗi, kema kuma da kinji daɗi, za kiga gata da ƙauna daga wurina, za ki mo re jin daɗin rayuwa, tun shigowarki a kallo ɗaya naji ina sonki”. Ta dubi su Adawiyya tace, “kuma fa ina sonku, amma naji nafi son Maryam”. Ta kamo hannuna ta haɗe da nata ba tare da ta ji ƙyanƙamina ba, sannan tace,”idan har kin kammala sakandire nan da shekkara huɗu to zan tafi da ke ethopia ki ƙarasa karatunki acan…me kike son zama idan kin gama karatu?”. Ina murnushi nace, “Gwaggona tace Lauya zan zama”. “to ki dage kiyi karatu sosai sai Allah ya cika burin mahaifiyarki”. Dukanmu muka amsa da amin inda nima nace, “Bella Allah ya ƙara miki llafiya da nisan kwana”. Jin shiru banji ta amsa ba yasa na ɗago ƙwayar idona ina dubanta, wadda idonta ya karkata gefen kunnena ta ɗaga yatsa tana nuni da wajen, maganar da zata yi ta yanke a san da Jakadiya ta faɗo ɗakin tana sanar mata da cewar tayi baƙi daga Sudan. Nan Bella ta miƙe ni kuma nabi bayanta da kallo, sai dai kuma abun da na gani a bayan wuyanta ne yasa na miƙe tsaye zumbur cike da al’ajabi. Na rumtse ido na dafe goshi hoton abubuwa da dama na haskawa acikin idona.

Mun ci abincin da aka kawo mana me daɗin gaske, ban kuma ji kunya ba na juye saurana a leda in kaiwa Gwaggona da Inna Amarya. Bamu muka dawo gida ba sai magriba, cike da sha tara ta arziƙi da muka samo a wurin Ammi da Bella.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sirrin Boye 9Sirrin Boye 11 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×