Area 4, House NO2, Asokoro District, Abuja
Gida ne na gani na faɗa wanda aka narka dukiya a wajen gininsa, tun daga waje kana iya ganin Ƙaton balcony da ke fuskantar gate ɗin gidan, dogon namiji ne me cikar zati yana tsaye ne daga cikinsa da irin tsayuwa ta jaruman sojoji ya sarƙe hannayensa ta baya, jikinsa sanye da t-shirt irin ta kakin soja haɗe da baƙin wando jeans, sumar kansa ba wata mai yawa bace sai dai irin askin da ke sumar aski ne bana musulmi ba, idanunsa kewaye da siririn medical. . .