Skip to content
Part 11 of 22 in the Series Sirrin Boye by Halima Zakariyya

Area 4, House NO2, Asokoro District, Abuja

Gida ne na gani na faɗa wanda aka narka dukiya a wajen gininsa, tun daga waje kana iya ganin Ƙaton balcony da ke fuskantar gate ɗin gidan, dogon namiji ne me cikar zati yana tsaye ne daga cikinsa da irin tsayuwa ta jaruman sojoji ya sarƙe hannayensa ta baya, jikinsa sanye da t-shirt irin ta kakin soja haɗe da baƙin wando jeans, sumar kansa ba wata mai yawa bace sai dai irin askin da ke sumar aski ne bana musulmi ba, idanunsa kewaye da siririn medical glass. Farin dattijo ne kyakykyawa me kimanin shekaru 56-57, a irin tsayuwar da yay zaka ce ko an dasa shi ne a wurin, hancinsa ne kawai ke fitar da numfashi sai ƙwayar idonsa da ke kan get ɗin da yake fuskanta, a kallo ɗaya zaka yi masa ka gane yayi nisa acikin zurfin tunani. Har tsawon wucewar wasu mintuna bai motsa ba, sai a san da me gadi ya tashi ya zuge gate ɗin da ake dannawa hon da ƙarfi, bayan da farar motar ta nauso ciki sannan ya haɗe murfin idanunsa ya buɗe kana yabi motar da ido har zuwa wurin da aka tanada na ajiye motaci. Mahaifiyarsa Madam Merry tare da Matarsa Madam Gloria suka fito daga bayan motar kowannensu hannunsa riƙe da jaka da alama daga wajen wani taron suke, bayan wucewarsu ne ɗansa Joseph wanda shi yay tuƙin ya fito daga mazaunin driver shi kuma hannunsa riƙe da jarida, yayi tattaki me ɗan nisa sannan ya tsaya yana nazari, sai ya juya ya koma motar ya jefa jaridar aciki, duk abun da yake idon mahaifinsa na kansa wanda ya fahimci dalilin da yasa ya maida jaridar mota, hakan ne yasa shi ɗan murmusa kuncinsa kamin ya daɗa lumshe ido ya buɗe.

