Skip to content
Part 22 of 22 in the Series Sirrin Boye by Halima Zakariyya

Cathedral Church of Christ, Marina

A harabar da aka tanada domin aje motoci ya faka motar, ya dubi Mairo da cewar ta fito. ita dai tunda ta fito sai take ji ajikinta kamar wani sabon abu ke faruwa da ita, ya za’ai tsawon rayuwar da tayi a duniya kuma ace bata taɓa ganin irin wannan yanayin ba, shi kansa church ɗin kamar bata taɓa zuwansa ba, sai dai hakan kuma ba zai kasance ba ta sani.

Tayi tsaye a jikin motar tana rungume da bible ɗinta tana jiran fitowarsa, kallon yanayin church ɗin take da kuma yanda mutane ke ta parking motoci su na fitowa su na shiga ciki a hanzarce, kowa dai da alama ba ya son rasa ibadar da zasu gudanar.

Ko a ciki da suka shiga kujerar kusa da ita Emanuel ya zauna, Mairo tana ƙarewa haɗuwar Church ɗin kallo tace,”it seems like bamu taɓa zuwa wannan church ɗin ba ko?”

Emanuel ya juyo ya kalleta jin abinda tace.

“Kin manta ke baƙuwa ce a garin.” sai ta ɗan rufe ido ta buɗe da faɗin,”ohh na manta, i feel like we are in Abuja”. yayi murmushi bai ce komai ba sai ƙara damƙe hannunta da yayi, ba su jima da zama ba pastor ya ƙaraso aka fara gabatar da addu’a kafin a gama a saki kiɗa ana rawa, sosai Emanuel ya zage yana chashewa, ita kam Mairo ganin yana rawa ya bata dariya ita ma ta fara yi kamar yadda taga kowa nayi.

Bayan wani lokacin aka gama suka fito suka shiga mota su ka koma asibiti, Deborah ta shigo dan yiwa Mairo Alluranta na ƙarshe, bayan tayi mata ne ta kalle shi wanda ke tsaye yana danna waya, ta faɗa masa tana son yin magana da shi, daga bakin room ɗin su ka tsaya ta sanar masa da saƙon likita, yay ɗan jim yana wani tunani cikin ransa, he feels like violating what the doctor says, to amma ko yayi ko bai ba, ko a daɗe ko ba jima Mairo fa zata yi regaining tunaninta, to gwara ma yayi amfani da maganar likitan. Dan haka jiki a saɓule ya dawo room ɗin, Mairo na dubansa da yanayin sauyin Mood nasa cikin ƙanƙanen lokaci ta jefa masa tambayar,”Uncle what happen to you?, did someone hurt you?”. ya ƙaƙalo murmushin da zai kira shi dana ƙarfin hali yace mata,”nothing, just like that”. sannan ya samu kujera ya zauna, ya karɓi story book ɗin da ya siya mata musamman dan english ya zauna a kanta, yaci gaba da karanta musu labarin tare, sosai kuma shi da ita ke jin daɗin labarin kowa da salon da yake auna daɗin labarin a zuciyarsa.

Ya nutsa cikin labarin sosai sai ya ajiye littafin yace da ita, “Beb lets go for a walk.” ta noƙe kai alamar ita ta gaji, yace da ita,”Sorry Beb yanzu fa zamu dawo.” ya faɗa yana riƙo hannunta ta sakko daga kan gadon.
fitarsu yawo suka yi sosai kuma duk a ƙafa, daga wannan store sai su shiga wannan store irin malls ɗin nan da suke a bakin titi.

Mairo kuwa duk inda suka shiga jidar kayan maƙwalashe take kamar wadda zata buɗe nata kantin, saboda kuɗi abin banza ne a wurin Emanuel har da teddy ƴar 27k ta ɗauka kuma ya biya kuɗin, shi tausayinta yake matuƙa a yanda ta rasa tunaninta ta shiga cikin wata sabuwar rayuwa, wanda ya zama shi ne sila, dan haka gani yake zai iya yin komai dan ta kasance cikin farinciki da jin daɗi.
A wani restaurant da suka tsallaka da ke gefe sun dawo za su koma asibitin, mota ta bige wani tsohon mutum da ya zo tsallakawa, dan haka nan da nan jama’a su ka taru akan mai motar, ita kuma Mairo a wannan lokaci tsoratar ganin accident ɗin yasa ta ƙanƙame hannun Emanuel tana ɓoye fuskarta ajikinsa jikinta na rawa, bata so idanunta su ci gaba da ganin wannan mummunan haɗarin, shi kuwa Wannan lokacin sai ya rufe idanuwansa ya kasa buɗewa, zuciyarsa na fargabar dawowar tunaninta, dan haka sai ya kasa taɓuka komai har tsawon daƙiƙa biyu da suka shuɗe sannan ita ta ɗago kanta ta kalle shi, har wannan lokacin bai buɗe idonsa ba, ya rasa me yasa yake fargabar samun lafiyar tunaninta, jiya zuciyarsa har faɗa masa tayi Allah sa kar ta dawo dai-dai, to amma bai san mene dalilin hakan ba.

