Skip to content
Part 20 of 22 in the Series Sirrin Boye by Halima Zakariyya

Lagoon Hospital, 17B Bourdillon Rd, Ikoyi, Lagos

Shigowarsa cikin hospital ɗin yana yin parking ko rufe motar bai tsaya yi ba ya ɗauketa ya nufi emangency da sauri, nurses ɗin da ke tsaye a emergency su na ganinsa suka turo gado su ka shiga special room da ita, Emanuel na tsaye a varander yana ta kaiwa da komowa hankali a hargitse, tsawon minti ashirin likita ya fito daga room ɗin sannan ya buƙaci nurse da ta ce Emanuel ya biyo shi office.

Acan office Dr Simon ke yiwa Emanuel bayanin sai anyi mata surgery aciki saboda glass ɗin da ya caki cikinta ya shige sose, kuma rashin aikin zai iya haifar da matsala babba ga yarinyar at the end ma a rasata.

Emanuel ya rumtse ido gam tare da dafe goshi, ba shi da wani choice da ya wuce ya amince, tunda shi ne silar halin da take ciki, kuma ko da ace ƴan uwanta za su zo suma amincewar za su yi saboda ta rayu. ya karɓi takardun da Dr Simon ya miƙo masa, yasa hannu akai sannan ya bar office ɗin ya koma mota, yana kallon yanda wayarsa keta ringing da sunan MD da kuma Sectery amma babu kiran da yayi picking aciki, ƙarshe da ya ga kiran na neman damunsa sai ya kashe wayar gaba ɗaya.

“Nurse! bring injection quickly.” Dr Simon ya faɗa yana ci gaba da aikinsa. da sauri Nurse ɗin ta miƙo allurar ya karɓa yaywa Mairo, tunda aka kammala tiyatar Dr ya tsaya yana duban fuskar Mairo da ƙirjinta na tsawon daƙiƙu, sannan ya maida dubansa ga Nurse ɗin kusa da shi yana girgiza kai yace,”her health is fading. Bring the oxygen fast”. yana saka mata oxygen ɗin ya ke ƙara faɗin,”Nurse prepare the CPR.”

Wucewar awa da mintuna shiru-shiru basu fito daga ɗakin tiyata ba, ganin shirun yayi yawa tsoron da Emanuel keji ya ƙara ninkuwa, ya fito daga motar jiki a mace ya nufa ward ɗin da suke, zuwansa yayi dai-dai da fitowar Dr Simon daga ICU da waya maƙale a kunnensa yana magana da wani likitan. Emanuel yasha gabansa dan sam Dr Simon bai lura da shi ba, ya dafa kafaɗar Emanuel yana ci gaba da tafiya. Emanuel ya tambaye shi,

“Dr what is her condition now?”. ya tambaya anxiously. “Your patient is in dire state, we can not say anything for now. but relax we are trying all we can.” Likitan yace da shi yana ci gaba da tafiya. Emanuel ya nemi kujera yay zaman daɓaro, yanzu idan yarinyar nan ta mace ya zai yi?

A can ɗakin tiyata kuwa ayanzu manyan likitoci uku ne akanta kowanne acikinsu jiki sanyi ƙalau, almost 3hours kenan da gama yi mata surgery ɗin amma har yanzu bata farfaɗo ba, wanda hakan yasa suka fara cire rai da farkawarta, rigima ta fara kaurewa a tsakanin likiticin su biyu, Dr David na faɗa akan mene ma yasa Dr Simon yay gaggawar yanke hukuncin ai mata Surgery, yanzu gashi nan idan yarinyar ta rasa ranta zai iya jawa asibitinsu matsala, shi ma Dr Simon masifar yake masa ai rashin sanin makamar aikinsa ne ya shi yake faɗin haka, Dr Friday da ya zama mediator shi ne me aikin basu haƙuri.

Sai kowannensu ya nufi ƙofa zai fita a zuciye, amma ƙarar na’urar da ke nuna cewar Mairo na da rai shi ya dakatar da fitar tasu, Dr David ya dawo da sassarfa, haka ma Dr Simon da Nurses suka ƙarasa gareta a hanzarce.

Bayan wucewar wani lokaci Doctor Simon ya fito, Emanuel ya tsaya jingine da bango yana fuskantar ICU ɗin, da sauri ya sha gaban Dr ɗin yana ƙara tambayarsa halin da ake ciki, yay masa murmushi tare da cewar ya biyo shi office, haka Emanuel yabi shi sai dai bai bar waigen bayansa ba, har sai da idanunsa suka ga an fito da Mairo anyi wani room ɗin da ita kana ya sami natsuwar bin bayan likitan, but still zuciyarsa bata bar taraddadin abunda likitan zai faɗa masa ba.