Madam Gloria ta ɗauki tsawon daƙiƙa 2 tsaye a bayansa amma sam bai san da zuwanta wurin ba, hakan yasa ta ƙara yin tattaki zuwa gabansa ta tsaya, anan ta fuskanci da gasken bai san da zuwanta ba, domin kuwa kansa a ƙasa yake idanuwansa a rufe. Tayi wani ɗan guntun tsaki na ɓacin rai sannan ta ƙara matsowa kusa da shi sosai ta ɗora hannu ɗaya saman ƙirjinsa, ta ranƙwafo da fuskarta saitin tasa, acikin harshen turanci tace da shi, “Me ya sami Jarumina?, ni ce ko kuma wani ne daga waje?”. A yanzu ne yasan da zuwanta wurin hakan yasa shi buɗe ido yana dubanta, gaba ɗaya ya ɗago kai lokaci ɗaya kuma cikin zafin nama yay wurgi da jaridar da ke hannunsa ta baya nan ta sauka a saman fuskar Joseph da ke shigowa, Joseph yasa hannu ya dafe jaridar a fuskarsa kamin ta kai ga faɗuwa ƙasa, tsoron abun da ka iya haifuwa yasa Madam Gloria saurin ja da baya, ta maida kallonta ga Joseph da ke tsaye suka haɗa ido yay mata alama da me ke faruwa, ta ɗaga masa kafaɗa na cewar bata sani ba itama. Ta marairaice fuska tayi ƙasa da murya cikin nuna damuwa ta sake cewa, “Oh Jesus Crise, Daddyn Emanuel me yayi zafi haka?, ko wani abu ka gani a jaridar da ya ɓata maka rai?”. Zuciyarsa na tafarfasa ya dubeta cikin ƙarajin murya yace da ita,”wai shin har sai zuwa yaushe ne ƙasarmu zata gyaru ne?, sai yaushe shuwagabanni za su gane al’umma amana ne a hannunsu?, har sai yaushe za su yi hani da aikata ta’addanci?, har tsawon wane lokaci za’a ɗauka kamin gwamnati ta fara martaba jami’an tsaro?, me yasa shuwagabanninmu basa tsoron Allah?”. Muryarsa ta fita acikin turancin da ya banbanta dana Matarsa, domin kuwa tamkar baturen america, yaja doguwar ajiyar zuciya sannan ya juya yay tattaki zuwa in da kujera ta ke ya zauna, ƙafarsa ɗaya kan ɗaya yana girgiza su. Madam Gloria ta ƙarasa inda yake itama ta zauna a kujerar dake kusa da shi, sannan tace da Joseph ya bata jaridar, ya miƙa mata jaridar, ya fita babu jimawa ya dawo hannunsa riƙe da glass cup da kuma kwalin exotic na pineapple, yaja ƙaramin glass table zuwa gaban mahaifinsa ya tsiyaya lemu aciki sannan ya ajiye, Dad yay masa kallo ɗaya sannan ya miƙa hannu ya ɗauki lemun yasha, ya ƙara damƙe kofin kamar zai fasa shi. Madam Gloria da ta gama karanta jaridar ta taɓe baki tana duban mijin nata tace,”sai kuma me?, wanne abu ne aciki da ya shafeka da har zai saka damuwa irin haka?”. Sai kuma taja tsaki ta ƙara cewa,”kayan haushinka yana da yawa, before duk ka ɗaga hankalina, nayi tunanin wata matsala babba ce, kawai sai kake ɗora damuwa akan mutanen da ba addininku ɗaya ba, if ace there are all chritians shi ne sai ka ɗaga hankali irin haka”. Ya kalleta yace,”baki gane rubutun da ke ciki bane?”. “na gane mana, ba magana bane akan kidnapping da akayi, to kai mene naka aciki?, akwai ɗanka ne ko kuma ɗan’uwanka?, ko kuma ance maka dani akayi garkuwa ko kuma Mama?” “take a look!”. Ya faɗi hakan yayin da yake ɗaga mata hannu da dakatarwa Kansa a ƙasa, sannan ya ɗago ya dubeta da jinjinawa rashin tausayi irin nata yace, “Addininmu bai ce muso namu ba, muƙi wanda ba namu ba…to bari kiji, da har yanzu ina kan matsayina na Major General na rantse miki da saina sadaukar da raina wajen ƙwato mutanen nan…ki kwatantawa kanki idan wani naki akai garkuwa da shi ya za kiyi? Ko da ace kuwa kina da kuɗaɗen amso shi, haka abun yake ga ahalin waɗan nan bayin Allah, su na nan hankalinsu ba’a kwance ba…saboda haka ni na ɗaukarwa kaina alƙawarin fidda dukiyar da Allah ya bani wajen ganin na ƙwato su”. Yana kai nan ya kwashi wayoyinsa ya fice ya barsu a wurin, mahaifiyarsa da ke hayowa saman benen ta bishi da ido har sanda ya shige ɗakinsa ya banko ƙofa garamm, ta girgiza kai sannan itama ta wuce balcony inda ta sami Madam Gloria tayi jugum, Joseph kuma na gefenta yana maganar cewar, “Mom ki dinga shiru da bakinki akan nuna tribalism a gaban Dad tunda baya so, hakan shi ne kwanciyar hankalinki dana kowa ma acikin gidan nan…eventhough nima ba wai son muslims nake ba, amma a ɓangaren kidnapping ina tausayin kowa musamman ace mata ne akayi garkuwan da su”. Cikin fusata ta kai hannu ta bugi bakinsa, hakan yasa shi tsuke baki yay shiru yana aikin sosa wurin. Madam Merry wadda ke tsaye daga bakin ƙofa tana kallon Joseph tace, “tashi anan wurin”. Ya taso ya tsaya a gabanta ita kuma ta kama hannunsa, sannan ta fara magana da Madam Gloria, “wannan ya zama karo na ƙarshe da za ki ƙara saka hannunki ga jikokina, na jima ina faɗa miki hakan da kike babban kuskure ne, ina tsananin son jikokina bana son abunda zai wanzar musu da ɓacin rai ko kuma abunda zai taɓa lafiyarsu.”