Ita dai sai ta bishi da ido, zatonta ko adu’a yake yi dan haka ta ƙyale shi har sai da ya gaji ya buɗe idon dan kansa ya saukesu akanta, da mamakinsa sai yaga saɓanin tunaninsa da kuma hasashen likita, bai san lokacin da ya sauke wata nauyayyar ajiyar zuciya ba ta farinciki, haka ya kama hannunta su ka tsallaka titin cikin sauri suka koma asibitin.

Washegari da safe da ya je amsar takardar sallama yay ma likita bayanin komai, shi ma kuma likitan ya ƙara tabbatar masa da cewar ai a binciken ma da ya ƙara yiwa takardar hoton da aka mata last bai zama lallai ma ta kai lokacin da su ke ƙiyasi ba, yanzu ana kan tsammanin faruwar abu biyu ne, ko ta wuce lokacin da su ke zato, ko kuma ta sami lafiya kamin lokacin. sai dai Dr Simon ya sake ba shi shawarwari na yadda za’a iya shawo kan matsalar tata da wuri.

Godiya yaywa likitan sannan su kai sallama ya fito, acan wani ɓari na zuciyarsa daɗi yake ji da ba zaman asibitin zasu ci gaba da yi ba balle likitan ya dinƙa kawo abubuwan da za su iya janyowa Mairo ta sami lafiya. A bakin mota ya tarar da Deborah tsaye ita da Mairo su na jiran isowarsa, Deborah tayi shaƙuwar da take jin tamkar kar su rabu da Mairo, jinta take kamar ƴar da ta haifa a cikinta dan ƴarta Ciyoma sa’arta ce.

A ɓangaren Mairo ma hakan take ta saba da Deborah sosai, ta shaƙu da ita da har take jin rashin daɗin rabuwar da zasu yi a yau.
booth ya buɗe ya zuba kayansu, ya ɗauko kuɗi ya ƙirga dubu talatin ya bawa Deborah yace sauran zai yi mata transfer, ta amsa tana yi masa godiya sosai, sannan tayi musu sallama ta koma cikin asibitin, shi kuma yace da Mairo ta shiga mota tukunna shi ma ya shiga, zamansa yayi shiru ya kasa yiwa motar key sai aukin shafa goshi da yake. da can bai yi tunanin zai yi facing matsalar komai ba akan sallamarsu a asibiti, sai yanzu ne zuciyarsa ta fara taraddadi akan kai Mairo can gidansu, sarai yasan wace Mom

Ko da giyar wake yasha yaje da Mairo gidan sai Mom ta saito mata hanya, balle kuma ace ya kaita a cikin hankalinsa, da sauƙi ma idan ace zata ce shi da itan su sauya sheƙa, to Mairon kaɗai zata sa security ɗin gidan yay waje da ita, kuma sai ta ci zarafinta kafin nan.

Mahaifiyarsa mace ce mai izzah da mulki akan irin dukiyar da Allah ya wadatasu da ita, akwai jakin kishi da ƙamƙam da abun da take so, ko kaɗan bata ƙaunar wani ya raɓi iyalinta, komai tafi so daga ita sai yaranta acikin gida, Kakarsu ma dan ita ta kawo mata mijinta duniya ne da bata isa ta rayu da su acikin gida ɗaya ba. shi yasa da yawa cikin family na su ba’a fiya son zuwa gidan ba, duk da cewar ita ba mazauniya bace ko da yaushe tana kan hanyar seminars to other countries.

