Skip to content
Part 4 of 22 in the Series Sirrin Boye by Halima Zakariyya

Daga can kujerar baya ɓarin dama na hangi Auwalu sai zare idanuwa yake yi, nayi ƙwafa domin tabbas da agabana yake zan iya shaƙe shi. matsawa nayi ɓarin da yake na tsaya, ina jin wannan saurayin ya fito daga mota idanusa kuma na bina da wani wulaƙattacen kallo, yaja mayafin da ke jikina ya riƙe, ni kuma na fizge domin bata tashi nake ba.

Auwalu ya fito ya zagayo daga in da yake zuwa gabana, sai wani takun isa yake irin ta samarin ƙauye, shi alallai yana tare da alhazawan birni, na tsartar da yawun bakina a gefen ƙafarsa inasa hannu na toshe hancina nace, “kai kuwa Auwalu yaushe rabonka da wanka, kaji yanda kake gumamar wari kuwa, ka gyara kaji, wataƙila ka samu ƴan matan ƙauyen da kake bi su daina gudun aurenka”. Sai kuma na bushe da dariya sannan nace, “ko da yake matsalar ba daga wurinka bane, ashe daga wurin tsoho na gida ne da baya iya bada sile a saya ruwa a gidansa, tsohon da baya gajiya da kunyatar da iyalansa”. Maganata ta soki Auwalu saboda haka cikin fusata ya kawo hannunsa fuskata na dakatar da shi da sauri.

“kul ɗinka, dan wallahi ka sake ka taɓani yau ba zaka kwana lafiya ba a garin bichi, dan sai nayi maka sharrin da zaman cikin garin bichi zai gagareka har a bada…Kuma dama zuwa nayi na maka fashin baƙi akan matsiyacin tsoho me farin gemu, wanda ba kowa bane sai ƙazamin Ladanin masallacin gidan ƙofa, baƙi wuluk da shi haƙoransa duk sun yi kanta da goro, yana tafiya a noƙe kamar mutumin kirki nan kuwa baƙin munafiki ne, mutumin da duk inda yaji ana raba zakka shi ne a sahun farko, wanda kullum ka gansa gaban masu kuɗi a duƙe tsabar maula, asararran tsohon da baya iyaci da iyalinsa sai dai matarsa taci da su, mutumin da ake zuwa har gida a titsiye ya biya bashin da yayi ƙarya da sunan ɗansa ya karɓa, uban da baya iya aurar da ƴaƴansa sai sanda yaji gwamnati na batun aurar da zaurawa sannan yaje ya kai sunansu, tsohon da ƴaƴansa basa ganinsa da gashin ido, mutumin da idan jama’ar gari suka bishi sallah a sanda tantantama akan sallarsu. Auwalu wannan shi ne matsiyacin tsoho me farin gemu na cikin garin bichi, idan kuma kana tantama sai na baje maka magana a fefai ta yanda zaka gane kai ɗin ƙaramin mara kunya ne, ka kuma gane ba kowa bane soko irinka da za’a taɓa mutuncin ubansa ya ƙyale”. Auwalu dai tuni yay suman tsaye, na gama da shi dan haka bana buƙatar ci gaba da tsayuwa kusa da inda yake, sai kai na dana ɗaga na maida dubana ga saurayi ɗan birni nayi masa banzan kallo, kana na dubi Adawiyya kafin nan na yatsine fuska cike da takaici nace mata, “ke daman wannan tsamurmurin kika kasa maidawa martani, dube shi fa abu kamar maburgin kaɗa kuka, ke ba kyace ɗan birni ba, dan yafi kama da mutanen ƙauyen da basu ci sun ƙoshi ba, to har me zai tsorataki a tare da shi, farin ko kuma tsayin? To idan farinsa ne farare nawa Allah ya bayar acikin gidanku, idan kuma tsayinne dogaye nawa ne acikin gidanku wanda idan wannan tsolon ma ya tsaya a gabansu shi wada ne, amma dai kin gwaigwayi asara da yawa, ko da ike shi ya fiki asarar da ya kasa amfani da iliminsa, kinga kuwa da shi da jahilin duka ɗaya, kuma banda abinki ai sai ki faɗa masa tsohuwa ma ta gida asalinta ƙauye, wataƙila ma naku ƙauyen yafi nasu arziƙi dan ba lallai anasu zamanin turawa sun shiga ƙauyen ba, ƙila ma bata san da jar fata ba sai da arziƙin aure ya fito da ita daga ƙauye zuwa birni, ƙoɗaɗɗun kaya kuma ai sai kice yaje ya tambayi tsoho ko kuma tsohuwa acikin wacce iriyar sutura suka tashi, idan su basu saka ba na sama dasu ai sun saka, kinga kenan koɗaɗɗun kaya ba daga ke bane daga zuri’a uban kowa ne”. Na kama hannunta ina cewa muje, kafin na kai ga ɗaga ƙafata naji an riƙo mayafina da ƙarfi har yana kusa zamewa daga jikina, na juyo a fusace. “wai kai wanne irin mara ɗa’a ne da zaka dinga kama suturar macen da ba muharramarka ba. nan fa ba can idan aka raineka bane, dan haka kasan a inda kake, ko kuma dan kaji mara kunyar yaronka na cewa muna yawo kwararo-kwararo shi ne kake neman wuce gona da iri, to ai gaka ga shi nan sai ka tambayeshi zamanin da yaji anyi waɗannan ƴan matan fanɗararru, kace ya baka labarin ita kanta shugabar tasu nawa aka zubar kafin ai mata maganin abun a ɗaureta da igogin aure har aka haife shi. Dan haka ni sakarni idan ba haka ba kuma nayi maka ihun kwarto”.

