Skip to content
Part 14 of 22 in the Series Sirrin Boye by Halima Zakariyya

Muna buɗa ledar wani daddaɗan ƙamshi ya bugi hancinmu, na fito da kwalin da ke ciki wanda aka nannaɗe shi da abun ado, Adawiyya ta karɓa daga hannuna ta shiga kiciniyar buɗe shi amma saboda irin naɗin da aka masa ta gagara kuncewa. “kinga ki bari Ya Kabiru ya dawo ya buɗe mana.

“Bata saurareni ba taci gaba da ƙoƙarin yanke abun da reza, na tashi na fita daga ɗakin ina ce mata, “ni dai idan kin buɗe kin gama gani kya kawo min ɗaki.” Gaba ɗaya ma na manta da babin wata Kulu, sai da na shigo ɗakin naga ta tsareni da ido. Na turo baki na wuce na zauna ina cewa, “ai kin fara magana dan haka idan ba za ki min magana da baki ba to ki bar kafeni da wannan manyan idanun na ki masu firgitarwa.”

Naci gaba da abin da nake yi, ihun Adawiyya da ya karaɗe gidan shi yasa ni tashi na fita da gudu, cirko-cirko na samesu bakin ƙofar ɗakinsu Mu’azzamu sai Inna Zulai da ke cikin ɗakin tana watsa ruwa a wutar da ta kama a ɗakin, na zaro ido waje wanda tashin hankali ya cika cikinsu na dubi Adawiyya da ke aikin yarfe hannu nace da ita, “garin ya haka?”

Bata bani amsa ba sai Habiba ce tace,”ina ga fa fitila ce ta suɓuce daga hannunta ta fashe, ƙila kuma da kaya kusa da wurin ta kama bata sani ba.” “Allah ya kiyaye gaba.” Na faɗa ina riƙe yatsan Adawiyya da ta ƙone ina mata tofi, ta rungumeni tare da fashewa da kuka tana bani haƙuri, haƙurin da ban san na menene ba har sai da ta ce min ledar kayan da Bella ta bani ce ta ƙone.

Har raina naji babu daɗi sai dai to ya zanyi tsautsayi ne, saboda haka ma ban tsaya jin ba’asin Kyautar mene aciki ba sai dai da Gwaggo ta dawo na faɗa mata, tace to ai babu komai ba rabo bane ita kuma Bella an gode mata.

Hankalin kowa a gidanmu bai gama kwanciya ba sai da Auwalu yazo yace sunyi waya da Ya Amadu yace sun sauka lafiya, idan ya sauka a masaukinsa zai kira, Nan Baba yayma Auwalu godiya da ƙoƙarinsa.

Bayan anyi sallar magriba Ya Kabiru yace nazo na raka shi unguwa, Inna Amarya tana tayi masa tsiyar wai ko taɗi zan rakashi, shi dai murmushi kawai yay bai ce komai ba, ya kama hannuna muka fita, wani shagon kayan kwalliya muka je ya siya min ɗan kunne da turare, akan hanyarmu ta dawo sai dana sa ya siya min tsire tukunna muka ɗauki hanyar gida. “idan kin aje kayan kizo.”

Yace dani san da muka shigo zaure. Ina shiga na bawa Gwaggo kayan nace ta ajiye min kuma kar aci min tsire, tace na dawo na ɗauki kayana ita bata amsar kayan kashedi, ina ƴar dariya na wuce ina cewa, “ni dai na bada kuma na faɗa kar aci min tsire.”

Na fita fuskana ɗauke da dariya sosai saboda mitar da naji Gwaggona nayi wai tasan saboda Basma nake kora wannan kashedin.

Da sallamata na shiga ɗakinsu Ya Kabiru, yana zaune kan yaloluwar katifarsa da littafi a hannunsa, haka yake shi sam baya gajiya da duba takarda. Na ƙarasa kusa da shi na zauna na sarƙafe hannayenmu sannan na ɗora kaina bisa kafaɗarsa. “Yaya wai baka gajiya da duba takarda ne?”

