Muna buɗa ledar wani daddaɗan ƙamshi ya bugi hancinmu, na fito da kwalin da ke ciki wanda aka nannaɗe shi da abun ado, Adawiyya ta karɓa daga hannuna ta shiga kiciniyar buɗe shi amma saboda irin naɗin da aka masa ta gagara kuncewa. "kinga ki bari Ya Kabiru ya dawo ya buɗe mana.
"Bata saurareni ba taci gaba da ƙoƙarin yanke abun da reza, na tashi na fita daga ɗakin ina ce mata, "ni dai idan kin buɗe kin gama gani kya kawo min ɗaki." Gaba ɗaya ma na manta da. . .