Skip to content
Part 16 of 22 in the Series Sirrin Boye by Halima Zakariyya

To babu yanda dai Baba ya iya, dan bin umarnin Yagana dole in har ana son kwanciyar hankali, sannan kuma Baba yana neman albarka.

Ta yunƙura ta miƙe Sannan tace da Ya Kabiru,

“Tashi muje ka rakani kamin lokacin tafiyar ta ku yayi” Yace da ita,”A’a fa Yagana ki kama hanya ki tafiyarki ke ɗaya kawai, ni da zan kai yara makaranta, yaushe muka je muka dawo har na shirya”

“To amma dai naga ai da sauran lokaci tafiyar, yanzu ne fa zamu dawo ba zama za muyi ba…ina so ne a haɗa har kai da Amadu na amso muku na farin jinin ƴan mata ko Allah yasa a dace” Ta faɗi hakan tana ƙunshe dariyarta. Nace da ita,”abun ai ba rashin farin jini bane kije ki duba kiga irin tururuwar da ake akan su”.

Ya Kabiru ya kalleni yace,”barta ni tuni ina da matata a hannu, dan haka ta riƙe taimakonta Amadun ma baya so”. Ta doki cinya tayi bakin ƙofa tana faɗin,”kwayi da wata”. Ta fice tana cewa su Gwaggo sai ta dawo, su ka rakata da adawo lafiya.

Tana nufar zaure tana jaddadawa Gwaggo a jiƙa min tagarzaje na sha, shi ma ance yana maganin mayu, kamin dai Allah yasa taje ta dawo ɗin. Ya Kabiru na bin ta a baya yace,”ke dai a dawo lapia…zancen tagarzaje kam ba zata sha ba haka kawai ya kuma hargitsa mata ciki…mu magani in dai ba Nafdac bama sha.”

Ta tsaya sololo tana dubansa tace,”shi kuma Naufdak ɗin mene?”. Yace,”ba ki san shi ba”. a ƙufule tace,”saboda ban sani ba ɗin ai na tambayeka, Allah sa kuma ba zagina kayi da harshen nasara ba…daɗin Amadu kenan shi magana bata dame shi ba balle har ya faɗa maka ba daɗi”

Ya Kabiru ya girgiza kai,”to ni yanzu Yagana me nace acikin maganata mara daɗi”. “yo gashi kuwa ina cewa a bawa yarinya maganin da zai taimaketa kana ce min ba za’a bayar ba…to ka tambaya Uwar zoman da ta karɓi haihuwarka ko Uwarka Allah ya jiƙan rai sai da ta sha tagarzaje kamin ta sulluɓoka, ah to kuma bata mutu ba a lokacin sai da ta haifi biyu bayanka.”

Bai ƙara cewa da ita komai ba ya wuceta zuwa ɗakinsu. Mu na jiyota a zaure ita da Auwalu wanda ya kawo waya Ya Amadu ya kira, ya bata wayar su gaisa tana ce masa a’a ita ba sai sun gaisa ba sauri take akwai in da zata je me muhimmanci, a dai ce tana gaishe shi, kuma dan Allah kar ya manta ya turo mata sallahun manja da ta ba shi. abun takaicin manjan ma kwalba biyu ne, wai ƙawarta ta faɗa mata ɗanta da yake zuwa lagos yace acan akwai ragin ɗari a kowacce kwalba akan yanda ake siyarwa anan, haushi ya cika Lukman yace da ita.

“Idan ba ki cika ɗari biyu kin siya anan ba kya kuma biyan kuɗin manjan gaba ɗaya a kuɗin mota.” bata dai ce da shi komai ba tai gaba tana zikiri.

Sai da kowa ya gama gaisawa da Ya Amadu sannan na karɓa, yay min sannu da jiki sannan yace na kaiwa Gwaggo wayar, tana ɗaki tana aikin mai da kayana ƙasan gado na miƙa mata wayar, kamar ba zata amsa ba sai kuma ta karɓa tana amsa sallamarsa aciki ciki, da tana tsakar gida ne a zaune, amma tun da taji maganar Auwalu yana cewa Amadu ne ya kira ta tashi tayo ɗaki, sai kuma tayi rashin sa’ar gashi na biyota da ita, kuma na saka a handsfree.