Auwalu ya ka da baki naji yace da shi, “Yallaɓai sakarta dan zata aikata, kuma wallahi ka shiga hannun mazan ƙauyen nan sai dai a haifi waninka”. Naja musu dogon tsaki na kama hannun Adawiyya muka barsu a wajan.

Dai-dai da zamu shiga gida muka jiyo maganar Mubarak a bayanmu yana kwaɗa mana kira. Muka juya ni da Adawiyya muna dubansa, ya ƙaraso gabanmu yana cewa, “lallai Mairo, shi ne kika yiwa manyan mutane rashin kunya ko, bayan kin san Baba ya ce mu dinga girmama na gaba damu a duk inda muka gansu ba lallai sai na cikin gidanmu ba, kuma ma ai an hanaki faɗa ko”. “to ai su suka yada girman nasu ni kuma nabi ta kai”. Na faɗa ina hararsa gabana kuma na faɗuwa, dan babu makawa wannan zancen ƴaje kunnen Baba na kaɗe dan ko neman ba’asi ba zai tsaya ji ba. Adawiyya tasa hannu ta dungure masa kai bayan ta harare shi tace, “munafuki kai aina ka ganmu ma”. Yana jijjiga kai yace, “ni ne munafukin? Za kiga ƙarshen munafurci”. Ya faɗa yana sa kai zai shiga gida muka yi saurin riƙo shi, muka hau lallashinsa muna ba shi haƙuri akan dan Allah kar ya faɗa, da ƙyar muka sha kansa yace ba zai faɗa ba amma sai mun ba shi naira hamsin, na marairaice masa fuska nayi kalar tausayi.

“haba Mubarak duk wanda fa ya rufawa wani asiri shi ma Allah zai rufa masa. Yanzu idan kace mu baka hamsin aina zamu samu mu da babu abin da muke siyarwa”. “ai gobe za’a koma makaranta dan haka idan an bamu kuɗin kashewa sai ku haɗa ku bani”. Tare muka haɗa baki ni da Adawiyya muka ce masa, “to shikenan mun ji”. Yana munafukar dariya ya ce, “Allah in dai baku bani ba ko ba gobe ba sai na faɗa.”