Emanuel ne zaune kan kujera yana facing likitan tare da sauraron bayanin da yake masa, tun a furucin farko da ya ambaci amnesia yaji hankalinsa ya kai ƙololuwar tashi.

“Mun samu ta farfaɗo and we thank God jikin nata da sauƙi, sai dai kuma ta sami matsala ta Memory Loose ciwon da muke kira da amnesia saboda buguwar da tayi aka, so she will be Inability to remember her past for a long period of time…”

Ya sauke ajiyar zuciya yace da Dr,”for how long will she remember everything?”. “zai iya taking nata 3-5months.” Ya miƙa hannu ya karɓi kati na magungunan da za’a siya sannan ya fita. kai tsaye pharmacy ya nufa ya siyo magunguna da alluran duk da ake buƙata kana ya wuce ɗakin da aka kwantar da ita. tun daga window yay tsaye yana kallonta yanda aka ɗaura mata drip, fuskarta naɗe da bandage haka ma ƙafarta ɗaya, yafi tsawon daƙiƙu uku a bakin tagar yana jin kamar ba zai iya shiga ciki ba saboda yanda tsigar jikinsa ke tashi, sannan ya dawo bakin ƙofar room ɗin ya tsaya, har san da Nurse ta shigo ta karɓi ledar pharmacy ɗin daga hannunsa, ta ƙarasa taje tayi allura a ruwan drip ɗin, bayan fitarta ya ɗaga ƙafa kamar mara lakka ya ƙarasa bakin gadon, tsananin tausayinta yay mugu mugun kama shi, daga irin yanda take numfashi ya isa ya fahimtar da shi irin mawuyacin halin da take ciki.

Jin zafin ciwon nata yake ajikinsa, haka duk wani shiga da fitar numfashinta auna shi yake da nasa. ya zauna a gefen gadon ya kai hannu ya taɓa wuyanta yaji temperature nata very high, yayi saurin ɗauke hannu sannan ya miƙe ya fita da sauri ya koma office ɗin Dr Simon ya shaida masa yanayin zafin jikinta da ya zarce tunani, tare suka dawo da Dr wanda yana zuwa ya kuma yi mata aune-aune sannan ya ƙara tabbatar masa da babu wata matsala da zarar ruwan ya ƙare zata farka kuma temperature nata ma zai dawo normal, kuma ko da ta farka kar abata komai because aikin da aka mata general anesthesia ne zai iya ɗaukanta 24hrs kamin taci wani abun, amma idan an samu Bowel sound ya zama present to za’a iya bata ruwan tea tasha, Emanuel babu abunda ya iya ce masa sai nodding kansa da yayi.

Bayan fitar likitan Emanuel ya roƙi Nurse ɗin da ke gyara table ɗin da aka ɗora magunguna alfarmar ta zauna ta kula da ita zai je ya dawo.

Baifi 30 minutes ba sai gashi ya dawo hannunsa riƙe da manyan ledoji, ya zaro 5k a aljihu ya bawa Nurse ɗin ta amsa tana ta murna. shaf ya manta da batun wata waya sai ayanzu da ya jiyo ringing ɗin wata wayar daga waje sannan yasa hannu ya ɗauko tasa a aljihu ya kunna.

Yay dialling number MD sai da kiran ya kusa yankewa sannan MD ya ɗaga yana masa masifar ina ya saka wayarsa. yace da shi,”i got an accident…hankalina bai dawo jikina ba sai yanzu.”

A zafafe Md yace, “Emanuel are you Mad?” You have an accident kuma ba zaka kira ka faɗi situation ɗin da kake ciki ba…yanzu kana wane hospital?” “Ka bari zuwa safiya zan sanar da kai, amma please karka bari Dad ya san da wannan. idan ya tambayeka akaina ka san ƙaryar da zaka yi masa.”

Dan haushi ma Md ya kashe wayar ba tare da ya amsa shi ba, shi kuma yaƙi faɗa masa ne gudun kar ya faɗawa Dad ko kuma shi yace yanzu zai taho alhalin kuma yana da iyali.

Har drip ɗin ya ƙare bata farka ba, sha biyu na dare yana tare da ita kamin ya tashi ya tafi hotel ya kwana acan, ya barta da Nurse ɗin ɗazu yace ta kwana da ita. washegari bai shigo asibitin ba sai around 9, hankalinsa gaba ɗaya na kan Mairo da ita ya kwana a ransa, abunda ma ya hana shi sammakon shigowa sai da ya biya office.