“To ya wajen na ku?” Ta tambaya shi kamar wadda akaiwa dole, ko da yake dolen akai mata. shi ma da ya gane yanayin muryar tata acikin sanyin murya yace “lafiya lau, yauma na fara zuwa aiki, kuma Alhamdulillah wurin yana da kyau…ga ogan ba shi da wata matsala, yanzu haka ma ya bani dubu hamsin yace na siyi kayan abinci da abubuwan da zan buƙata, albashina kuma duk wata za’a ke bani dubu ɗari…insha’Allahu gobe zan buɗe account zan turo dubu ashirin da biyar sai a siyi kayan buƙatar gida.”

“To Allah ya shi albarka…ya yanayin ibadarka a wurin tun da ance babu musulmai?”

“Gwaggo ai babu wani banbancin addini a wurin, sallolina duk nayi su a office ɗina.” “to yayi kyau a dai ƙara kulawa.” ya amsa da, “insha’Allahu” sannan ya ɗora da cewa,”cikin kuɗin Gwaggo sai a bawa Mu’azzam dubu biyar ya sai waya a hutar da Auwalu haka…Kabiru ma ashe ya gyaro tasa ban sani ba sai yanzu yake faɗan.” “umm ya gyaro jiya, shi ma ai tafiyar tasa ta matso kusa sun ce jibi zai wuce…sun gama yi masa komai na tafiya jiya ma ya amso tikitin jirgin”. Ya Amadu yace,”haka yake faɗa min…ai nace da Baba ya daure yaje masarautar da kansa yayi musu godiya.”

Gwaggo tace, “nima na faɗa masa sai yace ai niyya suka yi ba shi ya roƙa ba, baya son yaje a fara cewa yana zuwa maula…to ɗazu dai Yagana ta masa magana yace zai je bayan tafiyar Yaran nan.” shiru kamar babu me kuma cewa komai sai Gwaggo ta numfasa tace da shi,”ni dai dan Allah ka dinƙa kulawa da arna nan Amadu…Allah yi muku abarka sai anjima.”

Bayan duk mun gama shiryawa Inna Zulai ta aikemu gidan ƙawarta da za’ai bikin ƴarta, ta sai mifitai dozin biyar da za’ai rabon kamu. ta gargaɗemu sosai akan karmu zauna Kabiru ya shiga wanka kuma shi shirinsa ba mai wuya bane. mu na kan hanyar dawowa muka ga Malam Liman, har ƙasa muka duƙa muka kwashi gaisuwa da neman tabaraki.

“Mairo dai ƙara girma ake gashi nan har kin gama taddo Yayar taki”. mu kai murmushi bamu ce komai ba, sai ya ƙara cewa,”Malam Adamu kam ai ya kamata yanzu kuma ya karkata hankalinsa kanku…ku ƙarasa gida Allah yay muku albarka”. can mun yi nisa Adawiyya ta kwaɗa uban tsaki tace,”Allah Mairo kina baƙantan rai”. ta faɗa cike da zafi. ban dubeta ba naci gaba da jan karana ina tafiya nace da ita,”yi haƙuri to…amma dai ma me nayi miki?”

A yanzu dana ɗaga kai na kalleta sai naga ta zabgeni da uwar harara, ta nuna ni sama da ƙasa da hannu kana ta kuma cewa,”dan Allah dube ki…Wai ke sai yaushe za ki sauya ne, duk san da za’a fita ba ruwanki da wani gyara jiki ke kawai ki fita a harbutse, haba dan Allah kinfa girma yanzu, ki fara cin ganiyar ƴan matancinki kuma”. taja tsakin takaici, “shi yasa ai har yanzu gaki nan kin gagara yin saurayi, ba me kawo miki sile da sunan kyauta…su ma mazan ƙauyen fa sunfi son mace ƴar gayu, ke ba ki kalla yanda samari suke rawar jiki akan Sadiya da Habiba bane.