Gaba ɗayanmu bamu farga daga rashin hankalin da muka yi ba sai da muka shiga gida, domin kuwa dai langar Gwaggo mun barota acan wurinsu Auwalu, Adawiyya na yafitoni akan mu koma muje mu ɗauko, sai kawai na dake nace mata muje ai ba zata san bamu kai ba. “to idan kuma ta aika a karɓo langar fa Babaa tace bamu kai mata ba, muce me?”. Ganin yanda Adawiyya duk ta tsure yasa ni komawa zaure ina aikin ƙyalƙyala dariya har da riƙe ciki, taɓata rai tana cewa,”ke dai wani bin akwai ki da abun haushi wallahi. Da wannan shirmen da kike ma da tuni munje mun dawo, Allah ina jiye mana hukuncin Gwaggo dan kin san da Sunusi zata haɗamu”. Na kuma ƙyalƙyalewa da dariya har ina zama akan wani buhun yashi dake ajiye a zaure, tayi tsaki zata bar wajen na riƙo hannunta. “ke dilla can ki tsaya kiji”. Ta kuma ƙwace hannunta tana cewa,”ai ke kayan haushinki yawa gare shi, sai lokacin da ake abun hankali ki dinga yiwa mutane dariya bayan kin san kuma bana so”. “yi haƙuri Amini, kece yanda ki kai wuƙi-wuƙi kamar kazar da aka tsoma a ruwan zafi kika ban dariya. Allah Adawiyya ki rage tsoro ki zama jaruma, yanzu akan ɓatan langa za ki bi ki tada hankalinki, kuma fa langar nan yanda muka kaita wallahi har a shafe rayuwar Babaa Lami Gwaggo ba zata aika a karɓo ba sai dai idan ita Baaba Lamin ce ta aiko mata da ita. Kinga kuma ba’a kai mata ba balle har tayo aikenta”. “to ai ba haka tace mu bar mata ba, cewa tayi ta juye ta bamu”. Na tsayar da dariyata ina cewa,”ke dai Allah baki da wayo, sai muce mun kai mata tayi godiya iyaka godiya har tace ba zata iya bada langar haka nan ba adawo da ita saita saka wani abun aciki da za’a kawowa Basma saboda haka ne ma muka daɗe, kuma shiru-shiru yaron da ta aika bai dawo ba sai muka ce mata mu dai mun tafi kar Baba ya dawo”. Adawiyya ta rungomoni tana cewa, “kai ƙanwalli shi yasa nake sonki saboda akwai kawo mafita”. Yanda muka haɗa kuwa haka akai, dan Gwaggo ta tsaru da tsarin dana yi mata.

Bayan sallar magriba muna zazzaune a tsakar gida yaro ya shigo yace ana sallama da Kabir, Gwaggo tace yaje yace baya nan amma idan ya dawo suwa za’ace masa, tunda yaron ya juya bai dawo ba, sai can kusan daƙiƙu biyar da aiken sai ga Saleh ya shigo da gudu, ya nufa hanyar bayi yana bada saƙon wai abokan Ya Kabiru ne suka zo daga birni su na ƙofar gida sunce a miƙa musu ruwan alwala, yana faɗar hakan ya faɗa bayin dama shi kusan kullum haka yake baya shigowa a nutse, ko dai ya dawo da kashi ko kuma fitsari. Gwaggo ta miƙe ta zuba ruwa a butoci guda uku sannan ta dawo ta shiga ɗaki ta ɗauko sabuwar tabarmarta, anata jiran Saleh ya fito ya kai musu shiru bai fito ba, gashi duk mazan gidan basa nan sai shi ɗaya da ya shigo yanzu. Inna Amarya tace, “Ni dai Saleh na rasa wane irin ciki ke gareka, idan ka shiga bayan gida sai kace mace mai naƙuda… Kinga Mairo sanyo mayafinki ki kai musu an barsu sunata jira ba daɗi, ga lokacin sallah ma har ya wuce…ke kuma Adawiyya ɗauki tabarmar ki shimfiɗa musu daga zaure, sai kuce musu Kabiru bai dawowa ba amma dai yana kan hanya dan lokacin dawowarsa yayi, ko kuma su kirashi a waya saboda wataran yana tsayawa ɗaukan karatun dare a masallacin Liman.”

Gwaggo tace,”to ba’a sanma ko su nawa bane a kai musu buta biyu, ko da ike idan kinje sai ki tambayesu idan da buƙatar ƙari sai a kai musu.”