Ƴaƴan ƴan’uwa da dama idan sun zo Abuja karatu ta ƙwammaci ta basu gidajenta na haya su zauna aciki akan dai su zauna tare da su, ita matsalarta bata da yarda, gani tke kowa macuci ne, currently rigimar ma da ake da ita akan student ne mata masu zuwa neman taimakon registration, tayi rantsuwa kan cewa ba taimako suke zuwa ba kalle mata miji suke zuwa yi, ya tsufa ɗinma amma mayu sunƙi barinsa, to balle ya kai Mairo gidan da sunan zama tare da su na tsawon wani lokaci, ita da bata son zuwan budurwa, acewarta Mace shaiɗaniya ce zata rabata da ƴaƴanta ne da mijinta.

Ya sauke numfashi tare da jinginar da kansa jikin kujera, ɗaya ɓari na zuciyarsa kuma ya fara tunasar da shi waye Mahaifinsa, Mom na matuƙar shakkarsa, tun aurensu ma balle kuma da ta sha bulalar soja, mutum ne shi da ba ya ɗaukan shirmen banza thats why ake samun sauƙi a wasu lamuran nata, amma duk da haka za’a sha cin magani tare da fushi da fad’a.

Mairo ta katse tunaninsa da faɗin, “Uncle why the silence, ko kaima baka so mu tafi mu bar Aunt?”

Yay murmushin da shi kaɗai yasan ma’anarsa sannan yaywa motar key suka bar asibitin, daga nan kuma direct office ya wuce. Tun kamin su shigo company ɗin Mairo ta saki baki galala tana kallon tsaruwar ma’aikatar, da su ka shigo daga ciki kuwa sai ta rufe baki dan ta lura idan ta biye ta kallonsa a haka to soon zata fara dalalar da yawu. da sauri PA ta ƙaraso ta buɗe masa ƙofa tare da amsar jakarsa, sannan ya umarceta da ta zagaya ta buɗewa Mairo ma, ai fitowar Mairo a motar sai yasa ta kusa suman tsaye, saboda gamo da kyawun halittar da bata taɓa gani ba, _aina Oga ya samo wannan Beb ɗin?_ ta faɗa a ƙasan zuciyarta, sai kuma tayi wata munafukar dariya, _ina ma Joy tana nan._ ta ayyana hakan a ranta.

Hannun Mairo ta riƙe suka bi bayansa tana tambayarsa,”Sir where did you find a beautifull Lady?” Ta tambaye shi kai tsaye dan ita su na ɗasawa da shi.

Yayi gudun wannan surutun, kuma dama yasan za’a rina sai dai idan PA bata ganta ba. dan haka gudun kar surutun yay tasirin da zaija su kawo wata manufar sai ya bata amsa a taƙaice.

“Little daughter of the family”. “wow”. ta faɗa tana duban Mairo saboda zuzuta zance har da cewa aikuwa ga kamanni.
“our little what is your name?”. ta tambayi Mairo tana shafo fuskarta. Mairo dai aikin yatsine fuska kawai take. jin tambayar da ta yi mata da sauri ya juyo ya bata amsa a taƙaice, “Gift”. sannan ya kamo hannun Mairo suka yi ciki. saboda matsawar ya barta da PA har ta yanda aka haifeta sai ta tambaya.

Su na shiga office yay mata nuni da wurin zama, ta ƙarasa ta zauna tare da cire takalmi, shi kuma ya shiga toilet ya fito sannan ya ɗauki suite ya saka. sannan ya dubi Mairo da ke kan doguwar cushion ɗin office ɗin tana bin ko’ina da ido, murmushi yayi ya isa fridge ya ɗauko 5alive ya aje agabanta.

“Beb zan fita but i will be back soon, ga laptop nan the passwrd is Ema1988. if the landline rings, you pick up its me oak”. Bai jira me zata ce ba ya juya ya fita dan MD jiransa yake zasu fita tare.

Ta buɗe 5alive ɗin ta zuba a cup tayi masa shan gayu, sannan ta ɗauki ɗan ƙaramin bible ɗin da ke kan center table ta shiga karantawa, kamin daga bisani ta ajiye shi ta kunna system ɗin, sai kuma ta bar kanta ta kunna tv tana kallon labarai a BBC News.