Amma ke kullum jiki ba man arziƙi balle ƴar hoda ko jambaki, a’a ke kawai ki fita zaro zaro kamar tsohuwar bazawara in dai za ki je ki biya buƙatr kanki shikenan, kina tafe sangalolo babu rangwaɗa babu ɗan karya ƙugu, alhalin ke jiki ba jiki ba kamar sillan kara, gaba a shafe baya a shafe”. na kalleta na harareta nace,”wallahi ƙarya kike kice ta ko’ina a shafe nake, ai ba ki leƙa ƙirjin kin gani ba.”

Ta kawo min duka da karan da ke hannunta, har yanzu kuma bata saki fuska ba. “ni Allah maganar gaskiya nake miki ba wasa ba, bi ki san irin kishin da nake ba idan naga ana zuwa zance wurina ke banda ke, kar ki buɗa zuciyata kiga irin damuwar dake ciki tun ace naga samari na kawo min kayayyaki ke kuwa sai wanda aka sai miki a gida… ko me baƙin jini ai sai haka, ki fita babu me kulaki sannan a gida ma babu me zuwa wurinki, sai kace wadda aka yiwa asiri da mujiya…kina biye maganar Yagana tana hure miki kunne da cewar ke matar manya ce.

To matan manya ai sai waɗanda su ka fito daga babban gida, ke kuwa ba ƴar kowa ba…to Allah ki gyara haka, in dai ba so kike mu kuma yin faɗa ba, kina dai jin abunda Baba yace ko ba muyi candy ba mijin aure yazo aurarmu zai yi.”

Na dakatar da zancenta da cewa,”kinga maida wuƙar ki daina ɓacin rai, kishin samari akaina kiyi fatali da shi…dan in faɗa miki maganar gaskiya burin rayuwar Mairo bata gina ta akan samari ko aure nan kusa ba, tun da Mairo ta mallaki hankalin kanta, ta gina burin rayuwarta akan karatu, karatun boko, karatun da zai bata mutunci da martaba a duk inda ta shiga…amma saurayi kam baya gaban Mairo.”

Ta tuntsire da dariyar ƙeta har da sunkuyawa,”sai dai na jiki amma ba in yarda ba, dan wallahi babu macen da zata ce saurayi ba ya gabanta, ko da ike ance abin da baka samu ba haɗa shi da baka so…a ƙaddara ma hakanne, yanzu alal misali Suhail yace yana sonki za ki amince masa ko kuwa shi ma za ki fatali da shi ne?”

Na waigo na dubeta, “wane kuma Suhail? Nai tambayar bilhaƙƙi ba da rainin wayo ba. tace, “Suhail dai da kika sani ɗan ethopia abokin Ya Kabiru”. nayi tsaki, “to ai ba shi ba, ko sarkin ethopia ɗinne da kansa wallahi ba ya gaban Mairo balle wata tsiya Suhail.” Nayi gaba abuna na barta da maganganunta.

A taƙaice dai da gudu na shiga gida saboda cikina da ya murɗa, ina sallama kuwa na faɗa banɗaki, ruwan tsarki ma ce nayi da Zubaida ta biyoni da shi. gama tsarkina kenan na miƙe, kallon gabana da zan yi naga maciji sharfaɗeɗe baƙi wuluk ya ɗaga kai yana ƙoƙarin kawo min sara, a gigice cikin ɗimauta na kurma ihu ina kiran sunan Gwaggo, “na shiga uku Maciji a banɗaki”. na sandare saboda hasken idonsa da ya dallare ni da shi, ƙafafuna suka kasa gaba suka kasa baya, na zama kamar wadda aka dasa a wurin, dan ko motsi na kasa, ba wai saboda tsoro ba, sai dan nima ban san dalili ba. Ku ka nake ina neman agajin jama’a, ga mazan gidan duka sun fice, Matan babu abun da za su iya yi min, duk sun yi cirko-cirko a bakin ƙofa su na kallona su na ihu da neman taimakon maƙota, kan kace mene wannan gidanmu ya cika, kuma da yake juma’a ce maza duk sun wuce masallaci.