Na ɗebi butoci nayi waje Adawiyya na biye dani, a ƙofar dakalin gidanmu na tarar da mutum zaune ya bani baya, na nutsu sosai sannan na ƙarasa ta gabansa, na tsuguna ina ajiye butocin tare da gaishe shi. Suhail wanda yake jin kamar ya san muryar yay saurin ɗagowa yana duban fuskarta, babu shakka ita ɗin da yayi tsammanin gani ce dan bai manta da muryarta da har yanzu kalaman tsiwarta ke zaune cikin kunnensa. Laɓɓan bakinta masu cike da tsiwa ya ƙurawa ido kamar yanda ya ƙura mata ido a ɗazu ba tare da saninta ba, lokacin da take tsaye gaban abokinsa tana ramawa ƴar’uwarta abunda yayi mata, shi kuma a sannan yana zaune daga cikin motar duk yana jinsu, ta kuma burgeshi matuƙa, har yaji ta cancaci da ai mata kyauta, domin hakan ya nuna masa tasan mutuncin mahaifinta dama na ƴan’uwanta, ba kuma zata bari wani yaci mutuncinsu ko kuma ya wulaƙantasu ba dan kawai su na talakawa kuma mutanen ƙauye. To amma wace ita da ya ganta a gidansu Kabir? Bata yi kama da kabir ba ko kaɗan balle ya bata matsayin ƙanwarsa, dan kamannin Kabir na cikakken Bahaushe ne, ita kuma kamanninta sunfi kama dana shuwa arab, ta iya yiwuwa kuma uba suka haɗa, ita tayi kama da mahaifiyarta ne, ya ɗauke ido daga ɗan tsukeken bakinta da yake kallo ya mayar ga fuskarta, yana kallon yalwataccen gashin da ya shimfiɗe a saman goshinta kamar na jarirai, duk da ɗankwalin dake ɗaure ruf akanta hakan bai hanasu bayyana ba, ta ko’ina bata yi kama da mutanen ƙauye ba, dan komai nata tsab. Bai san lokacin da murmushi ya suɓuce masa ba tunawa da yanda ta-ke tsiwarta har yaji inama kar ta daina ya sami damar ci gaba da kallonta.

Jin yayi shiru bai amsa gaisuwar da nayi masa ba yasa na ɗago kaina daga duƙen da yake, na sake gaisheshi dan ta iya yiwuwa a ɗazun baiji ni ba saboda muryata da ta ɗan sarke, ya amsa gaisuwar tawa ta biyu acikin taushin muryarsa me daɗin ji. Na fakaici idonsa dake kallon gefe wurin dana aje butoci zai ɗauka, kyawun halittar fuskarsa dana gani ne yasa na tsaida idona akan kwantacciyar sumar gashin kansa da babu hula, irin sumar da kana gani kasan ta buzaye ce. Na miƙe tsaye da sauri gudun karna tafka abun kunya ya kamani ina kallonsa, dan nasan halina na bada kai, a yanda nake da matuƙar son ganin abu me kyau banƙi nayi zaman daɓaro ba a wurin ina kalle shi. Na kama gefen mayafi ina ce masa,”Ya Kabiru ɗin baya nan sai dai ka jira shi yanzu zai dawo babu jimawa, amma Inna tace ko kirashi a waya za kayi, kuma wai a ƙaro maku ruwan alwalar ko ya isa haka?”. Bai amsani ba sai bayan da ya kwance tsadadden agogon da ke hannunsa, wanda ni ban taɓa ganin irinsa a fili ba, sai me shigen kamarsa dana taɓa gani a hannun Obi abokin Ya Amadu, ya miƙo min agogon yace na riƙe masa, na rissina na karɓa da hannu biyu, tukunna yace,”babu damuwa zamu jirashi ya dawo ai, dan tunda muka iso garin nan na keta kiran wayar tasa bata shiga. Kicewa Inna mun gode, ruwan alwalar ya ishemu ai mu biyu ne kawai”. Na amsa shi da to, naci gaba da tsayuwa ina jiran ya kammala alwalar da yake na ba shi agogonsa da ya bani riƙo, ko da ya kammala alwalar ya miƙe tsaye dubansa akaina, na tari nunfashinsa da miƙa masa agogon, yana saka maɓallin hannun rigarsa yace na shiga da shi gida na ajiye masa, idan suka shigo gaida su Inna zai amsa, sannan ya tambaye ni sunana nace masa “Mairo”. Yace, “Maryam dai ko”. Nace “a’a Mairo dai”. Yace, “to ai shikenan Mairo sannunki, ke ƙanwar Kabiru ce?”. Na ɗaga masa kai alamar ehh, Sannan na juya na tafi, ina ji yana kiran abokinsa me suna Jawad da ya zo yayi tasa alwalar lokaci ya ƙure, ko kuma shi yayi tasa sallar ya barshi, dan ya lura idan yana wannan wayar tasa baya la’akari da tafiyar lokaci.

Da shigata gida tunda na faɗawa su Inna za’a shigo a gaishesu ban zame ko’ina ba sai cikin ɗakin Gwaggo, na taka kujera na ɗauko wata kwallar ajiyarta da ke saman sif, na saka agogon aciki sannan na rufe na mayar. A tsakar gida kuwa tuni an shimfiɗa tabarma da babbar sallayar Baba wadda me anguwa ya bashi tsaraba dawowarsa daga saudiya, aka soka turare ɗan tsinke a jikin garu.