“Yes Come in.” Ta faɗa a san da taji anyi knocking door, kuma ba tare da ta dubi wanda ya shigo ba ta ci gaba da kallon tv, hankalinta ya karkata ga labaran da ake akan Covid19 da ta dawo. Ahmadu ne ya shigo hannunsa riƙe da files ya aje akan table ɗin Emanuel, ganin ba ya kan kujerarsa sai ya kalli inda ya san shi ne mazauninsa bayan wannan kujerar, to amma yana kallon kujerar sai yay saurin ɗauke kai saboda yanda yayi tozali da santala-santalan cinyoyin Mairo farare ƙal da su duka a waje, zatonsa ma PA ce sai kuma ya tuna PA bata kai hasken haka ba, kuma yanzu ma ai ya barota a waje, sai daga baya ya tuna Sectery ɗin MD da Marketed sun guntsa masa gulmar Oga yazo da wata haɗaɗɗiyar Beb, amma yace musu ƙanwarsa ce, sun dai ji shi kawai amma ba su yarda ba, to ashe da gasken suke tunda ga idanuwansa sun gani.

Yanayin yanda Mairo take ayanzu zaka rantse da Allah cewar bata taɓa haɗa hanya da musulunci ba, gaba ɗaya ta gama sajewa da arna ta ko’ina, a kafiranma irin waɗanda sukewa addini riƙon gamgam, saboda haka ba zaka taɓa iya shaidata ba a kallo ɗaya balle kuma ace gefen fuskarta ne kawai ka iya gani, wannan dalilin yasa ko kusa ko alama Amadu bai shaida tasu bace dan ba ta inda alama ta nuna akwai haɗi.

Dago kai yay zai yi magana da ita sai ya saurin saukewa dan ba zai iya yin magana da ita a yanda take ɗin ba, rigarta ma bata rufe mata cibiya ba, dan haka kansa a ƙasa ya tambayeta,”ina Oga?”. ba tare da ta dube shi ba tace, “He left but said he would be back soon”. ta faɗa har lokacin hankalinta naga labaran, bata ko kalli inda yake ba.

Yay ɗan jim kamar wanda zai ƙara cewa wani abu sai kuma ya fita, baiyi minti goma da fitar ba ya kuma shigowa, ya ƙarasa har inda take ya aje takeaway saman table, sai da ya juya zai fita sannan ta ɗago taiwa bayansa dubi ɗaya ta ɗauke kai.

Ɓangaren Emanuel kuwa bayan fitarsu da Md Fidson Healthcare Plc suka nufa, daga nan suka ƙara wucewa Federal Palace Hotel and Casino inda Dad ya turasu akan wani program da za’a gabatar. a hanyar dawowa Emanuel kewa Md complain ɗin yanda zai yi da kai Mairo gida, yana gudun ɓacin ran Mom matuƙa, duk da cewar Dad yasan da komai.

MD yay tsaki da faɗin,”kai kake neman ɗorawa kanka. tunda yarinyar nan taji sauƙi we should take her to radio station a bada a sanawa idan iyayenta sunji su nemeta a wurinka amma ka tsaya kana damun kanka…”

Emanuel ya katse shi, “kaga maganar kai cigiyarta ma bai taso ba, zata zauna damu har sanda zata ji sauƙi sannan ta faɗi inda take mu kaita…so dont talk to me anymore akan wani kai cigiyarta”. Md yay ɗan jim yana kallonsa sai bai ce komai ba, dan a yanda yaga ya ɗauka da zafi idan ya kuma cewa wani abu to zasu iya yin rigima.

Dan haka suka bar batunta suka kama na company, bayan dawowarsu kuma Emanuel ya ke sanar masa, “idan zaka wuce you are going with her ba zan kaita hotel ba.”

“Ka fara sanar da Favour tukunna”. ya ba shi amsar yana ɗaukan hanyar office ɗinsa, Emanuel yay ƴar dariya saboda fushin da Md yake mara dalili.

A office da ya koma ya tarar Mairo tayi bacci, bai tasheta ba ya shiga toilet ya watsa ruwa, bayan fitowarsa kuma ya isa ya zauna kan kujerar kusa da kanta, sannan ya ɗauki sauran abincin da ta ci ta rage ya cinye. yay dialling number PA ta kawo masa coffee dan ba ya rabo da shansa. Amadu ya shigo yay masa bayani akan files ɗin da ya ajiye masa, yace da shi zai duba sai zuwa gobe. da mamakin Emanuel sai yaga Amadu ya tsaya bai fita ba, abunda bai taɓa yi ba, sai dai a yanda alama ta nuna yana da abun cewa mai muhimmanci, a ransa har yana kawowa ko jikin Mamar tasu ne ya ƙara tashi, dan satin da ya wuce ya kuma zuwa gida, saboda haka ya tambaye shi.