Madam Gloria ta ɗago kai tana duban sirikar tata tace, “Ma! Yanzu ba ki duba yanayin damuwar da nake ciki ba sai ɗan dukan da naima jikanki…ke kenan duk sanda ɗanki ya ƙunsa min kema sai kin ƙunsa min, shikenan ai”. Ta ƙarashe maganar tana tasowa ta wuce ta gabansu har tana bangaje Joseph. Ya kalli Kakarsa da damuwa yace,”Granny…”. Bai faɗi abunda zai ce ba tasa yatsa a leɓensa, “Shhhh dont stress your self kaji…indai akan banbancin addini ne Mominka ba zata taɓa sauyawa ba, saboda haka kaima kake daina zuwar mata da zancen da ya danganci hakan”. Ya ɗaga mata kai, suka maida hankali kan Kukun gida da ke sanar musu cewar Lunch is ready. Nan suka sauka ƙasa inda suka wuce dining section, har tsawon wucewar rabin awa Dad da Mom basu fito ba, dan haka sai su uku suka yi lunch ɗin, su na kammalawa kuma Joseph da Obi suka fita ɗauko Yayansu Emanuel a airpot wanda jirginsu zai sauka da ƙarfe huɗu.

*****
A ɓangaren Dad kuwa zaune yake bakin gado, yana shafa kamfutar da ke gabansa, wayarsa a gefe tayi ƙara, ya miƙa hannu ya ɗauka ba tare daya duba sunan me kiran ba, sai da ya kara a kunne daga can ɓangaren aka kira sunansa da, “Major naga kiranka ina bakin aiki shi yasa ban ɗaga ba”. Jin muryar amininsa ne yasa shi dakatawa da shafa kamfutar da yake sannan yace, “yayi kyau, nayi tsammanin ma ko kana gida kana hutawa ne”. Daga can ɓangaren Major Josiah yace da shi, “ina babu hutu ai, yanzu haka fitowarmu babu jimawa daga meeting da President”. Dad ya sauke numfashi yace, “Kuna sane kuwa da garkuwar da akayi ta mutanen da ke kan hanyarsu ta zuwa zamfara state?”. Josiah yace,”ƙwarai mun sani”. “to amma kuma babu wani mataki da za ku ɗauka akan hakan kenan?”. Daga ɓangaren Josiah shi ma nunfashin ya sauke sannan yace,”bamu da ikon ɗaukan wani mataki, saboda ko a yanzu da aka zauna meeting na miƙa wannan issue ɗin, amma shugaban ƙasa yace bai yarda da mu kai farmaki wurin ba…hasalima duk wata magana da muke kawowa akan bada tsaro ga ƙasa sai ya daƙile hakan”. “to amma zaman naku akan menene ku ka yi?”. “akan basu tsaro ne iyaka yasu bada sauran al’umma ba”. Cike da takaici Dad ya girgiza kai sannan yace,”Allah ya kyauta…yanzu abunda nake so da kai Emanuel zai dawo yau, shi ne ina so a haɗa shi da gwarazan securities da zasu raka shi amso mutanen da akayi garkuwa da su”. Josiah yace,”babu matsala, we will talk letter yanzu zan shiga office ne”. Daga haka suka yi sallama. Dad yaci gaba da scrolling ɗin hotunan waɗanda akayi garkuwa da su ta cikin kamfutar, mata sunfi maza yawa, sai dai abunda ko da yaushe yake ɗaure masa kai shi ne me yasa ba’a garkuwa da christians sai musulmai?, kuma me yasa abun kullum ke ƙarewa akan talaka?

Da dukkan hannunsa biyu ya shafi sumar kansa tare da kwanciya saman gadon fuskarsa na fuskantar POP…ya lumshe ido yayin da hoton wata rayuwa can baya ta shiga haskawa acikin idonsa.