Idan Gwaggo tai yunƙurin shigowa sai ya maida bakin saran nasa gareta, hakan yasa na haneta shigowa. siffanta munin kamanninsa ya zarce tunani, ganin yana ƙara kusanto ni na rumtsa ido gam so nake naja da baya amma ina abu yaci tura kamar aikin tsafi. hawaye ne ke gangaro min kawai, rayuwa kam tuni na sallama da ita. na riga na gama fidda tsammani da sake yin nunfashi a doron ƙasa, sai ji nayi an riƙo hannuna, na buɗe idanuna da ke a rufe ina kallon Kulu wacca ta yi shahadar shigowa, ita kanta sai ta bani tsoro, dan ko a maza babu me ganin wannan macijin yace zai kawo ɗauki in dai ba wai dama da shirinsa ba, to ko Uwar da ta haifeni ma ta kasa wannan sadaukarwa, amma ita saboda ganganci da rashin hankali tana ganin mutuwa tana tunkararta.

Na haɗiye wani wahaltaccen yawu a maƙoshina a san da na maida kallona ga Macijin da a yanzu ya maida harinsa kan mu biyun.

Kulu ta damƙe hannuna sosai, su Inna kiranta su ke da kwakwazo akan ta fito amma kamar bata jin su. murya tana rawa nace, “ki fita dan Allah kar kema ya cutar da ke.”

Ganin dai ba ta da niyyar fita nai ƙoƙarin hankaɗata gefe amma ko kusa na kasa motsa jijiyar jikina. sai muka tsaya muna kallon kallo da ita, kamin tasa hannu ta juyar da fuskata ga majicin da bana ƙaunar ganinsa saboda girmansa da baƙinsa. “wallahi Kulu idan biki fita ba yau zan tona miki asiri acikin gidan nan.”

Na faɗa ina kuka. tayi ƙasa da murya tace,”alƙawari kika ɗauka, kuma alƙawari kaya ne, wanda kuma duk ya saɓa wutar Allah zata ci shi.” ta kasheni da dukkan jijiyoyina, dan tabbas nayi mata alƙawarin ba zan faɗawa kowa tana magana ba har zuwa ranar yankewar numfashina, duk da cewar bata san dama can nasan tana maganar ba.

Ta ƙara yin ƙasa da murya sosai tace,”ke ɗin ƴar baiwa ce, kina da baiwar da ba kowa Allah ke bawa ba cikin bayinsa, dan haka za ki iya da wannan macijin duk ƙarfin cutarwar kuwa da yake da ita, karki karaya, ki buɗe ido ki razanar da shi daga baiwar da Allah ya halicce ki da ita.”

Na rumtse idanu gam ina girgiza kai da cewar ba zan iya ba, ni ban da wata baiwa.
“zai sare ni Mairo”. sautin Muryar Kulu cikin kuka ya sauka a kunnena, nai hanzarin buɗe ido na dubeta da yanda ta kare jikinta da hannunta tana ƙudundunewa a jikina. ban san lokacin da wani ƙarfi yazo min ba, nasa hannu na kaiwa kansa duka, shi ma sai yay saurin kautar da kansa. mamaki, al’ajabi da kuma tsoro suka kamani a san da nayi jarumtar ƙura masa ido, sai naga nan take ya karayar da kai ƙasa sai kuma jikinsa ya motse, da gudu kuma ya fara jan jiki yay hanyar rariya, kamar ƙiftawar ido sai na neme shi na rasa.

Daga haka kuma ban ƙara sanin me ya faru ba, sai farkawa nayi na ganni shimfiɗe kan tabarma, Baba a gefen damana yana min tofi, Gwaggo na min firfita, sai sauran ƴan gidan da su ke kewaye da ni. Inna Amarya ta kamani na yunƙura na miƙe zaune ina mai da numfashi. Baba yace da ni, “Sannu”. na amsa da,”yauwa Baba.”