Ya rufe littafin yana ce min,”lokaci ne Mairo kema soon za ki zama irina tun da ba kya wasa da karatu.” Ya faɗi hakan yana shafa kumatuna. “Yaya ɗazu Suhail yazo baka nan.” “ehh munyi waya da shi yake faɗa min.” “yana da kirki sosai…yauwa ka kalla ma Bella ta bada kyauta a kawo min.”

Ya muskuta yana gyara zama yace, “ahh ke dai akwaiki da farin jini, Allah ya haɗa jininku da Bella, to shi ne kuma ba za’a nuna min kyautar ba.” “Ta ƙone.” Ya kalleni ta gefen ido sannan yace,”kaman ya ta ƙone?”

“Tsautsayi, Adawiyya ta ɗauko fitila ta suɓuce ta faɗi kuma a kusa da ledar, kamin ta ɗebo ruwa ledar ta kama gaba ɗaya.” Shirun da yay yasa na ɗago na dube shi, kamin nayi magana ya tari numfashina da cewar, “wannan ai shashancin banza ne.” Ganin zaiyi faɗa na hau ba shi haƙuri.
Ya sarƙafe yatsun hannunmu wuri guda yana ce min,”Mairo nah”. “na’am Ya Kabiru nah.”

“Do you know what i want from you?” Tuni na ɗauke tambayar da yayi min cikin harshen turanci, kasancewar tun da akace zamu tafi makaranta yana zaunar damu ya koya mana kalmomin turanci, kuma ina ganewa sosai dan a makarantarmu ba wani turanci ake mana ba malamai sunfi yin hausa wai saboda makarantar gwamnati ce. Na gyaɗa masa kai, “No Yaya sai ka faɗa”. Ya gyara zamansa in da ya fuskantoni, yasa hannu ya ɗago haɓata, ya umarce ni akan in sanya ƙwayar idona cikin nasa.

Murmushin fuskana yaƙi ɗaukewa a sa’ilin da ƙwayar idona ta sarƙafe cikin tasa, kallona yake babu ko ƙiftawa ya ce,”ki kula min da kanki a makaranta dan Allah, banda shirmen banza da ƙawaye, Karatu ya kai ki dan haka shi kawai za ki yi, ki dage ki zama mai ƙoƙari abar kwatance a wurin Malamai…sannan ban lamunce miki ba dai-dai da ranar ɗaya Suhail yaje makarantar ya buƙaci ganinki kije, bar ganin su ne silarku a makarantar, wallahi naji labari sai ranki ya ɓaci fiye da tsammaninki, karki ga bana ƙasar kiyi tunanin ba zan sani ba…zuciyata zata ke sanar min halin da kike ciki da dukkan abunda kike aikatawa…kuma ki tabbata in har kika wuce ta ɗaya a aji to la shakka zamu yi hannun riga da ke.”

Na gyaɗa masa kai nace, “insha’Allahu Ya Kabiru zan zama mai kiyaye dukkan umarninka.” Na faɗa ina ƙoƙarin maida ƙwallar da ta taru a idona. Ya ɗauko wani zobe a aljihunsa fari mai kyau ya saka min, sannan yace na tashi naje na kwanta da wuri kar azo tafiya gobe bacci bai isheni ba. Ina shiga na tarar kowa na zaune yana cin abinci, yau an makara acin abincin dare kasancewar Inna Amarya ke da girki kuma yau sunje unguwa basu dawo ba sai gabanin magariba. Na wuce na zauna kusa da Adawiyya ina cewa, “lallai ma ke ɗinnan, to kinci rabonki.”

Fuskar nan tata a haɗe ta galla min harara ta ɗauke kwanon abincin ta juya min baya, idan nayi amfani da hankalina har yanzu dai bata bar fushi dani ba, saboda haka na miƙe naje nace da Inna Amarya ina nawa abincin, tace na tambayi Adawiyya ai haɗe mana tayi, kamar ba zan tambayeta ba kuma sai nace da Basma ta tambayo min ita aina ta aje min nawa.

“Ta duba ɗakin girki yana murfin tukunya.” Abin da tace da Basma kenan a ƙufule. Na shiga na ɗauko, abincin ma naji duk ya fita akaina dan haka na tashi daga kansa na fita na bawa almajirai, dan har ga Allah ni bana jin daɗin cin abincin ba tare da ita ba.