Bichi
“goben ƙarfe nawa zaka wuce?” Baba ke maganar da Amadu wanda ke zaune a gefen mahaifin nasa. “jirgin ƙarfe bakwai zai tashi, saboda haka fitar asuba zanyi inda tsawancin kwana”. Baba ya jinjina Kai sannan ya kuma ce masa,”zaka yi kamar watanni nawa kamin ka leƙomu?”. “wallah ban sani ba Baba, a yanda nake so dai ace duk wata biyu zanke zuwa, to amma sai abunda ma’aikatar tace.” Baba ya numfasa kana yace,”shikenan Allah ubangiji yayi jagora, Allah ya tsare hanya…sai dai idan ka sauka bamu san taya zamu sani ba tunda ba waya a gidan”. Ya ɗago da kai ya dubi mahaifinsa cike da tausayawa, yana jin kamar ma yace ya fasa tafiyar, dan tun a ɗazu da suka taru su na masa nasiha sai duk jikinsa yayi sanyi, sai dai babu yanda zaiyi ya san hanyar arziƙi ce ke kiransa. “Baba karka damu dana sauka zan kira wayar Auwalu ɗan gidan Malam Ladan sai ya kawo muku, na faɗa masa zan dinga kiransa yana kawo muku har zuwa lokacin da Allah zai sa ai min albashi na siya muku wayar, ga Lukman sai ya nuna muku yanda ake sarrafata duk da shi ma ba wayewa yayi akanta ba sosai”.
Na buɗa baki nace,”tabɗi Ya Amadu Allah kam karka wani sa wannan mara mutuncin yaro ya dinƙa zuwar mana gida, gaskiya ƙwamma ba muyi wayar da kai ba indai haka ne, ranar nan fa ya gama zaginmu a waje wai ƴaƴan me faskaran icce”. Mu’azzam ya dokan tsawa da cewar, “dilla can rufewa mutane baki, manya na magana kina sako baki”. Na turo baki gaba nace,”Baba fa ya zaga”. Yana jifana da mugun kallo yace,”nace ki mana shiru ko, indai ba ki rama ba ai nasa uban ya zaga”. Inna Amarya tace, “rabu da ita dan yace Ƴaƴan Me faskare da ba ƴaƴan nasa bane?”. Nace, “to ai Inna ba iyaka nan ya tsaya ba, ni dai sai dai idan bai shigo gidan nan ba Allah saina rotsa wayar tasa dan na tsane shi”. Ban ida rufe baki ba Inna ta gwaɓe min laɓɓana, zafi yasa ni sosa wajen ina yarfe hannu.

Gwaggona wadda ke zaune daga can ƙofar ɗakinta tace da Ya Amadu, “ni dai na faɗa maka, idan kaje ka ƙara riƙe addininka karka yi wasa da shi tunda kaga dai kai ɗaya ne musulmi acikinsu karsu dulmiyar da kai, kuma kayi taka tsan-tsan dasu domin basu da amana macuta ne, ni wallahi da ace na isa da kai Amadu wannan tafiyar ba zaka yi ta ba, hanyar arziƙi ai da yawa take, baka san ta inda Allah zai kuma ɓullo maka da wata ba…shawarata ka kula da mutuncin kanka”. Ya Amadu ya dubeta yana amsawa da, “insha’Allahu Gwaggo zan yi kamar yanda kika ce”. Inna Zulai tace,”tafiya ce dai tunda ni dana haife shi na amince to sai yayi ta, babu batun wani da kin isa, ko kin isa ɗin idan nace a’a wannan isar taki bata isa ba…saboda haka ni dai ki rabar min da ɗa da wannan maganganun naki na jafa’i da kike jifansa da su, Ba komai ne ke damunki ba sai baƙinciki da arziƙin da ya same shi saboda ke Allah bai ba ki ɗa namijin da zai hidimta miki ba”. Cikin ɗaga murya Baba ya dakatar da maganarta, “Ke Zulai bana son shirmen banza, wannan wanne irin magana ce, Ke ko kunya ma ba kya ji a gaban ƴaƴanki kike wannan sokiburutsun, to ki rufe min baki tun kamin na saɓa miki, shashancin banza kawai.”
To haka dai Baba yay ta bawa Ya Amadu shawarwari da kuma nasihohi akan zaman da zaiyi idan yaje can, ya jima yana jaddada masa akan yayi ruƙo da gaskiya akan aikinsa, domin ita kaɗai ce zata ba shi nasara a aikinsa ta kuma ɗaukaka shi harta ba shi kariya, shi kuma yana amsawa da insha’Allahu, muma ƙannensa duk muka bishi da adu’a, ni dai harda guntun hawayena alokacin da Ya Amadu ya miƙe zai wuce ɗakinsu, yake cewa mu yafe shi kuma muyi masa adu’a dan ba lallai mu gana ba gobe tunda daga masallaci zai wuce, sai naji kamar yana mana sallamar ban kwana ne ba zamu ƙara ganawa da shi ba.

Sai ƙarfe kusan goma sannan kowa ya wuce ɗaki dan kwanciya, har na kwanta naji shiru shiru Adawiyya bata shigo ba, na sauko daga kan gado zan fita, Inna da ke sauya kaya tace ina zani, nace mata,”naga Adawiyya bata shigo bane”. tace min, “ki ƙyaleta kawai ba lallai uwarta yau ta barta kwana nan ba”. Nace,”a’a bari dai naje na gani, dan naji tace min kanta na ciwo ɗazu.”