Kai tsaye ɗakin da take kwance ya shiga, tare su ke shi da Md, da mamakinsa sai yaga bata kan gadon kuma babu kowa a ɗakin, yana dube-dube sai yaga Nurse ta fito da ita daga toilet tana dafe da kafaɗar Nurse ɗin tana takawa da ƙyar, ya zuba mata ido sai ya miƙe ya ƙarasa ya ɗaukota ya kawota kan gadon ya jinginar da ita ajikin pillow.

Nurse ɗin tayi masa bayanin jikin nata da sauƙi dan Dr ma yace zuwa dare za’a iya warware mata bandage ɗin fuskarta.

Mairo tayi shiru tana sauraronsu dan jinta take a wata sabuwar duniyar, ita kanta maganar da suke yi ba ganewa take ba, gashi ba ganinsu takeyi sose ba hasalima sai ta kusa rumtse ido gaba ɗaya ne take samun ganin abu very tiny. “How are you feeling now?”

Emanuel ya tambayeta yana kamo hannunta ya riƙe cikin masa. ta dai ji maganar da yayi amma bata san me yace ba, tayi shiru sai Nurse ɗin ce tace da shi,” I noticed like she doesn’t understand English.”

Md ya girgiza kai da cewa, “I also noticed that.” Emanuel ya dube shi yace,”to mene abun yi kenan?”. “Amma ai losing memory ba ya shafar language na mutum”. Debora tace”um ba ya shafar yaren mutum, ita ɗin bahaushiya ce tun da ɗazu da hausa tayi magana.”

Md ya ɗaga kafaɗa, “Alright, shi ma english ɗin da sannu ai zata iya making.”
“Me taci da ta farka?”. Emanuel ya tambaya. Deborah tace da shi,”babu komai yanzu dai za’a iya bata”. ta ɗauki ƙaton tea flask ɗin da suka zo da shi ta zuba tea a mug sai ƙamshi yake, ta miƙawa Mairo cup ɗin tana cewar ta amsa da yake ita tana jin hausa kaɗan-kaɗan kasancewar tayi zaman Kano.

Mairo ta miƙa hannu tana laluben ta inda zata amsa Cup ɗin, suka tsaya dubanta da mamaki kafin Debora tace da ita,”me ya sami idon naki ne, ga ta inda na ke miƙo miki abu ke kuma kina miƙa shi ta wani wurin.”

Muryarta na rawa kamar zata yi kuka tace,”ai bana ganinki ne.” “Ba kya gani?”. Mairo ta ɗaga kai,”ehh ina ganin duhu amma bana ganin hannun naki”. Debora ta sauke numfashi sannan ta dubi Emanuel wanda ya tsareta da ido yana jiran cewarta tace masa

“Akwai matsala fa a idanunta, she says she cant see very well.” Emanuel ya juyo yana duban Mairo da mamaki, how comes hakan zai kasance, to ko dama ita makauniya ce shi yasa ta sanyo kanta kai tsaye titi har ya kasa kauce mata.

Md ya katse masa tunani da cewar,”what are you thinking?”. yace da shi, “ina tunanin mene yay cousing na ciwon idon nata, dama can da ciwon ko kuma a accident ɗin nan ne?”

Md yace, “Gashi kuma babu wani abu da zata iya tunawa bare ta bada amsa.” Emanuel yayi shiru, Md ya ƙara cewa da shi,”ya kamata fa Police su shigo cikin lamarin nan, tun da ba za kai ta zama da yarinya ba, ai kayi iyaka yinka tun da ka kawota asibiti akan lokaci.”

Ya girgiza masa kai,”bana so Police su shiga zance i have already told you that…ko asibiti ma da su kai maganar rufe bakinsu nayi da kuɗi”. “to kana nufin zaka ke ta zama da ita ne?”. ya ba shi tabbacin hakan ta hanyar jijjiga masa kai. “to office fa?”. “ai kana nan, ko ba zaka iya aiwatar da aikin company ba idan bana nan?”

Md bai ce da shi komai dan ya rasa ta cewa gaba ɗaya. Debora ce ta bawa Mairo tea ɗin tasha, sannan ta bata magunguna da allura. Emanuel ya tashi daga kan kujerar da yake ya koma gefen gadon ya zauna, yana riƙe da hannunta ya tambayeta, “what is your name?”