Yagana ta taso daga in da take ta juye rubutu a kofi ta miƙo min tace na shanye, zanyi gardama ta rufeni da faɗa, ba shiri na amsa na kafa baki zan sha amma sai na kasa, Ya Kabiru ya karɓi kofin daga hannuna ya buɗe bakina ya toshe min hanci ya tsiyaya min a haka har na shanye. “Ina ne kuma yake miki ciwo?”

Yagana ta tambaya. “ba ko’ina, aini lafiyata ƙalau”. na faɗi hakan ne gudun kar na ɗaga hankalinsu, na yi silar rugujewar tafiyar su Adawiyya, amma a zahirin gaskiya idona da nake kallonsu da shi ba sose nake gani ba, ganina ya sauya dishi-dishi nake gani, ga zafi da jijiyar idon nawa ke yi. Inna Zulai tace,”kin tabbatar dai babu abunda ke miki ciwo ko?”

Nace,”ehh Inna ni lafiyata lau”. Yagana tayi ƙaramin tsaki tana cewa,”mun sani dama, in dai kece ai ba kya cuta.” Sai kuma Gwaggo ta hauni da faɗa akan ai bana adu’a nake shiga banɗaki, nace mata wallahi ina yi yaune kawai na manta ban yi ba kuma shi ma dan na taho a matse ne.

Baba yace to karna kuma mantawa, ita adu’a ba’a sakaci da ita.

Su Adawiyya suka ci gaba da shirin tafiya makaranta, zumuɗi yasa ko abinci ma ta kasa ci, tunda Ya Kabiru ya tafi nemo mota ta kasa zaune ta kasa tsaye dan daɗi, faɗi take yanzu tunda ba tare zamu tafi ba zata wuceni a aji kenan. nace mata ai nima ba jimawa zanyi ba, da zara wannan tsohuwar ta gama rigimar tata shikenan zan taho.

Jikina duk yayi sanyi lokacin da suka fito za su tafi, na ƙanƙame Adawiyya ina kuka itama tana kuka, ina cewa ba zan iya zaman gidan babu ita ba dan Allah a barta mu tafi tare, itama kukan take tana faɗin ba zata iya zaman makarantar babu ni ba, sai da Baba ya tsawatar mana sannan ta muka saki juna.

Ba zan iya kallon tafiyarsu ba dan haka na juyo gida na bar su Gwaggo a waje, na shigo ina bin jikin bango, Kulu ta taso tana tambayata menene, na kaɗa mata kai nace, “ba komai” dan ita ma nasan muddin na faɗa mata cewar bana gani sosai to zata iya faɗawa Gwaggo, saboda ita ma na lura ta damu da al’amurana kamar ciki ɗaya muke, har na shige ɗakin Inna Amarya ina jin kallon da take bina da shi, na malale akan gadon ƙarfen Innata ina fuskantar rufin kwano, idona a rufe yake inaji da raɗaɗin ciwon da yake min.

Nayi shiru kamar mai bacci, amma ba bacci nake ba, na lula ne acan wata duniya ta tunanin wasu murɗaɗɗun al’amura da ke addabar ƙwaƙwalwata tun kwanakin baya, to amma ba su suka fi damuna ba ayanzu. ayau rana ta farko bacin tausayin Kulu da nake ji sai naji ina sonta, na san a haife ta haifeni, dan haka naji ina mata so irin na uwa, ba dan komai sai dan sadaukarwar da tayi akaina yau, banda taimakon Allah da kuma taimakonta da tuni na zama tarihi, dan tabbas macijin nan sai ya sareni…lallai ya kamata na saka mata da wani abun a rayuwarta, take zuciyata ta ƙudurci aniyar nemawa Kulu hakkinta na wofuntar da rayuwarta da iyayenta suka yi.

Dan haka dole na miƙe tsaye, na ƙara ɗaura ɗamarar yin karatun boko mai zurfi dan ganin na cimma matakin da Gwaggona ke so na kai, bayan Babana da zan taimakawa ita ma Kulu na taimaka mata.