Mun gama cin dambun acca da Inna Zulai tayi mana shi a abincin dare, dambun yayi daɗi sosai, ina bakin rariya ina wanke hannu muka jiyo sallamar mutane, ban bar wurin ba sai sanda na gama kuskure baki, lokacin yaran gida duk sun gaishesu kowa ya koma ɗaki.

Naja ƙafafuna na tsayar lokacin da idanuwana suka yi tozali da ɗan iskan saurayin ɗazu da ya ciwa Adawiyya mutunci, a raina nace shi kuma me ya kawo shi gidanmu?, kar dai ƙarata ya kawo, ko kuma tare suke?. ajiyar zuciya na sauke, ban yarfar da ruwan hannuna ba sai da nazo saitinsa, tukunna na wuce naja kujera na zauna, ina jinsu su na ta ɗan hirarrakinsu, su na faɗin ai ƙilama zasu kwana ne anan, domin basa son tafiyar dare, kuma kusan sun sauka ne a hanya tunda inda zasu sauka gobe yafi kusa da nan. ni dai Alla Alla nake Gwaggo ta tsagaida da maganarsu ita da buzu na amayar da abunda ke cikina ko na samu na huta.
Aiko shiru na gimlawa a tsakani na kada baki nace, “Gwaggo wai dama ƴan birni na cin arziƙin Ƴan Ƙauye ne? Ai ce nake a yanda suke jin kansu sunfi ƙarfin nan”. Gwaggo ta wani juyo ta min wawan kallo, kanta kai ga magana Inna tayi caraf tace,”Mairo shiga ɗaki ki ɗauko musu mukullin ɗakinsu Kabiru”. Oho dai duk korar da za’a min maganata dai ta isa in da nake so taje, kuma ko mutum yace zai fasa kwana a gidan ya dai yi alwala da ruwan gidan, ya kuma yi sallah a dakalin gidan, ya kuma shigo har cikin gidan ya zauna.

Ina shiga ɗakin Gwaggo na tarar da Adawiyya zaune gaban fitila tana rubutu a littafi, ni na manta ma da wani Home work sai yanzu, ta bani hannu muka kashe tana faɗin,”daɗina dake iya yaɓa magana”. Nayi mata banza na hau gadon ƙarfenmu na kwanta, ba bacci nake ba sai dai nayi shiru ne kawai, a samana naji mutum tsaye ce nake ma ko Gwaggo ce dan haka nayi saurin rufe idona dan bana son ƙara haɗuwarmu sai gobe, kamin nan nasan ta huce da abunda nayi. Ni’imtaccen tafin hannun da ba zan mance da irin ni’imarsa ba dukkuwa da cewa sau ɗaya ne ya taɓa taɓani, naji an ɗaga kaina daga saman hannuna dana kwanta akai an maida min saman filo, na rumtse idanuna sannan na buɗe saboda yanda ɗumin hannun ke ɗumamamin jiki da wani irin yanayi. Na turɓune fuska na juyo cikin tsiwa ina cewa da Kulu,”wai ke Ba Gwaggo tayi min tsakani da ke ba”. Naga ta kafeni da ido tana kallona, na murguɗa mata baki na harareta, na ɗauki filon na jefar a ƙasa tukunna na koma nayi kwanciyata. Ina jinta ta miƙa hannu ta ɗauki bargon kwanciyarta dama lokacin baccinta ne yayi hakan ya shigo da ita ɗakin. Ina jin Adawiyya na cewa na rage Masifa, nayi mata banza, Sai Kuma ta hau yi min hirar sabon saurayin Sadiya, ina ta dariya saboda yanda ta-ke ta zuzuta muninsa, daga can tsakar gida naji Gwaggo na ƙwala min kira, na diro ƙirjina na dukan uku-uku na fita, tana daga cikin ɗakin girki na ƙarasa a ɗarɗarce, ta galla min harara sannan ta miƙo min kwanukan hannunta guda biyu, “shashashar banza ungo ni riƙe ki kaiwa baƙin nan, kuma ki basu haƙurin maganar da kika yi ɗazu dan sai su zata da su kike”.”Gwaggo to ai dama da su ɗin nake, amma da wannan me ƙasumbar nake, Kina ganinsa ya sunkwi da kai ƙasa kamar mutumin arziƙi to wallahi ba ƙaramin mara mutunci bane…”. Ban kai ga ƙarasa zancena ba tasa hannu ta gwaɓeni, ba kuma ta ƙara ce min komai ta fice ta barni. Sosai naji zafi dan sai da laɓɓana suka ca-ke da haƙori, na kuwa ɗau alwashin abincin nan dai ba zasu ci shi ba.
Zaure na nufa inda ɗakinsu Ya Kabiru yake, takalmi ɗaya na gani a ƙofar ɗakin, na kuwa sa ƙafa nayi fatali da shi gefe dan nasan bana wancan buzun bane tunda bashi nagani ɗazu a ƙafarsa ba lokacin da yake alwala. Kamar ma na juya na fasa shiga ɗakin, sai nayi tunanin Gwaggo zata iya ganewa banje ba, na ko shiga ɗakin babu ko sallama, kasancewar akwai wutar nepa wadda a ɗakinsu Ya Amadu ne kawai aka jona, sai ɗakin ya gauraye da haske, yana daga zaune bakin katifar Ya Amadu yana latsa waya, naji kamar na ƙarasa na juye masa abincin duka a jikinsa, saboda gaba ɗaya haushinsa nake ji. sai kuma na shiga laluban inda Buzu yake ban ganshi ba, kenan baya ɗakin. Na juya zan koma Jawad ɗin ya ɗago yana ce min,”mara kunya ya akayi ne, ba aikoki akai ba bismilla aje anan”. Na juyo na ɓalla masa harara na murguɗa masa bakina kamar zasu cire, dariya kawai yayi yana dubana kamin yace,”ashe wuyanki dai kaurinsa da yawa yake, Rashin kunyarkin ba a iyaka waje ta tsaya ba har da cikin gida, to Allah ya shiryeki”.Nace,”amin kaima kuma ya shiryeka yasa ka gane mace da daraja ta-ke ba sai wacce ta kawoka duniya kaɗai ba…kuma ko banza anji kunya wallahi tunda har akazo ƙauye gidan marasa ilimi cin arziƙinsu”. A yanda yake kallona maganar kamar bata soke shi ba, kuma ƙarya yake wallahi.