Da mamakinsa sai yaji tace,”my name…”. sai kuma tayi shiru. “ehen said it your name is what?”. “i dont know my name”. a yanda tayi maganar sai ta ba shi tausayi. 
su na ta hira shi da Md ita kuma duk tana jinsu bada sanin abunda suke faɗa ba ko kuma ganinsu ba, ita dai har tsawon awannin da suka shuɗe Emanuel bai saki hannunta ba.

Sai around ƙarfe biyu na rana sannan suka fita shi da Md zuwa restaurant suka ci abinci suka dawo, time ɗin kuma tayi bacci, ya tambayi Deborah ya sauƙin jikinta tace masa, “ai bayan tafiyarku tana ta kuka wai idonta na ciwo”. “ko asibitin ido za’a kaita?”. ya jefa tambayar ga Md. sai Deborah tace masa akwai likitan ido da yake zuwa da daddare.
misalin bakwa na dare Md ya umarci abokin nasa da ya tashi su tafi.

Emanuel yace da shi ya tafi shi zai kwana nan ne. Md ya dube shi da tsantsar mamakinsa yace,”zuwa wane lokaci zaka bar yarinyar nanne ka koma harkar gabanka?”

“Ni kuma for how many times kake so nata maka repeating cewar zanke zama da ita anan zuwa lokacin da za ai discharging nata.”

“Amma kana tunanin za su sallameta nan kusa ne? muna fa da meeting cikin satin nan kuma kasan ya kamata kake shigowa office saboda hakan”. “zan yi posponding meeting ɗin”. “zuwa yaushe?”. “time ɗin da zamu bar asibiti”. “then sai kayi ya da ita kuma?”. “zata zauna tare damu har lokacin da tunaninta zai dawo a nemi iyayenta”. Md ya tsaya yana yi masa wani irin kallo, ya lura gaba ɗaya nema yake ya maida al’amarin yarinyar kansa, shi kuwa Emanuel gani yake kome ya faru da yarinyar shi ne sila dan haka dole ya tsaya ya kula da ita.

Md ya nufa ƙofa yana ce masa,”so ni dai good nite”. kamar ba zai ce masa komai ba sai yace, “karka kawo mana tea da safe na lura kaman bata sonsa”. “to sai mene take so?”. Emanuel ya ɗago yana tsareta da ido, dariya ta suɓucewa Md yace da shi,”ask her mana.”

Emanuel yay masa wani wawan kallo sannan ya ɗauko wayarsa daga aljihu ya kira Deborah, ko minti biyu ba ai ba sai gata tazo, yace ta tambayi Mairo abunda tafi son ci, Mairo ta girgiza kai a san da Deborah ta tambayeta alamar babu komai.

Emanuel yana latsa wayarsa yace da Md, “abu soft ake da buƙatar taci so please ka taho da curstard and do not be late.”. Md ya kyaɓe baki yace,”aini ba ɗan aikinka bane da har kake faɗa min wani karna makara, you will see me a duk san da na gama hidiman gabana”. “ka barshi ma ba sai kazo ba”. Md yay dariyar ƙularwa sannan yace,”anyway no escort?”

“Kasan hanya ai.” Deborah dai murmushi tayi saboda tun ɗazu tana ganin yanda suke buga dirama, kuma duk Md ke jansa da tsokana.

Yayi shiru ya kasa ɗauke ido daga kanta, tausayinta yake da dukkan ransa, kansa yake ta ɗorawa laifin duk da cewar ita ma akwai nata na rashin bin ƙa’idar tsallaka titi, dan haka ba zai yafewa kansa ba har sai ta sami lapia completely.

Around 9 likitan ido yazo dubata, yay gwaje-gwajensa ya tabbatarwa da Emanuel tana da buƙatar aikin ido a babban asibiti da yake musamman na ido ne, amma for now zai bata wasu maganin da zata yi amfani dasu ciwon ya lafa. tare suka fita da Dr ɗin yaje ya siyo maganin da ya rubuta, tana baccin ya ɗiga mata maganin sannan yaywa Deborah sallama ya wuce makwancinsa.
***
cikin kwanaki goma ciwonta Alhamdulillah ya fara sauƙi, ƙafarma an kunce bandage yanzu tana ɗan takawa a hankali, idonta kuma yanzu tana gani da shi sai dai ba wai yanda ya kamata ba. ta kuma saba da Deborah sosai dan 24hrs su na tare, tana koya mata lesson akan yanda harshenta zai kama da yaren da suke yin magana, wanda Emanuel ne ya sata hakan kuma yana biyanta da tsoka. Alhamdulillah tana ganewa sosai, ko magana akai tana ji sai dai ba komai take iya maidawa ba.