Da sallama na ɗaga labulen ɗakinsu, Inna Zulai na zaune tana jina amma bata amsa min ba, na shiga daga ciki ina cewa, “Inna ina Adawiyya?”. Ta ɗago ta kalleni da masifarta tace,”uwar me za ki yi mata da wannan daren, yarinya sai shegen kinibibi irin na uwarta”. Lallai ayau na tabbatar da cewar wani na cin darajar wani, banda haka tun a furucinta kan Gwaggona a ɗazu naso na yaɓa mata magana ba ruwana da girmanta, to sai taci darajar mahaifina da kuma ɗanta da ya maida uwata tamkar ita tayi naƙudarsa. “Inna naji tace ne kanta nna ciwo shi ne nazo dubata”. Cikin ɗaga murya ta kuma cewa dani, “to da kika zo nan lafiyar za ki bata ne uwar iyayi, to lafiyarta ƙalau kwana ne dai na haramta mata shi a ɗakinku, tun itama baku asirce min ita ba kamar Amadu, saboda haka zo ki fice min a ɗaki kamin ranki ya ɓaci, idan ma barbaɗe aka turoki yi aniyarku ta biku”. Ni dai ganin haukarta na daɗa yin yawa na bar gabanta na wuce wajen shimfiɗarsu Sadiya, tabbas akwai shaƙuwa mai ƙarfi tsakanina da Adawiyya, duk da cewar sun rufe kawunansu da zanen rufa hakan baisa na kasa ganeta ba, na yaye zanen daga saman kanta, haka kawai na saki murmushi saboda kallon fuskarta da nayi, nasa hannu na taɓa goshinta naji sanyi ƙalau, sai naji daɗi a raina kenan ta rabu da ciwon kan.

A hankali na shiga tashinta ina kiran sunanta, sai da aka daɗe sannan ta amsa min, na kamo tafin hannunta nasa a nawa na riƙe, na kai bakina saitin kunnenta nace,”tashi mu tafi ɗakinmu”. Daga irin yanda take motsa idonta nasan cewar ba bacci take ba tana jina. Nasa hannu ina girgizata da salon wasa, cikin hargowa tace dani,”dilla Malama ni ki ƙyaleni”. Sai na ɗanyi dariya na daɗa girgizata ina cewa, “to ki tashi mu tafi saina ƙyaleki, ai kan naki ya daina ciwo, kin san dai ba zan iya bacci ba kya kusa dani ba”. Taja tsaki ta juya kwanciyarta tana cewa, “Ni dama ba wani ciwon kai da nake…kuma idan ba ki kwana tare dani ba ki mutu, kinga ma wallahi idan ba ki rabu dani ba zan tashi na shaƙeki har sai kin bar numfashi, ko lallai ne saina kwana a ɗakin uwar kareren naki.”

Sosai naji ba daɗin kalamanta, na saki baki ina duban gefen fuskarta da mamaki, ban san me nayi mata ba yau, dan tun bayan dawowarmu daga masarautar bichi ta sauya min, ko magana nayi mata bata amsa min sai dai tayi ta jan tsaki, dana lura da wannan ne ma na tambayeta menene tace min kanta ke ciwo, ashe ba hakan bane, to ko dai nayi mata wani laifin ban sani ba?, tun tasowarmu wani abu bai taɓa shiga tsakaninmu ba akan rigima, dan faɗanmu ma na wasa ne, ko abinci ɗazu ma da aka zuba mana raba mana tayi kowa yaci nasa, bayan bamu taɓa cin abinci daban ni da ita ba, ko da an zuba mana idan ɗaya baya nan to sai ɗaya ya jira ɗaya, dalilin da yasa ma Baba wani lokacin ka kiramu da tagwaye. Na kuma kamo hannunta nace, “Adawiyya wani abun nayi miki?”. Sai ta fizge taja tsaki tana daɗa rufe kanta da zane, na miƙe na fita jiki a saɓule, Inna Zulai ma da nake mata sai da safe ci kanki bata ce min ba.