Na fito cike da jin haushinsa, na tsaya a bakin ɗakin ina jiran dawowar Buzu, Can sai gashi ya dawo da waya maƙale a kunnensa yanata magana acikin harshen da ban san wane yare bane. Ya tsaya a gabana ina jin kallon da yake min ajikina, ni kuwa idona na ƙasa ina kallon ƙafata. “Maryam ya kika tsaya anan baki shiga ciki kin aje ba, Jawad ai yana ciki, Kawo na tayaki ɗaukar ɗaya.”

Ina aikin ƙifta idanu na turo baki gaba na kuma haɗe gira wuri ɗaya, na ɗago ido na dube shi sannan nace, “ni dai ka min tsakani da wannan tsolon abokin naka. Allah kuwa ba ruwansa da ni”. Murmushin da ya bayyanar da haƙoransa naga yayi, sai dai kasancewar zauren babu wadataccen haske sai banga yanda fuskarsa ta ƙawutu da kyawun murmushin da yayi ba. Bai yi magana ba na shuɗewar wasu sakanni sai aikin sosa siririn sajensa yake. “kaima bayansa kake bi ko, ai duk da ban ganku tare ba ɗazu nasan dai kasan irin ɗibar albarkar da ya yiwa Yayata tunda abokinka ne kuma zai faɗa maka…wama ya sani ko mugun halinku ɗaya kaine siffarka tafi siffantuwa da ta mutanen ƙwarai a fili”. Ya kuma yin murmushi yana cewa,”au Maryam haka ma za ki ce”. Na ɗan murguɗa masa baki,”ni ka daina ce min Maryam, Mairo sunana, da shi ne sunan da Babana ya raɗa min, idan baka iya faɗe ba sai ka haƙura”. Sai naji ya kwaikwayi salon yanda nayi maganar yace,”ni kuma Maryam zance, sai dai idan na faɗa kar a amsa.”

Su Inna duk sun wuce ɗaki lokacin dana dawo, saboda haka na wuce na mayar da abincin ɗakin girki, tukunna na wuce ɗaki. Inna Amarya harta kwanta, dan haka nima na nemi wuri na kwanta, da yaƙinin idan da Safe Gwaggo ta nemi ba’asin abincin dana dawo da shi zance mata dana je banga mutane ba acikin ɗakin, kuma na jira na jira basu dawo ba, kuma wutar ɗakin ta jogane balle na shiga na ajiye, itama ai tasan ina tsoron duhu.

<< Sirrin Boye 3Sirrin Boye 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×