“Secretary is there any problem?” Amadu ya ɗago ya dube shi, dai-dai lokacin kuma da Emanuel ke gyara mata kwanciyarta yana juyar da kanta, garin juyi hannunta ya sakko ƙasa, ya maida kanta saman cinyarsa dan ya lura bata ji daɗin kwanciyar ba.

Amadu dai jujjuya maganar da zai masa yake acikin ransa, dan bai san ta yanda zai ɗauketa ba, sai da Emanuel ya katse shirun nasa ta hanyar sake tambayarsa sannan yace, “Sir dama i want to talk to you about your guest”. lokaci ɗaya Emanuel ya saki murmushin da suka bayyana haƙoransa dan ya san inda sauran zancen Sectery zai dosa.
saboda haka yace da shi,

“Kanwata ce ita ce autarmu. sun zo escourtion ne daga makaranta sai Dad yace ta zauna idan zan wuce sai mu tafi tare”. kunya ta kama Amadu yaji dama bai masa maganar ba, sam bai kawo batun ƙanwarsa bace kamar yanda yaji PA ta faɗa, to amma har ga Allah indai zaman da yake da uban gidansa na amana ne to lallai idan yaga zaiyi ba dai-dai ba ya tunasar da shi kamar yanda uban gidan nasa ya roƙe shi tun farkon zuwansa aiki, ba ya so ya zama kamar Md ko Accounter dan su waɗannan sheɗanu ne, ko a jiya yana jin faɗan wata da Accounter akan zata zubar da ciki.

“didn’t you trust me ne na kira maka Dad ɗin ka tambaye shi?” Ya faɗa yana ɗaukan wayarsa.  cikin sauri Amadu ya girgiza masa kai,”a’a na yarda da kai mana…kawai dai naji nauyinka ne akan yi maka maganar, kayi haƙuri ka yafe min”. yace da shi babu komai, shi ma kuma ya gode dan saboda yana sonsa ne har yasa ido akan abunda ba shi da kyau.

Da lokacin tashin Md yayi yazo da kansa ya ɗauki Mairo, sai dai Emanuel ya roƙe shi akan kar ya ci amanarsa, shi dai bai ce masa ƙala ba banda harara da yake binsa da ita. sai da ya bawa Mairo waya yace ta riƙe zai ke kira yaji idan sun je gida, ya kuma dubi Md yace,”in dai na kira wayar nan naji bata yi picking ba to wallahi da police zaka ganni.”

Md yaja tsaki ya fice yana faɗin,”me zai hana ka haɗata da wanda ka aminta da shi”.
acan gidan Md ma Favour matarsa ta karɓeta hannu biyu, amma still sai da ta kira Emanuel taji gaskiyar lamari sannan, a duk inda Mairo ta shiga sai sun saba da mutum, ko a yanzu cikin kwana ɗaya tal sunyi wata shaƙuwa da Favour, da yake ita teacher ce duk lokacin da zata tafi school tare suke tafiya. a haka sai da ta kwashe kwana biyar cif a gidan Md kafin Emanuel ya ɗauketa su wuce Abuja.

A wajen shiga jirgi ne suka buga dirama da ita, tun haɗuwarsu karo na farko da ya ji ta ɓata masa rai, iya yarfi ta yarfa shi, dan ba ƙaramin bada shi tayi ba a gaban jama’a. saboda haka ko da aka shiga jirgin sai yay mata nuni da economy class seat, shi kuma ya wuce first class seat.

Kuma har jirginsu ya sauka yana jin haushinta, ita ma kuma tsawar da yayi mata yasa take jin haushinsa, dan haka ko da jirgi ya tsaya ɗaukanta yay cak ya fito da ita gudun karta kuma buga masa hauka irin ɗazu.

Haushinsa ya ƙaru a ranta, ƙatuwa da ita ya wani ɗaukota kamar tace masa bata da ƙafa, saboda haka cikin ƙunƙuni tace da shi a sanda yake direta bakin mota,”kuma saina faɗawa Dad kayi min faɗa.” Ya galla mata harara ya shiga mota, sannan ita ma ta zaga ta buɗe baya zata shiga ganin cewar driver ne yazo ɗaukansu, sai dai tana ziro ƙafa cikin ɗagin muryar faɗa yace ta koma gaba.

<< Sirrin Boye 21

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×