Daga can kujerar baya ɓarin dama na hangi Auwalu sai zare idanuwa yake yi, nayi ƙwafa domin tabbas da agabana yake zan iya shaƙe shi. matsawa nayi ɓarin da yake na tsaya, ina jin wannan saurayin ya fito daga mota idanusa kuma na bina da wani wulaƙattacen kallo, yaja mayafin da ke jikina ya riƙe, ni kuma na fizge domin bata tashi nake ba.
Auwalu ya fito ya zagayo daga in da yake zuwa gabana, sai wani takun isa yake irin ta samarin ƙauye, shi alallai yana tare da alhazawan birni, na tsartar da yawun bakina a. . .