Tafiyarsu Adawiyya da kwana uku shi ma Ya Kabiru ya tafi, ranar tafiyarsa kuwa na sha kuka kamar raina zai fita, har nafi jin tafiyarsa akan ta Ya Amadu, dan shi da zai tafi da ƙyar aka ɓareni ajikinsa, shi kansa sai Yagana ce ta tuge hannunsa daga rungumeni da yayi, kuma har da ƙwallarsa, hawayen da naji su har ƙasan zuciyata, su ka kuma tugunzuma tunanina a san da ya duƙa ƙasa gabana ya zube gwiwoyinsa yana hawaye yana roƙona akan na kula masa da kaina, kar nayi abun da yake ba dai-dai ba, sai naji duk duniya babu wani abu da yake min daɗi, ji nake tamkar nayi bankwana da farinciki kenan.

A sannan nima na tsuguna gabansa na faɗa jikinsa na ƙanƙame shi, kuka nake me tsuma zuciya, ina kwaɓar zuciyata daga wautar da take yi. tun sa’ilin da na mallaki hankalin kaina na sani, bayan so na jini da zuciyata take yiwa Ya Kabiru har da wani ƙazamin so da ba zai zama me amfani a garen ba.

“Ya Kabiru dan Allah ka tafi dani.” Na faɗi hakan a san da na ɗago kaina daga ƙirjinsa na zuba masa idanuwana masu kama da jin bacci, ya ƙara damƙe hannuna yana faɗin,”banda iko, da ace ina da iko Mairo babu abunda zai min ni shamaki da tafiya da ke, to Baba ba zai bari ba…amma ki sani tafiyar nan zan yita ne saboda ke, haka abun da zanje nema acan zan nema ne saboda ke, saboda ke kaɗai Mairo, ke ɗaya tal da kika zama jini da tsokar Kabiru…burina a rayuwa na jiyar da ke daɗin cikinta, na shayar da ke farin ciki na rayuwa, na zama katanga a tsakaninki da baƙin cikin da duk zai kusanto ki…ki cika alƙawarin da kika ɗaukar min kinji ƙanwata.”

Yay furucin ƙarshe yana mai ƙaƙalo murmushin ƙarfin hali. A yanzu gidanmu da babu Adawiyya babu Ya Kabiru jinsa na ke babu daɗi sam, gidan ya zamar min tamkar kango, Sadiya ba wata hira muke zama muyi da ita ba saboda shegen son girmanta, Basma kuma Yayan Gwaggo da ya zo daga kano ya tafi da ita gidansa, wata ƙila ma ta koma can da zama a yanda naji Gwaggo na faɗa, Zubaida kuwa ba zama take ba saboda makarantar Allo.

Duk da cewar ina da karaɗi acikin gidanmu to amma yanzu babu jigona, duk sai nayi sanyi, dan tun tafiyar Ya Kabiru kullum ina ƙunshe a ɗaki ina kuka, na ci kukana na ƙoshi ba tare da sanin kowa ba, kukan da gangar jikina kaɗai tasan ma’anarsa, sai zuciya da ke jin zafi da raɗaɗin rashin Ya Kabiru a kusa da ita.
*****
kusan sati biyu kenan bani da cikakkiyar lafiya, ko da yaushe da ciwon mara nake yini, ga ciwon ido da ya uzzura min, ga munan mafarkai da nake ta famanyi kuma na kasa faɗawa Gwaggo.

Ina shanyar kayanmu da na wanke Mu’azzam ya dawo, ya miƙo min waya yace na riƙe Ya Amadu zai kira. na karɓa na soke a zanina ina jiran shigowar kiran nasa. Inna Amarya da ke zaune bisa kujera tana bakacen shinkafa tace dani, “ke wai ni anya yarinyar nan lafiyar ɗaya kuwa?, gaba ɗaya kin sauya, duk kin yi sukuku, aje shanyar nan kizo.”

Na bar shanyar na ƙarasa gareta na zauna kusa da ita, kaina a ƙasa ƙirjina na bugawa, zuciyata na taraddadin Inna Amarya ta gano SIRRIN ƁOYEN da ke shimfiɗe cikin rains.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sirrin Boye 15Sirrin Boye 17 >>

1 thought on “Sirrin Boye 16”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×