Cathedral Church of Christ, Marina
A harabar da aka tanada domin aje motoci ya faka motar, ya dubi Mairo da cewar ta fito. ita dai tunda ta fito sai take ji ajikinta kamar wani sabon abu ke faruwa da ita, ya za'ai tsawon rayuwar da tayi a duniya kuma ace bata taɓa ganin irin wannan yanayin ba, shi kansa church ɗin kamar bata taɓa zuwansa ba, sai dai hakan kuma ba zai kasance ba ta sani.
Tayi tsaye a jikin motar tana rungume da bible ɗinta tana jiran fitowarsa, kallon yanayin church ɗin take da. . .