Yau bai shigo da wuri ba, a ɗan turancin da bakin Mairo ya fara kamawa ta tambayi Deborah, “Aunt is that tall Man not coming today?”. Tayi mata murmushi da cewar, “his name is Uncle”. Mairo tace,”ohh Uncle, to zai zo yau?”. ta gyaɗa mata kai da cewar,”umm zai zo ƙila ko yaje office ne”

Tayi nodding kanta kawai sannan ta ɗauki littafinta taci gaba da rubutunta da Deborah ta bata. kuma rufe bakinsu kenan wayar Deborah tayi ringing, ta ɗauka ta kara a kunne tana gaishe shi, amma sai bai amsa mata ba yace ta bawa Mairo. ta miƙa mata wayar ita kuma tana ci gaba da yankan farce. daga cikin wayar ya kira Maira da,”Be.b”

Ta amsa masa, “Yes Uncle Good Morning”. “Morning Beb, how was your night and your body?”. “Uncle am feeling better”. “thats good. did you eat your breakfast?”. duk da cewar taci amma sai ta ce da shi, “no”. “why?”. tayi shiru bata ce komai ba sai yatsanta da ta saka a baki tana cijawa, cikin dabara ta raɗawa Debora cewar ta faɗa masa,”ta kasa cin komai ne tana son ferfesun kayan ciki ne.”

Deborah ta amsa wayar tana ce mishi,”wannan patient ɗin naka ta cika kwaɗayi, taƙi cin komai sai fefesu take son ci”. yace, “me yasa biki faɗa tun ɗazu ba, bari nasa ayi mata order yanzu.” kamin ya kashe wayar ya bawa Deborah uzurin rashin shigowarsa, yaje gudanar da wani meeting ne amma da zarar ya kammala zai shigo, hankalinsa gaba ɗaya yana nan ya kasa samun natsuwa.

Tace da shi, “ka nutsu kayi aikinka jikinta da sauƙi sosai”. “sai dai nazo na gani da idona”. ya faɗa yana kashe wayar.

Sai 7 na dare ya shigo asibitin, kana ganinsa kaga wanda gajiya ta yiwa duka, ya zauna kan kujera yana yiwa Mairo magana sai yaga tayi masa shiru taƙi kula shi, sai baki da ta turo gaba cikin salo na shagwaɓa. yace da ita,”Beb why are you frowning at me?”

Ya tambaya yana kama babban yatsan ƙafarta. ta kalle shi ta ɗan murguɗa masa baki, yay murmushi ya matso da kujerarsa bakin gadon sosai, ita kuma sai ta kwanta ta juya masa baya. bai saba da ganin rigima irin haka ba, ba su da yara kuma ba shi da me yi masa, dan haka sai yayi tunanin ko wani abun ke damunta, ya ɗauki waya ya kira Deborah ya hauta da faɗan akan mene zata tafi ta barta ita kaɗai, ai kuɗi yake biyanta ba kyauta take masa aikin ba.

Sai gata ta dawo da sauri har tana haɗa hanya tayi zaton ko jikinta ne ya tashi. tana zuwa ta leƙa fuskar Mairo taga idonta biyu, kawai dai ta ɓata rai ne tana neman fashewa da kuka mara dalili, ɗazu ma abunda ya haɗasu kenan ta fita ta barta da wannan turo bakin gaba. Emanuel dai bai daina faɗansa ba, “idan kin gaji ki faɗa min mana na nemi wata.”

Ta rissinar da kai,”sorry Sir ba fa wani abu ke damunta ba tana fushi ne akan baka zo ba, tun ɗazu take min complain har da cewan sai mun tashi mun bika. ƙarshe ma abincin da kasa akayi order bata ci ba wai hannun delivary Man ɗin da ƙazanta she cant eat.”

Abun yaso bashi dariya, dan haka ya miƙe ya ɗagota daga kwancen yana bata haƙuri da lallashi, sai da ƙyar ya shawo kanta tayi murmushi ta haƙura, tace masa,”amma Uncle idan ka sake me zan maka?”

Yace mata,”punish me…yanzu dai kici abinci”. ya faɗa yana buɗe takeaway ɗin da tun safe yake ajiye. ta dakatar da shi da faɗin,”ni fa ba zanci wannan ba, naka nake so”. ya mayar ya ajiye sannan ya fita zuwa siyo mata wani.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sirrin Boye 19Sirrin Boye 21 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×