A ɗaki na sami Gwaggo zaune tana sauraran radio, na tambayeta “Gwaggo ina ajiyata?” Tace, “na bawa Innarki.” Na wuce ɗakin Inna tana lazimi ta min nuni da inda ta ajiye naje na ɗauka, Basma tazo ta ƙaraci nacin zamanta na hanata ko ɗanɗane nace wallah bata ci.

Sai dai tun a yankan farko dana saka a bakina cikina ya ƙulle, ina gama ci kuma sai amai kamar zan amayar da kayan cikina, numfashina ya fara neman sarƙewa, tari yaci ƙarfina babu ƙaƙƙautawa cikin ƙanƙanen lokaci na fita hayyacina. Inna Amarya ta sallame daga lazimin tayo kaina cikin salati da kiɗima, ta shiga ƙwalawa Gwaggo kira itama tazo, ganin abun dai ba me ƙarewa bane Ya Kabiru ya bawa lukman yace yaje chemist ya karɓo maganin amai, babu jimawa sai gashi ya dawo, ba zan iya haɗiya ba saboda halin ha’ula’in da nake ciki, sai Inna Amarya ce ta jiƙa da ruwa kaɗan Gwaggo ta buɗe bakina aka tsiyaye min ya wuce da ƙyar, duk da jiƙe-jiƙen magungunan da Gwaggo keyi tana bani ina sha, da tarkacen magungunan asibiti da Ya Mu’azzamu ya ɗebo, amma abu babu sauƙi sai a wurin Allah dan abu sai gaba yake daɗa yi.

Baba duk ya rikice ya rasa abun yi, sai can da ya saita hankalinsa ne yay tunanin yi min tofi, haka Baba ya dinga tofin adu’a ana bani ina kwankwaɗewa.

Ya Kabiru na sassarfa ya fita ya kira Ado me chemist anan kusa damu, yana zuwa ya duba ni yaga mawuyacin halin da nake ciki, nan ya shawarci Baba akan a tafi asibiti kawai, Baba ya amsa masa da “to” ya kuma yi masa godiya dan yayi min allurar tsaida amai yace a bar kuɗin. Kowa yay jigum ana jiran ganin ikon Allah akan allurar da aka min, amma ina amai yace bai san wannan ba, ciwon ciki ma haka, kuka nake kawai ina kiran mutuwa zanyi, ina kiran a yafe min, furucina yasa jikin kowa yay sanyi, tashin hankali ya ƙara bayyana a fuskonin kowa.
Gwaggo kuwa kuka kawai ta ke tana riƙe dani ajikinta, ni dai na tabbata a yanzu babu abin da ya rage acikina illa kayan ciki, amma abinci da ruwa kam babu su, dan a yanzu haka idan nayi kakarin aman sai dai na tofar da jini, hankalin kowa ya daɗa tashi, ƴan’uwana duk kuka suke su na ta jera min sannu.

Ya Kabiru yace da Baba, “Baba mu wuce asibitin tun da kaga babu sauƙi.” Baba wanda damuwa ta bayyana ɓaro-ɓaro a fuskarsa, yay shiru bai ce komai ba, Inna Zulai da ke shafa min ruwa ajiki saboda zafin zazzaɓi ta ɗago ta dube shi tace, “Malam kayi shiru, halin da ta-ke ciki fa yafi kamata da asibitin.”

Baba kamar zaiyi kuka yace, “ku kun san halin da ake ciki, asibiti wajen kashe kuɗi ne masu yawa, a yanzu kuwa idan muje wa zai bamu? Aina zamu samo? Ni da ban ajiye ba ban bawa wani ajiya ba, yanzu haka babu ko kuɗin mota ajikina…dan haka mu zubawa sarautar Allah ido insha’Allahu sauƙi zai sauka gareta.”