Shigata ɗakin Inna tace, “kije Gwaggonki na kiranki, idan kin dawo karki manta ki rufe mana ƙofa bacci zai iya ɗaukeni kamin ki dawo”. Na amsa da to sannan na nufa ɗakin Gwaggona, ina shiga na tarar da ita ta gama wanke allo, na zauna gefanta kamar mara lafiya, zuciyata cike fal da tunanin laifin da nayiwa Adawiyya wanda ban san shi ba. Bayan Gwaggo ta gama bawa Basma rubutu sannan nima ta miƙo min sai aikin kauda fuskarta take daga gareni, na miƙa hannu na amsa nayi bismillah sannan na kafa baki na sha kaɗan, ina ajiyewa ta jefeni da wawan kallo, “ɗauki ki ƙarasa shanye shi”. Ba shiri na ɗauka na rumtse ido kace maɗaci aka bani, ina kuma shanyewa kawai sai na fashe da kuka ina kifa kai da gwiwa. “me aka yi miki kuma?, idan har akan rubutun nanne to kuwa tabbas yau zan fara sa miki waya ajiki”. Nai saurin girgiza mata kai ina cewa,”a’a Gwaggo ba rubutu bane, Adawiyya ce take jin haushina ko magana bata son yi min.”

Gwaggo taja guntun tsaki ta miƙe tana nufar gadon ta da cewa, “a halinki na rashin kyautawa kika yi mata wani abun.”

Nace,”Allah Gwaggo ni ba abunda nayi mata”. Ta ɗan murmusa sannan tace, “to ni yanzu me kike so nayi miki, faɗanku ne dai wanda ya shiga tsakani kunya kuke ba shi…kuma wata ƙila saboda faɗan da Malam yaywa Uwarta ne take tayata kishi”. “a’a Gwaggo tunfa dawowarmu a ɗazu ne”. Bayan ta kwanta tace, “to kin gani kuwa dole kin mata wani abun, ai shariya ba halinta bane, ke kuma halinki sai ke…ki kwana anan ba sai kin koma ɗakin Innarki ba”. Na miƙe kamar wadda ƙwai ya fashewa aciki na hau kan gadon, sai da na maƙalƙale Gwaggona sannan na samu bacci ya ɗaukeni sakamakon faɗuwar gaba da naji ya tsananta garen.

Can cikin dare na farka dan gabatar da sallar dare wadda a yanzu ta zame min jiki, idan ban riga Gwaggona tashi ba to ita zata rigani, dama ita kusan kullum cikin raya dare take, na murza idona dan wartsakar da baccin da ke cikinsa sannan na zuro ƙafata na ɗan ƙaro hasken fitila. A tunanina Gwaggona ce ke sallah sai da na ƙaro hasken fitila na ganta kwance tana bacci. Na ƙaro hasken fitilar sosai sannan na kai dubana ga Kulu wadda ta ɗaga hannaye sama tana roƙon ubangijinta, na zuba mata ido sosai kamin nayi la’akari da kukan da takeyi, kana iya jiyo kalamanta da take cikin yarenta, da sautin muryar kuka da ke neman cin ƙarfinta, tun muryar nata na fita a hankali har ta bayyana sose inda nake jiyo maganganun nata raɗau ba tare da sanin me take cewa ba tunda bada yaren da nake ji bane, hawaye gaba ɗaya ya wanke mata fuska, Fatarta ta koma ja. A hankali kuma sautin kukanta da na muryarta ya ragu, ta kifa fuska a tafukan hannunta tana mai ci gaba da kuka a hankali. Tsananin tausayinta ya kamani, nasa hannu na goge hawayen da nima suka sauko min, Lallai a duniya babu marasa tausayi irin iyayen Kulu, babu abunda zuciyata ta ƙissima min akan wannan kukan nata face rashin iyayenta, waɗanda suka manta da ita da rayuwarta tun tsawon shekarun da naji Ya Amadu ya labarta min.

Na sauka daga saman gadon cike da tausayi da jin ƙanta na isa gabanta, nasa hannu na ɗago da fuskarta, na sanya ƙwayar idona cikin nata wanda haskensa ya cika min idanu, lokaci ɗaya ruwan hawayen da ya kuma saukowa daga idonta nima ya sauka a nawa, nasa hannu na goge mata, ban ankara ba naji ta rungumoni jikinta ta matseni tsam a ƙirjinta har ina iya jiyo bugun zuciyarta.

<< Sirrin Boye 10Sirrin Boye 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×