Sunusi yace da Baba, “to ai Baba ba asibitin kuɗi za’aje ba, na gwamnati zamu.” Baba yay murmushi mai ciwo sannan yace, “Sunusu ina nusar da ku ne ku gane ko munga likita kyauta akwai kuɗin magani, ko shi ma maganin kyauta zasu bamu?” Shiru ya ratsa biyo bayan tambayar Baba, can Ya Kabiru ya laluba aljihunsa yace, “Baba muje ga ɗari biyar ajikina zata ishemu zuwa asibiti, magani kuma ko ba’a siya duka ba sai a nemi mai muhimmanci ciki a siya.”

Baba yana dubansa yace, “kana dana siyan magani kenan?” “Allah zai kawo Baba.” Gwaggo na gefe tana goge hawaye tace da shi,” Kabiru jeka da sauri samo mota, kaga numfashinta neman ɗaukewa yake gaba ɗaya.” Ya fita jiki na sassarfa jikinsa gaba ɗaya ya wanke da zufa, yana fitowa ƙofar ɗaki kuma yay karo da Kulu a tsaye tana kuka. Ya tsaya yana dubanta da kuɗin da ke hannunta, kuɗaɗen da bana ƙasar nan bane, yaja numfashi ya sauke, kamar zai ce da ita wani abun sai kuma ya wuce kawai, ta bi bayansa da ido a san da hawaye ke daɗa sauka saman fuskarta, sannan ta koma ɗaki taci gaba da ruzgar kukanta tare da nemawa Mairo sauƙi a wurin mahallicinta.

Babu jimawa Kabiru ya dawo da mai adaidaita, yana shigowa ya kinkimi Mairo wadda ta jima da sumewa, an watsa ruwa an watsa amma babu alamar zata farfaɗo. saboda a sami sauƙin kuɗin mota Malam yace Inna Amarya da Adawiyya ne kawai zasu je asibitin, Gwaggo dai taso da ita aka tafi, sai dai babu yanda zatayi dole tayi alkunya, kuma bata da haufi akan kulawar da Inna Amarya zata bawa Mairo kamar yanda zata bata.

Inna Zulai ta tattaro wasu ƴan canjikanta na saida mafici ta bawa Malam tace a haɗa da su, Malam ya karɓa ya baiwa Kabiru yace ya haɗa dana wurinsa.

Da zuwansu cikin ikon Allah suka sami ganin likita har aka basu gado, ɓangaren Gwaggo hankalinta yay ƙololuwar tashi da jin zancen, tace zata nemi kuɗi ta taho a yanzu Baba yace a’a ta zauna ai jikin da sauƙi tun da harta farfaɗo daga suman an kuma yi mata allurai bacci ya ɗauketa. A ɓangaren Malam kuwa faɗa ya sha shi a wajen likitoci, na ɓata lokacin da akai wajen kawota, har suke ce masa da sun ƙara wasu lokuta sai dai su kawo gawarta, sun kuma shaida masa a duk iya binciken da suka yi basu gano wani ciwo a cikin nata ba ko kuma wani abu da ya kawo sanadin hakan, sai dai sunyi ƙoƙarinsu wajen ganin sun bata taimakon da zai tsaida aman da shi ciwon da take ji idan ta farka.

An rubuta allurai da magunguna masu tsadar gaske wanda akai umarni da a gaggauta wajen siyo su, Baba yay shiru domin ba shi da ta cewa, dama tun farko abunda ya ke ji kenan, idan sun gudarwa asibitin kuɗi, nan ma fa ba komai ne zasu yi musu a kyauta ba. Yana tsaye ya zubawa Mairo ido, wadda fuskarta tayi muguwar rama kamar wacce ta shekara guda a kwance cikin ciwo.

Tausayin kansa dana iyalinsa ya daɗa kama shi, ya maida dubansa ga Kabiru wanda yasa kai zai fita cikin mutuwar jiki, ya dakatar da shi daga tafiyar da cewa, “Ban amince maka da rancen kuɗin kowa ba Kabiru, idan kuwa kai hakan to bada yawuna ba wallahi, kuma fushina zai tabbata akanka.”

Kabiru ba shi da tacewa saboda haka dole ya dawo ciki ya zauna, Inna Amarya tasa hannu ta goge hawayen da ya sakko mata, “To Malam ko can gida zaka kira a ɗebi samiruna akaiwa Matar liman ta siya.”

Malam ya girgiza kai yace, “babu abunda za’a siyar, mu jira ruwan da aka saka mata ya ƙare, insha’Allahu lafiya ƙalau zata farka.”
Har ruwan da aka sakawa Mairo ya ƙare bata farka ba, ma’aikaciyar jinyar tazo ta ƙare jarabarta ta tafi babu wanda ya tankata, dan tun a ɗazu take zuwa tana tambayarsu alluran da akace a siyo su na cewa tukunna dai kamin ruwan ya ƙare, ga shi har ruwan ya ƙare shiru.

Wata mata da ke kusa da gadonsu itama tana jinyar yaronta ta taso tazo kusa da Inna Amarya tayi musu ya mai jiki, Amarya ta amsa da Alhamdulillahi. Sannan matar ta dubi Malam tace da shi,” ku ƙara haƙuri nan da ƙarfe tara da rabi akwai wanda yake taimakawa marasa lafiya a wajen sayan magani da abubuwan dai da asibiti suka buƙata…su na yin abin nasu cikin tsari ne zasu bi gado gado har sai an biyawa kowa buƙatarsa.” Kabiru ya duba agogo yaga lokacin har tara da rabi saura minti goma, saboda haka suka fasa tafiyar da Malam yace ayi suka ƙara jira.

Tara da Rabi dai-dai kuwa sai ga wasu maza sun shigo su biyar jikinsu da rigunan aikin asibiti, sai mata biyu dake biye da su, ɗaya dattijuwa ɗaya tsohuwa. Madam Merry da Madam Gloria kenan, daga kan gadon su Mairo aka fara amsar katin, Madam Merry ta karɓi katin daga hannun Kabiru ta saka hannu sannan tace ya wuce can wajen karɓo magani ya amso, a haka suka dinga zagaye gado zuwa gado har sai da ta tabbatar ta saka hannu akan katin kowa sannan suka bar ɗakin, masu zaman jinya suka rakata da godiya da kum adu’a.

1:00pm
Agogo ya buga ɗaya na dare, A hankali na shiga buɗe idanuna waɗanda naji sun matuƙar yi min nauyi saboda kukan dana sha, ko’ina na jikina ciwo yake saboda tsananin galabaitar da nayi, bin ko’ina nake da kallo da son tantance a inda nake dan ban fidda tsammanin na mutu ba.

Ina kallon gefen haguna Adawiyya ce ta kwantar da kanta kusa dani, hannunta cikin nawa ta riƙe gam, sai Inna Amarya da ke shimfiɗe a ƙasa da gani bata ji daɗin kwanciyar ba. Na maido idona ga hannun damana inda Ya Kabiru ke tsaye a kaina ya jingina da bango, da alama tsumayin farkawata yake dan ina ɗaga kai muka haɗa ido da shi, ya kuwa sauke wata wawiyar ajiyar zuciya tare da lumshe ido sannan ya buɗe. “Sannu”. Ya faɗa a san da yake taimaka min wajen tashi zaune. “ina ne yake miki ciwo yanzu?”

Ya tambayeni yana duban yanda nake aikin cije fuska. Nayi masa nuni da cikina, “Ya cikina ne wani abu ke yawo yana karta min farcensa.” Yay gajeran murmushi tare da cewar, “yunwa ce.” Na girgiza masa kai cikin ƙarfin hali nace, “Ya wallahi ba yunwa bace, yawo yake yi ta ko’ina fa…zafi sosai.” Yay ɗan jim yana dubana da nazari kana yace, “ko lokacin al’adarki ne yayi?” Na kuma girgiza masa kai, “a’a Ya ai a farkon wata nake yi.”

“To ƙila an sami sauyin yanayi ne, sannu bari kici abinci sai kisha magani za ki ji sauƙi kinji Mairon Yayanta.” Na buɗa idona da ya cika da ruwan hawaye saboda irin azabar da nake ji na kalle shi, ina fashewa da kuka nace, “Ya ciwo sosai, zafi yake min, ina jin kamar ana tsatstsagani da reza ne”. Ya matso kusa ya kwantar da kaina saman ƙirjinsa yace, “yi haƙuri zai daina kinji.”

<< Sirrin Boye 13Sirrin Boye 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×